Ticker

6/recent/ticker-posts

Addu'ar Istikhara

TAMBAYA (33)

Dan Allah malam 'addu'ar istihara

AMSA

Addu'ar Sallar Istihara (Neman Zabin Allah Idan Mutum Zai AikaTa Wani Abu).

Jabir Ibn Abdullah, Allah ya yarda da shi da mahaifinsa, ya ce; Manzon Allah (SAW), tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana koya mana yin istihara (neman zabin Allah) a Cikin dukkan al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga Cikin Alkur'ani, yakan ce, "Idan dayanku ya yi niyyar yin wani al'amari to ya yi sallah raka'a biyu ba ta farilla ba, sannan ya ce;

اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْألُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيم، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلا أَقْدِر، وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَم، وَأَنْتَ عَلاّمُ الغُيوبِ، اللّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ- وَيُسَمِّي حَاجَتَهُ - خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، عَاجِلِهِ وَأَجِلِهِ فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ شَرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ.

Allahumma innee astakheeruka bi'ilmik, wa-astaqdiruka biqudratik, wa-as-aluka min fadlikal-'azeem, fa-innaka taqdiru wala aqdir, wata'lamu wala a'lam ,wa-anta 'allamul ghuyoob, allahumma in kunta ta'lamu anna hazal-amr (sai ka fadi buwatarka) khayrun lee fee deenee wama'ashee wa'akibati amree fakqurhu lee, wayassirhu lee, thumma barik lee feeh, wa-in kunta ta'lamu anna hazal-amr (sai ka fadi buqatarka) sharrun lee fee deenee wama'ashee wa'aqibati amree fasrifhu 'annee wasrifnee 'anh, waqdur liyal-khayra haythu kan, thumma ardinee bihi.

Ya Allah! Ina neman zabinka domin iliminka, kuma ina neman Ka ba ni iko domin Ikonka, kuma ina rokonka daga falalarka Mai girma; domin Kai ne mai iko ni kuwa ba ni iko, kuma Kai ne Masani, ni kuwa ban sani ba, kuma Kai ne masanin abubuwan fake. Ya Allah! Idan ka san cewa wannan al'amari sai ya ambaci bukata tasa alheri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata, da kuma karshen al'amarina a wata rayuwar; da magaggaucin ala'marina da majinkircinsa Ka kaddara mini shi, kuma Ka saukake mini shi, sannan Ka albarkance ni a cikin sa. Kuma idan Ka san wannan al'amari sharri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata da karshen al'amarina a wata ruwayar; da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa – Ka kawar da shi daga gare ni, kuma Ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddara mini alherin a duk inda yake, kuma Ka sanya ni in yarda da shi".

Duk wanda ya nemi zabin mahalicci, kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma ya yi azama a Cikin lamarinsa, to ba zai yi nadama ba, domin Allah madaukakin sarki Ya ce;

(وَشَاوِرْهُمْ فِي اْلأَمْرِ فَإِذَا عَزَمْتَ فَتَوَكَّلْ عَلَى اللهِ)

(Washawirhum Fiyl Amri Fa'iza Azamta Fatawakkal Alallahi).

"Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka kuduri aniya, to ka dogara ga Allah".

SHARHI: Da akwai wasu da suke cewa wai saidai ayiwa mutum istihara, to nidai abin da a wanne waje suka samo wannan nassi ba, domin kuwa sahihan hadisai sun tabbatatarda cewar Annabi SAW yana koyawa sahabbai Istihara kamar yanda yake koyardasu ayoyin Qur'ani. Don haka duk wani wanda ya ce zai yi maka Istihara to dan damfara ne number 1. Sannan kuma ba a nafarki ake gani ba, kamar yanda kwanaki wata yar uwa take cemin ta ga wani haske a mafarki bayan ta yi Istihara wanda wai a tunaninta hakan na nufin saurayinta alkhairi ne a rayuwarta. Wannan duk rudin shaidanne. Allah yabamu ikon kiyayewa

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments