Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sayar Da Maganin Karfin Maza

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, Malam mutum ne yana da chemist yana sayar da magunguna. Ya halatta ya sayar da maganin qarfin maza ga wanda yake so ya biya bukatar iyalinsa? Allah ya qarawa Dr. Jameel imani da lafiya da ilimi, gaskiya muna amfana

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, In har an jarraba an samu yana amfani kuma likitoci sun tabbatar ba ya cutarwa ya halatta a siyar da shi don aure ya gyaru, a kara samun donkon soyayya, saboda saduwa tsakanin ma'aurata turke ne tsayayye, wanda in ya goce aure ba zai tafi saiti ba, yana daga cikin ka'idojin Sharia duk harkokin mutane na yau da kullum waɗanda ba ibada ba ne sun halatta, in har ba'a samu nassin da ya hana ba.

Addinin musuluci ya haramta duk abin da yake cutarwa, kamar yadda nassoshi masu dinbin yawa suka tabbatar, wannan ya sa duk maganin da likitanci ya tabbatar cutarsa ta fi amfaninsa yawa ya wajaba a guje shi, Tunkude cuta ginshike ne a cikin addinin musulunci.

Allah ne mafi sani

Dr Jamilu Zarewa

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀��𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments