Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halatta Mace Ta Auri Wanda Ya Taɓa Yin Zina Da Ita?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalam alaikum malam ina gajiya ya aiki, malam na kasance shekararmu 4 da saurayina muna biyewa san zuciya muna aikata saɓon ALLAH watau (zina) acikin hakan har Takai ga munyi ciki yana wata 2 sai muka zubar toh ahalin yanzu mun tuba har za muyi aure mallam yaya matsayin auren mu yake? kuma ALLAH zai karɓi tuban mu?? wlh mallam bada san raina hakan tadinga faruwa ba, duk sanda za muyi nakoma gida sau naita kuka ina nadama.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Hakika kun aikata babban kuskure, domin zina ita ce laifi mafi girma acikin kaba'irori in banda shirka da kisan kai babu wani laifin da ya kaita girman azaba awajen Allah.

Amma kasancewar kinyi nadama bisa abin da kika aikata, ba shike nan ba. Akwai wasu abibuwan da suka wajabta gareki ki aikata domin cikar tubanki.

Misali wajibi ne ki yi istibra'i (jini uku domin tabbatar da tsarkake mahaifarki) Kuma ku nisanci juna sosai alokacin da kike cikin istibra'in kada ku kusanci juna ballantana har Shaiɗan ya sake ruɗarku.

Kada ku sake aikata wata haramtacciyar mu'amala. Ku hakura da junanku har sai bayan an daura muku aure. sannan daga cikin sharuddann tubanki akwai ɗaukar niyyar har abada ba zaki sake komawa cikin laifin ba. Sannan ki kaurace wa duk dalilan da za su kaiki zuwa ga wannan laifin.

Hakanan laifin zubar da cikin nan da kukayi, shi ma babban laifi ne. Amma mutukar kun tuba Allah zai yafe muku domin yana daga cikin siffofinsa tsarkaka cewa Shi mai gafara ne kuma mai rahama ga bayinsa.

Kuma niyyarku ta yin aure, abu ne mai kyau. Muna muku fatan Allah ya sa auren ya zama sanadiyyar shiriya da rabauta gareku, sannan ya zama sanadiyyar shafe dukkan kusakurenku na baya.

Sannan kuci gaba da gyara rayuwarku ta hanyar yawaita sauraron wa'azin Maluma, da neman ilimi da kokarin aiki dashi. Allah yana cewa :

لْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنْفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِنْ رَحْمَةِ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ ٣٥۝

Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi ɓarna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai." (Suratuz Zumar ayah ta 53).

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments