Ticker

6/recent/ticker-posts

Fajaruddeen (Kashi na 15)

Lokacin da Fatiha ta faɗa masa mahaifinta ya ce ya turo aifa yai murna iya murna ji yake kamar anbashi sarautar mulkin mutan Nigeria koma na nahiyar Afrika baki ɗaya ashe ada shi ba so yai ba shirme ne kawai yanzu ya san mene so me ake nufi da ƙauna yadda kawai cewa akai ya turo anman farin cikinsa yazama maras misaltuwa.

 Lokacin da ya jema mahaifin sa da batun shi ma yaji daɗi yadda fajar yaga farin ciki fuskar mahaifin nasa ya masa daɗi gami da yadda mahaifin nasu ya wuce masa gaba duda kuwa ba shi yaje ba amininsa ya sa saidai yaji daɗi dan ada baya sa baki a abun da ya shafesu.

 Lefen da ya haɗawa Fa'iza da suka dawo masa da shi shi ne aka fito da shi ya haɗo abubuwan da ba'a rasa ba maza ne suka kai duda kasantuwar lefen ba wani mai yawa bane sai dai za a iya cewa a dangin su Fatiha ba'a taɓa kamarsa ba sakamakon auren zumunci suke ba kuma arziƙi ne dasu ba.

 Kan ka ce mene wannan maganar lefen ta baza gari duk dsngin nasu maganar lefen suke inda da yawa maganarsu ita ce anya ba lashe kurwar yaron mutane taiba har yaji zai aureta ya haɗo da uban lefe haka.

 Sudai shiru sukai suka toshe kunnuwansu inda ummanta tafi kowa farin cikin ganin ɗiyar tata tasamu miji kuma wanda take so yake santa.

 Wata shida aka saka wanda shi ma yayyenta ne suka zaɓi hakan dan su samu su kintsa sosai yadda zasu fidda ƙanwar tasu inta fajar ne shikam asa ko wata guda ma yana jin yai nisa Yaita ma Fatiha mita ita dai dariya ma ya dinga bata.

 Cikin lokutan da suka rage soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi ƙara ƙaruwa tsakanin masoyan biyu gurin Zamansu na agric yazama matattar fajar dan yanzu ko zaman office baya yi yana fitowa daga aji zai yo gurin ko ba ta nan haka zai zauna yana jiranta yana kallon hotunan da ya mata awaya.

 Inko suka ɗan samu saɓani taƙi zuwa gurin sedai ta koma gida ta ganshi a ƙofar gidansu sosai suke san junansu kana ganinsu kaga masoya duda da wuya kaji suna hirar soyayya ko dan sun riga sun saba da hirar rayuwa ne oho.

 Tun Fatiha na jin kunyar kar ‘yan ajinsu suzo suganta da shi a gurin tun da sunsan malami ne dandai ya ɗaukesu GSP harta sake dan randa ta karanbanin ce masa dan Allah ya dena zuwa gun tun da dai yana zuwa gida kaca kaca sukai yaita mita wai ya gane shi baikai wanda zataso wasu su ganta da shi bane shi ya sa take faɗin haka taita ba shi haƙuri daƙyar tasamu ya yaƙura.

 Duk wanda ya san Fajar ya san da Fatiha ta jima da zama a ransa ɗalibansa ma sun sanda akwai wata me suna Fatiha arayuwar sa dan kuwa ko misali zai basu lokacin karatu za ka tsinci sunan Fatiha shi ne kan gaba.

Wannan sabuwar ɗabi'ar tasa ita tafi ɗagawa Farida hankali yadda taga ya dulmiya cikin kogin san wata duk damuwarta dai ta ƙaru duda kuwa ayanzu sun saba da shi sosai takan kirashi ma awaya su gaisa har wasa da dariya suke duk sanadin project ɗinta.

 Ada tana jin daɗin kiransa dam har hira suke ta chat ma haka sai dai banda ayanzu domin kuwa maga ɗaya biyu zai fara mata hirar wata Fatiha itakam ta tsani sunan sosai takejin kishin me sunan duda batasan ta ba.

 Ji take ina ma ita ce ta samu fajar tasan ko bakomai zatasha kulawa dan yadda ya damu da mesuna Fatihan nan ko ba ta waje tasan kam tanashan kulawa irinsu malam Fajar ne basu iya soba in kuma suka fara shi basu san wani abu denashi ba.

 Tausayin kanta ya cika ta itakam wannan masifa har ina haka.

 Fatiha kanta har tausayin fajar take yadda yakesan ta musanman in ta tuno ta mutuwa sai tausayinsa ya cikata ko ya zai yi in ta mutu tasan tana san sa sai dai yadda take ganin ƙaunarta ƙara ra atattare da shi ya sa take ƙarasa godewa Allah da yabata me ƙaunarta.

 Farida ce zaune a office in Fajar ita da Ma'u yana duba project ɗin da ta kawo masa sa'a ma taiyi taga office ɗin abuɗe ta shiga ta hau roƙensa kan ya duba dan ta kwan biyu da kawo wa kullin baya nan baya zama suna hira sama sama.

 Fatiha tai Sallama sanye take da leshinta milk da hijabinta ruwan zuma tai kyau sosai yana jin muryarta ya ɗago yana murmushi ta jima batazo Department ɗin yau mamaki tai niyar bashi.

 Yadda yake faman washe baki ya sa faridar Fahintar wannan ce Fatihan da alama ta zuba mata ido ta ganeta ita ce yarinyar da ta gansu kwanaki sai dai yau da ta kalle ta sosai se take mata kallon sani sedai ta rasa ina tasan ta.

 Fajar ya katse mata tunani da Faɗin Farida ga ƙanwata Fatiha ku gaisa farida ta daure suka gaisa yadda ya mai da hankalinsa kan Fatihar yabar duba project ɗin ya sa Farida miƙewa Sir za muje mu dawo ok kawai ya ce sukai waje.

💞 Don't forget to vote, comment and follow 💞

 Ayanzu fajar baya jin kunyar kowa kan Fatihar sa dan ko faculty ɗinsu ta je shi yake riƙo mata takaddun ta zuwa gun motarsa da yawa cikin ɗalibansa sun san yana san yarinyar yadda yake wani walwala in ya ganta.

 Yanzu ma zaune suke a kujerun da suke bakin political science department suna hira wucewa kawai zasuyi Fatiha ta dubi gurin ta ce gurin nan zai daɗin zama ya ce ko mu zauna ne a'a ta ce tunawa datai shifa malam ne beci aganshi da wata zaune ba gurin yai yazauna ta ce pls kazo mu ƙarasa ta nuno masa sociology department kaga fa har munzo kinga sedai in nine kike kyamar aganki tare dani.

 Kusa da shi ta je tazauna suka hau fira yana nuna mata posting ɗin mutane a twitter dan ita ba ta wani abu da ya shafi social media sosai suke jin daɗin yanayin kana ganinsu kaga masoya.

 Duk asabar da lahadin duniya inka lalubi fajar za ka sameshi a unguwar su Fatiha dan ma tana ƙi da tashi ne kullun shi zai ɗaukota yakawota makaranta ya kuma mai da ita ada ko old campus ɗinma ta dena binsa sai da taga yai fushi sannan sukai yar jejeniya kan iya old campus.

 ***

Ta ɓan garen Faruk kuwa abin duniya ya masa yawa tun lokacin da ya samu labarin saka ranar yarinyar da ya riga ya gama tsara rayuwarsa da ita yarinyar da dukkan burinsa akanta yake.

 Lokacin da ya zo gidansu Fajar ya zo yadda yaga ta sake tana ta walwala da wanda aka ce masa shi ne za ta aura ya tabbatar masa da tabbas yayi rashin burin zuciyarsa sedai duk da haka ya kasa zuwa ya kalle ta duda ba ta sani ba kusan kullin sai ya zo inda take sana'a wani zubin ma sai ta tashe yake barin gurin cike da tausayin kansa dan ya san shikam tuni ta mance da shi yadda yaga ita rayuwar ta kawai take.

 Ya san ta mance da babun sa tun da sau ɗaya suka taɓa haɗuwa ta da sunan so daga nan ta dena fitowa dan ta ji me kawoshi shi kuma ya ba ta hutu ko tayi tunani ashe besani ba hakan shi ne babban kuskuren da yai ya san ta jima dasashi a kwandon shara ya san tuni tai zaton daman ba son gaske bane duda ya san da wanda take so ɗin baya mata rabin son da shi yake mata nace uhummm faruk kenan kanka kawai kasani.

 Komai aka sa lokaci asannu zai zo yau take ɗaurin auren Fajar yadda yake ta wani rawar kai da kai kawo har kunya yake baima ummansa itakam gwanda aɗaura auren na akawo ma Deeni matar nan ko ta samu ta huta da zumuɗi dan ita a gurin ta duk zumuɗi ne da ango kanyi in za a kawo masa amarya.

 Yayin da shi kuwa gurin fajar duk cikin farin cikin Fatihar sa ta kusa zama tasan agaske ta kusa dawowa kusa da shi suyi rayuwa ta har abada shi baima san yana wani abin ba sai an masa tsiya yakanyi murmushi kawai dan yanzu ya riga ya gama yadda da so kan mai da mutun zuwa wani daban da shi kansa baisani ba dan shi da kansa yana mamakin anya shiɗinne kuwa true love make life colorful.

 Ƙarfe uku dai dai aka ɗaura auren Fatiha Abdurrashid da Fajarudden Isma'il anan masallacin juma'a na BUK old campus.

 Fatiha na zaune ya kirata yana tsokanar ta kaga uwar gida gurin Deeni ta turo baki kamar yana ganinta wane irin uwar gida yai dariya mai da wuƙar ina nufin amarya kuma uwar gidansa ke ɗaya ce ki yi mulkinki daga ke ba ƙari tai murmushin jin daɗi har kasa na ji kunya wallahi.

 Hira suka ɗan taɓa irin ta masoya kamin suyi sallama ta rungume wayar tana jin daɗi wai yau ita ce tai aure kuma Deen ɗinta ta aura saƙon da ya shigo wayar ya sa ta duba wayar.

Assalamu alaikum

Sunana Faruk bana jin zaki gane ni ina miki fatan alkairi arayuwar auren ki Allah ya sa albar yabada zurriya ta gari na gode.

Tsintar kanta da cewa amin tai ta fice daga ɗakin jin ana kiranta.

 Shiko Faruk yana tura saƙon ya goge number ɗin da yai mata ma'ajiya da matata gami da share hawayensa yai inda ya ajiye motarsa ya jata yabar harabar makarantar.

 Kai tsaye gida ya wuce ya ɗauki kayansa driver ya jashi zuwa Aminu kano airport dan daman ya shirya kan zai halarci ɗaurin auren dan ya tabbatar da cewar da gaske ya rasa Fatiha dan baya san zuciyarsa ta dinga kawo masa tantama.

 Huɗu dedai jirginsu ya tashi inda ya nufi Jordan dan can ya nufa ba kuma ranar dawowa dan ji yake duniyar ta masa zafi musanman ƙasar tasa Nigeria.

 Da yan macin ranar juma'ar ne da aka ɗaura auren Fajar ya zo gidansu taƙi fitowa aikuwa yaƙi tafiya har magariba ganin haka ya sa ummanta tasa dole ta fito aiko ta haɗe rai sedai yadda yaketa zolayarta yasata dariya ta ce wai mutum shi ma dai anman ai lahadi kaman yaune ya langwabar da kai ni wallahi dama abar bikin mayi abunmi haɗe da na suna ta zaro ido kaga nayi gida tai ciki tana dariya ya hau kwala mata kira shi ma yana dariya ganin taƙi dawowa ne yasashi jan motarsa yai gida ransa fes.

Ranar asabar aka sa ita ce kamu anan gidan maƙotansu za'ayi inda ‘yan uwan Fajarudden zasu zo dan kama amarya.

 Amarya tai kyau sosai kamar wata zinariya kai bazaka ganta ba kai zaton ‘yar gidan talaka ce ba zato zakai wata ‘yar hamshaƙin mutun ce duda ba wata shigar alfarma taiba.

 Fatiha Fara ce ba sal ba mai tsayi ce cikin mata tana da jiki ko ba za a kirata siririya ba haka baza'a kirata lukuta ba tana da yalwal sumar kai wanda ta sakko bar wuya yayinda gaban goshinta ma gashinta baƙi siɗin ne a kwance dake ƙara mata kyau kazalika tana da dara daran idanu wanda suke farare tasa gashin idanunta ma zara zara ne girarta kamar zana mata akai ba ta cika dogon hanci ba sai dai ya dace da yanayin ta ita ɗin me sanyi ce hakan yake ƙarawa fajar san ta dan yansan mace me sanyi arayuwar sa komai tai birgeshi yake.

 Kowa yaganta sai ya yaba da yanda tai kyau jan les ne a jikinta mai adon baƙi da zaiba simple make up aka mata tai kyau sosai kowa yaganta ya san tabbas ita ce amarya ita da kanta tasan tai kyau har mamaki take na kyan da tai take .

 Cikin ‘yan uwan Fajar ɗin da suka zone Hajiya Basira Matar aminin mahaifin Fajar ta fito da sauri tana faɗin Ubaida ubaida!!! Wadda ake kira ɗin ta juyo ganin me kiran tai saurin ƙarasowa tana murmushi suka gaisa Hajiya Basira ta ce kardai ki bikin ɗiyar tawa kika zo eh anman ta gurin ango ayya nifa ince suka kuma gaisawa gami da tambayar juna bayan saduwa.

 Kinga ikon Allah aure me haɗa zumunci bayan lokaci mai tsayi min sake haɗuwa wallahi fa ai kimma san mahaifiyar Amaryar inji wadda aka kira da ubaida dan Allah fa inji Hajiya Basira nifa ince danaga yarinyar na rasa ina na san me kama da ita .

 Yarinyar fa wajen Sakina ce sakina dai wacce sakinar Saliman ki fa karfa kice tun abin da ya faru ba'a zuminci ke wace Sakinar kar kice mun yayar Salima eh ita fa innalillahi wa'inna ilahi raji'un to ai yaron Deeni ne ɗan wajen Salim Haj. Ubaida ta zaro ido na wajenta eh subhanallah anso ayi kwaɓa aibabu aure tsakaninsu.

 Ya akai aka ɗaura maza basu fahimta eh to kinsan mahaifin yarom beje ba itama na yarimyar baijeba to da madatsala shi ya sa nace suyi bincike suƙa ƙi inji Haj. Ubaidah kinga ban ga ta zama ba daman gurin Sakinar zani zan amso abu sai insanar mata inui Haj. Ubaida ɗin nima kinga bari mu koma asan abinyi tun kan duniya ta ɗauka an ɗaura auren Yaya da ƙanwarsa...

[10:42 am, 10/10/2023] Faɗima Fayau: Binto

1

Da sunan Allah me rahma mejin qai.

****

Tunkinta take cikin kwanciyar hankali dan har sakin murmushi take lokaci zuwa lokaci kai ka ce ba'abin da ke damunta cikin duniya,motar kanta abar kalo ce.

Kamar wadda aka ce tai unguwar kawai ta murda sitiyarin motar zuwa unguwar dorayi, nima dai yau bara inga ya dorayin take ta fada aranta.

Titin qonannen gidan mai tai wanda yai har yan babura ahankula take jan motar gurin ya sauya mata sosai dan ta taba zuwa tun da jimawa, gurin ya sauya sosai ya cika ga jama'a ko ina.

Matasa ne da sauran mutane keta hada-hada a dan qaramin titin wasun su hira suke zazzaune gaban kantunan da ke gefen titin wasu kuwa harkar sa'ar su kawai suke.

Sosai ta qara rage saurin motar koma ta mance a titi take oho hakan sosai yaja hankalun matasan dake ta hada hadarsu, wadanda bamasu da niyar kallonta se sun kalle ta.

Kashi tamanin na masu kallon nata zaginta suke wai su za'ama qaryar mota kadan ne kawai ke kalla suyi shiru, yayin da wasu ke fatan dama sune da motar.

Dai dai layin da za ta keta taga wata matashiya gaban kasko na suya mutane sun bai bayeta yara ko ina na harkarsu, duda batasan me ake soya wa ba jitai kamar ta je ta siya sosai ta ji sun burgeta ita unguwarsu seka gama yawonka ma baka kowa ba balle yara.

Idanta ne yakai kanwata yar matashi goye da yaro wani tana jansa sosai ta ji ta burgeta dudu yarinyar batafi sa'ar su taslim ba ina ita ce abin da take fada aranta kenan.

Tazo dedai mararrabar da ke yan kifi tadan kalla gani tai ba wadda tai mata kawai ta miqe zuwa unguwar bello, tama mance da yanma tayi tamance da fadan momy tafiya kawai take hankali kwance.

Unguwar ba ta kuma birgeta ba seda tashigo unguwar kuka sai take ganin kamar a kauye komai yai mata dai dai da tsarinta, arayuwarta tana san jama'a kazalika tana san qauye.

Mai kifin da tagani gabanta kadan ya sanya tadan faka motar gaba kadan da shi dan tana san karfashe sosai balle wannan da kamshinsa ya cika mata hanci, gabaki daya idan yan matansan dake gun kifin yayo kan motar danma basu kula da wadda ke ciki ba.

Bashir ne tadan bugi tsalha da ke zaune baiko kalli inda motar take ba ya ce kaga wata shegiyar mota ya dan juya ya kalle ta gami da dan jan qaramin tsaki, Bashir ka cucen wallahi kasa na baima Uzairu mashin dina jibi yanzu yaqi dawowa kai kuma kana nan kallon motoci.

Rufe bakin tsalha da sun kuyar da kansa ga tunanin mashin dinsa yai dedai da futowarta daga mota, tijjani ya saki wani ashar kut....kai kaga wata halitta tsalha ya dago yadan kalle ta gami da sakin dariya kai da kake wannan ashar haka in ance ka kulata za ka iya.

Tijjani ya ce ban ga fuska bane anman mazaje ai basa tsoron mace duk kudinta ah lallai aiseka zage kwanji suka saka dariya me kifi da ke ta faman debewa da juyewa ya ce basshi dai tsalha.

Assalamu Alaikum ta fada cikin muryarta me sanyaya zuciya cikin zumudi su Tijjano suka amsa, kifi nake so dan Allah mai kifi yai saurin baro kaskon yana fadin na nawa ake so hajiya.

Na dubu biyu da dari biyar ta ce to to ya fada gami da qarawa da manya ko qanana ahadamin duka dan inji wanne yafi dadi dan gaba.

Yawwa gashi hajiya anzuba harda gyara tai dariya aiko ba gyara haka za ka ce da gyara yai dariya hajiya kenan ta zaro dubu uku ta miqa masa gami da daukan kifinta ta juya Habu yai saurin miqa hannu zai amsa kawo akai miki ya ce tai dariya a'a basshi na gode.

Hajiya canjinki inji mai kifi ta juyo No basshi kawai nagide ai zan dinga zuwa naga guri kodan adinga samin gyara ta fada cikin yanayin barkwanci mai kifi ya hau godiya,Tsalha da tun dazu bai dago ba yai saurin dagowa danjin anbar har dari biyar kodai kunnensa ne beji dedai ba.

Dagowarsa tai dedai da juyowarta wanda hakan yabasu damar kallon juna nadan sakanni taja qafarta tabar wajen.

Kai tsaye gida ta nufa se yanzu hankalinta ya koma gida tasan tabbas za ta sha fada gurin Mommy yayin da gefe daya kuma zuciyarta ta cika taf da tunanin matashin saurayin da ta gani gurin me kifi wanda batasan komi kansa ba ko sunansa bataji wani ya kiraba.

Tai sa'a mumy ba ta nan taslim qanwarta ke fada mata tun rana momy ta tafi unguwa dadi ya cikata kashedi tai ma qannen nata sannan tai daki.

Saida tai wanka tai sallah ta hau kan dinning za ta fara cin abinci sannan tama tuna da kifinta.

Kadija qanwarta ta kira dje kinga na sayo kifi na mance shi a mota pls jeki ki dauko mun ki dumamamin shi a oven.

Kai yaya dan Allah waike baki da aiki sai wahalar da mutane ina ba akwai kifin agida ba shi ne zaki sayo wani wataqil ma kwantai ne, na ji ni maza jeki ki dumama min shi ki raba biyu kashi daya kibaima taslim tamin miya dayan ki dansa yai zafi ki kawon kidan yanka masa albasa.

Ta turo baki ni wallahi na gaji gashi kuma an bamu aiki a sch kuma da yawa Binto tai dariya indan aiki ne ki kawao in miki, ba ta kuma cewa komi ba ta dau makullun motar tai waje rai duk abace.

Abincin ta hau budewa sakwara ce miyar ajuji dadi ya cika ta best food dinta kenan ba ta jira komi ba tahau ci.

Jin shiru kadija ba ta kawo kifin ba ya sa Binto miqewa tai waje wataqil ma ba ta je ta dauko ba, baya motar da alamu tama barshi ya gama qonewa tana can tana kallon indian da ta saba ta fada cikin ranta da sauri tai kitchen din.

Ga mamakinta su ta gani sunyi rashe rashe a qas suna cin kifin salame na gefensu suna miqa mata kai da qaya se yar tsoka insun ga dama.

Haushi ne ya cika ta ta ce oh kwantan kenan kike ci ko inda yai dedai da lunkuma wata qatuwar tsoka da kadija tai abaki cikin irin murya ta wanda yake cin abinci ta ce kai yaya wannan wane irin kifi ne kwai dadi wallahi.

Taslim ta ce kema ai fade kike dadinsa ba'a magana salame dake gefe itama cikin muryarta ta yan qauye ta ce danma ba kansa kuke ci ba sauri binto tai ta dauke farantin da kifin ke kai tai waje.

Biyota sukai suna roqon ta temaka ta basu hakan yai dedai da shigowar momy mene hakan kike gudu kamar wata yarinya ta fada haba momy na siyo abu dan inci anman yarannan sun zauna suna cinye min shi ne na dauko abuna.

Eyye banda shirme duk kifin dake gidannan sekin sayo wani momy dan baki ci wannan bane na daban ne inji taslim.

Dady(qaramin qanunsu me sunan kakansu) ya ce nima zanci wallahi Binto taja tsaki Allah yan gidan nan kwadayayyu ne, momy ta ce eyye karki qara cemusu kwadayayyu kya siyo abu kice bazasu ci ba inkinsan bakya san bawa kowa ki dinga cinyewa a waje.

Muji irin kifin inji momy din ta dauki guda ta fara ci momy da ke faman mitar akwai kifi agida se gashi ta cinye ta kuma dauka ta cinye ta kuma dauka ganin za ta cinye ya sa Binto dauke abinta tai daki dady yabi bayanta kan ta dada masa.

Zonan dady inji Momy kyaleta in ta ajiyema Abbanku sai ya baka kasan halinta duk girman nan naka bataqi ta dakeka ba yai dariya maza jeka ka daukon abinci na bazan iya zuwa dinning ba to ya ce ya miqe.

Sai da hajiya ta cika cikinta da abinci ta dubi taslim ta ce taslim wai yaushe yayarku ta dawo, Taslim tadan muskuta gami da cewa ai mum baki dade da fita ba momy tadan kalle ta kamin ta ce ok duda ta gano qarya take.

Jin tsaiwar motar Abbansu(me gidan) ya sa duk sukai waje har ita momy din kamar koyaushe binto ce ta amso kayansa tana manne jikin baban nata dan sunfi shaquwa da shi kan kowa a agidan suka rankayo sukai ciki cikin farin ciki kamar koyaushe.

Tun da Abban ya gama cin abinci ake labarin kifi kaini na banu ya fada wannan wani irin kifi ne Kadija ta miqe tai kitchen ta dauko wanda binto ta ajiye masa a oven tana tafe tanaci.

Wata uwar harara Binto ta aika mata tai saurin dauke ido gami da mai da kifin ganin binton ta dauke ido yasata saurin dauke abinta gami da hadawa da wani dan qarami.

Abba kaji irinsa inji kadijan kai nifa abin da harkar qarni kun sani Binto ta dan ba ta fuska irin na shagwaba Allah Abba da dadi ya amsa yafara ci.

Binto wai a ina kika sayo kifinnan tai saurin cewa lah Abba a dorayi ne Momy ta saka salati yanzu Binto bakyajin kunyar qarya dazufa a gadon qaya kika ce hanyarki ta dawowa daman na san baki dawo da wuri ba duk kinbi kin koyawa yara qarya.

Kunya ce duk ta rufe Binto sin sin ta miqe tai dakinta momy da dady suka kalli juna sukai murmushi tabbas yaransu sun shaqu dasu sosai ta yadda ko yaya sukai abin rashin gaskiya basa buqatar su taresu se sun fada musu suna zaune zasu fada in hira tai dadi.

Tun bayan da ta hada kayan lecture dinta na gobe tai nafilfulunta ta fada gado danyin bacci sai daime tafi awa biyu a kwance baccin yaqi zuwa ranta zuciyarta da idanunta cike yake da tunanin matashin saurayinnan da tagani gurin me kifi a dorayi idanunta sun bushe babuma alamar bacci a tattare da su.

Ta dade akwance qannenta su taslim suka zo basu fi minti goma ba ta fara jin saukar numfashinsu alamar sunyi bacci.

Duk yadda taso cireshi aranta ta kasa adazun tayi zaton kamar da ne in taga mutun me kyau ta ji tana sansa saidai ba ta ta6a kasa bacci kan tunanin wani ba sai yau.

Wayarta ta dauka ta kunna data tuni messages suka fara shigowa ta WhatsApp yawanci na Isma'il ne duk na neman soyayyarta tsaki taja gami da fita daga WhatsApp din tai Facebook nan dinma shi ne aranta tai tsaki ta koma Instagram tahau duba hotunan mutane da gajerun videos.

Batafi minti biyar da shiga insta dinba saqon Isma'il ya shigo taja tsaki gami da kashe datar can kuma hawaye ya biyo kuncinta itakanta ta rasa meke damunta tarasa me ya sa indai namiji zaice yana santa sai ta dinga jin haushinsa anman zuciyarta se ta dinga hango mata wasu daban itaman zuciyarta ba ta mata adalci ba ko kadan.......

Pls vote,

Comment and

Share.

Binyo

F.A.Ya'u

****

Batasan sa'adda bacci ya d'auketa ba tana can tana ta saqe-saqen shirme, sai kiran asuba ta ji koda ta idar da sallah bacci ta koma da yake yau ba ta da aji da safe, Sai wajen goma ta farka.

Agaggauce tai breakfast sannan ta shirya tsaf ta fito cikin shigarta ta hausawa atamfa ce green super wax ba wata kwalliya tai ba sedai tayi kyau sosai salma taima mum ta fice.

Tana fitowa ta ci karo da yaya Isma'il yana shirin shigowa tana ganinsa ta had'e fuska yayin da shi kuwa bawan Allah gabaki d'aya ya tattaro fara'arsa guri guda adan qagare irin na wadda aka takurawa ta ce yah "Barka da safiya" dadi ya cika shi ya amsa lafiya qalau qanwarmu.

Yadda yaketa wani washe baki ya qara ba ta haushi ta rasa me ya sa shi baya fishi ko kadan duk abin take masa se ka ce ba jiya ne ba taga saqunansa sunfi aqirga ba taqi amsa masa ko daya anman duda haka ko ya nuna yaji haushi.

Katse mata tunani yai da fadin "qanwar anfito ne" tad'an ta6e baki gami da turoshi ta ce "eh" to ko inzo inkaiki" ya fad'a tai saurin cewa a'a basshi kawai ai kaima kana da abinyi yai dariya ganin yadda tai din "to aini ba ni da wani aiki da ya wuce naki Allah."

Wayyo ni na shi na take fad'e cikin ranta ni wallahi da yah ba d'an uwana bane da se ince maye ne duk cikin ranta take magana bama tasan ta fito fili ba ya sa dariya to ai sani ne bakiyi ba tuni na zama mayen saurin toshe bakinta tai tayi waje kunya duk ta rufeta shi kuma yai ciki yana dariya.

Tana tafiya a mota tana dariya wato maganar zuci kan iya fitowa fili kenan.

Yau lecture uku take da ta kammala biyu ta ukun sai yanma wajen uku hakan ya sa ta garzaya matattararsu ta yan bautar qasa da yawa suna wajen maza da mata yadda ake firar ne yad'an d'ebe mata kewar matashin da ta gani jiya ad'orayi wanda ta kasa cirema ranta tunaninsa mintina kadan kamanninsa kan fado mata rai.

Ba ita ta fito daga F.C.E ba sai wajen biyar saura hakan ya sa take ta sauri dan ta je gida domin tana san ta had'a questions d'in exam da aka ce ta kawo na students din da take dauka ta yunwa da take mugun ji.

Batai aune ba ta hange su daf da ita suna qoqarin tsallaka titi duk yadda taso kauce musu ina dan gudu take sosai da gudu sauran suka tsallake yayin da dayar ta tsaya diri diri yayin da akai rashin sa'a sai da ta bugeta.

Hankali tashe ta fito daga mota ganin yadda jini ya malale gurin yasata fashewa da kuka kasantuwar yanma ce ya sa tuni gurin ya cika da jama'a cikin police d'in da ke zaune nan zone one d'aya ciki ta taso ya d'auki yarinyar yasata cikin motar tata.

Yaran da suke tafe tare biyu ciki suma ya ce su shiga dan suje suga inda za a kwantar da ita yayin da sauran ya ce su je gida su fad'a.

Kasa tuqa motar tayi kuka kawai take dan ita ko kad'an batasan taga jini irin mutanen nance da suke da blood phobia police dinne ya amshi key din yau driving seda ya hau titi ya ce wani asibiti za mu ta ce Nasarawa.

Suna zuwa aka amshe ta sabida sunzo da police sa'annan da dama cikin ma'aikatan sun saba da binto sosai, temakon gaggawa aka baima yarinyar seda binto ta tabbatar ta fita daga danger hankalunta yad'an kwanta, se asannan ta kira mum ta fad'a mata.

Bada jimawa ba mum ta iso ita da yah isma'il da abinci se asannan Binto tama tuna wai d'azun yunwa takeji sosai taci sannan tai sallah ta zauna tana kallon yarinyar.

Yarinya ce qarama batafi shekara goma ba anman sabida tsabar rashin kula ace an turota tallah ta dubi sauran yan mayan da suka tawo tare daga ina kuke zuwa nan?

Bilki ta ce daga garu Binto tadan zaro ido inane garu kuma sukai dariya qauye ne can ta ce yakai fanshekara sukai dariya ai gaban nan ne sosai towo to me kuke siyarwa nidai Gyad'a ce inji Bilki.

Au ba abu daya kuke saidawa ba eh kowa da abin da yake saidawa ta6 kunqi cin abincin fa suka kalli juna alamar tsoro.

Daqar tasha kansu suka ci, sai bayan isha ta kira Toli qawar service dinta ta roqeta kan gobe ba za ta iya shigowa da wurwuri ba za ta turo mata questions din ta WhatsApp ta temaka ta mata submitting.

Washe gari da safe bayan kadija ta kawo musu abinci dan Binto qin tafiya gida tai anan ta kwan shi ma isma'il qeme-me ya ce ina yana nan bayan sun karya ta ce kadija ta zauna da kubra ita kuma za ta sauke Bilki ahanya seta je gida ta fadi inda suke dan tasan yanxu hankali duk ya tashi.

Haka kuwa akai a malan qato ta sauke Bilkin ita kuma tai gida dan shiryawa ta tafi sch dan tasan yanzu an kusa shiga exam din tata.

Bata wani jima a gida ba tai makaranta dan tana san ta je taga komi yana tafiya dedai.

Ko da Bilki ta isa gida tun abakin titi ta hangi jama'u tsububu ana jiran ganin ta ina zasu bullo yayin da iyaye mata hankalinsu ya tashi sosai dan zatonsu ko an sace su duka ukun mahaifiyar bilki na hangota ta share hawaye gami da yo wajenta haka ma mahaifiyar sahura tambaya take ina sahun take.

Nan ta zayyene musu komi harda qarin bayani kan lefin tsahare ne sunyi sunyi su jata ta maqale kunsan ita wani irin hali gareta.

Iya aikin san asibitin nasarawa ko Tsalha ya tambaya eh ba inda Salamatu ta kwanta ba eh nanfa to ku tawo keda umma Bilki inyaso se in d'auki Bilki a mahin d'ina muje.

Anman ai ka bari ta ci abinci ko inji ummanta Bilki tai saurin cewa wa ni Yau dai kam na qoshi da abincin daza abinci mukaci me rai da lafiya ni binsa zan yi ko nasamu na dare tana fad'e tana d'ane mashin d'in baice komi ba yaja zasu tafi.

Kasan asibitin da girma ina za mu ganku iya tai saurin tambaya ya ce kinji ta ce emergency to inda aka fara kai Salamatu kafin asauya mata guri oh oh na ji seka bamu kud'in mota yazaro dubu uku ya miqa mata gami da jan mashin d'in dan yanzu se ta ce bai isa ba shi kuma dubu biyu suka rage masa kar yaje ko se yasai magani.

Binto ba ta jima a sch ba ta tawo ana gama papers din yan NCE one ta kamo hanya kai tsaye asibitin ta wuce.

Ko da ta dawo cewa kadija tai suje gida ita da sahura tayi wanka kafin Bilki din ta dawo.

Ganin mara lpy tata na bacci ya sa itama ta d'an kishin gid'a bakin gadon tuni bacci ya d'auketa.

Tun da Sahura ta shiga motar take zuba qauyanci ta kalli can ta ta6a can dan ba irin motar da suka saba shiga bace.

Bata qara sakin baki ba saida suka shiga gidan tamfatsetsen gida ne na qin qarawa nan dai kasa shiru tai seda tai magana ca6d'i ta ce kadija ta ce mene gani nan mu ahe gidajen da muke zuwa talla mugansu na gayu ahe ba komi bane.

Kadija tai dariya kawai sahura ta kuma qarawa mu kan ahe a dajin Allah muke kadija ta sheqe da dariya kai sahura baki da dama kam.

A hankula Bilki ke ta6a Binto da ke bacci ta bud'e idanunta alamun me bacci da sauri ta ware su sosai gani fuskar da tun da ta ganta ta kasa sukuni arayuwarta sai take zaton mafarki take hakan ya sa ta mai da idanunta ta rufe da zummar ci gaba da baccin ta.

Bilki takai hannu za ta kuma tashinta Tsalha ya ce kyaleta bacci ne a idanta tabbas muryar namiji ta ji hakan ya sa tai saurin tashi gami da gyara zama tad'an saki fuska gami da fadin sannu ko ga guri ta nuna masa daya kujerar da ke gefen gadon tsahare.

Shuru suka zauna na tsawon lokaci ba wanda ya ce da kowa komi yayin da Binto take da abubuwan fad'e da yawa kwarjininsa ya hanata fade.

Ahankula tsahare ke bud'e idanunta da saure ta bud'esu ganin ta d'orasu kan tsalha dake zaume gefenta cikin qaraji ta fada Baba da sauri shi ma ya qarasa Tsahare kin farka sannu yarinyar ta fara kuka Baba qafata.

Hankalin binto tuni ya tashi wato ma yanada aure harda yarinya Ni kam nashi na.....

[10:42 am, 10/10/2023] Faɗima Fayau: Binto

2

****

Ta farka abin da ya ce da ita kenan tai qoqarin danne damuwarta kamin ta ce bari in kira likita ta miqe gami da yin waje jiki ba kwari.

Sun dawo ita da doctor ya dubata ya ce ba wata matsala asannu a hankali za ta warke ok doctor za ta iya cin abinci binto ta tambaya eh why not ya ba ta amsa binto tai waje ina zuwa ta ce musu.

Yau ba kowa gurin tsahare umma bilki dake gunta ta fita alwala sai binto tana ba ta abinci nan cikin dabara take tambayarta alaqarta da mutumin nan me zuwa kullun ta ce ai Baba ne binto ta kuma mai-maitawa aranta kamin ta kuma tambaya to ina ummanki naga ba ta ta6a zuwa ba ita.

Tsahare tadan sunkuyar da kanta ta ce ai bazata zo ba Binto tai saurin cewa sabida me bazata zoba ai nice yar fari inji tsahare awwo.

Hawaye tagani idon tsahare mene na kuka kuma umma ta na tuna ni banma san ta ba kamar ya bakisanta ba inji binto aita mutu tun ina qaram ayya Allah ya jiqanta.

Dan zaman tsahare a asibiti sun saba sosai da binto wadda take kira aunty haka shi ma baban nata wato tsalha sun saba sosai dan sukan zauna suyi hira sosai yake jinta aransa musanman ma yadda yaga tana kula masa tilon yarsa.

Abu kamar wasa saiga shaquwa mai tsanani ta ta shiga tsakanin Binto da tsalha sun saba sosai wanda har gidansu yake zuwa su sha hirarsu duda an jima da sallamar tsahare dan ta warke sarai.

Wasa wasa sai ga soyayya mai qarfi ta shiga tsakaninsu irin wadda turawa ke kira da pure lada ada tsalha ya dauka bayan mutuwar salame matarsa bazai ta6a san wata mace ba.

Baima yi tsammanin zai iya kula wata macen ba sai gashi yanzu yana jin Binto aransa sosai fiye ma da ita Salamen.

Ita kanta Binto jinsa take sosai aranta gani take inbata aureshi ba bazata ta6a jin dadin aure ba bama tajin za ta iya auren wani ba tsalha ba, duda dai jama'a suna kallonsa dan qauye bagidaje ita kuwa tasan tsalhanta na dabanne ya iya soyayya sosai ya san takan mace ya kuma san ta yadda zai yi taso shi indai har za ta saurareshi to zatasoshi duk matsayinta.

Dalhat sunan da Binto ta sauya mai kenan zaune yake yana jiran fitowarta Taslim ce ta fito suka gaisa dauke da turen lemo da ruwa ta ce kadan yi haquri gatanan ok bakomi ya ce tai ciki.

Bata jima da shiga ba Binto ta fito sanye take da shigarta ta gado wato riga da zani na atamfa super wax me yarfin ja batai wata kwalliya me yawa ba tai kyau sosai musan man a idon tsalhanta tun da ta fito yake kallonta yayin da ita kuma ta ke sakin murmushi.

Binto ba wata me kyau bace Baqa ce sosai mai matsakaicin tsayi dan ba ta cikin dogaye haka babu me kiranta qajera ita din mace ce me yawan sumar gashi wanda bai cika laushi ba wanda mutane kan kira da gashin Hausawa saidai ita nata yanada tsayi sosai wanda kuma ya zo har gaban goshi.

Bata da qiba saidai baza'a kirata da ramammayiya ba ita din mace ce me yawan tsafta kwalliya da ado hakan ya sa mutane bama sa ganin muninta ko kadan kunsan ance mace yar kwalliya ce.

Sai da ta zauna suka gaisa gami da tambayarsa diyarsu wato salame dan ta ce yarsa yarta ce.

Suna zaune suna hira yaya isma'il yaxo zai shiga ciki duda yagansu yai fuska danshi inda abun da ya tsana to be wuce ganin binto da wani ba.

Da sauri ta ce Yah ya juyo yama mance da kishin da yake danshi din yana san yaji ta masa magana shi kadai ya san dadin da yajeji aransa.

Daf dasu ya zo na'am qanwar ta gaidashi cikin fara'a shi ma sosai ta masa kyau se ma ince fiye da yadda taima Tsalha kyau.

Dalhat ga yaya na ku gaisa ta ce da tsalha cikin girmamawa ya gaida Isma'il din duda kuwa zasu iyayin sa'anni.

Tace yah ga Dalhat shi ne mijin da zan aura yadan kalle ta araze ta kuma mai maitawa to to masha Allah ya fada Allah ya sa albarka ya sa za mu gani suka amsa da amin.

Can isma'il ya ce to a ina yake kafin tsalha ya ce wani abu ta ce agaru yanama da yarinya daya mahaifiyarta ta tasu oh Allah sarki Allah yajiqanta suka ce amin bari naje ciki ko inji isma'il din.

Yana shiga ya bille ta qofar baya yai garden din gidan jiri na daukansa duk dauriyarsa kasa daurewa yayi ya fashe da kuka sosai yake san Binto har cikin ransa yakuma san kowa zai aura bazai ta6a dena san ta ba.

Seda yai kuka me isarsa har ya godema Allah ya miqe yaje ya wanke fuskarsa gami da samin guri ya zauna dan ya san yanxu in yafita da matsala dan har lokacin be dena jin jiri na dibarsa yayin da can ransa yake jin wani irin baqin ciki na taso masa wayarsa ya dauka yahau karatun alqur'ani.

Binto ce zaune tana sana'ata wato karatun novels khadija ta dubeta yaya wai yaushe zaki kuma siyo mana irin kifinnan me dadi Binto ta dan kalle ta aiko yau ma ta ajiye littafin ku tashi muje suka sa ihu duka yee that's our babbar yaya .

Kai ku tsaya to dama kudunwa kuke nufi suka marai raice haba babbar yaya aikinsan da kudinki muke nufi ta koma ta zauna ta6 ka ce zaku mutu baku ci kifi ba.

Mum dake zaune tana jinsu ta ce haba kekuwa yayan duwa inbaki siyawa yan qannenki ba wazaki siyawa ta turo baki kai momey sunfa fini kudi aike babbace babba juji inkinayi se su koya ta6 nidai ba ni da kudi.

Taslim ta ce to zanbada 1k seki cika to yawwa se yanxu na ji batu ku tashi mu tafi ta zari mayafinta mum se mundawo.

Suna saukowa talon qasa inda TV ke akunne binto na kallon ta taja ta zauna wallahi bazani ba drama din data fi so ake Saloni wai yaushe ma suka fara maimaita shirin nan duk qannen sukai mata banza gami da komawa sama suna qunquni gami da Allah ya isa ga wanda yabar TV din akunne.

Tsalhane zaune yana jiran fitowar Binto hankalinsa duk atashe dan jiya ta kirashi take fada masa Abbansu na san ganinsa hakuma komi ya ke daga masa hankali ba sai sanin matsayinsu dana binto ba daya bane ba kuma ko wani mai kudi irin na Binto bane zai bada diyarsa ga talaka irinsa.

Satin da ya wuce da ya zo gunta kan jirkitaccen tsohon mashin dinsa duk yai futu futu da shi kayansa duk sunyi qura gashin kansa jar qasar garinsu ta rineshi zuwa ja mahaifinta ya fito zai fita yana sauri ya taddasu tana zuba masa ruwa yana wanke qafa.

Da alama sauri yake yakan ya sa sama sama suka gaisa kamin ya ce Binto waye wannan din tadan sauke ido qasa Abba shi ne wanda nake baka labari yai saurin qara kallonsa sosai kamin ya ce ba laifi ya shige mota, baifi minti biyar ba ya dawo yai ciki tana Abba ya kadawo da wuri haka yai mata banza haka da zai kuma fita bai amsa ada lafiyar suba.

Ji yake kamar cewa mahaifin binton zai yi ya fita harkar diyarsa gashi shi ayanzu yana jin rabashi da binto kamar rabashi da ransa ne san ta a ruhinsa yake.

Tsoronsa kar iyayanta su hanashi ita duda bazai ga lefinsu ba matsayinsu ba daya ba ita yar birni shi dan qauye ita yar masu kudi illimi gamida mulki shi ba dan kowan kowa ba wanda aqauyensu ma ba kowa ya san dasu ba.

Ita yar boko wadda har takaiga kammala degree dinta yayin da shi secondary dinma daqyar ya kammala baida wata sana'a sama da noma se dan acabar da yake tabawa shi ma iya qauyensu ya san baushe ma kance qwarya tabi qwarya sedai shi so da qaunar Binto ta hanashi kallon tarin banbancin dake tsakaninsu balle yai tunanin kwarya tabi kwarya din.

Binto

F.A.Ya'u

****

Asalin Binto

Alhaji mahmud Hashin shi ne sunan mahaifin Binto haifaffen garin kano ne awannan unguwar mai dunbin tarihi da ta hadar da manyan mutane kama daga professors, Doctors da manyan yan kasuwa.

Su takwas mahaifinsu ya haifa shi ne na shida gidansu ma na sahun jerin masu karatun boko kaf gidan babu wanda bai boko ba.

yayyensa mata biyu se maza biyu sauran qannensa duk maza ne se autarsu mace.

Lokacin da yai kammala degree dinsa ne ya hadu da karima wadda sika qulla soyayya bada jimawa ba aka daura musu aure.

Auransu aurene na jin dadi gami da kwanciyar hankali se irin dai matsala da dole in an hadu mutun biyu za a samesu anman da yake duk su biyun sun san me suke babu wanda ya ta6ajin kansu.

Aurensu da shekara daya karima ta haifi yaronta namiji abinka da masu bin al'ada duda bokonsu aka saka a cirema yaro beli sedai yaita zubar jini bai kwanba ya mutu.

Haka haihuwa ta biyu shi ma da aka ma yaron kaciya basu zo gida ba yaro ya koma alokacin suka gano ashe haemophilic suke haifa.

Lokacin suka tada hankalinsu sosai hakan ya sa yayan Alhaji Mahmoud ya ba shi dansa ganin yadda suka damu mafarin dawowar Isma'il gidan kenan.

Ahaihuwa ta uku ne suka haifi mace wadda taci sunanta Binta wadda suka dauki san duniya suka dora mata haka shi ma isma'il murna sosai dan yayi qanwa lokacin zai shiga Jss 1.

Komi ya samu na Binta ne duk kudin makarantarsa ma ya dena kashewa shidai kawai yasaima Binta kayan wasa.

seda tai shekara shida suka haifa mata qani wanda take sansa sosai.

Lokacin Isma'il zai shiga level 1 yana da shekara goma sha shida cif wanda alokacin ita binta za ta shiga primary 1, qanin ta Bashir wato jaririn da aka haifa sosai suke sansa ita da isma'il se arasa wanda yafi sansa.

Danma in yan kishinta suka motsa setace ina bazai dauki isma'il ba se ita haka zaitai mata doki tanama jaririn qwalo.

Shekarar Bashir uku Binto na shekara tara hartayi jarrabawar tafiya qaramar secondary jira kawai ake ta fito ta fara zuwa.

Tun Binto nada shekara bakwai lokacin Isma'il na level 2 ya fara san ta sedai shi kansa baida tabbacin wani irin so yake mata ba akullin zatonsa sone irinna dan uwa da dan uwa.

Bashir shi ne bai iya fadin binta ba cikin gwarancinsa yake kiranta da Binto tun bataso har sunan ya bita.

Bashir be cika shekara Hudu ba aka haifi taslim batai shekara biyu ba aka haifi kadija.

Binto na Ss 2 lokacin isma'il na shekarar qarshe akaratun likitancinsa alokacin tuni ya gama gane haqiqanin wani irin so yakema yar qanwar tasa sosai yake san ta duniya ba shi da wani tunani se nata.

Yayin da ita kuwa aduniya wani malaminsu ke burgeta sosai sedai shi din kokadan babu baqar mace a tsarinsa danko amsa in baqace ke bama zai nuna kiba balle ki amsa.

Lokacin da ya dena zuwa ne ta gane basansa take ba burgeta kawai yake.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya isma'il na mutuwar san Binto yayin da ita kuma zuciyarta akullun ke hango mata wasu daba.

Binto ba ta da wata qawa ko aminiya sama da isma'il yayanta komi da shi suke haqawa su binne ba me ji duda zurfin cikinta baisa koda dawasa ta taba fadawa masa gawanda takeso ba hakan yai masa dadi dan ya san kenan ba ta kula kowa.

Lokacin da tai candy yabayyana mata burinsa nan tai fur ina ita batasan zanceba babu ta yadda za'ai ta auri yayanta cewarta kallon sibling dinta take masa babu batun aure tsakaninsu.

Tun bai damuwa yana zaton yarinta ce har kawo yau da take nuna masa wani matsayin mijin aurenta da zuciyarta tai mata zabi ji yake kamar zuciyarsa za ta fashe.

Cigaban labari

Da fara'arta ta qaraso inda tsalha yake cikin barkwanci take fadin kaidai kaqi zama dan gida kullin kazo seka tsaya afarfajiya yai dariya ai wataran dai zan shiga in huta da gorin nan tai yar dariya gami da dan rissinawa ta gaidashi ya amsa cikin jin dadi.

Yana daya daga abin da ke qara masa sant shi ne girmama mutanen isso tai masa zuwa dakin mahaifin nata.

Cikin mutunci ya amshe shi suka gaisa yai dan masa tambayoyi abinka da masu illimi awayance ya kammala nazarinsa kan tsalha tuni ya gano mutumin kirkine matsalar sa kawai talauci toh malan tsalha ka iya tafiya zakaji komi gurin ita binto din yamiqe yana godiya ya fito.

Yadda mahaifinta ya amsheshi ya gano inda ta gado karamci ko kadan bai wani nuna masa kyama ba ko irin danme zai ce yana san yarsa duda baice masa yabashi ko zai ba shi ba sai yake jin fargabarsa da yawa ta ragu.

Duk wani bincike da yakama sunyi babu wata matsala dan tuni ma suka ce sun ba shi matsalar daya ce ita ce inda binto za ta zauna qauyene gidan yawa ta ce ita ta ji ta gani za ta iya tuni aka sa bikin wata biyu.

Tuni gidansu tsalha ya dauka ai tsalha zai auri yar birni yaqi auren yar qauye duk tarin matan dake sansa na garin.

Ita kuwa diyarsa murna take sosai dan za ta samu umma musanman ma dataji wace Abban nata zai aure.

Yan gulma basu qara tsorata da lamarinsa ba seda sukaga uban kayan lefen da ya hada wanda ko a auren farinsa be rabinsa ba dan wani dan birnin ma ba lallai ya iya suba.

Umma bilki ta kirashi ta ce yakamata arage ya ce ina shi inda yanada abin da yafi hk wallahi shi zaima binto dan ta fi qarfin haka agunsa.

Lokacin da dangin tsalha suka kai lefe se suka raina abin da suka kai tun daga qofar gidansu binto yadda suka ga girman gidan tukwicin dubu dari ala basu banda soye soye.

Tuni qauyensu ya dauka wata sabuwar gulma wai ana san cutar tsalhane kodai yarinyar tayi cikin shegene ko kuma yar tsuntuwa ce inba haka wani me kudinne zaikai diyarsa qauye shidai tsalha ya toshe kunnensa kamar besan anaiba.

Danshi ya san samun kamila kamar bintonsa sai antona duda kasantuwarta yar birni yar boko anman su yan qauyen nasu da suke ganin kamar sune masu tarbiyya tafisu sosai.

Yarinya qarama da batafi sa'ar tsaharensa ba sekaji suna kawo masa hari wai shi takeso wasuma har girke girke suke masa abin bai fara tsorata shiba seda wasu cikinsa suka fara kawo masa kansu kan su koda bazai auresu ba suna sansa sosai yake mamakin yaran hakan ya sa ko kadan bai sakar musu fuska.

Tun saka ranar Binto isma'il ya tattara yabar nigeria inda ya tafi china dan ya ce yana san karanta likitancin gargajiyarsu yayinda azahuri kuwa ya tafine dan ya san zuciyarsa za ta iya tarwatsewa indai aka daura auren bintonsa da wani.

Duk yadda akaso ya zauna ayi biki yaqi ya ce in time din yayi zaizo yayin da dangi suka rabu biyu gidansu Isma'il na asali suka haujin yaushin mahaifin Binto kan yaqi dan uwa yabaima bare.

Sosai family dinsu suka dau zafi da shi ya ce shifa bemasan da isma'il na santa ba ko kadan zatonsa shaquwar yan uwantaka ce kawai.

Dayawa cikin dangi sunce ya fasa baima tsalha yabaima Isma'il ya ce ina shi bazai zama qaramin mutin ba ko kadan ai tun farko isma'il yai nauyin baki.

Rana ba ta qarya yau aka daura auren Binto da angonta tsalha biki sosai aka sha na gani na fade dan kunsan in abu ya hadu tsayawa bada labarinsa qauyanci ne kawai.

Ranar lahadi da yamma aka dauki amarya se garin garu da yamma liqis aka kai amarya dakinta bayan ankaita ban gare ban gare aka dawo da ita barinta yayinda yan kai amarya kowa yaqi zama kowa nafadin ina ai su bazasu iya ko rabin awa aqauyeba.

Haka suka tafi suka bar Binto amarya zaune ita kadai saman gadonta adakinta da yasha gyara wanda inkana ciki bazaka taba cewa kana kauye bane.

Rubutawa

Faɗima Fayau

Fajaruddeen

Post a Comment

0 Comments