Ticker

6/recent/ticker-posts

Haduwar Harafin ‘m’ Da Wakilin Suna

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

328. Harafin m da za ka furta can laɓɓai,

 Shi muka mai da hankali na yallaɓai,

Harafin m idan ya zo farkon gaɓɓai,

Matuƙar dai akwai wakili ya raɓai,

Kuma a gabanta ga gaɓa mai bijirowa.

 

329. In ta zo kusan waƙilin sunaye,

 Ga ta a manne zan kula sai a kiyaye,

 ‘Ma’ ta biyo a sa wakilin sunaye,

 Ka tsaya tsab ka gane komai kai waye,

  Sai a haɗe su tare can ga rubutawa.

 

330. A misalan da za su zo ba inkari,

 Kalmomin suna ga jimla bari zari,

 Dakanta ka daina jawo mini tari,

Saƙona garai ya kawo mini gari,

  Tare da bokitin ruwana na jiƙawa.

 

331. Yau kam za ni taimaka miki dole na,

 Ita ko sai ta taimaka maka tilas na,

 Kar ki sake ki takura mishi yaro na,

Ga zatona Abubakar yai miki ɓanna,

  Na ga yana gudu yana wawwaigawa.

 

332. Tashi da hanzari ki miƙa mata Saude,

 Ungo haɗa ki je ki damƙa mata ludde

 Miƙa mata fittilar ta ko samu ta yade,

Bari sai ta fito ka tura mata Kande,

  Yanzu ta maƙare ta sai ta yi haraswa.

 

333. Lura ka mai da hankali don ka yi koyo,

 Baƙi sun ka zo muna masu oyoyo,

Mun gaji ‘yan wajen ƙasa nai mana wayo,

Sun bar mu da ɗakuna suna yi mana yoyo,

  Mu da ƙasarmu dukiya su ka rabawa.

 

334. An yi zaton da mun gani ai mamu wayo,

Ɗabi’un duk da sun zo su muka koyo,

Sun kwakkwashe dukiya sun mana wayo,

Noma arzikin ƙasa su muka tanyo,

  An ga irin zubinmu tamkar ƙauyawa.

 

335. Nai muku tambaya kuna son ku ƙure ni,

Kuma na lura dai kuna son raina ni,

Me ke sa maza fita don ci rani?

Ga ɗabi’unmu yanzu mi ke muna rauni?

  Ga amsa ƙiri-ƙirir kun ƙi gayawa.

 

336. To ka dai ga muku yadda ka zana ta,

 In ka rubuta mu ku tabbata ka ɓata ta.

Zauran nan da yab biɗa tai masa cuta,

Tai masa yaudara da har ya ƙyale ta,

  Ta cinye shi har ƙashi bai da ta cewa.

 

337. Yara a ko’ina suna son su ga taro,

 Yanzu a zamanin ga sun gagara horo,

 Ga su tsayensu, mu muna garkar Gyauro,

Regon rijiya yana sa masu tsoro,

  Ko ɗiban ruwa sukai ba a regawa.

 

338. Harafin m cikin wakilin sunaye,

Ba a raba su ko’ina sai su yi goye,

To daɗa mai da hankali sai ka kiyaye

Sai ka haɗe cikin rubutu kai waye,

  Tare suke zama suna tattaunawa.

 

339. Ba a raba su ko alama ga rubutu,

Sa su a tare don rubutu ya karantu,

Haka nan ƙa’ida ta bayar ta rubutu,

A haɗe ba space a huta ga karatu,

  In ka raba su kai kure sai gyarawa.

 

340. In ma ta biyo wakili a taƙaice,

 Ba a raba su wanga tsarin kalma ce,

 Doka ta taho da tsarin a rubuce,

Ko jam’u walau tilo in ya kasance,

Duk ka haɗe su kar ka zan mai ruɗewa.

 

341. Shi suna akwai lamirin kowanne,

 Sa tilo ga su jam’u nunin rukuni ne,

 Ni, kai, shi, da ke da ita tilo ne gane,

Mu, ku, su, waɗanga nan duk jam’i ne,

  Ka ji kashinsu ukku farko da tuƙewa.

 

342. Ni, ke, ta, zubin tilo ne ka kiyaye,

 Ka, da ya, da ki, fa duk ka kiyaye,

 Ai shi da ita suna da kaya jajaye,

 Yanzu da ni da ke har da ƙawaye,

  Sa, na, duk gidansu ɗai ba a rabawa.

Post a Comment

0 Comments