TAMBAYA (47)❓
Slm malan mijina
yarasu mene ne dokokin takaba
AMSA❗
Waalaikumus,
Warahmatullahi, Wabarakatuhum
Alhamdulillah
An karbo
hadisi cewar bazawara za ta nesanci abubuwa guda 5 kuma za ta aikata abubuwa
guda 5
1) Ta tsaya a
gidan da take a lokacin da mijinta ya rasu, har zuwa karshen iddarta, wanda ake
kammalawa tsawon watanni 4 da kwanaki 10, sai dai idan tanada juna biyu iddarta
tana karewa ne idan ta haife, kamar yanda Allah SWT ya fada:
( وَاللَّائِي يَئِسْنَ مِنَ الْمَحِيضِ مِن نِّسَائِكُمْ إِنِ ارْتَبْتُمْ فَعِدَّتُهُنَّ ثَلَاثَةُ أَشْهُرٍ وَاللَّائِي لَمْ يَحِضْنَ ۚ وَأُولَاتُ الْأَحْمَالِ
أَجَلُهُنَّ أَن يَضَعْنَ حَمْلَهُنَّ ۚ وَمَن يَتَّقِ
اللَّهَ يَجْعَل لَّهُ مِنْ أَمْرِهِ يُسْرًا )
الطلاق (4) At-Talaaƙ
Kuma waɗanda suka yanke ɗammãni daga haila daga
mãtanku, idan kun yi shakka, to, iddarsu watã uku ce da waɗanda ba su yi haila ba.
Kuma ma'abũta cikinna ajalinsu, (shi ne) cewa su haifi cikinnansu. Kuma wanda
ya bi Allah da taƙawa, (Allah) zai sanya masa wani sauƙi daga al'amarinsa
Kada mace ta
bar gidan face da wata ƙwaƙƙwarar hujja kamar: zuwa
asibiti idan batada lafiya ko kuma siyan kayan abinci a kasuwa idan ta rasa wanda
za ta aika. Idan kuma gidan ya rushe ne to sai ta koma wani gidan ko kuma idan
batada wata (muharrama) wadda za ta tayata zaman kadaici to ya halatta tabar
gidan saboda halin tsaro
2) Kada ta
saka kaya masu ado, kamar jajaye ko yellow da sauran kayan da ka iya jan
hankali ga maza. Sai dai za ta saka kayane marasa kyau ko dai bakake ko koraye
da sauransu. Abin lura anan shi ne kada ta saka kayan da za ta janyo hankalin
wani saboda wannan umarnine na Annabi SAW
3) Ta kiyayi
saka sarƙar gold,
silver, lu'u-lu'u ko mirjani da makamantansu ko dai na sarƙar wuya ne ko awarwaro ko
zobe da sauransu har sai ta kammala iddarta
4) Ta kiyayi
saka turare, ta kiyayi fesawa kanta bakhoor (incense) ko kuma kowanne kalar
turare har sai ta tsarkaka daga bayan al'adarta wanda a sannan ne za ta dan
saka turaren bakhoor
5) Kada ta
saka kwalli ko kuma duk abinda ka iya zama kwalliya ga fuskarta wanda zai ja
hankalin mutane gareta. To amman abinda ya shafi kwalliyar yau da gobe ta
hanyar amfani da ruwa da sabulu wannan ba matsala. Amman kwallin da zai saka
idanu su yi kyau ga mace wannan bai halatta ba
Wadannan sune
abubuwa 5 da mace mai idda za ta kula dasu sosai. Amman gameda kare karen da
wasu mutane suka kirkiro cewar mai idda bazatayi magana da kowa ba a wayar
salula ko kuma kada ta yi wanka sama da sau daya a sati, ko kuma kada ta dinga
tafiya ba takalmi a tsakar gida, ko kuma kada ta fito cikin hasken farin wata
da dai sauran camfe camfe dukkan wadannan babu su a addini
Zata iya
tafiya a tsakar gidanta ba takalmi ko da takalmi, za ta abinda take so a tsakar
gidanta, ta yi girkinta ko tayiwa bakinta, ta fito cikin farin wata, za ta iya
wankanta ko sau nawa ne a sati, kuma ta yi magana da kowa ta hanyar da ta dace,
za ta iya gaisawa da kowacce mace da kuma muharramanta, za ta iya cire khimaar
(dan kwalinta) ga iya muharramanta
Amman kada ta
yi lalle (henna) ko turare ko saka saffron, ko a kayanta ko a coffee saboda
saffron shima kamar turare yake. Kada wanda ya nemi aurenta sai dai a yi mata
alamu (kamar wani ya kai mata kyauta haka) amman a nemi aure kai tsaye bai
halatta ba
Allah shi ne
abin neman taimako
(Fatwar Shaikh
Ibn Baaz, daga Fatawa Islamiyya, vol. 3, p. 315-316)
Domin neman
karin bayani duba al-Imdaad bi Ahkaam al-Ihdaad na Fayhaan al-Mutayri; Ahkaam
al-Ihdaad na Khalid al-Muslih
Wallahu ta'ala
a'alam
Source: Shaykh
Muhammad Saalih al-Munajjid tambayata 10,670
Amsawa:
Usman Danliti
Mato (Usmannoor_As-salafy)
https://chat.whatsapp.com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.