Ticker

6/recent/ticker-posts

Daurin Harafin ‘r’ a Karshen Suna

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

Ɗaurin Harafin ‘r’ a Ƙarshen Suna

164. In aka ɗauri ‘r’ ga suna ka kiyaye,

 Wata ‘yar ƙa’ida ake son ka kiyaye,

 Ita taka rawa takai ga jinsin sunaye,

 Kuma ta karkata ne a gefen mataye,

  Sunan mace ne ga tsarin Hausawa.

 

165. Muddin dai gaɓar ta zan ita ce ƙarshe,

 To ita za a sa ga kalma koyaushe,

 Babu kininta nan, a sa  ‘r’ ba kushe,

 A yi ɗauri, a sanya ‘r’ a gaɓar karshe,

Kuma an ɗaure ‘r’ da ƙyar taka motsawa.

 

166. In an ɗaure ‘r’ ya zam ba ta motsi,

 Ba wasali gabanta mai sa ta yi motsi,

 Ya zama yunƙuri takai ba ta motsi,

 In ta yunƙura kamar za ta yi motsi-

  Harshe na rawa abin ya ƙi fitowa.

 

167. A misali kamar ka ce rigar Manu,

 Motar nan da an ka ba kwarkwar Sinu,

 Matar nan da taf fito Under Kanu,

 Tamkar da ka ce a ban sarƙar hannu,

  Ko hular Bala ta ƙube ga saƙawa.

 

168. Misalan saman ga ‘r’ ba ta motsa ba,

 Rigar Binta doguwa ba raini ba,

 Ga gonar Kabiru can bai nome ba,

 Ko butar fura cikin jikkar Baba,

  Ko garar |ula abincin Rundawa.

 

169. Duk a wurin da kag ga ‘r’ an ɗaure ta,

To a saka ta kar a ce sai an/kuskura sauya ta,

Shi ne ƙa’idar da dokar rubutu ta hukunta,/ta karanta,

Ƙarshe tah hito ga kalma ka rubuta,

  Suna ya riƙe ta ba ta kuccewa.

 

170. Harshe kan kaɗa wurin yin furucinta,

 Amma ɗaure taf fito ba motsin ta,

 Ko kalmar da ba haraf mai damun ta,

 Matuƙar dai ka furta kalmar tsurarta,

  Za ka ji ‘r’ tana rawa ba dainawa.

 

171. A misalan da za su bayyana sautin ta,

 Kalma ce guda kacal za ka faɗin ta,

 ‘Matar’ yanzu ‘r’ ka ɗaure ƙarshen ta,

 In kuwa ka haɗe da kalmar da ka bin ta.

  Za ka ji ta shige tana son nashewa.

 

172.

 Kalmar duk da tab bi in ka yi furtawa,

 Za ka ji ‘r’ tana ta ɗokin sauyawa,

 Naso za shi faruwa ga rubutawa,

 Sautin ‘r’ a nan yana bukatar canzawa,

Ta bi siffar baƙin da duk za ya biyowa.

 

173. Mai nazari ka lura don kar ka ɗimauce,

 Naso ne kawai take yi a magance,

 Doka ta hana a sanya shi rubuce,

 Ko da ka ji ta bi siffar lafazance,

  Kar ka kula da shi a can ga rubutawa.

 

174. A misalan da za su zo malam duba,

Rigar baba kar ka ce, rigab baba,

Hular baba, kar ka ce hulab baba,

Wato dai kamar a ce motar baba,

  Motab baba za ka ji gun furtawa.

 

175. Ko hulab Bala walau rigam Manu,

 Sa hular Bala, a nan rigar Manu,

 Naso ne kawai ya zo sai ka bi sannu,

 ‘b’ ko ‘m’ su nashe ‘r’ bi ni a sannu, 

  Ko garaɓ ɓula misali ka fitowa.

 

176. Za ka ji sautuka suna sa ‘r’ tauye,

 Ɗaurin dai na ‘r’ ya dace a kiyaye,

 ‘r’ ta bi sautukan da ke can gaba saye,

Wannan duk cikin kure ne ka kiyaye,

  Ba a rubuta yadda sauti ka fitowa.

 

177. Sunan wanga tsare-tsare madanganci,

 Doka ce ta tsara komai bari huci,

 In an bi ta tabbata an fita ƙunci,

 Sautin ‘r’ a nan wurin ya danganci,

  Ɗaurin ‘r’ wurin tana dangantawa.

 

178. A rubutu na Hausa kam an lamunce,

A madanganci na ‘r’ takan zo a rubuce,

 Wani sa’in takan rabe jinsin mace,

 Za a saka ta kun ga doka ta amince,

  A wajen macce nan take jinsantarwa.

 

179. Sautin ‘r’ yana rawa mai burgewa,

 Ga aiki tagwai garai riƙa ƙirgawa,

 Gun dangantaka yana daɗa haskawa,

Sai na biyun ga mallaka taka kutsawa,

  In ta zan gajeruwa gun tsarawa.

180. An karkasa mallaka ka zan mai ganewa,

 Ga mu da doguwa, gajera ka biyowa,

 Su ne mallaka da an ka ruwaitowa,

 Ita ‘yar mallakar baƙaƙe ka biyowa,

  Su yi kalma guda ya zan ba a rabewa.

 

181. A misalan da ke biye sai ka karance,

 Kai nazari ka gane komai a rubuce,

 Gurbin ‘r’ a mallaka san shi a furce,

Ce rigarsu ta fi hularsu kwatance,

  Ko matarsa ta fi farkarsu ƙwarewa.

 

182. Duba misali a hankali don gane ta,

Ba gefen da ‘r’ ta juya ga sifarta,

 Nan aka sa ta, ba a tauye haƙƙinta,

 Shi ne daidai a duba dokar zana ta,

Haka aka son ta can ga dokar ɗaurewa.

 

183. In naso ya wanzu to lura kure ne,

 Ko da ko a baki ka furta hakan ne,

 Faɗi rigassa hadda hulassa kure ne,

 Ko mussassa, hadda motassa ka gane,

  Ko matassa duk kure ne muka cewa.

 

184. Bi bayanin a sannu don ko muhimmi ne,

 Sanya fahimta ga ɗalibai kuwa tilas ne,

 Tafi dai sannu wanga babban rango[1] ne,

 Du kalmar da tak kasance naso ne,

  Ba a kula da diddigin lafazantarwa.

185. Dole mu jinjina wa ‘r’ dai sautin nan,

 In ta wanzu nan gaban suna ke nan,

 Nan taka warware duk dambarwar nan,

 ‘R’ a fagen ga ta yi aiki biyu ke nan,

  Ɗaya dangantaka ɗayan jinsintarwa.

 

186. Mun dai san da ‘r’ tsarin furta ta,

 Harshe kan kaɗa fitar tai sautinta,

 Ko dangantaka da sauran siffarta,

 Kowane sai kula idan za a rubuta,

  ‘R’ na nan zamanta ba ta sauyawa.

 

187. Ɗaurin ‘r’ wuri biyun nan a kula ta,

 Ko dangantaka ta zo ga bayanin ta,

 In kuma ta fito ga jinsi mu rubuta,

 Ba wasalin da zai biyo ta ya tada ta,

Kuma harafin gabanta ba ya nashewa.[1] Rango wannan kalma ce da ake amfani da ita a ƙasar Kabi musamman a duk faɗin jihar. Kuma wannan kalma na nufin wani daji mai itace masu duhu da suka sarƙe tare da yawan gebbu (guru ko gebe ko zaizayar ƙasa) wadda ke zaizayae ƙasa ya bayyanar da sayyun itacen a waje.

Post a Comment

0 Comments