Ticker

6/recent/ticker-posts

Daddagen Harafin z A Karshen Gaba

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

638. In aka sake nunka z can gun ƙarshe,

 Z kan rikiɗe a daddage ta a ko cashe,

Nan aka sanya j  ta zo a gaɓar ƙarshe,

To ita z idan tana ƙarshe tarshe,

  Rikiɗewa takai ta zan mai sauyawa.

 

639. Cizo, cije-cije zai zama nunkawa,

 Dabba in tana da haurun cizawa,

 Ni ban sanya hannuwa ko farawa,

 An cije ka ba ka ma iya ramawa,

  Cizajje dukan su z na juyewa.

 

640. Murza, murje-murje shi ne nunkinsa,

 Murza ki wuce, ki bar shi nan yai aikinsa,

 Mummurje idonki, Binta ɗauko muna fansa,

 Masu ginar gyaɗa suna neman kwasa,

  Murzajje cikin gyaɗa sai tamnewa.

 

641. Darza, darje-darje nan za shi fitowa,

 Wanda ya taka dakkali sai darjewa,

 Daddagi z ta sauya j ga rubutawa,

 Kalmar nan guda ta darzan darjewa,

  Darzajje da an gama sai bushewa.

 

642. In ka gane ƙa’idojin ga misalai,

 Ƙirƙiro naka sa su dace tuballai,

 Sai ka gina ka tsara kalma ta wakilai,

 Doka ta yi nata tsari na misalai,

  To ka kiyaye wanda za ka rubutawa.

Post a Comment

0 Comments