Farajuddeen (Kashi na 2)

    Shiko Deen suna fita yaja tsaki sosai ya tsani yarinyar tsabar ji dakai koma ya ce wulaƙanci ma ta zo zai mata make up dan isa saidai wata tai bayanin da ita ya kamata tai tsaki ya kuma ja akaro na biyu zan koya mata hankali kuwa in ta kawon raini.

     Farida ke nan yarinya mai ji da gata ƙuruciya, kyau gami da illimi domin ita ke jan ajin su.

     Yawancin yan ajinsu yadda take da ƙoƙari yake birgesu har suke sha'awar zamowa cikin abokan hulɗar ta inda wasu kyanta ke ruɗarsu ciki kuwa harda wasu malaman inda wasu dukiyar mahaifinta ke jansu sedai ciki babu wanda yake gabanta bare yasamu masauki gurimta.

    Tsabar tsare gida na Farida ya sa mutane ke shakkar ta ba ta da wata ƙawa a sch ɗin bare kuma aboki inka ɗauke Asma'u wanda ƙarfi da yaji Farida ta mai data ma'u.

     Farida ɗiya ce ga Hanshaƙin ɗan kasuwar nan wato Alhaji Nasir Dala wanda yake sananne ga kowa bawai iya ƙasa Nigeria ba a'a Nahiyar Africa baki ɗaya.

    Su bakwai mahaifinsu ya haifa mace ce ta fari wadda tuni aka jima da bikinta kusan tun kan ahaifi Farida sauran kuwa duk maza ne bayan haihuwar Faruk wanda shi ne na shida an jima ba'a haifi Farida ba dan har sun bar shi matsayin auta.

     Katsam Hajiya kubra ta sake samun ciki lokacin autanta Faruk nada shekara bakwai alokacin da aka haifi farida babu wanda bai murna ba san duniya kowa ya ɗauka ya ɗora mata musamman ma mahaifinsu da indai yana gari za ka ganshi riƙe da ita tafi shaƙuwa da shi kan kowa.

     Tun tasowar Farida batasan babu ba komai ta nema samu take danma wani abin mahaifiyarta kan rife ido ta nuna mata ba komi kake so kake samu ba.

     Lokacin da Farida ta kamla secondry mahaifinta ya ce yafisan tai karatunta agabansa dan baya san rabuwa da ita.

     Itama ɗin kwata kwata ba ta wani damu ba dan batasan nesa da iyayanta kazalika tana san nunawa ƙawayenta na online cewar ɗan mai kuɗi ma zai iya karatu a Nigeria yakuma fito da grade mai kyau dansu sunce ai yaran masu kuɗi ba abin da suka iya bazasu iya karatun Nigeria ba na wajen na yawanci kwalin kawai ake sai musu.

     ba ta wani sha wahala ba ta samu admission kasantuwar tana san karantar kimiyar Nazartar halayyar ɗan adam babu wanda ya hanata dan abin da take so takeyi bada jimawa ba suka fara lectures tun suna level one take ganin D. Saidai ko kaɗan bama ta tsayawa ta ko kalle shi bare ya birgeta.

     Suna level 2 yanzu ke nan akwai course ɗin da zai ɗaukesu yanayin yadda tsarinsa yake da yadda komi nasa ashirye yake ne yafara burgeta asannu ahankali yanayin tsare gidansa yazama shi ne abu mafi girma da ta fikalla agame da shi sosai take san Namiji mai iya tsare gida tun abin na burgeta har zuciyar ta sauya akala zuwa soyayyar sa so ke zafi kuma.

     Ma'u ce ta ce to muje gida sai mu kuma tattaunawa No bayanzu zan tafi ba inji Farida anman..ɗaga mata hannu tai inzaki tafi Ma'u ban hanaki ba daman ai ba tare muka zo ba ok sorry Mrs D. Farida ta kalle ta tai murmushi dan ta ji daɗin sunan da ta kirata da shi aranta tana fatan wataran yazama gaske.

     Sun jima cikin motar kamin ya fito daga office riƙe da wasu takaddu idon ta ƙyar ƙofar office ɗin tana ganinsa ta saki ajiyar zuciya wanda sai da ma'u ta kalle ta tausayin ƙawar tata ya kamata ada itama tana jin yana birgeta sai dai ganin wanda suka fita komi ma bai ɗaga ido ya kallesu ba ya sa ta shafawa kanta lafiya ta riƙe Muhammad ɗinta suke baza love ɗinsu.

     Sai da ya jima da jan motarsa kamin Farida ta kalli ma'u ni zan wuce Asma'u ta ce ai tare za mu tafi kin manta yau driver na bazaizo ba oh haka ne fa saiki jamu ok kawai ma'u ta ce tai kunna motar suka bar makarantar.

     Seda suka hau titin tsohuwar jam'a sannan Farida ta dubi Ma'u ta ce pls ma'u fara kaini gida inya so na turo a amso motar ok kawai ma'u ta ce ta cigaba da tuƙinta, Akan layinsu ta sauke ta sukai sallama Asma'u tai nasu gidan.

     Koda Farida ta shiga gida babu kowa a falon ɗakinta na ƙasa ta shiga ta watsa ruwa ta fito tai ɗakin mom ɗinta.

     Mom na dawo ta faɗa momyn kallon ta tai gami da ɗan nazarinta zo Farida ta ce Faridan ta shiga ta zauna jikinta mom ɗin ta ce autana meke damunki tai saurin ɗagowa lah ba komi me kika gani mom basar da hatun tai ta ce jeku maza ki ci abincinki abin da kika fi so ne.

     Tai ɗan murmushin nuna na jin daɗi tai waje gurin cin abincin Faruk ta gani yana bubbuɗe kwanukan tai saurin ƙarasa tana ɓata fuska yah Faruku mene haka kasan dai ba abin cin ka bane ko ya turo baki irin yadda take to se aka ce ke ke naki ne eh mana bayan mom ta ce min nawa ni kaɗai.

     Kinga malama abincin nan se naci kome zakiyi danma kinyi sa'a anyi kareren ki an temaka an tsinto ki ta watsa masa harara gami da juyawa seka cinye bama naci tabar gun yai dariya duk gidan shi ne abokin faɗanta tun suna yara inkaji kukanta to faruk ya maketa dan yana jin haushin da shi ake ɗauka yanzu kuma jariri dan ko kallon jaririyar bayai ranar da aka haifeta ma kuka yaitayi ummansa sai ta ajiye jaririyar ta ɗauke shi.

     Ganin da gaske dai bazata ci abincin ba ya sa shi zuwa falon sai dai ba ta nan ɗakinta na ƙasa yai tana ciki tai uban tagumi abinka da jini ɗaya sai duk tausayinta ya kamashi ya koma ya haɗo mata abincin ya dawo yar ya dawo batasan yashigo ba.

     Dafo ta yai tai saurin kallonsa ya ce haba jaririn umma mene haka sunan da yake faɗa mata ke nan tun yarinta ta ɗago ta kalle shi tana san ‘yan uwanta sosai ya ce na ji na fasa cin abincin kinji ‘yar ƙanwata tai dariya yawwa kabari inci se in rage maka yai dariya ai ba komi tun da dai ni aka fara haifa naci girma

     Tasan magana ya faɗa mata ta harare shi irin hararar wasa kaiko yai dariya ayi haƙuri yanzu dai sauko ki ci ta sauko ya zubo mata ta ce to muci a'a nifa senaga jaririn umma ya ƙoshi ta ce Allah inbaka ci ba na koshi ya kai hannu yafara ci suna ci suna hirarsu irinta ‘yan uwa sakwanni duda kuw ba sakon nata bane saidai yana jin daɗin tsokanar ta sosai.

    💞Don't forget to vote, comment and follow.💞

    Zaune suke suna hira wadda yawancin hirar ta ƙoƙarin sanya farida farin ciki ne kanta bisa cinyar ummanta idonta lumshe duk a ƙoƙarin boye damurwata dan kar su gano.

     Yaya bashir ne ya shigo riƙe da abu ahannunsa wanda ya ɓoye shi ta baya yana kiran autar umma ana ina ne baiyi zaton tana falon ba dan tana ganin ɗaya cikinsu ya dawo take tawowa da gudu ta taresu tai saurin buɗe ido tana dariya gami da miƙewa tana duban Dad ta ce dady yaushe yaya ya dawo abin dai ba.

     Dad yai murmushi irin nasu na manya ki tambayeshi mana ta turo baki gami da Faɗin Dady ya kwaikwayi maganar ta ya ce jaririna tai saurin dawowa tana buga ƙafa nifa Dad nace bana san Jaririn nan Faruk da yake ƙoƙarin shigowa ta cillawa filo duk kaine kawani samin Jariri ya sa dariya dole kuma a amsa ko amaida mutun inda aka tsintoshi.

     Dad ka ganshi ko Dad ya haɗe rai abin da haka ka na ji na ko ayi haƙuri dad tai dariya gami da masa gwalo ya cije leɓe alamar za mu gamu ne.

     Yah Bashir ne ya juya alamar zai fice tai saurin yin gunsa da gudu tana faɗin sorry bro yah faruk ne yaban haushi me ka siyon ina tsarabata hoo farida rikici bazakimin sannu da zuwa ba sai tsarabar ki au sorry yah namanta ne to nima na mance da tsarabarki ta turo baki idonta yai rau rau yai saurin miƙo mata ta amsa tana dariya tana faɗin bari inga mene.

     Sabuwar waya ce dalleliya sai makullin mota ta miƙe tana ihuu gami da rungume yayannata tana faɗin na gode Yaya shi ya sa nafi sanka duk gidan nan kome ta tuna ta ce a'a bayan su Dad yai dariya shi ma sosai suke san ƙanwar tasu.

     Gun su momy tai tana nuna musu eyye yar gidan yayanta ai saiki koma gidansa inji dady ya faɗa yana ɗan haɗe rai ta ɗago fuska a cakule eh mana bakinfi sansa ba inji mum Bashir yai dariya aiko dana ji daɗi fa ta ce nifa dady ba ina nufin harku ba a'a nidai jinai kince duk gidan nan kyalesu kinji Baby na kizo kawai mutafi ta maƙe ƙeya ni ba inda zani hawaye ya biyo fuskarta.

     Dad yai saurin janyota ya goge mata ah mene na kuka kuma ba inda zaki da wasa nake kinji Jaririna ta ce Dad yai dariya oh sorry Faridan Dady.

     Waje ta fita dan ganin motar sosai ta ji daɗi su momy da dady suka shiga ta zagaya dasu zuwa bayan gidan suka sa albarka.

     Koda ta koma ɗaki wayarta ta ɗauka ta kira Ma'u ta faɗa mata sosai ma'u ta tayata murna sukai gobe za ta zo ganin motar dan week end basu da sch kan su haɗu sai mondy.

     Da motarta da ta yafi da ita gida ranar Alhamis ta tawo dan Faridan ba ta aiko ta amsa ba.

     Sosai Farida ta ji daɗin ganin ma'u mutan gidan nasu duk sun saba da ma'u sosai suke san ta ganin yadda yar lelen gidan ke santa.

     Sosai sukai hira Ma'u ta ce nifa gaskiya ya kamata inje in ɗana motarnan farida tai dariya banda abin ma'u ran monday ai saki ɗana kinga ni daman kwaɗayi nakeji wallahi kizo muje kisaimin shawarma Farida ta kalle ta taɓ zaki ɗige kowa kuɗin sa ya fiddashi ma'u tai dariya to na ji zo muje ko ice cream ta hamsin ai nasha suka fito suna hira

     Yaya Usama suka gani zaune suna hira ta ce lah yah yaushe kazo yai murmushi ban jima da zuwa ba kinga yanzu zan juya ta ɓata rai shi ne da ban fito ba shi ke nan yai murmushi ah haba ai nai kaɗan yanzu nake shirin miƙewa inzo mu gaisa nan ta gaidashi Ma'u ma ta gaidashi

     Wani gun zaku ne eh wallahi wannan sarkin kwaɗayin ce wai muzo muje taci shawarma ma'u ta ce a'a banda sharri nifa mota nace zan ɗana to na ji koma dai mene ga wannan kwaci awara ya zaro dubu hamsim ya miƙo farida ta amsa tana mai godiya suka ma momy sallama sukai waje.

     Suna fita ta miƙawa ma'u dubu talatin kinga ni banda kuɗi sosai naɗau ashirin gashi kin sai ice cream ɗin ɗari ma'u ta zaro ido Farida basuyi yawa ba kuwa farida ta haɗe rai saidai in karɓa ne bazakiyi ba kawai Hajiya wane yawa ai da inada kuɗi da duk zan baki.

     Godiya ma'u tahau yi farida ta haɗe rai wallahi ma'u kina da matsala wallahi ko mene na godiya oho.

     Kaf ta kaso dubu ashirin ɗin a alawowi dan sana'arta ke nan shan zaƙi ita dai ma'udan ma faridan ta takura ne ta kashe dubi biyar.

     Mahaifin ma'u ba laifi yana da arziƙi saidai yawansu ya sa ba komi ake iya musu ba saidai basu rasa ci da sha ba gami da sutura sa'annan ko nawa ne kan karatu zai kashe musu ba wadda ya baima mota saidai duk inda zaki akwai driver zai kaiki kuɗi dai mai sunan kuɗi inkaga ya bawa yarinya to na makaranta ne shi ma baya wuce ɗari biyar.

     Koda suka koma gida sai mangariba Ma'u tai sallama da Farida dan wucewa gida kwata kwata ta mance ta sanar da driver ya zo ya ɗauketa tun da ita takawo kanta ta dubi Farida pls kicema driver inku yamaidani murmushi farida tai ta ce amshi nan.

     Ma'u ta duba taga makulli mota me kuma zandashi gani nan yah Bashir yaban waccan ta nuno sabuwar motarta shi ne nace ke ki riƙe wannan ta zaro ido kai Farida wannan fa ba waya bace da kika saba ba ni eh mota ce ai na sani tawace ai nikuma na baki kinga bari dai inje gida zan aiko adawo da ita kina san Abban mu ya kashe ni ya ce ina na samo mota.

     Ni ba aro na baki ba in kuma kika dawo da ita sai nai miki rashin m munma ɓata tai ciki abinta.

     Kamar Ma'u tasani tana komawa gida Abbansu ya kirata dan kishiyoyin ummanta sun kai mai gulmar ta zo da mota tun ran alhamis yaiko ta masifa tana zuwa yahau faɗa uban waye yabaki mota cikin rawar murya ta ce Allah ba tawa bace arowa nai ta farida Nasir ce.

     Yaɗan koma yazauna sabida ki zubarmin da mutunci shi ne kika koma aron motar mutane ko duk diribobin da naɗauka sabida ku ko cikin rawar murya ta ce wallahi ni mancewa nai in faɗawa driver ya zo ya ɗauken kuma ba ni da kuɗin motar dawowa yayi kyau ban makullin motar yanzu zansa amayar mata to ta ce tai waje tana ajiyar zuciya da bai hauta da duka ba.

     Koda aka mai da mota tana zaune tana cin abinci musa ya shigo wai gashi inji malam bala daga gidansu ma'u ya ce acewa Hajiya Farida wai Abban Asma'u ɗin ya ce karta ƙara bawa Asma'u ɗin aron mota dan ba ta da kuɗin gyarawa inta lalace farida ta miƙe ka je ka ce ai na bar mata to ya ce ya fice daɗinsa da yarinyar kwai kyauta koshi da yamata abin kirki yanzu za ta ɗauƙi wani abin ta ba shi kuma ba mai cewa a'a.

     Yana fita tacewa mom ni wallahi momy ma'u so take mu ɓata dan na mata kyauta saita ƙi amsa mom tai dariya aikinsan Abbansu da kin sani kin faɗa sai asa aje a sameshi to mom yanzuma kisa yaya Mansur ko yah Bashir suje to shi ke nan autan mom.

     Koda akaje da batin bada motar Abban ma'u bai yadda ba dan mota ce me kyau babba saida Bashir ya zo ya masa bayani sannan ya yadda dan kowa ya san yadda Alhaji Nasir Dala ji da kuɗi shi bema san Asma'u ƙawar ɗiyarsa ce ba dan shi bai shiga sabgar yaransa bare ya san su waye abokansu sosai yaji daɗi dan daman akwai wani kasuwanci da yake san yi ya rasa inda zai sami Alhaji Nasir ɗin dan ganinsa sai an shirya.

     Kuma murmusawa yai yajin sauƙi ya zo masa cikin ruwan sanyi zaiga Alhaji Nasir na san me zan yi ya faɗa.

    💞Don't forget to vote, comment and follow.💞

    Hajiya Bariya ya kwalawa kira bayan ya dawo falonsa tai saurin fitowa daga bedroom inda take ta faman gyara cikin fara'a ta dubeshi harka dawo eh ya ce kiramin Hadija ta haɗe rai anman Alhaji kasan fa yau ba kwananta bane eh na sani kwananki ne ko ce miki akai kwana zatai anan Allah ya huci zuciyarka ta faɗa gami da fita rai aɓace.

     Hajiya Hadiza ta rafka tagumi tana jiran kiran minin nata dan ma'u ta faɗa mata komi tasan yanzu akanta zai hakke danshi in ɗansa yau lefi har uwar yaro yake haɗawa ya ci mutunci.

     Ummin Hajiya Barira ce ta shigo umman su Asma'u wai umman mu ta ce ki je inji Abba to ta ce gami da da ɓoye damuwar ta dan yana ɗaya daga halinta baka taɓa ganin damuwar ta ko ɓacin ranta hakan ya sa mutan gidan ke zaton Alhaji yafi san ta baya mata faɗa basusan ko yanai ba shanywa kawai take ta fito ranta fes.

     Yana zaune ta shiga saidai ba yadda ta za ta bane fuskarsa asake hakan ya sa taɗan samu nutsuwa ta ƙarasa tana faɗin barka da dare ya amsa ta ce Alhaji ka aika an kirani baka bari tun da gobe kwana na zai shiga mayi magana.

     Ai maganar ce na ƙagu muyita towo ta faɗa kan Asma'u ne ya faɗi saida gabanta ya faɗi kwana biyi na fahinci baƙuwar mota a gidan nan to da na bin cika aka ce ita ta zo da ita tasan sarai babu wani kawai gulma aka kawo masa tasani.

     Eh ta faɗamin tun randa ta zo da motar nace ta waye ta ce ta Farida ce ba ta jin daɗi takaita gida ita kuma ta tawo da ita gida kan Farida ɗin za ta aiko ta amsa to dayake na san Farida ɗin ya sa ban damu ba.

     Washe baki yai au ashe kema kinsan ƙawar tata eh ta faɗa cike da mamaki ƙawar ta ce tun suna secondry yanzu suke Faculty guda duda dai ba Department ɗaya ba anman zumuncin su kullin ƙaruwa yake.

     Toto Allah sarki ya faɗa na kiraki ne ki kaima Asma'u ɗin wannan ya miƙo mata makulli na amshi motar dan amaidawa mai ita to ta ce ashe wai barmata tayi ku shirya keda ita gobe sai muje musu godiya ganin yai shiru ya sa ta miƙe to Allah yakai mu tai waje.

     Koda suka je makaranta ma'u taita godiya tana faɗin ai za muzo nifa ummanmu da Dad ɗinmu godiya kinsan nai mamaki da ya yarda da motar nan Farida tai dariya ai shi ya sa nake san yah Bash na san shi yaje ya tsara shi suka sa dariya.

     Da daddare mahaifin ma'u ya kwashi ma'u da ummanta suka tafi matan gidan sai gulma ake ko ina zasu oho dan baya fita da kowaccen su unguwa ba dan komi ya sa shi zuwan daren ba dan yana san ganin Alhaji Nasir ɗin dan ya san da rana ba tabbas.

     Su suka fara shiga tuni farida ta sanar da zuwansu gida an musu hidima sosai kai baka ce godiya zasu zo ba basu jima da shiga ba Alhaji Nasir ya fito haba baka shigowa se yanzu suke cewa tare kuke.

     Abban ma'u sai ƙasa yake da kai alamar girmamawa kunsan baba ma ance da babansa.

     Yar ƙaramar walima sukai Abban ma'u sai godiya ake mamaki kawai yake ganin yadda ɗiyar tasa ta sake agidan da mutan gidan baujin ko agidan nata uban gaban nata uban wato shi za ta iya sakewa haka.

    Godiya yai sosai mahaifin Farida ya ce ai karkaji komi mun zama ‘yan uwa daman su matan tuni suka saba dan sina ziyartar juna mune de sabgogin mu sunyi yawa haka ne ga musanmsn kai Alhaji inji Abban ma'u kwanaki ai inata san ganinka Allah beba.

     Kaji ko duk rashi sani ne inba haka ba ai da ba haka ba nandai cikin wayo mahaifin Ma'u ya fito da buƙatarsa mahaifin Farida ya biya masa daɗi kam ya cika shi tabbas haihuwa tana da rana.

     Sai dare sukai sallama ran kowa fes suka baro gidan Abban ma'u ranar shi ne harda ba ta kuɗi ta ji daɗi sosai kam.

     Ba'abin da kema Farida ciwo irin dare yayi lokacin kwanciya bacci ya kawo kai domin ayayin da kowa ke bscci yana jin daɗi ayayin da ita kuma za ta faɗa duniyar damuwa da tunane tunane.

     Yanzun ma haka ne kowa yai sallama ya tafi ɗakinsa sedai ita tun ɗazu take faman juyi kan gadon tama kasa bacci tsaki taja gami da tashi zaune.

     Wayar ta taɗauko kamar ko yaushe ba ta da aiki saidai kawai ta shiga twitter taita duba tweet ɗin sa.

     Facebook ɗinta ta fara hauwa saida kwmar kullin yauma ɗin bai accepting frnd request ɗinta ba sabon post ɗinsa ta karanta ta jima tana kallo post ɗin sannan ta koma IG nan ɗinma dai bai accepting ba account a private yake hakan ya sa ta tafi dai twitter ɗin duda ta fahinci nan bai cika haka ba.

     Yau kam da dare baiba sai tayi ihu hotonsa ne sanye da babbar riga yai kyau sosai tagani ya sa da a profile na Twitter ba shiri tai saving ɗinsa tana kallon saƙunan mutane na shigowa ta WhatsApp ta share gami da kashe data ta hau kallon hoton da ta ɗauko yanzu akaro na farko ta sami hotonsa itakam yau tafi kowa jin daɗi.

     Ta jima tana kallon hoton kamin ta ajiye wayar ta tashi dan yin Alwala taga uku ta kusa dan kaiwa Allah buƙatunta.

     Washe gari fes ta tashi ranta kai ka ce D ne ya furta yana san ta ko kuma ma an ba ta labarin ɗaura mata aure dashi.

     Tana idar da sallah ta ɗauko wayarta ta kalli hoton gami da rungume ta wani daɗi na shigarta ta ajiye wayar a hankula gami da shigewa toilet dan shirin makaranta.

    💞Don't forget to vote, comment and follow.💞

    Rubutawa

    Faɗima Fayau

    Fajaruddeen

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.