Ticker

6/recent/ticker-posts

Daurin ‘n’ A Nasaba

  

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

209. Nasaba dai abin nufi sai makusanci,

 Na zaman tare ne walau dai mazumunci,

 Asali shi ka sa kare alli zai ci,

Ita nasaba abin nufi nuna kusanci,

  Na alaƙar jini walau nasabantarwa.

 

210. Sa natsuwa ka duba misalin nan,

Ga dokin kara da dokin ƙarhe nan,

Danbun dankali da dambun rogo nan,

Jirgin laka, hadda keken ƙarfe nan,

  Ga wundin kaba Bukar na saƙawa.

 

211. Su biyu an ka sa suna da kusanci ne,

 Wandon ƙarfe, ganinmu ya fi a kece ne,

 Jirgin leda misalce, bai keta hazon ne

Rawanin ɓartake naɗinsa jidali ne,

  Ga shi gudan tuli naɗin bai kamewa.

 

212. Aikin ‘n’ da ɗai ta nuna, zumunci ne,

 ‘Yan matan garin ga jirgin laka ne,

 Ba sa kai ka ganga, ko kai malam ne,

Yaran zamaninmu wandon roba ne,

Ba wani kwankwason da ba sa kamewa.

 

213. In ka fahimta duk a nan ‘n’ nasaba ce,

 A misalan da mun ka sa farkon zance,

 Dokin ƙarfe an ka sanya da kwantance,

 Doki wanda an ka sa ya ya kasance?

  Dokin nan kara yake nasabantarwa.

 

214.  Shi wundin kaba, kaba ce ta haɗa shi,

Nasaba tai tana kaba an gane shi,

Ita ce assali da an ka yi saƙar shi,

‘n’ ta nuna duk alaƙa da kabar shi,

  Matuƙar ba shi ba kaba ba zaunawa.

 

215. Rawanin nan da ɓartake aka saƙa shi,

Nasaba tai zare, da shi aka ƙera shi,

Ai asalinsa yanzu kan an nuna shi,

Kwai dangantakar da tan nuna silar shi,

  In an zare ɓartake babu naɗawa.

 

216. Yaran zamani kamar yadda akan ce,

 Yaran nan a zamani sun ka kasance,

 Daman dai a Hausa, an bayyana zance,

Yara da zamani zumuntar ƙarni ce,

  Ba ƙarnin da bai da yara na nunawa.

 

217. Dudduba abin ga don ka yi ganewa,

 Za mu tarar da ‘n’ tana dangantawa,

 Kalmomi biyun zumu take daɗa nunawa,

Don haka ‘n’ a nan tana nasabantarwa,

Na bayanin abin da duk za shi biyowa.

 

218. A bayanai da mun ka yo na rubutawa,

‘n’ tai ƙoƙarin rawarta ta takawa,

Kuma ta fayyace misalin nunawa,

Za ka ji ‘n’ tana fita ba sauyawa.

  Gun lafazinta ha kaza gun zanawa.

Post a Comment

0 Comments