Ticker

6/recent/ticker-posts

Sauyawar Harafin z Zuwa j

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa 

631. Harafin z yakan zamo j ga rubutu,

 Sauyawa yakai, ku lura masu karatu,

 An tanadi tsare-tsare gun masu rubutu,

 Su lura da wanga tsari na rubutu,

  Daidai gun gaɓa ta ƙarshe ga kulawa.

 

 

632. Shi ma kan sa gun tilon dai aka zance,

 Kalmar duk da taz zamo ɗai ga kwatance,

 Kwai tsari na sauya shi z a misalce

 In aka so a mai da ita jam’i to ce,

  In aka mai da shi yawa ga rubutawa.

 

633. Ga kalmar maza idan aka sauya ta,

 Kwai ƙari gaban ta malam ka rubuta,

 Ai sauyin baƙi na z an ka hukunta,

 Ƙarin j ake gaban z a rubuta,

  Gun jam’inta ai mazaje aka cewa.

 

634. Sa natsuwa ka dubi geza ga tilon ta,

 Ƙari za ka yo gaban z ka rubuta,

 Shi ma za ka sanya j don a karanta,

 Lura da kyau, ga furucinta ka furta,

  Gezoji ga nata jam’i aka sawa.

 

635. Reza za ta zamto rezoji ke nan,

 Wannan da ake saye a yi askin nan,

 Ko kuma wadda an ka yanke akaifan nan,

 Malam lura wagga kalmar rezan nan,

  Z ta birkice zuwa j aka cewa.

 

636. Gwarzo ya buwaya tilas a yaba shi,

 Ya sha ɗamara a yanzu ba masu taɓa shi,

 Ya gawurta babu kowa a gaban shi,

 Kowa na faɗin mu je ka mu gai da shi,

  Dole yabo ga duk gwarajen Hausawa.

  

637. Harafin z wajen tilon bai sauyawa,

 Lura da kyau shi tilonsa ba ya canzawa,

 Banza, banza-banza, ai z ka biyowa,

 Reza in guda tazo z aka sa wa,

  Gun jam’insa lura j shika komawa.

Post a Comment

0 Comments