TAMBAYA (39)❓
Dan Allah
inaso a taimaka ayi write up mai dumi akan mata masu Neman yan uwasu mata wllh
kazantar ta yi yawa takai har basajin kunyar bayyana kansu a cikin jamaa.
Menene hukuncinsu (Daga: Abu Said BUK)
AMSA ❗
Innalillahi
wainna ilaihirrajiun
Rashin kunyar
bayyana kansu a cikin jama'a yanada nasaba da raguwar imaninsu, kuma daman ya
tabbata a hadisin Abu Hurairah RA ya ce ma'aiki SAW ya ce mutumin da yake
aikata zina ana a cire masa imaninsa ne, imanin zai dinga yawo a saman kansa
kamar hadari, bayan ya gama zinar sai imaninnasa ya dawo jikinsa (Abu Dawud da
al-Hakim suka rawaitoshi, Shaikh Albani ya ingantashi a cikin Silsila Ahadis-Assahiha
mai lambata 509)
Lesbianism ga
mata wadda ake kira da madigo da hausa basada banbanci da Homosexuality ga maza
wato Luwadi halayyar wasu daga cikin mutanen Annabi Lud AS, jinsi ne kawai ya
banbantasu amman sun kasance daga cikin manyan alkaba'ir wadanda kan iya zama
silar salwantar imanin mai aikatawa idan bai tuba ba, a karshe a tashi mutum
cikin al'ummar Annabi Lud AS wadanda Allah ya hallakar
A binciken da
nayi kwanannan naga wasu Archeologist (masana tarihin ragowar kasa da abin da
ta kunsa tun zamanin da) sun gano wani gunki mai suffar mace a garin da aka
halakar da mutanen Annabi Lud AS (Ana kiran wajen da "Dead Sea" wanda
yake a kasar Jordan) da sukayi bincike sai sukaga gunkin macen ya dace da abin
da ya faru a yankin shekaru dubunnai da suka gabata (Wallahu a'alam)
Allah SWT ya
sanardamu irin zunubin da mutanen Annabi Lud AS suke aikatawa na neman jinsi a
cikin Suratul A'araf ayata 80:
"Da Lũɗu, a lõkacin daya ce wa
mutãnensa: "Shin, kunã jẽ wa alfãsha, bãbu kõwa da ya gabãce ku da
ita daga halittu?"
81)
"Lalle ne ku, haƙĩƙa
kunã jẽ wa
maza da sha'awa, baicin mata; Ã'a, kũ mutãne ne maɓarnata."
82) "Kuma
bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa, fãce ɗai
suka ce: "Ku fitar da su daga alƙaryarku: lalle ne sũ, wasumutãne ne mãsu da'awar tsarki!"
83) "Sai
Muka tsĩrar da shi, shĩ da iyãlansa, fãce matarsa, ta kasance daga mãsu
wanzuwa"
84) "Kuma
Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa; Sai ka dũba yadda ãƙibar
mãsu laifi ta
kasance!"
Haka kuma
bayanin hallakar da tsohuwar (wato matar Annabi Lud AS) da kuma mutanensa ya zo
a cikin Suratu Ash-Shu'araa daga ayata 165 har zuwa ayata 175:
165)
"Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai?"
(Yana nufin kuna
luwadi ?)
166)
"Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku
mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa!"
167) Suka ce:
"Lalle ne haƙĩƙa
idan ba ka hanu ba, yã
Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa
daga waɗanda ake
fitarwa (daga gari)."
(Ya zama tilas
ga kowanne musulmi ya yi hani kuma ya qyamaci wannan ta'asa ta auren jinsi
kamar yanda Annabi Lud AS ya qi sa)
168) Ya ce:
"Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa,
inã daga mãsu ƙinsa."
169) "Ya
Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa."
170) Sabõda
haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya
( إِلَّا عَجُوزًا فِي الْغَابِرِينَ )
171) Fãce wata
tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa
(Wannan
tsohuwar ita ce matar Annabi Lud AS, wadda masu bincike suka gano gawarta a
suffar dutse wanda ke daukeda sinadarin gishiri a kasar Jordan. Wallahu a'alam)
172) Sa'an nan
kuma Muka darkãke wasu
173) Kuma Muka
yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda
ake yi wa gargaɗi ya
mũnana
174) Lalle ne
ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba
(To ammanfa
dukda haka idan sun tuba Allah mai Jin Kai Ne ga bayinSa kamar yanda ya rufe
labarin da:)
( وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ )
175) Kuma
lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa,
Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai
Hakama a cikin
addinin Judeo-Christian (Juda/Nasara) an haramta wannan babban laifi a cikin
littafin Genesis Surah ta 19 ayata 4 zuwa 11, a cikin labarin Sodom da Gomorrah
(mutanen Annabi Lud AS) sannan kuma Clement na Alexandria da Novatian ya kawo
qwararan hujjojin haramcin madigo da luwadi inda ya ce yana cikin al'adun
yahudawa qyamatar wasu dabbobi kamar irinsu zomo da weasel saboda nuna wasu
sababbin dabi'u ya yin jima'insu (ma'ana suna auren jinsinsu) to indai yahudawa
za su qyamaci dabba silar wannan mummunar dabi'a ta auren jinsi ai mu musulmai
ne mukafi cancanta mu tsani wannan kazamar dabi'a (Karin bayani yana cikin
littafin "World Of Homosexuality" ma'ana "Duniyar Yan
Luwadi" babin "Addini da Luwadi" shafi na 39, wallafar
shahararriyar Marubuciyar India, Shekuntala Devi)
Zanso mutane
su karanta daya littafin nata mai suna "World of Lesbianism" ma'ana
"Duniyar Yan Madigo"
Wasu sun mai
da abin sana'a wadda da ita suke ci suke sha harma su dinka sutura. ya yin da
wasu kuma shaidan ya qawata musu laifin a matsayin dabi'a, qwalamar son abin
duniya da kuma rashin kiyaye al'aura ke sa shaidan ya qawata musu zunubin a
matsayin dabi'a wadda yana wahala kaga mutum ya tuba, sai fa wanda Allah SWT ya
tseratar. Haka kuma yawan kallace-kallacen fina-finai yana taka muhimmiyar rawa
wajen fadawa tarkon zina, madugo da luwadi domin kuwa wasu abubuwan mostly anan
ake koyonsu. Addu'ar da Ma'aiki SAW ya roqa ta kada Allah ya halakarda
al'ummarsa kamar yanda ya halakar da na baya ita ce dalilin da ya sa har yanzu
Allah bai sa an halakar damu ba dukda cewar laifuffukan da mukeyi ma sun shafe
na al'ummar da suka gabacemu
Gashi mun
tsinci kanmu a wani zamani na hauhawar farashin komai da komai, to wannan
jarabawace kamar yanda Allah SWT ya fada a cikin Suratul Mulk ayata 2, kuma
idan mutum ya ci test din ya kiyaye hannunsa daga sata silar talauci, ya kiyaye
abin da ke tsakanin cinyoyinsa (farjinsa kamar yanda Allah ya fada a cikin
Suratul Mu'uminun ayata 5) dakuma abin da ke tsakanin lebbansa (wato harshensa,
Mu'uminun ayata 3) to Allah yana masa albishir da Aljannah (Mu'uminun ayata 10
zuwa 11) idan kuma masu kuɗi
sukai amfanida kudinsu wajen lalata mata da maza ta hanyar sakasu a wadancan
kazaman hanyoyi to saidai muce "Inna rabbaka labir mirsad" maana
"Allah yananan a madakata" yana jiran kowa. Zabi ya rage namu
Rashin ambaton
Allah shi ne dalilin dayasa muketa kidimewa, yanzu dai ka duba kaga mutane duk
sun daga hankali akan tashin farashin petrol, to idan Dajjal ya bayyana wanne
halin rikici za a kasance ke nan, kaga ai sai wanda Allah ya tserar kawai. Kuma
daga cikin yawan wadanda za su bi Dajjal a karon farko sune yahudawa 70,000
sannan kuma sai mata dayawa da kuma yayan da aka haifa ta hanyar zina wanda
kuma ya tabbata a cikin hadisin Abi Umamah Al-Bahili RA ya ce: Ma'aiki SAW ya
ce: "An nunamin a cikin mafarki na ana yiwa wasu maza da mata azaba a
cikin wani kwatami mai tsananin doyi, da na tambaya sai aka cemin ai wannan
mazinata ne" (Ibn Khuzaima lambata 1986 da Ibn Hibban da wasunsu sannan
Nasiruddin Albani ya ingantashi a cikin Sahihut Targhib lambata 991)
A kula: Wannan
fa makomar mazinata ke nan wadanda ba su tuba ba, ina kuma ga makomar masu
luwadi da madigo ?
A shawarce ina
son nayi amfanida wannan damar wajen janyo hankalin iyayenmu da kuma malamai
akan su daina amfanida littafin "Queen Primer" Part II wajen koyar da
yayansu na Nursery da Primary domin kuwa manufar mawallafan wannan littafin
(Nelson Publishers Limited) shi ne su koyawa yayanmu musulmai aqidar auren
jinsi (Homosexuality, Lesbianism da ake kirada LGBTQ). A shafi na 5 cikin littafin
sun rubuta "Let us be gay. Let us run" ma'ana "Mu zamo gay. Mu
gudu". Sai kuma shafi na 22 inda suka rubuta "Is this the way. Yes,
let us be gay" ma'ana "Wannan ce hanyar. Eh, mu zamo gay"
(Wal'iyazubillah). Silar hakan tuni gwamnatin jihar kano ta umarci malaman
Nursery da Primary da su gaggauta dakatarda amfani da irin wannan littafin da
makamantanshi wajen koyarda yayanmu yaren English
Hakama a
hanasu kallace-kallacen Tom & Jerry domin kuwa akwai bincike mai zaman
kansa da nayi wanda babu lokacin fayya ceshi anan. Sannan kuma a hana yara
amfanida Games irinsu Subway Surfers wadda itama a hankali a hankali sun fara
bayyana manufarsu ta auren jinsi ta hanyar updating game din da wata sabuwar
fuska mai suna "Rain" yar jihar New York da ke Amurka mai sanye da
kaya launukan bakan gizo (Rainbow) wanda daman shi ne alamar masu aqidar auren
jinsi (LGBTQ). Na bibiyi posting dinsu inda sukace "Subway Surfers da
hadin gwiwar LGBTQ da kungiyar taimakon marayu na muku maraba da sabon
tsarinsu". Sun saka kungiyar taimakon marayune saboda yawancin marayu
sunada naqasu da kuma neman taimako na gaggawa musamman idan akwai qarancin
fahimtar addini a taredasu. Kumadai munsan yanda wannan Game ta Subway Surfers
ta samu karbuwa sosai. Saidai muce Allah ya tsare mana imaninmu baki daya
A karshe ina
mai bawa kaina shawara da kuma masu karanta wannan sako da ma sauran musulmi
baki daya, da mu yawaita istighfari, sannan mu yawaita halartar karatuttukan
addini ko don samun bonanzan taka fuka-fukan mala'ikun rahama, zanso mu nemi
littafin "Adabul Mufrad" wallafar Imam Al-Bukhari, mu karanta
littafin "Talbis Iblis" wallafar Ibn Al-Qayyim dalibin Ibn Taimiyya
kuma mahaifi a wajen Ibn Khathir, a littafin zakagane yanda Iblis yake danawa
musulmai tarko, kai har malamai ma bai barsu a bayaba
Sannan mu
karanta littafin "Zaadul Ma'ad" wato "Guzurin Alqiyama" na
Ibn Al-Qayyim" domin kuwa ko sanda aka sakani makarantar boarding saida
aka hadani da Provision (Guzuri) ballantana kuma zuwa Lahira, tabbas ita
yakamata a hadawa guzuri tun da zuwanta ya zama dole
Ku tayamu yada
wannan saqo, Allah kadai ya san adadin mutanen da za ka zama silar shiriyarsu
Amsawa
Usman Danliti
Mato, (Usmannoor_As-salafy)
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.