TAMBAYA (32)❓
TAMBAYA 2 na
kwanta barchi sai nai mafarkin nahaifi jariri namiji sainaganni agidan iyayena
mahaifiyata tamikoman jaririya mace ta ce anban nace wayaban ta ce itama ba ta saniba
wata kil kowaye yason kinason diya macen ne saina ansa inata murna nazauna
nafara shayar da ita harta koshi naajeta nadau namijin shikuma yaki shan nonon
sainikecema mahaifirtawa innakoma gidana yazancema dangin mijina bachin sunga
da daya nahaifa,kuma lokacin akwai jinin haihuwa jikina ruwan nono kuma nata
zubarman duk yabata man kaya sainaga bayaran ahannuna sai wani abu guda biyu
ban iya tantance miye amman naganshi shiba dutaiba shiba tsokaba abudai medan
baki jikinshi saina nafarka kuma na kasa mantawa shi ne nace bari nai tambaya.
Don girman Allah malam ka amsaman tambayoyina
AMSA❗
A cikin
littafinsa mai suna Fassarar Mafarki, Imam Muhammad Ibn Seerin (Tabi'i kuma
dalibin Imam Malik) ya ce:
Mafarkin
haihuwa na nufin samun sauqi daga wahala, samun waraka, ko kuma tashi daga gida
ko maqota. Haka kuma haihuwa na nufin nutsuwa, hutu, biyan kudin ba shi da kuma
tuba ga Allah. Idan mace ta yi mafarkin haihuwar namiji na nufin karshen
wahalarta, albishir, biyan ba shi, ko kuma tuba ga Allah
Idan kuma ta
haifi ya mace na nufin daraja, daukaka da sauqi. Idan mabuqaci ya yi mafarkin
haihuwa hakan na nufin sauqin rayuwa. Mafarkin dan kasuwa ya haihu na nufin
asara a kasuwanci
SHARHI:
Na biyu kuma.
A fahimtata akwai hakkin wasu akanki. Idan kinsan ana binki ba shi to ki
gaggauta biya tun kafin ki koma kabari da hakkin ba shi akanki
Allah ya
kiyayemu da kiyayewarsa.
Amsawa:
Usman Danliti
Mato (Usmannoor_As-salafy)
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.