Fajaruddeen (Kashi na 14)

    Fatiha ta jima tana mita aranta kamin tai tsaki ta miƙe tai inda suke zama.

     Rai duk atunkushe ta gaidashi abinka da psychologist tuni ya fahinci akwai damuwa yaɗan murmusa aransa ya ce mata se abarsu ƙaramin abu su babba ne gurinsu.

     Ƙanwata ya kirata ta kalle shi batare da ta amsa ba ya ce am sorry kwana biyu banzo ba bankuma kira na ji ya kike ba aranta ta ce ashe ya san be kyauta ba.

     Banzo bane sabida mahaifina beji daɗi ba duk na rikice jiki na rawa cikin nuna nadama take tambayar me ya sameshi tun yaushe.

     Faɗuwa yai yau kwanansa biyar kenan a asibiti muna sa ran ko yau ko gobe ma asallameshi dik se ta ji babu daɗi taita Allah ya sawwaƙe yana amsawa da amin.

     Kinsan me ya sa ya faɗi ta girgiza kai yaɗan murmusa ya tambaya ne ba dan daman ta bada amsa ba dan ya san ba ta da ita.

     Any way abin da nazo mu tattauna kenan nan ya ba ta labarin auren da fasawa gami da dalilin fasawa ta jinjina abin aranta gami da afili shiru ya ratsa.

     Can ya ce Fatiha zaki iya aurena ta dube shi kawai pls kiban amsa zaki iya aurena ban ɓoye miki komai ba game da abin da na sani akaina sedai kawai ina da tabbacin iyayane sune suka haifen duda banda tabbacin niɗin sun haifen lokacin da sukai aurene ko kuwa kasuyi.

     Kiban amsar da take ranki karki damu wallahi bazan zargeki ba dan kince bazaki auren ba dan na san kina da hujja me ƙarfi.

     Indai har kana jin za ka iya aurena ni babu wani aibu dazaisa in kasa auren ka ta faɗa ya dubeta ni kuwa fatiha mezai sa ince bazan aureki ba a'a yah karkayi bincike ka ce bazaka iya .

     Bazan bin cike ba Fatiha ki faɗan da kanki wallahi kinji na rantse miki zan yadda da kome kika faɗan bazan taɓa tunanin kin ɓoyen wani abu kamar yadda na ban ɓoye miki komai ba sedai ni bazan ce ki yadda da abin da nace miki ba ki fara bin cikawa.

     Murmushi tai bana buƙatar bin cike domin ba ni ma da wanda zai bin cika min wanda zan aura dan ba wanda ya damu da rayuwata karka damu.

     Na ji yimun bayani na miki alƙawarin ba abin da zaisa in fasa aurenki tai shiru kamin ta fara.

    Ni haifaffiyar kaduna ce.....

    Thanks for reading 😍

    Fatiha ta cigaba.

     Mahaifina sunansa Abdurrashid muktar haifaffen kano ne komai nasa na kano ne.

     Malam muktar shi ne mahaifinsa wanda ya kasance yanada mata biyu umma salamatu da umma Barira ko waccensu tana da nata yaran umma Barira ce uwar gida tanada yara biyar sai umma Salamatu wadda take ita ce amarya tana da yara takwas ita ce kuma mahaifiyar mahaifina wanda shi ne na huɗu a ɗakinsu.

     Gidansu mahaifina shahararren gida ne a unguwar su da maƙotansu koma ince a garin kano baki ɗaya daga nisan duniya in ka ce akawo ka gidan Malam muktar sarkin mayu za a kawoka yar gidan kakana wato mahaifinsu babana.

     Shi ne sarkin mayun garin nasu sana'arsa ita ce bada magani babu lefi Allah ya hore masa dan maganin nasa yana ci sosai kamar yankan wuƙa indai ya baka insha Allahu za ka warke saidai fa in mutuwa ce to ba yadda za'ayi.

     Kasantuwar yanayin gidansu mahaifin nawa ya sa mutane basa san mu'amala dasu duda kuwa sunsan da fewar maitar gidan ba me cutarwa bace dan kuwa bazaka taɓajin ƙorafin wani ɗan gidan ya kama wani a waje ba.

     Duk wanda ya isa aure ayaran iyalin akan yaɗa shi aure da ‘yar uwarsa ko ahaɗata da ɗan uwanta domin kuwa mutane basa yadda kan su basu auren yaransu ko kaɗan hakan baya damunsu domin kuwa suma ba lefi suna da dangi masu yawa ta inda wani be rasa abokin aure.

     Da yawa cikin ‘ya’yan kakana basu da sha'awar sana'artasa duda kuwa yana san ace yasamu Magaji cikinsu Baba musa ne ma wani zubin yakan nuna kulawa ga yaga yadda mahaifin nasu ke abubuwa.

     Cikin masu ƙin sana'ar mahaifin nasu harda mahaifina wanda shi ya zaɓi sana'ar fatauci dan karatun ma yaƙi duk yadda mahaifinsu yai yaƙi domin iya primary bn kawai yayi itama daƙyar ya ƙarasa hakama na addini ba wani nisa yai ba dan ko hizifi guda ba'ace ya haɗa ba tun da ya samu na sallah ya dena zuwa.

     Cikin iko da ni'imar Allah sai kasuwancin nasa yai albarka domin kuwa komai ya taɓa sai yazama kuɗi hakan ya sa mutane ke cewa ai shi ɗin akwaishi da nasibi.

     Ganin Allah ya sanyawa kasuwancin nasa albarka ne yana samu sosai ya sa mahaifunsu ya buƙaci da yai aure nan ya ce yana san ya nemi yar gidan ƙaninsa wato Batulu domin alokacin kusan ita ce sa'ar aurensa duk yarane ‘yan.

     Saidai fa kwata kwata Batulu ba ta cikin tsarin matan da Abdurrashid yake ganin sun dace da burin zuciyarsa na mace hakan ya sa ya ce shifa gaskiya baya santa duda kuwa ya san afaɗin garin kano babu mai ba shi ɗiyarsa ya aura anman haka ya nuna shifa tabbas baya santa.

     Hakan ya sa mahaifinsa zuba masa ido kawai ya ce aƙyaleshi inyaje yaga ya rasa matar aure zaizo da kansa yana neman auren batulun yana bada haƙuri.

     Fatiha ta ɗan numfasa kamin ta cigaba inbaka mance ba nace maka mahaifina Fatauci yake.

    A harkar fataucinsa babu garin da baya zuwa cikin Nigeria wani zubin har maƙotan Nigeria fataucinsa ya kaishi garin makurɗi fahintar da yai kasuwanci agarin da riba ya sa har shago ya kama inda in ya zo yake zama masaukinsa.

     Yakanyi watanni agarin kan ya waiwayi gida hakan ya sa yasaba da mutane da yawa musanman ‘yan unguwar da yake zaune domin shiɗin akwaishi da saurin sabo saboda mutun ne shi mai faran faran da jama'a ga zaulaya.

     A garin makurɗin ne Allah ya haɗashi da wata yarinya mai suna sakina wadda gidansu ke lokon da ya kama haya daga gaisuwa wani zubin kuma sukan ɗanyi hira dan takan ganshi agidansu wajen yayanta har suka saba indai ya ganta saiya zaulayeta.

     Sannu ahankali shaƙuwa ta shiga tsakaninsu dan haka kawai takan fito susha hira ita da shi koda yayan nata basa nan kafin wani lokaci sun fahinci irin soyayyar da suke ma juna .

     Sakina haifaffiyar garin makurɗi ce mahaifinta ɗan kano ne aikine yakaishi makurɗi har ya haifesu daɗin zama ya sa ya kasa dawowa gida kano sedai suzo da ziyara duk ‘yan uwansa suna garin kano shida yayansa ne kawai anan makurɗin wato Alhaji sule wanda shi kasuwanci ne ya kawoshi nan makurɗin.

     Iyayan sakina su bakwai suka haifa shida mata sai ɗaya namiji yayin da kuma alhaji sule yake da yara uku duk maza hakan ya sa suke san ɗiya mace da yara domin su haihuwar ba me yawa suka samu ba.

     Ganin mahaifin sakina yana da yara masu yawa ya sa matar Alhaji sule ta nemi da subata biyu ta riƙe sukako ji daɗi dan ba wani arziƙi suke da shi ba Salima da Sakina suka basu wanda Sakina ce babba dan inda take Ss 1 zasu tafi 2 yayin da ita salimar ke a JSs 2.

     Akoyaushe burin Hajiya Shatu shi ne sakina tai candy su aurawa Babban yaron su ita ita kuma salima su aurawa ɗan autansu itadan harma sun sanarwa da iyayansu sakinar sun kuma yi murna sosai.

     Yadda suka riƙe su sakina riƙone na amana kamar yaransu suka ɗaukesu habu abin da su sakinan zasuce sun rasa sedai ma ace sunfi jin daɗi anan fiye da agidansu dan gidansu suna da yw yayin da kuma mahaifinsu bai da ƙarfi sosai.

     Saidai fa kan kowa ya ankara soyayyar Abdurrashid tai ƙarfi azuciyar Sakina wanda har batajin za ta iya rayuwa ba da shi ba sun shaƙu irin shaƙuwar da mai rubutu bazai iya rubutawa mai karatu ya fahinta ba.

    Sakina suna Ss1 3rd term Abdurrashid ya nuna shifa yana san ya futi ai aure dan ya jima da shiryawa ta nuna itafa tafisan tai candy abinka da shi ba wani mahincin illimin ya sani ya dage harseda ya juyo da hankalinta ta amince abinka da shi namiji ne kuma ya girme mata.

    Yayin da shikuwa tsoron girman yarinyar yai da yadda yaga tana kuma kyau ga farin jinin samari hakan ya sa yakeso suyi auren kar aje amasa ƙafa dan yana santa sosai in yai sake ya rasata ya san zai sha wuya.

    Ganin dai ya takura da batin auren ya sa ta cire kunya ta tunkari mariƙiyar tata da batun hankalun Hajiya shatu yai mugun tashi dan tasan shirun su ya tasarma rushewa na haɗa auren zuminci dan yadda tasan sakina da kunya tun da ta zo mata da batun auren take so tasan tabbas tana matuwar san yaron.

    Duk yadda ummanta mahaifiya da mahaifinta suka so fahintar da ita kan kartai butulci taƙi ta nuna itafa Abdul kawai takeso ganin haka ya sa kowa yai fishi da ita kowa ya fita sabgarta duk dan ta mance da batun Abdul ɗin saidaifa kamar ƙara mata sansa suke dan lokacin da kowa ya fita sabgarta shi ne yake kwantar mata da hankali yake kuma nuna mata irin san da yake mata yake kwaɗaita mata irin daɗi da kulawar da za ta sha agidansa akuma gurinsa hakan sai ya ƙara ninka shaƙuwarsu.

    Ko makaranta ma Sakina dena zuwa duk kuwa da yadda ada ta ɗaukaki karatu ta ba shi mahinmanci duk ta faɗa ganin kar yarinyar mutane ta cutu tumda iyayanta sun musu kara ya sa Alhaji Sama'ila da kansa yasamu mahaifinta ya ce shi gurinsa babu komai suma karsuji komai ai sakina ɗiyarsa ce dan haka bazai mata auren dole ba akwai wasu yaran ƙanne da yayyenta se ayi zumuncin.

    Haka iyayanta suka haƙura duda basu soba Alhaji sama'ila ya wuce gaba wajen auren nata.

    Koda mahaifinta ya sa aka masa bin cike akan Abdurrashid ɗin nan suka gano ko shi waye da sana'ar mahaifinsa nanfa hankalinsu ya tashi nan suka saka Sakina a gaba suka mata bayani da fatan ta ce ta haƙura bama sai an mata dole ba.

    Buɗar bakinta ta ce ina ita ai a musulunci babu maita sai kanbun baka wanda kuma dan mahaifi nada kanbun baka ba yana nufin cewa ɗan sa yana da shi ba dan haka Abdul ɗinta ba dole bane yana da shi ta ji ta gani tanasam sa za ta aureshi.

    Duk zagi da hantara da iyayenta ke mata haka ta rufe ido taƙi haka suka haƙura da faɗan dan sunga ba zai yi ba suka koma lallashi da nasiha anman ta ƙi sairaronsu.

    Ganin ta bijire ta nace ya sa mahaifinta da mahaifiyarta suka ce sun janye hannu dags kanta basu ba ita ta ce itafa ta ji ta gani dan tana ji aranta fishi ne kawai sukai in lokaci yaja zasu haƙura aganinta.

    Alhaji Sama'ila ne da matarsa su sukai mata komai aka kaita ɗakinta wato ɗakin mijinta anan makurɗin inda za ta zauna ba shi da nisa sosai da gidan iyayanta.

    Sakamakon Alhaji Sama'ila sun saba da riƙe mace ya sa lokacin bikin cikin yaran da sukazo daga kano suka roƙi Balaraba da ta bar musu ɗiyarta Hadiza su haɗa da Salima ƙanwar sakina tun da mahaifin Hadizan ya rasu aiko Balara ta ji daɗi nan ta bar hadiza kan sauran kayanta za a aiko Driver ya zo ya ɗaukar mata.

    Watansu Sakima takwas da aure suka taso suka dawo kaduna dam kasuwamcin sa alokacin yafi ci a kadunan.

    Zaman aurensu zamane me ban sha'awa domin indai ka gansu sai sun baka sha'awa abu guda ke damunta shi ne rashin haihuwa musanman yadda dangin Abdul suka takura mata danma ba gari guda suke da su ba.

    Shekarar sakina ta biyar da aure sedai Allah bai ba ta haihuwa ba abin duniya duk ya isheta dam in ta zo kano gidan su Abdurrashid iyayansa da ‘yan uwansa suyi ta mata gori banda hantara dan abunne ya haɗe gs haushin yaƙi ‘yar uwarsa ya aureta ga haushin kuma rashin haihuwa.

    Akoyaushe ta je kano da kuka ko da takaici take dawowa haka ma in waninsu ya zo da ƙunci suke barinta Fahintar hakan ya sa Abdul rage mata zuwa kanon kazalika in sukazo baya zuwa ko ina dan in yananan basa iya mata hakan ya maya daɗi sosai yakuma ƙara mata san mijin nata.

    Sedai matakin Abdul ya ƙara tura tsanar sakina ga dangin nasa suka ƙara sama ransu tafa shanye musu ɗan uwa.

    Seda suka shekara shida suna shirin shiga ta bakwai sannan ta samu ciki murna gurin ta ba'a magana haka ma Abdul dan zanma iya cewa yafa fi sakina murna.

    Alokacin kuwa Abdul ya zama babban Alhaji dan kuwa Arziƙinsa sai san barka dan tun suna shekara ta huɗu da aure sukaje saudiyya shida matarsa.

    Watanta tara ta haifi yaronta santalele me kama da mahaifinsa ya ci sunansa Abbakar aiko an kashe kuɗe ranar suna alokacin sakina ta kuma tabbatar wa Abdul ita yake so ba wani abu nata ba dan alokacin se take ganin kamarfa sabon shafin soyayya ya buɗe agareta da yaronta.

    Haihuwar Abubakar se ta zama kamar an buɗe mata haihuwar dan tana yaye shi ta Haifi umar sannan usman datai na huɗun ne ta roƙi ya sa mata sunan mahaifinsa shi ne ya sa Ibrahim nanmafa taga jalala a family ɗinsu wai besa sunan mahaifinsa ba se nata ita dai ta toshe kunnenta kawai.

    Tun haihuwar Ibrahim se yazama kamar an rufe mata haihuwar sedai alokacin ba ta wani damu dan tana ganin su Abbakar agabanta kuma alokacin babu me kiranta juya dan ta aje har huɗu.

     Seda ta shekara takwas dan har ma sun cire rai suna zaton ko ta gama ne sannan ta kuma samun ciki murna gurin ma'auratan kai ka ce haihuwar fari ce.

     Alhaji Abdul alokacin ma dai yafi Hajiya sakina murna sanshi aduniya yana san yara musanman ma ace Sakinansa ce za ta haifa masa.

     Lokacin da sakina ta je asibiti aka ce mata macece tai murna sedai fa Abdurrashid yafita murna danshi akwai da san ɗiya mace duk se ya ƙagu Sakina ta haife masa me kama da ita.

     Tun cikin na yaro yake waƙar Fatiha zai samata.

     Tun farkon cikin abubuwa marasa daɗi ke samun mahaifina akasuwancinsa na asara.

     Abinka da ‘yan gargajiya nanfa danginsa suka hau faɗin anya ba hannu aka saka masa ba tun da da lokacin da auri sakina arziƙinsa haɓaka yai bare suce ita ce me farar ƙafa.

     Yanayin yadda yake asarar ya sa ya fara yadda da hannun aka sa masa abinka da wanda be wani illimin addini me nisa ba .

     Ran Litinin mahaifiyata ta fara naƙuda hankali tashe mahaifina ya ɗauketa sukai asibiti dan Allah ya temaka lokacin ya zo dan lokacin yakan yawan tafiya hakan ne ma ya sa ya ɗauko kakarsa dan kar haihuwar ta zo yazama ita kaɗaice agidan.

     Basu jima da zuwa ba nurse ta fito take faɗa masa ai ta sauka ta samu ɗiyarta mace murna gurin sa ba'a magana ya miƙe yana faɗin zan iya shiga in ganta ta ce eh dan asibitin kuɗi ne ita kaɗai ce aɗakin.

     Wayarsa ce tai ƙara ya dakata ds shiga ya ɗaya muryar yaronsa ya tsinkaya yana faɗa masa ai wuta ta tashi a kasuwa cikin shagunan da suka kama harda nasa bakuma yajin akwai mamora kasa shiga ɗakin yai ya koma ya zauna daɓas hankali tashe yana faman innalillahi wa'inna ilahi raji'un yayin da kaka kuma keta faman faɗin kai ita dai wannan yarinya batazo da arziƙi ba yayinda shi bama jinta yake ba dan shi kaɗai ya san me yakeji aransa.

     Ya jima azaune kamin ya miƙe zai bar asibitin nurse ɗin ta fito riƙe da baby ta miƙa masa ya amsa yana shafa kanta ya shiga ɗakin da matarsa take wato ummana ya mata sannu sannan ya faɗa mata abin da ya faru hankalinta ya tashi ya ce shi zai je dan ganin ya ake ciki seda yamin huɗuba da Fatiha ya kwantar dani gefen ummana yana shafa kaina kamin ya fice.

     Koda yaje alokacin hankalinsa ya kuma tasha dan be yi zaton abin yakai haka ba dan babu wani abin mora komai ya ƙone abinka da wanda ya nema da gumin sa yai kuka sosai dan ya san zafin dukiyar sa.

     Yayin da Danginsa daga kano ke ta faman cece kuce kanwai yarinyar nan ita ce silar komai duba da tun randa aka samu cikin yake tafka asara kama da haihuwar ta.

     A cewarsu wai na kwaso babbar maita daman akan samu haka wani maitarsa tafi ta kowa zafi.

     Ummana ce ta sayi ragon suna ganin ko maganar bayau zatonta sabida matsalar da ya faru da shi ne dan batasan tayar masa da hankali.

     Watana uku a duniya mahaifina ya tattaro iyalinsa daga kaduna zuwa kano dan kasuwan cin kadunan yaƙi ci.

     Lokacin da muka dawo kano yana da gida anan rijiyar zaki da ya sa ‘yan haya kan mu dawo ya tashesu nan mukai masauki.

     Alokacin rayuwa tai mana zafi dan kuwa komai yafaƙi ci hakan ya sa ummana ta ce tun da gidan da muke ciki babbane kuma unguwar tanada daraja mai zai hana ya saida gidan ya siya mana ƙarami anan gaida sauran kuɗin sai yaja jari sosai yaji daɗi kuwa dan hakan yayi yaja jari.

     Babu lefi kasuwamcin yana garawa sai dai duda haka ba kamar da ba alokacin ida shekara guda harda watanni ina yawona ka ina sai dai tun alokacin mahaifiyata ta fahinci mahaifina baya shiga sabgata dan ko abu ya ce ummana ta masa in ta ce Fatiha takema abu yanzu zai balbaleta da faɗa wai tana sangarta ni yai waje cikin fishi.

     Ranar da aka sa za a yaye ni alokacin ne akai wata gobara a sabon gari ciki kuwa harda shagon mahaifina hankalinsa ya tashi sosai dan kuwa har faɗuwa yai.

     Duk wanda ya zo daga gidansu Abdul ɗin wato mahaifina jaje sai kaji suna shaguɓe kan wai sanadiyya ta komai ke faruwa da shi ahankali mahaifina ya gama yadda da batun ‘yan uwan nasa duba da hujjojinsu abinka da wanda bai wani illimi mai ƙarfi ba.

     Ya riga ya gama yadda da cewar indai har abin farin ciki zai sameni to tabbas abin takaici zai sami me ɗaukan nauyina sabida wai nice na gaji wata yayar kakarmu domin maitarta mai zafi ce itama haka abubuwa ke samin mijinta indai zai faranta mata maganin abun kawai shi ne fita sabgata da nunan tsana.

     Duda kuwa duk yaron da aka haifa ana karya masa maitarsa saidai acewar su irin tawa tafi ƙarfin karyuwa.

    Alokacin inada shekara uku aduniya aka haifa min ƙani wanda ya ci sunansa Aliyu tun lokacin ko faɗa mukai da yaro se yaita cuta ko dan iyayansu sun canfa ne oho hakan kuwa ya ƙara tunzira mahaifina da ƙara tsanata aduniya babu wanda nake tsoro kamarsa dan kuwa yana ganina zai hau muzurai yakuma hauni da faɗa gashi lokacin kakana yarasu wato mahaifinsu su babana bare ace zai yi maganin abun su kuma yaransa basu wani san komi kan sana'ar tasa ba.

     Mahaifina bai shawara da mayaifiyata ba ya saida gidan da muke ciki na gaida tun tana jin jita jita ba ta yadda ba har seda ya zo da akori kura ya ce wai kaya za a kwashe za mu koma gidansu wato gidan kakana dan daman duk mara ƙarfi kawai shatar guri yake ya zauna shida iyalinsa dan gidan akwai girma.

     Koda ummana tai magana ya hauta da faɗa wai ai duk lefinta ne da ta haifo masa masifa haka kawai yana zaman zamansa ds arziƙinsa ta haifo masa tsiya alokacin ummana tai kuka sosai na bijirewa iyayanta dan tasan baƙin cikin da tasasu ke bibiyarta.

     Lokacin Aliyu nada shekara 3 inada 6 ummana ta nemi akaini makaranta Abbana da kansa yakaini dan har lokacin be gama cire hannunsa akaina ba nan yakaini primary ta gwamnati da ke unguwar tamu nai murna sosai dan kuwa akwaini da san karatu.

     Banda yaya mace se yayye maza tun haihuwata nake yar gata agunsu komi suka samu na Fatiha ne ko Ali dake ɗan auta basa ji da shi sabida suna san mace ni kaɗai kuma suke dani hakan ya sa sabida yarinta banwani damu da rashin kulawa ta mahaifina ba.

     Sesai lokacin dana shiga primary ‘yan ajinmu kowa kance babansa ko Abbansa yai masa kaza yai masa kaza sai na fara damuwa nagane bawai fa iya kulawar yayye nake buƙata ba ta uba ma ita ce mafi a'a la.

     Babana bai sati da kaini makaranta ba ya tafi Nijer da kuɗin gidan da ya seda dan sayo shinkafa dan yaji labarin alokacin cinikin shinkafar ke garawa.

     Cikin rashin sa'a duk wanda ya sayi shinkafar se ya dawo masa da ita dan kuwa duk ciki tai hunhuna alokacin mahaufina ya fidda hannunsa akaina dan ya riga ya gama yadda da soki burutsun danginsa.

     Tun tasowata mahaifiyata ta koyar mun da komi nagani insa mass albarka hakan zai sa komada dagaske ne inada kanbun bakan to babu wani abu da zai sami wannan abin da ya birgeni hakan kuma nake.

     Tun bayan asarar shinkafar da yaine ya ce shifa ina yama dena neman kuɗin inje inci kaina da kaina badai dukiyar sa ba tun da dai inrasa wa zanma zalunci sai ubana.

     Kwata kwata ya dena zuwa ko ina sedai ya ci yashi yaje salla ya dawo ya shige ɗaki yai kwanciyarsa.

     Ummana ita take mana komi da temakon yaya Habu in yaje makaranta ya dawo yakanyi buga bugarsa ya kawo ahaka muke rayuwa.

     Kamin wani lokaci aka samu wanda sukai convincing ɗin mahaifina cikin danginsa kan cewar dole sai ya auri ‘yar danginsa arziƙin sa zai dawo aiko dai ya yadda nan aka sa lokacin bikin nasa shida Batulu wadda akai akai ya aura abaya yaƙi dan kuwa har lokacin batai aure ba.

     Duk wainar da ake toyawa ummana batasan anai ba sai ran kai amarya ta samu labari dan ba gida guda muke dasu batulunba bacin ma haka mu bama shiga sabgar ‘yan gidan dan sun ware ummana.

     Aikuwa ranar tai kuka sosai taita masifa mahsifina ya mata banza zan iya cewa shi ne karo na farko dana ga faɗan ummana.

     Washe gari ta kwashemu mukai makurɗi saidai fa ba ta wani samu karɓuwar kirki ba bare ta musu bayanin me Abdul yake mata dan babu fuska duda dai bakamar daba da suke korarta satinmu guda acan ta tattaro mu muka dawo kano dan tabar Yah Habu da yah Ummaru akano sabida su suna exam.

     Ina primary 6 matar babana ta haifi ɗiyarta mace inda Abba na ya sa mata Sakina aikuwa taita masifa baza'a sama ɗiyatta sunan kishiyarta ba nan yaita rantsuwa ba sunan matarsa ya sa ba kawai dan yana san sunan ne ta ce to ta ji anman wallahi baza'a ɓoyeba dole kowa ya ce mata sakina ya ce Yaji yagani.

     Duk soyayyar da mahaifina kema ɗiya mace se ya ɗiba ya ɗora kan ɗiyarsa sakina dan ya jima yana san mace.

     Mahaifiyata ba ta ankara ba sai labari ta ji wai zai koma kaduna anman da iya amaryarsa zai tafi tai kuka iya kuka har ta godewa Allah dan kuwa tasan ba ta isa ta hanashi ba inko ba haka ba yanzu aji kansu.

     Tun daga wannan lokacin da yabar kano se lokaci lokaci yakanzo hayan watanni ya ɗan kawo abin da ba'a rasa ba yaɗanyi kwanaki ya tafi wanda in ya zo ɗin mu hankalin mu atashe shi nasa atashe dan in ya zo yadinga masifa kenan ta bagaira bare dalili seda yakai ya kawo kar cikin mu babu me san zuwan nasa.

    Kusan ina Jss ne ya dawo kano inda ya zo gida wurjan jan bayan wajen wata takwas da ya kwashe bezoba yaita mun masifa wai duk sanadinane wallahi in ban sake masa mara ba yai kasuwancin sa zai koreni daga gidan ya cireni cikin yaransa.

     A wannan zuwan ne ya ce ya cireni amakaranta yakuma hanani fitowa koda tsakar gida ne indai yana nan sedai inna ji fitarsa masallaci in maza in abun da zan in koma ɗakina.

     Alokacin bamu san me yasame shi bakuma musan asarar me yaiba har ya dawo kanon.

     Alokacin babu lefi yayyena sun tasa su ke ciyar damu yayana usman shi ne yaban jari ya ce ba talla ba indunga zuwa bakun lokon mu ina suyar ko waina kuma awara na zaɓi awara duk wanda yake gida acikinsu to za ka sameshi gurin awarata suna tayani zama hakan ya sa babu me kawon wargi in ba ita kazo siya ba kawai kazo surutu ne yanzu zasu nuna maka hanya.

     Kwanansu biyar mahaifina agida ya kwashi amaryarsa da iyalinta suka bar gidan bamu san inda suka koma duda de har yanzu suna kanon sedai lokaci lokaci yakanzo anman ya dena kawo mana komai sedai ya kwashe abin da yayye na suka kawo yai gaba dasu.

     Idan ummana tai magana yahauta da masifa yana faɗin shida da yake kawowa me ya sa ba ta magana se yanzu da yaranta ke kawowa to daɗinta bafa ita kaɗaita haifesu ba kuma ayanzu ai haƙƙin ci da shi yana kansu.

     Ana haka yayana ya kammala makaranta yah Abu da yah ummaru inda yah Habu yasamu aiki da FG suka tura su jigawa shi kuna ya ummaru yake kasuwanci babu lefi yana samu.

     Lokacin danai candy yah usmanma ya kammala karatunsa yana koyarwa a secondry babu lefi yanzu ta fi mana da yayyena suka biyamun kuɗin jamb cikin ikon Allah naci aka ban abin da na nema agric naita murna.

     Alokacin damuwata biyu ce ta farko ita ce ta mahaifina yadda kullum kamar ƙara masa tsanata ake wanda lokacin da ya samu labarin ai naci gaba da karatu harnai candy na cigaba da jami'a yaita bala'i wai zai koren daga gidansa.

     Sai abu nabiyu shi ne afamily ɗinmu kaf wanda suke sa'oin aurena mata an musu aure mazan da suka rage kuma ba wanda yake sha'awar aurena dan tsoron kar masifa ta dinta afka masa.

     Yah Bashir ya dage shi zai auren iyayansa sukace zasu tsine masa ina ji ina gani ya auri Badariyya duk da kuwa har yanzu yana sona sedai ba inda muka iya.

     Tun ina primary ba ni da wata ƙawar kirki dan uwa ta samu labarin ɗiyarta na abota da Fatihan gidan sarkin mayu tuni za ta raba mu.

     Hakama ina secondry rimi rimi za mu fara ƙawance da yarinya ta zo gidanmu se ta fara tsorona tun da dai gidanmu gidan mayu ne hakan ya sa kaf rayuwar karatuna nake ni kaɗai banda wata ƙawa ko aboki.

     Tun rashin saurayi na damuna har ya dena sabida ada babu fitar da zan banyi saurayi ba sedai fa yana zuwa gidanmu zai dena zuwa wani zubinma ‘yan gidan ke korarsa.

     Hakan ya sa kawai na rungumi ƙaddarata nake komai nawa ni kaɗai har ko yaushe kake gani na anan ni ɗaya dan abin da in saba da mutane su gujeni inzo ina damuwa.

     Yayye na duk sunyi aure ina level 1 going to 2 babban yayi aure yah Habu dansu yah Usman sun rigashi aure.

     Duk da sunyi aure basu fasa ɗaukan nayun karatunmu nida su yah Ibrahim ba sun jima da hanani yin awara sedai dan bana san cika tambayarsu dansuma ba wani ƙarfi garesu ba ya sa naƙi denawa.

     Ayanzu nice kamar ‘yar auta dan ko Ali da yake ƙarami da ya samu abu to yanzu zai kawon gabaki ɗayansu tausayina suke danma ummana ta hana da tuni ina Jigawa gurin yah Habu ta ce ina bazai yiwu daga aurensa akaimasa yarinya budurwa ba.

     Fatiha tai shiru kamin ta ce wannan shiene ataƙaice wace ce Fatiha.

     Cigaban labari.

     Shiru kawai Fajar yai yana kallon ta hankalinta ya tashi kodai shi ma tsoron nata yake ne ta ce daman na sani indai kaji ni wace tuni za ka sauya ra'ayi ta faɗa tana share hawayen da ya zubo mata.

     Yai murmushi ba hak bane Fatiha kawai tausayin kine ya cikani ya hanani magana ai shi so baruwansa da waye mutum kuma shi so na gaskiya shi ne kaso mutum ka rungumi komi nasa ka maidashi naka sanki a jina yake bazan denashi ba kamar yadda ummanki ba ta yadda da maitaba haka nima kawai ki fara amsa sunan Amaryar Deeni tai murmushi dagaske.

     Ba wasa nake ba ki faɗan yaushene Abban naku ke zuwa zanzo in sameshi eh to ba shi da taka mai mai lokacin zuwa sai dai in ya zo zan kiraka awaya in faɗa maka.

     In za ka zo karka zo da mota karkayi wata shiga me kyau in yafe mene sana'arka ka ce koyarwa ya ce sabida me tai murmushi sabida in ka je da mota bazai baka aurena ba inkaje da shiga me kyauma haka zaiji tsoron kar kaima ƙaddarar data faɗamasa ta faɗa maka dsn haka zaice zai baka Sakina ƙanwata.

     Inko yaga baka da komi ko kusa ka kaɗan bazaima sakina sha'awar auren ka ba dankuwa yana santa da yawa.

     Ok kin ba ni satar amsa suka sa dariya gami da sauya wata hirar zukatansu cike da annashuwa musanman Fatiha dan Fajar duda ya san mahaifinsu zai amince sedai ta wani ɓarin yana tsoron mahaifiyarsa kar taƙi amin cewa.

    Koda Fajar ya koma gida baima mahaifiyar sa maganar Fatiha ba sai da ya bari mahaifinsu ya dawo sannan ya faɗa masa komai game da game da fatihan ya ce ba komai indai ya tabbatar yana san ta shi ke nan ba komai.

     Sai dare suna cin abinci sannan mahaifin nasa ke faɗawa ummam nasu.

     Salima ya kira sunanta ta amsa gami da mai da hankalin ta gunsa daman maganar Deeni ne kan aurensa na samo masa yarinyar da nakesan ya aura ta ji daɗi aranta aƙalla dai ya sa hannu akan Deeni sanin halin sa ya sa ko tambayar sa wace yarinyar ko a ina ya samo masa ita batai ba.

     Kwana uku da yin maganar su Fatiha ta kira shi take faɗa masa cewar Abbansu yadawo yako ji daɗi aransa ya ce zaizo kan ya tafi.

     Da yan macin ranar da sukai waya da Fatihan ne ya shirya tsaf cikin shigar farin yadinsa da yasha guga wanda inkai ba mai mu'amala bane da ya dudduka bazaka taɓa banbance shin mai tsada bane ko mai arha duda kasancewar simple shiga yai saidai yai kyau sosai kwarjinin sa da zatinsa ya kuma bayyana.

     Fajar Dogo ne bacan ba shi ba fari bane bakuma baƙi ba kalarsa wasu kekira da ruwan tarwaɗa sumar kansa akwance take luf akansa wanda ko bai ta je ba ko bai aske ba za ka ganta akwance yayin da sajen fuskarsa ke ƙara masa kyau da kwarjini duda yana yawaita aske shi sai dai kan wani lokacin ya kuma kwanciya a fuskarsa.

     Hancinsa da idanunsa duk na mahaifinsa ne wanda idanunsa suke dara dara hancinsa har baka ataƙaice dai Fajar mai kyau ne kyansa ke jan mata da yawa wajen kamuwa da soyayyarsa.

     Sau da dama shike haska kaya inya saka ba kaya ke haska shi ba hakan ya san ko wacce irin shiga ya ɗauki hankalin mai kallonsa.

     Kai tsaye bakin titi yai dan tarar ɗan sahun da zai kaishi unguwar su Fatihan.

     Ji yai ana Malam ya juya jin kamar ya san muryar murmushi yasaki ganin Faiza ashe dai zan ɗauki murya itama murmushin tai kamin su gaisa ya ce daga ina haka naje gidansu Fadila ne suka ɗan taɓa hira nan take ba shi haƙuri kan abin da mahaifinta yai ya nuna mata ai komai ya wuce ya kuma nuna jin daɗinsa na yadda yaga ta saki ranta tana rayuwa ta masa godiya kan admission ɗin da ya samo mata ya ce ba komai sukai sallama yai gaba.

     Ta jima tana kallon sa har ya ƙule sannan ta share hawayen da tuni fa yanzu tana gidansa yana kiranta mamata tana kiransa mijina Allah ka ciremin san wannan bawan naka ta faɗa sannan tai gida.

     Har unguwar su Fatihan mai adaidaita sahun ya kaishi abakin lokonsu maiɗan sahun ya ajiye shi inda ya sauƙa ya miƙa masa kuɗin nan ya hangi Fatihansa tana suyar ta sai yanzu fa ya tuna bai ce mata yau zai zo ba ya ɗan jima yana kallon ta yadda ya ganta fes duda ba kwalliya tai ba sai yaji ta burgeshi aƙalla ita ɗin mai tsafta ce.

     Gurin ya ƙarasa tana ganinsa ta diririce shi kuma yahau dariya haba tawan mene haka kuma daga gani na sai ki wani daburce yah Ibrahim yatoso lafiya dai Malam yai ɗan murmushi Ibrahim ko eh nine fatiha tai mamaki yadda ya iya gane yayan nata da sunansa bai bari ya kuma magana ba dan yaga ɗan zafi ne yai saurin cewa pls gurin Abbanku za ka min jagora Fatiha tai saurin cewa yawwa yah kuje ɗin.

     A hanya yake faɗa masa abin da ya kawo shi Ibrahim yaji daɗi ya godewa Allah da baisa ya kwafsa ba wajen yima Fajar ɗin rashin mutunci.

     Daman kasanni ne inji Ibrahim nop but taban labarinku ta ce daka kai sai ita duda ka ba ta 8yrs but jikinka baya nunawa Ibrahim yai dariya ai sun rainani ita da Ali Fajar yai dariya haka ƙanne suke ai shi ma yai murmushi inda yai dedai da zuwansu ƙorar gidan Ibrahim ya shiga bari in maka iso to Fajar ya ce.

     Babu yabo babu fallasa yadda mayaifin nata ya amsheshi kamar yadda ta faɗa aiki da sa'arsa ya tara tambaya kamin ya ɗora da ince kasan me za ka aura dan bana san se abu yai nisa ka ce na munafunceka Fajar ya ce ya san komai ya yadda ya amince yakuma ji yagani mahaifin nata ya ce to ka je zan sanar mata da matsaya ta inna gama nazari to ya ce sukai sallama.

     Yana fitowa daga ɗakin zauren ya ci karo da Fatiha ya ce sana'ar fa tai murmushi yah Ib. Ya ce zai jire nan suka sami waje suka hau hira wanda sai bayan lisha sukai sallama da juna cikin shauƙin ƙauna ya tafi tai gida.

     Cikin kwana biyun nan duk hankalinsa atashe yake ya kasa kwanciya sabida zullumin kar Abban Fatiha ya ce bazai ba shi ita ba dan sai ayanzu ya kuma fahintar irin son da zuciyarsa kema Fatihan wato zazzafan sone wanda bayajin ya taɓa ma wata irinsa wanda kuma ya san babu wata mace da zai iyama irin wannan son shi kansa har mamakin irin yadda yake jin ta aransa yake.

     Kwana biyun nan sabida fargaba har faɗawa yai duda yana jin kamar mahaifin nata bazai ce bazai ba shi ita ba sedai yana tsoron kar ya ce sedai ya ba shi Sakina ƙanwarta.

    💞 Don't forget to vote, comment and follow 💞

     

    Fajaruddeen (Kashi na 6)

    Tun daga wannan ranar lokaci lokaci takan kirashi inda yake katse kiran ya kirata haka shi ma yakan kirata kamin wani lokaci har sunyi sabo me ƙarfi wanda har basa iya yini ɗaya bai kira ɗaya sun gaisaba ba.

     Azahirin gaskiya Fajarudden mutun ne me murɗaɗɗen hali wanda in be baka fuska ba zakai zaton ko kaɗan bai san maine kirki balle kai zaton yana da shi anman in kai dace ya nuna maka other side ɗinsa zakai zaton samun mutum mai kirkinsa zai matuƙar wuya.

     Koda aka kafe result ma shi ya kirata yake tambayarta Reg number ɗinta kan in ya shiga zai faɗa mata me ta samu tai murna sosai dan ba ta Whatsapp bare a turo ta duba gashi ba ta da number in kowa bare ta tambaya.

     Sosai yai mamakin abin da ta samu danshi zatonsa damuwa bazata bari ta iya karatu ba da ƙarfin gwiwa ya faɗa mata ta samu 4.6 tai murna sosai gami da masa godiya sun ɗan taɓa fira kamin su ajiye wayar.

     Gun ummanta ta nufa nan take faɗa mata an kafe sakamako ta faɗa mata me tasamu umman tai murna sosai itama.

     ***

    Faiza ce zaune abin duniya duk ya isheta gashi sanyi ake an bada hutun makarantar mangariba bare taga malam hankalinta ya ɗan kwanta ita ba abin ta kirashi ko ta je gidansu ba tun da bama tasan me za ta ce ta je ko ta kirashi danshi ba.

     Aɗa ɓangaren yaya Bashir yaƙi kiranta bacin da ya san sunyi zai kirata yanke shawarar zuwa gidan su Bashir ɗin kawai tai dan ba ta da aminin da ya fishi so take ta taɗa masa abin da ke damunta dan gani take rashin faɗawa kowa ya sa abin ke cin ranta.

     Tsaf ta fito tai ɗakin ummanta, umma zani gidansu yah Bashir umman tai ɗan shiru alamun tunani take kamin can ta ce me zakije yi tai shiru shi ke nan ki je karki zauna kar kuma ki kawon ƙorafi inkin dawo game da zuwan naki ta ce to umma gami da ficewa.

     Kai tsaye titi tai ta tari ɗan sahu basu da wani nisa sosai hakan ya sa befi minti goma sha biyar ba suka iso danma ɗan sahun bai cika gudu ba.

     Har ƙofar gida yakaita ta ba shi kuɗin sa sai da ta zura ƙafarta gidan ta ji faɗuwar gaba kamar ta juya ta dai daure ta shiga.

     Da Balara mai wanke wanke ta fara gani suka gaisa tai ciki tayi sallama yakai biyar ba'amsa haushi duk ya cika ta kamar ta juya tadai daure ta kuma yin sallama can aka ce cikin faɗa waike kurma cene tun ɗazu ana amsa dan wulaƙanci shi ne zaki ishemu da ihu ta shiga tana me sunsin da kai.

     Kamar yadda ta za ta umman su Bashir ɗin na kujerar bakin ƙofa amsa sallamar ne kawai ba zatai ba anman tahau ta da faɗa tana faɗin wai ta amsa aƙas ta zauna tana gaida ita ƙasa ƙasa ta amsa.

     Lafiya dai naganki da rana fatsar fatsar haka cikin rawar murya take faɗin gun yaya Bashir nazo baya nan umman tai saurin ba ta amsa to bari in jirashi a'a ba yanzu zai dawo ba kizo ki tafi inyadawo ya zo to ta ce gami da yin waje idonta na kawo ruwa ace kai bawa kaida gidan yayan Babanka sai dai kallo.

     A ƙofar gida suka ci karo da Bashir yadda ya ganta yasha jinin jikinsa a'a ƙanwar kinsan daga gida nake mami ta ce kin tawo nan taɗan saki yaƙe harma zan koma ah haba ai kuma kinyi kaɗan se kin koma munyi hira tai saurin zama a rumfar farfajiyar gidan dan tasan dai bazai barta ta tafi ba tun da ya dawo.

     Sun ɗan taɓa fira kamin ya tambaye ta me ya kawo ta tai ɗan fari da ido kamin ta ce kaji yaya shi ke nan bazan zo mu gaisa ba sai wani abin ya kawoni shi ma yai fari yana kwai kwayonta yana faɗin kaji ƙanwar shi ke nan ni bazan tambayi sis ɗina ba gabaki ɗaya suka sa dariya.

     Faɗa masa abin da ke damunta tai kan kaceme bugun zuciyarsa ya ƙaru yayin da muguwar faɗuwar gaba ya ziyarce shi ɗan taɓo shi tai yaya baka ce komai ba yai saurin sakin yaƙe ina tunanin mafita ne tai murmushi bari in tafi kawai kayi tunani me yawa yanda za ka ban shawarar da za ta anfaneni kaji yaya na yai murmushin ƙarfin hali yawwa kamar kinsan meke raina kuwa tai murmushi gami da yin hanyar waje.

     Juyowa tai yah ba rakiya yai saurin miƙewa yayo inda take tsaye bari kawai ƙanwar inata tunanin mafita tai saurin cewa ahto yi zaman ka kawai yai murmushi ah haba ai dole in raka ƙanwata danma ina san yin tunani me kyau da ai kaiki zan yi tai murmushi kaji yaya karfa ka ce na kawo maka aiki shi ma yai murmushi badai kiji na faɗa ba.

     Seda ta hau ɗan sahu ya juyo dan komawa gida sai dai yadda yakeji aransa baya jin zai iya komawa gida bai fashe da kuka ba gidansu Salim kawai ya shige ya san bayanan ya shige ɗakinsa kamar yadda ya za ta kuwa salim ɗin baya nan ya kullo ƙofar ɗakin gami da rafka uban tagumi shikam wannan wace irin ƙaddara ce tahau shi yarinyar da yakema matuwar so ya gama shirya rayuwarsa da ita ace ita ce ke tambayarsa shawarar ya za'ai wani namiji ba shi ba ya sota shikam yau baƙar rana ce agare shi.

     Be san sanda hawaye ya hau kai kawo akuncinsa ba tabbas ya san ya rasa Fa'iza yadda yaga san wani ƙarara a idanunta takaicin sa ɗaya wai ace ma shi zai bada shawarar yadda Rival ɗinsa zai sota wannan wace irin masifa ce ya faɗa.

    💞Don't forget to vote, comment, share and follow 💞😍

    Kafe result da akai za mu iya cewa yafi komai yiwa Farida daɗi duda ta ga me ta ci a group hakan besata cewa za ta je ganin result ba abin da ba ta taɓa yi ba.

     Sedai abin da ta je danshi ko sahunsa ba ta gani ba bare tai nasarar ɗora idanunta kan kyakkyawar fuskarsa ko zuciyarta za ta ji sanyi ganin abin da take muradi haka ta dawo gida rai duk a aɓace.

     Yadda ta tashi yau kan ta tafi makaranta ganin result yaiwa iyayanta da ‘yan uwanta daɗi sai dai yadda ta dawo a cun kushe ya tada musu da hankali wato dai ana ‘yar gidan jiya mahaifinta yafi kowa damuwa domin yana matuƙar san ɗiyar tasa ko kaɗan baya san ganinta cikin damuwa shi kam da zai san meke damunta ko dukiyar sa za ta ƙare sai yai mata maganinsa.

     Tunani tai ko dan sau ɗaya ta je shi ya sa ba ta ganshi ba hakan yasata sauya shawara.

     Gurin Dad ɗinta ta je ta ce ya ba ta kuɗin registration za ta je tayi ba musu ya ba ta dan baya san abin da zai ɓata mata rai ganin yau tana cikin walwala fiye da sauran kwanakin da yake ganin ta duda tun da ta fara makarantar ko sau ɗaya ba ta taɓa zuwa yin wani registration ba baima jin tasan yadda da inda akeyi.

     Kai tsaye gidansu Ma'u ta wuce sosai Asma'u tai murnar ganinta Farida ta tsuke fuska ai kyayi murnar ganina mana mara M ace tun da akai hutu sau ɗaya zaki kawon ziyara ma'u ta ce ai dai gara ni ke aikinzo Farida ta harareta yanzu ai ba ni bace ko wallahi zaki sa in koma Ma'u tasa dariya sorry hajiya wasa nake.

     Seda suka ɗan taɓa fira kamin Farida ta ce pls rakani sch zakiyi ma'u ta ɗan waro ido an koma ne mtsss farida taja tsaki abin da wulaƙanci aikema kinsan ba'a komaba dai ko to inba'a koma ba me zakiyi farida ta kumayin tsaki kefa kinada matsala yaushe kika koma ‘yar jarida koma barrister zance ne mai da wuƙar bari in shirya faɗawa umma to.

     Farida ta miƙe bari in faɗa mata kawai malama kisa hijabi mu tafi to jeki ki faɗo mata bari in ɗauko hijan ɗin farida na ficewa ma'u ta shige toilet.

     Koda farida ta dawo masifa tahau yi ita ala dole ma'u za ta makarar da ita itadai ma'u haƙuri kawai take bata.

    ******

    Fatiha ce zaune tana gyara waken awarar ta suna ɗan taɓa fira sama sama da ummanta wanda duk yawanci kan kuɗin karatun su ne wanda yayansu zai kawo sai dai har yau baizo ba.

     Fatiha ta dubi ummanta ta ce ina ganin umma kuɗin gurin ki na mai da kuɗin da nake ajiyewa na awara za mu haɗa inyaso ko rancene ki yi a haɗa in yi registration ɗin nan shi ma yaya Bashir sai yayi nasa in yaso in yah Umar ɗin ya zo se mu biya bashin da kuɗin gurin sa.

     Eh to kin kawo shawara anman me zai hana mu jira zuwan nasa ai umma matsalar kar su rufe karɓa in suka rufe ka kori kanka shi ya sa eh to da haka kuma zammasa waya ya haɗa kuɗin a natse in ya yaɗa ya kawo yawwa umma bari in duba inga nagun naki zasuyi nawa baza su wuce dubu ashirin da ɗaya ba inji umman.

     Fatiha ta miƙe bari in ɗebo in irga tana shiga ɗakin ta ji sallamar babansu tai saurin ƙulle kuɗin a bakin zaninta gami da tuttule mansau cikin ƙatuwar langa ta tura can ƙarƙashin gadon umman tabar ɗan kaɗan taliyar su ma ta tura ƙarshin gadon tabar guda huɗu shinkafa daman sauran kaɗan tabarta nai tahau ninkin kaya.

     Tana jerawa a adaka ya shigo ɗakin ganinta yasashi sakin tsaki gami da faɗin ke ban hanaki shigowa ɗakin nan ba in ina gida tai saurin zubewa aƙas tana faɗin lah baba sannu da zuwa ya watsa mata harara dan gidanku baki ji me nake faɗa ba tai saurin cewa wallahi baba abin da ka zo ba.

     Munafukar banza munafukar wofi ki dinga wani sun sun da kai se ka ce wata ta gari fice ki ban guri mara mutunci da tai gadon tsiya hawayenta ta goge tai saurin shigewa ɗakinta tana shiga kuka ya kwace mata itakam ta rasa me taiwa babanta ya tsaneta da badan abubuwa da dama da suka tabbatar da kasantuwar ta ɗiyarsa itakam da ta ce ba mahaifinta bane.

     Tana jin fitar sa zuwa Masallaci tai saurin fitowa ta deɓo kayan da ta tura ƙarƙashin gado ta kawo nata ƙarƙashin gadon dan tasan in ya dawo ko ina sai ya dube a ɗakin in yaga an ɓoye a ƙarƙashin gado kowa na gidan ya shiga uku ba ita ba.

     Itakam ummanta bawai rashin zuwansa ko rashin ci dasu da yake ƙinyi ke ba ta takai ci da shi ba face yadda yakewa tilon ɗiyar su mace kan hujjar sa mara kai bare makama.

    ****

    Ita kam Fa'iza ganin tsahon kwana uku ba yaya Bashir bare shawarsa ya sa ta kiransa bugu ɗaya ya ɗaga cikin shagwaɓa take faɗin yah kafasan kai nake ta jira yai murmushi har tana jiyo sautin sa ya ce hoo Ƙanwar gaskiya malam ɗin nan ya tafi dake da yawa tai dariya bari kawai yaya kofa Bacci banayi wani takaici ya ziyarci zuciyar Bashir yaɗan daure kinga yanzu rubuto miki nake bai ƙarasa ba ta ce to bari in kashe ina jiranka.

     Kamin ya ce wani abu ta kashe yabi wayar da kallo azahiri dan besan shawarar da zai ba ta bane ya sa ya ce rubuto mata yake shikam bema san me zai ce mata ba gidan rubuta saƙo ya shiga ya rubuta mata ya daɗe yana kallon abin da ya rubuta kamin yai gun dun balar turawa.

     Tana karantawa ta buga tsalle ji take kamar Malam fajaru ya zama mijin ta ma ya gama sakon ta turawa yayan nata

    "shi ya sa nake sanka yaya na nakaina na gode sosai Allah barmu tare"

    Yana zaune ransa cike da tunani kala kala saƙonta ya shigo kawai tsintar kansa yaida jin daɗin saƙon nata kasa dena karantawa yai ayayin da farin ciki ya cika masa zuciya ya rungume wayar yana sakin murmushi.

     Kome ya tuna oho yai cilli da wayar yana furzar da iska.

     Nace towo kai kuma ko lafiya dago idanunsa da yai naga sun koma jawur na san inna kawo wargi zan iya shan naushi ya sa na fice nayo gida.

    💞 Don't forget to vote, comment, share and follow 💞😍

    A'a umma wanke wanke kike haka ina Fatima inji Fajarudden umma tai ɗan murmushi ba ta jin daɗi ne ina za ka haka ya kalli kansa ba ko ina da na ɗan fito zan leƙa ne se ka dawo ai na fasa fitar ma ya faɗa yana cire doguwar rigar jikinsa.

     Kawo in wanke ya faɗa yana ƙoƙarin durƙusawa a'a kaga basshi ka je inda za ka kawai nifa ba inda daman zani pls ki kawo ai na ma gama sedai ka ɗauko waken can ka tsincen to ya ce yai inda waken yake.

     Yana tsintar waken sina fira da ummansa ya ce wai kuwa umma ina Abba ya fice tun safe kai shi ma dai Abba baya gajiya da fita duda jikinsa be cika masa daɗi ya za'ayi tun da yafi san fitar inji umma maganinsa ma ya kusa ƙarewa kuwa gwanda ka siyo tun kan ya san ya ƙare ya ce karka siyo kasan dai halin sa.

     Yau zan siyo insha Allahu yawwa gwanda dai yaɗan dubi umman ya ce umma yadda yai maganar yasata fahintar me yake san faɗa mata sai dai ba ta da tabbas takan ya sa ta tsaida abin da take ta mai da hankalinta kansa na'am ta faɗa.

     Ya ce umma daman wannan dai maganar ce tai saurin ɓata fuska cikin fushi take faɗin wai kai wane irin mutum ne nace karka kuma mun wannan maganar indai baso kake nida mahaifinka mu mutu mubar ma duniyar ba nace karka kuma anman dan ka raina ni shi ne dole sekayi ko to wallahi ka kiyaye ne karka sake inji koda dawasa kaiwa mahaifinka ita inko kasake ko abayan idona ne ban yafe ba.

     Fuuu ta miƙe ta shige ɗaki hankalin fajar yai mugun tashi ba abin da ya tsana sama da tadawa iyayansa hankali ruwan da ya ɗorawa umman ya haɗa mata ɗakinta ya shiga kuka kawai take nan hankalinsa ya kuma tashi yai saurin ƙarasawa ya riƙo hannunta yana ba ta haƙuri.

     Ganin taƙi dena kukan ne shi ma ya sa kuka ganin haka yasata yin shiru to mene kuma na kuka ta faɗa shidai cikin kuka yake neman afuwar ta tai murmushin ƙarfin hali shike nan ya wuce yai murmushi yawwa umma na kin yafe min tai dariya ai daman bance kayi lefi ba ina kuka ne dan ganin mun tauye ku matsayin ku na yaranmu mun ɓoye muku abin da yake haƙƙinku ku sani sedai ɓoyewar shi ne mafi alkairi kayi haƙuri kamin alƙawarin dena wannan maganar.

     Ya kuma riƙe hannunta indai hakan zai saku farin ciki insha Allahu bazan kuma ba tai murmushi yawwa jeka yanzu zan fito Allah ya muku albarka ya ce amin umman mu ya fuce tana binsa da kallo tasan me ke damunsa tausayin ƙanwar su fatima yake sedai suma duda kasan tuwar su maza abin tausayi ne ta share hawayen cike da tausayin yaranta da mijin ta ta fito tai bayi.

     Seda ya gama girki ya yankawa umman tasa salak sannan ya leƙa ɗakin fatima tana kwance da alamu ciwon ya lafa ya ce salak ɗinnan na kawo ki ajiye na Baba ne na san insu Usman suka zo cinyewa zasuyi karki basu kinsan kan salak se yaƙi ci abinci ta ce to yaya seka dawo ya ce Allah ya ƙara sauƙi ya fice.

     Fajarudden kenan indai yana gida baida abinyi ba abin da baya yi tun tasowar sa ummansu ta sabar musu da taya ta aikin gidan kasantuwar duk maza Allah ya albar ka ce ta dasu autar ta ce kawai mace sun riga sun saba indai ummansu na girka abu to duk wuyar sa kuwa suma sun iya dafa shi.

     Umman su ko kaɗan ba ta da matsalar ɗiya mace dan yaranta sun iya komai basu da kyashi musanman fajar da baida san jiki ko fita zai inyaga tana aiki indai ba abu me mahimmancin gaske ba se ya taya ta komai tare suke baida aminin da ya wuce ummansa.

     Abu guda ne matsalar sa da ummansa yadda ya kasa daure dena tambayarta sirrin da suka binne suke ganin ya binnu sedai tana jin kamar daga yau bazai kuma ba dan tasan baya saɓa alƙawari.

     ****

    Ita kam Farida ko da suka je makarantar me makom taja kan motar zuwa inda zatai registration Faculty ɗin su ta nufa inda ta saba tsayawa dai ta tsaya sun kusan awaya uku babu alamun malan ma'u ce ta gaji da zaman shiru ta ce pls Farida muje mana mutumin nan fa ba zuwa zai ba kema kin sani.

     Ta ina kuma na san bazai zo ba sai dai in ya faɗa miki ne ki faɗan ma'u ta zaro ido ni asuwa a ina zan ganshi ya faɗan kawai dai kinsan ko lokacin ba'ai hutu ba inbaida lecture baya zuwa bare kuma cikin hutu kinsan baida dalilin zuwa.

    Dan Allah muje kar ace mun yi zuwan kawai abin da muka zo danshi bamu samu munyi ba dan dai kin nace ne anman ai registration ba dole se munzo sch ba shirun da ta ji faridar tayi ne ya sa ta saurin kallonta ga mamakinta kuka faridan take.

     Ya ilahi ni ma'u Farida dan Allah ki sama kanki haƙuri kan mutumin nan indai har mijin kine da kansa zai kawo kansa ki rage takurawa zuciyar ki in ba mijin ki bane ba yadda zakiyi cikin kuka me tsuma zuciya Farida ke faɗin na sani ma'u nima abin da meke damuna ba da na kasa cire soyayyar sa cikin raina wallahi ina san sa ma'u banjin zan iya auren wanin sa zan iya zama da shi kome zaimin.

     Dafe kanta ma'u tai ranta fal cike da tausayin ƙawar tata tasan tabbas tana matuwar san Malam tarasa wane irin so take masa haka tausayinta duk ya cikata.

     Fita tai daga motar ta zagayo koma can naja muje ba tare da musu ba Faridan ta koma kujerar me zaman banza Ma'u ta koma gurinta kafin taja ta ce ki yi haƙuri yau befi sati biyu ba a koma tun da kika iya haƙurin rashin ganinsa na watanni na san zaki iya daurewa na sati biyu.

     Ki dunga Allah ya sassauta miki sansa karki tsaya iya kan ya soki kawai kinji farida ta ɗaga kai kamar wata yarinya alamar to suka ja motar suka bar Faculty ɗin....

    💞Don't forget to vote, comment, share and flow 💞😍

    Rubutawa

    Faɗima Fayau

    Fajaruddeen

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.