𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam
Alaikum. Mutum ne auri mace watanni uku kenan da ɗaura
musu aure amma ba ta yarda da shi ba, wai tsoro yake ba ta. Yanzu dai ya aiko
mata da takardar saki zuwa gida. Shi ne suke tambaya: Yaya maganar iddarta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus
Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Abin da Allaah
Ta’aala ya ce dai shi ne:
یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوۤا۟ إِذَا نَكَحۡتُمُ ٱلۡمُؤۡمِنَـٰتِ ثُمَّ طَلَّقۡتُمُوهُنَّ مِن قَبۡلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ فَمَا لَكُمۡ عَلَیۡهِنَّ مِنۡ عِدَّةࣲ تَعۡتَدُّونَهَاۖ فَمَتِّعُوهُنَّ وَسَرِّحُوهُنَّ سَرَاحࣰا جَمِیلࣰا
Ya ku waɗanda suka yi Imani! Idan
kuka auri muminai mata sannan kuma kuka sake su tun kafin ku shafe su, to babu
wata idda da kuke da ita a kansu. Ku ba su mutu’a na saki, kuma ku sake su saki
mai kyau. (Surah Al-Ahzaab: 49).
Sannan a wurin
tafsirin wannan ayar Sahabi Abdullaah Bn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce:
فَهَذَا الرَّجُلُ يَتَزَوَّجُ الْمَرْأَةَ ، ثُمَّ يُطَلِّقُهُا
مِنْ قَبْلِ أَنْ يَمَسَّهَا ، فَإِذَا طَلَّقَهَا
وَاحِدَةً بَانَتْ مِنْهُ ، وَلَا عِدَّةَ
عَلَيْهَا أَنْ تَتَزَوَّجَ مَنْ شَاءَتْ
Wannan a kan
mutumin da ya auri mace ne, sai kuma ya sake ta tun kafin ya sadu da ita. Idan
ya sake ta saki ɗaya,
to ta yanke daga gare shi kenan, kuma babu idda a kanta. Tana iya auren duk wanda
ta so.
Game da ɓangaren farko na ayar
kenan.
Amma a kan
sashen ƙarshenta
sai ya ce:
إِنْ كَانَ سَمَّى لَهَا صَدَاقًا ، فَلَيْسَ لَهَا
إِلَّا النِّصْفُ ، إِنْ لَمْ
يَكُنْ سَمَّى لَهَا صَدَاقًا مَتَّعَهَا عَلَى قَدْرِ عُسْرِهِ وَيُسْرِهِ ، وَهُوَ السَّرَاحُ
الْجَمِيلُ
Idan ya riga
ya yanka mata sadaki kafin sakin, to ba za ta samu komai ba sai dai rabin
sadakin kawai. Idan kuma bai riga ya yanka mata sadaki ba, sai ya ba ta mutu’ar
saki da gwargwadon talauci ko wadatarsa. Wannan kuma shi ne ma’anar: ‘Saki mai
kyau.’ (At-Tafseerus Saheeh: 4/134).
Wannan ya
nuna:
1. Babu idda a
kan macen da aka sake ta matuƙar dai an tabbatar cewa mijin bai yi
kwanciyar aure (watau, bai sadu) da matar ba.
2. Idan a
lokacin sakin mijin ya riga ya ambata mata sadakin da zai ba ta, to rabin
sadakin kawai shi ne haƙƙinta.
3. Idan kuwa
bai riga ya yanka mata sadaki ba, to babu wani abu na sadaki a kansa sai dai
mutu’a (alherin) saki kawai, da gwargwadon ƙarfinsa.
4. Mijin da ya
sake ta kafin tarewa ba shi da ikon yin kome (komo da ita), sai dai da sake
sabon ɗaurin aure,
idan ta amince.
5. Idan kuma
ba ta amince ba, to tana iya ƙulla aure da duk wanda take sonsa, ko da
kuwa ranar da mijin ya sake ta ne.
6. Idan miji
ya saɓa wa wannan ƙa’idar, to bai bi umurnin
Allaah Ta’aala ba na cewa,
ya sake ta saki kyakkyawa.
7. Idda tana
zama wajiba ce a kan mace ta dalilin rabuwa da mijin ko dai ta hanyar mutuwar
auren ko kuma mutuwar mijin.
8. Babu
bambanci a nan ko sakin a bayan sahihin ƙullin aure ne ko kuma a bayan lalataccen ƙullin
aure ne.
9. Idda a kan
mace da aka saki tana zama Wajiba ce ko da sakin na-farko ne, ko na-biyu ne, ko
kuma na-uku ne.
10. Amma idan
rabuwar auren ta zama saboda mutuwar miji ne, to a nan wajibi ne ta yi idda na
tsawon watanni huɗu
da kwanaki goma ko mijin ya sadu da ita ko bai sadu da ita ba. (Tamaamul
Minnah: 3/219-220)
Allaah ya ƙara
mana ilimi mai amfani.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad
Abdullaah Assalafiy
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.