Daurin Sauran Bakake

     

    Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

    About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

    196. Babu baƙin da zai buwaya ga ɗaurewa,

     Duk harafin da kas sani na rubutawa,

     Za ya rubutu yadda za a karantawa,

     Ɗauri in ya wanzu, ba a musantawa,

      Matuƙar za ya furtu gun mai zanawa.

     

    197. Doka dai ya zan baƙin an ɗaure shi,

     Ai masa tarnaƙi, ya ɗauru a tanke shi,

     Ya bayyana ko’ina ya zo a rubuta shi,

     Ba sauya shi, babu halin nashe shi,

    Kuma ya zamo guda ga tsarin ɗaurewa.

     

    198. Ɗaurin bai wuce gaɓa ɗaya a kiyaye,

     Wato kan gaɓar ta ɗauri ka kiyaye,

     Farko an ka sa walau dai ƙaraye,

     Ko kuma tsakkiya, buƙata ka kiyaye,

      Bakin dai gaɓar abin za shi tsayawa.

     

    199. Ɗauri ɗaure sautuka ma’ana miƙe,

     Ɗaɗɗaure baƙi akai a gaɓa saƙe,

     An samu gaɓa, a yanzu aikinmu a miƙe,

     Matuƙar ga baƙi da ɗan wasali liƙe,

      Aka kawo baƙi guda sai ɗaurewa.

     

    200. Duba misalin ga don ya zan ka gane shi,

     Sanyi yanzu ‘n’ a nan an ɗaure shi,

     Ƙamshi, m a nan a duba shi kan shi,

     Babba daddage dafaffe tirƙashi!

      Gaggawa da gardama gaggautawa.

    201. Shi ɗaurin baƙi muna da misalin shi,

    Lura da kyau idan baƙi an ɗaure shi,

    Ba wasali gabansa mai iya motsa shi,

    Kuma buɗaɗɗiyar gaɓa ce ya rufe shi,

      Ba ‘yanci garai ba don bai motsawa.

     

    Ɗaurin Harafin ‘n’ A Ƙarshen Gaɓa

     

    202. Sautin ‘n’ yana da tsari bar kushe,

     Ɗauri za ya wanzu can a gaɓar ƙarshe,

     In an ɗauri ‘n’, ka gan ta a can tarshe,

    To sanya ta, kar ka sauya ta a ƙarshe,

      Ba ta sauyuwa wajen lafazantarwa.

     

    203. Faɗi kalmar da ‘n’ takan zo ga rubutu,

     Za ka ji ‘n’ kake faɗi kuma ta furtu,

     To lura idan ka zo muhalli na rubutu,

    Haka nan za a sa ta ko da a rubutu,

      Ba ta sauyuwa ga tsarin zanawa.

     

    204. Malam yanzu duba tsari na waɗancan,

    In nuni kakai ka ce wannan, wancan,

     Haka nan za ka sa wurin zana waɗancan,

     Wanda ka wanga aiki fa yana can,

    Da waɗannan, waɗanga can masu matsawa.

     

    205. A misalan da sun ka zo dai ka kiyaye,

    Ɗaurin ‘n’ ya wanzu kullum ka kiyaye,

    Lura gaɓaɓuwan akwai ‘n’ ciki saye,

    Ko haka nan, walau da nan, duk ka kiyaye,

      Harafin ‘n’ da ke a nan bai juyawa.

     

    206. Nan ba za ka ce da wannan wannam ba,

     Doka ba ta yarda sanya waɗancam ba,

     Haka ma bai kamata zana waɗannam ba,

     In ma haka nam ka sa kure ne kuma babba,

      Balle cam da nam abin bai dacewa.

     

    207. Don haka duk kuren rubutu bari daina,

    Da waɗannam bale waɗancam duk daina,

    Ba a rubuta ‘m’ muhallin ga kure na,

    ‘n’ aka so ta zo muhallin ɗaurin ‘n’

      Ba a sauya ‘n’ da ‘m’ ga rubutawa.

     

    208. In an ɗauri ‘n’ ka sa daina hasashe,

    Ba canza ta, babu mai cewa kwashe,

    Sa ta a inda an ka so je tafi toshe,

    Matuƙar ta fito ga ɗauri kuma ƙarshe,

      Ba a taɓin ta nan wurin ko farawa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.