Ticker

6/recent/ticker-posts

Mafarkin Tashin Alqiyama

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Na kasance mai yawan mafarkin tashin alqiyama kuma acikin mafarkin saida naga na tsira, dan Allah kokasan fassarar abun da mafarkin ke nufi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله.

Gaskiya abin da fassarar wannan mafarkin ba, nidai ban iya fassarar mafarki ba kowanne iri domin bankoyi yanda akeba.

Tabbas akwai fassarar mafarki acikin shari'ar musulunci saidai ba haka kawai mutum zai goge fuska ya ce yanada kansa amatsayin mai fassarar mafarki ba, Saidai yanda zamani yagurbace kuma galibi mun ɗauki mafarki kamar wata al'amara shi ne ya sa kwata-kwata babu mutanen kirki afannin fassarar mafarki, yawanci saidai madamfara masu cin dukiyar mutane batareda hakkiba da masu ci da addinine suke riqe da fannin ayanzu awannan zamanin.

Amma tabbas akwai fassarar mafarki a musulunci kus-kurene kai mafarki kabarshi haka kawai baka samu malamin Allah wanda ya iya fassarar mafarki yafassara maka wannan mafarkinba.

Shaik usmanu Bin fodio rahimahullahu acikin littafinsa ihya'ussunnah ya ce: yana daka cikin bidi'ar da mutane suka auka cikinta shi ne insunyi mafarki ba sa zuwa afassara musu mafarkinsu.

Shawara kawai da za mu iya baki Shi ne: Kilazimci yin Addu'ar da Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yakarantar damu dangane da mafarki Maikyau ko mara kyau, domin Inkikace zaki a fassara miki tabbas zaki wahalar dakankine kawai, addu'ar ita ce:

Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: idan mutum yaimafarki yaga abun da ya burgeshi mafarkin yagodewa Allah, sai ya ce: ( Ya Allah ina rokonka Alkhairin wannan mafarki da Alkhairin da ke cikinsa) Idan kuma mummunan mafarkine saiya ce: *(Ya Allah ina neman tsarinka daka sharrin wannan mafarkin dasharrin abun dake cikinsa) Bayan yai tofi abarin hagunsa na hagu. kuma karya bawa kowa labari.

Sannan lallai kada kibiyewa rudin Shaiɗan dangane dagani dakikai amafarkin cewa kin tsira ki godewa Allah akan hakan, kuma kada yasaki ki saurara wajan biyar Allah dakiyaye dokokinsa saidai kiqara kaimi da himmah darike dokokin Allah, Allah yaimiki tsari daka sharrin Shaiɗan dakuma sawa kicika da imani.

Inkika ɗauka keɓance cikin mutane, babu shakka Shaiɗan ne zaici nasara akanki yalalata miki imaninki.

kiyi koyi da Annabawa da salihan bayi da magabata nakwarai, duk da sun san cewa Allah yaimusu alkawarin su 'yan aljannane hakan baisa sunyi rauniba sunshantake ba, A'a kara kaimi da himma suke akan biyar Allah, Allah maɗaukakin sarki ya ce:

كَانُوا يُسَارِعُونَ فِي الْخَيْرَاتِ وَيَدْعُونَنَا رَغَبًا وَرَهَبًا ۖ وَكَانُوا لَنَا خَاشِعِينَ

Sun kasance suna rige-rige wajan ayyukan Alkhairi, kuma suna rokonmu dare darana suna masu saka rai daka rahamar Allah dakuma tsoran Azabarsa, Sun kasance masu tsoran mune. (Suratul Anbiya: 90)

Tare dacewa Su Annabawane, Sahabbbaine Allah yaimusu Alkawarin Aljannah tun suna aduniya, Amma hakan baisa Sun nade kafaba.

Ina kuma gamu nakusa dakarshen duniya, kuma tare da hakan bamu dayakini ko tabbas akan abun da muka gani cikin mafarkin.

Ga wasu kadan daka cikin litattafai na fassarar mafarki kina iya samun malamin Sunnah mai tsoran Allah tsayayye yabincika yafassara miki mafarkin ki.

Littafin fassarar mafarki na muhammad Ibnu sireen. Saidai shi malamin zai fada miki cewa ba a dogara da abun da yake ciki na fassarar mafarkin da ke cikin wannan littafin da sauran litattafan fassarar mafarkin sai abun da dalili nashari'a ya nunar ko wani abu dayake nuna hakan amma kada mutum yadogara da fadin wani akan fassarar mafarki.

Atakaice dai idan mutum yai mafarki mai kyau yana aikata alkhairi koya kubuta daka wani bala'i ko macen dabata hai-huwa tai mafarkin Samun haihuwa kota haihu duk wani mafarki dai na alkhairi mutum zai godewa Allah a kansa yakuma fadawa wanda yaso cikin mutane.

Amma idan na sharri ne kamar yanda muka fada mutum zai nemi tsarin Allah daka Shaiɗan dakuma tsarin munin mafarkin yatofa ahagunsa sau uku, Sannan kada yabaiwa kowa labarinsa wallahu A'alamu.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments