Ticker

6/recent/ticker-posts

Haduwar Kalmomin Jam’u da Wakilin Suna

 Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

343. Mun sa jam’u can a baya ka tantance,

 Mun ko ga yadda nasa tsari ya kasance,

Kalmomi na jam’u babbar tawaga ce,

Za a biyo da nasu tsarin a rubuce,

  Ga bayaninsu ko guda ba ya ragawa.

 

344. In suka gwamatso lamirrai ga zubinsu,

To a yi ƙa’ida a gwama su dukansu,

Ba a raba su dole sai an gwama su,

Tare suke zuwa a dokar tsarinsu,

  Sai su shige gida guda ba su fitowa.

 

345. Babu buƙatar daɗin bayanin jam’un nan,

Ka san jam’u tun tuni mun gama wannan,

Mun yi bayanin su baya ai ka riƙe wannan,

Har da misalansu mun ka yo tun babin nan,

  Fasali kansu ya wuce tun da daɗewa.

 

346. In mun tuna jam’u tsari na lamirai,

 Wakilcinsa ga ɗaukacin halitta duka mai rai,

 Sai ka ga ya taho jikinai da lamirai,

To in ya haɗe a ƙarshe da lamirrai,

  Can ƙarshensa gun gaɓa mai ƙarewa.

 

347. Za a haɗe su tare don ba a raba su,

 Gun furuci a tare za ka ji sautinsu,

 Haka a rubuce tare ne aka zana su,

 Ka yi kure idan ka ce za ka raba su,

Dubi waɗanga ‘yan misalai da ka zowa.

 

348. Zancen dukkaninsu koko dukkansu,

 Ka yi kure idan ga zane ka rabe su,

 Haka ma ba a so ka zana dukkan su,

 Doka tai hanin ka ware rubutunsu,

Haka nan kowannensu can ga rubutawa.

 

349. Ga misalinsu nan ga jimla a rubuce,

 Dukkaninsu tun tuni suka lamunce,

 Kowannensu ya faɗa mini keɓance,

In ka ji tarsashinsu duk sun lalace,

  Ma’ana babu ko guda mai tserewa.

 

350. Kowannensu na da haurensa talatin,

 Dukkanninsu yanzu sun zarce sittin,

 Katin gayyatar ga, ga ƙwara metin,

Matan kowacensu ta haura talatin,

  Ba sauran ƙurciya sai tsohewa.

 

351. A misali ka duba ƙari ga waɗannan,

 Ga sharaɗi dukanku ko kun san wannan?

Ban son kowanenku in gan shi wurin nan,

 Tuni dai kowannensu ya kauce dan nan,

Na fi da son ku gurgusa can a ƙurewa.

 

352. Sam ba a sanya dukkanin ku rubuce,

 In ka zana kowannen ku to ka kauce,

 Ga misali ka sanya kalmar kowacce,

Don me kowacenku in za ta yi zance,

  Sai ta gilma rantsuwa don shaidawa?

 

353. A misalan da za su zo kai dubawa,

 Ba a raba su in ka zo ga rubutawa,

 Dukkanninku, sai ku duba da kulawa,

Ɗaiɗaikunku na ga kun fara shigewa,

  Sannu dukanku hankali na kawowa.

 

354. Lamirin jam’i idan ya zo nan a rubuce,

To a haɗe su babu sauran wani zance,

Ga wata ƙaida ku duba a rubuce,

In jam’in sifa ya ɗau nsu ga zance,

  Sai a haɗe su bai guda ba a rabawa.

 

355. Yanzu biyo na ba ku misalinsu,

 Tamkar babbaƙunsu duk an ɗebe su,

 In ka rubuta babbaƙun su to ka ɓata su,

 Ko jam’i na ja in a ƙarshe ya ɗau nsu,

  Jajayensu an rufe ba su fitowa.

 

356. Kyawon farfarunsu leshi da atamfa,

 Korayensu, ɗazu na gan su a Kwaifa,

 Shuɗayensu ga su can a cikin rumfa,

 Guntayensu ga su baki na kumfa,

  Dogayensu munduwa suka ɗaurawa.

 

357. Saurara ka kakkaɓe muna kunnenka,

 In ka tuna sifa ana nunnunka ta,

 Haka kan nsu kan zame ɗan rakiyarta,

Ƙara kula sifa idan an nunka ta,

  In ta haɗe da nsu to ba a rabbawa.

 

358. Siffofi baƙi, fari ana ninninka su,

 Sannan sai a liƙa nsu tare a jera su,

 Za a haɗe su, babu mai ware gaɓarsu,

Lura idan ka ce baƙaƙe-baƙaƙensu,

  Sun ɗara farfarunsu sauƙin ganewa.

 

359. A misalan da za mu kawo na irinsu,

 A mutane muke buƙatar mu gwada su,

 Duba kalarsu yanzu ko za a rabe su,

Amma juriyar farare-fararensu,

Ya fi na babbaƙunsu in za a gwadawa.

 

360. Je ka yi bincike da himma ga shirin ga,

 Za ka tarar da su ya su dukka waɗanga,

 Su duka an haɗe su ba ware wa’yanga,

 Kar ka taƙaita kan misalanmu na nan ga,

  Dangoginsu duk a nan ba a rabawa.

 

361. Lura aboki an ya zam kanka a waye,

 In ka lura nan wakilin sunaye,

 A misalan da mun ka kawo jeranye,

 Su suka bayyanar da jam’i kai waye,

Jam’u yake zuwa da shi dinga kulawa.

 

362. Suna in ya zo da liƙi na ɗafi ne,

 Ko a tilo ya zo walau ko jam’i ne,

 Shi aka ɗofana a san wane nau’i ne,

Ɗofane nsu babu shakka jam’u ne,

  Ɗofane nsu ko tilo shika nunawa.

 

363. Ka dai ga irin gamon wakilin sunaye,

 Kalmomi na jam’u ga su a jeranye,

Dubi abin da hankali don ka kiyaye,

A misalan da mun ka ba da ka kiyaye,

Kuma ka yi binciken misalan badawa.

 

 

364. In ka bincika ka samu fahimtar su,

 Yanzu ka sa natso[1], lura dukkansu,

 Ba a raba ba lura nan ga rubuta su,

In ka bi sannu sai ka hardace dukkansu,

  Sannu da hankali abin ba rikitarwa.

 


 [1] Natso a nan na nufin natsuwa wato dai mutum ya kasance cikin yanayi mai kyau wanda zai kasance da dukkan tunaninsa, da hankalinsa a kwance.

Post a Comment

0 Comments