Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Sadaka Da Dukiyar Miji Ba Tare Da Izininsa Ba?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin ko ya halatta Mace ta ɗauki wani abu a dukiyar Mijinta ta yi sadaka ko kyauta da shi ba tare da izininsa ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Dangane da hukuncin cewa Mace taɗauki wani abu daga cikin dukiyar Mijinta ta yi tasarrufinta cikin wani aikin alkhairi kamar Sadaƙa, Kyauta, Taimakon Mabuƙaci, dadai sauransu, Malamai suka ce hukuncin yin tasarrufi da dukiyar Mai-Gida ya kasune cikin halayene kamar guda uku:

1. Hali na Ɗaya shi ne, idan ya kasance dama Miji yayiwa Matarsa izini abayyane cewa ta yi tasarrafi acikin dukiyarsa gwargwadon yadda yadace, to anan babu wani Ishkali (Rikitarwa) acikinsa, danhaka kai tsaye ya halatta ta iyayin sadaka daga cikin dukiyarsa, domin Mαиzoи Aʟʟαн() ya ce: Baya halatta ga Mace ta yi kyauta (da dukiyar mijinta) Sai in da izinin Mijin nata.

2. Hali na Biyu shi ne, ya kasance abayyane dama Miji ya hana Matarsa ta yi tasarrufi acikin dukiyarsa, to shima wannan babu wani Ishkali (Rikitarwa) acikinsa gameda cewa kai tsaye haramun ne Mace taɗauki wani abu acikin dukiyar Mijinta ta yi Sadaƙa ko Kyauta da shi tunda ya hanata, saboda Aηηαвι() ya ce: Baya halatta (ayi tasarrufi da) dukiyar Mutum sai in da daɗin ransa (yardarsa)

3. Hali na uku kuma shi ne, ya kasance abayyane Miji bai bawa Matarsa izinin ta yi tasarrufi cikin dukiyarsa ba, haka kuma azahiri baifito fili ya hanata ba, wato shidai bai hana ba Sannan kuma baice ayiba, to dangane da wannan hali na uku sai Malamai sukayi Saɓani akansa, Wani Sashe daga cikin Malamai sukatafi akan cewa ya halatta Mace ta yi tasarrufi acikin dukiyar Mijinta, za ta iya bada Sadaƙa ko Kyauta daga ciki gwargwadon abinda ba zai zama ɓarna da dukiyarba ko ya tozartar da'ita, danhaka za tayine daidai gwargwadon (Urfi) bisaga yanayin yadda koda Mijinta yaji labari ba zai damuba, Misali kamar idan yakasance abisa ga al'adar yanayin yadda akasaba gani a garinsu idan wani Almajiri ko Mabuƙaci yazo yana neman taimako galibi akan bashi daga 1000 zuwa ƙasa da haka a Misali, to babu laifi tabayar da hakan, amma idan taɗauki 10,000 ko 100,000 tabayar ko shakka babu tawuce gona da iri, amma idan tayine daidai yadda yadace to shikenan babu laifi, sai dai in dama tasan halayyar Mijinta Mutum ne da bayason ataɓa masa dukiya danhaka koda ta bayar idan yaji labari zai nuna damuwarsa, to anan haramun ne Mace tadauki wani abu nasa komai kankantarsa ta yi sadaka da shi.

Daga cikin Dalilan Malaman da suka ce ya halatta Mace ta yi tasarrufi batare da izinin Mijintaba sunkafa Hujja da wannan Hadisi na Mαиzoи Aʟʟαн() da yake cewa: Idan Mace ta ciyar daga ɗakin (dukiyar) Mijinta batare da ta yi ɓarnaba to tana da lada shima kuma yana da lada

Awata ruwayar aka ce: "Ta kasance tana da lada saboda kyakkyawar niyyarta, haka nan mai dukiyar shima yana lada misalin haka"

Sai dai wasu daga cikin Malamai suntafine akan cewa idan yakasance Miji baifito fili ya ce tayiba haka kuma baifito fili ya hanataba, suka ce to bai halatta ba ta ɗauka ta bayar dole sai in tanemi izininsa, idan kuma tadauka to ta aikata haramun kuma sai tabiyashi aranar Kiyama, daga cikin Dalilansu sunkafa Hujja da wannan Hadisi na Aηηαвι() da yake cewa: Kada Mace taciyar da wani abu daga ɗakin (dukiya) Mijinta sai da izinin Mijinta, sai aka ce Ya Ma'aikin Aʟʟαн() koda abincine tabayar? Sai ya ce to ai wannan (abincin) shi ne mafi falala acikin dukiyoyinmu.

Amma magana mafi rinjaye acikin zantukan da Malamai sukayi ita ce, idan yakasance Miji bai hanaba kuma baice ayiba, to ya halatta Mace ta yi Sadaka da daidai gwargwadon abinda zuciya bazatayi ƙyashin abayar da shiba.

шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

Mυѕтαρнα Uѕмαи

              08032531505

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments