Ticker

6/recent/ticker-posts

Tun Da Nayi Aure Babu Kwanciyar Hankali Mijina Baya Gamsar Dani

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salamu Alaikum, Tun da na yi aure yau kusan shekaru huɗu da rabi ke nan, babu kwanciyar hankali: Mijin ba ya haihuwa. Ga rikicin dangin miji. Sannan bayan shekaru biyu da auren ya samu matsalar rashin ƙarfin iya gamsar da iyali. Kodayake daga baya ya ɗan samu sauƙi, amma dai a lokacin ya riga ya fita a raina, kuma ba ya iya gamsar da ni. Na kai kuka wurin iyayena amma sun gaza fahimta ta. Sun ɗauka wai na ƙi yi musu biyayya ne, alhali ni kuma ina cutuwa ne. Ina tunani a raina kamar in kai shi ƙara kotu. Na rasa yadda zan yi. Ku taimake ni, pls.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Matsalar rashin kwanciyar hankali, da rikicin dangin miji, wannan ana fama da shi kusan a kowane gida a wannan zamanin. Kuma mace ita take ɗaukar matakan da suka kamata yadda da sadda suka kamata a cikin hikima da kyautatawa da biyayya ga manya da tausaya wa ƙanana, bayan yawaita adduoi ga Ubangijin Halittu har ta ciwo kan alamura, ta warware su da izinin Allaah Mabuwayi Mai Iko.

Amma matsalar rashin haihuwa da rashin ƙarfin miji waɗanda suka kai ga har ya fice miki a rai, waɗannan ne muhimman matsalolin da ya wajaba a samo maganinsu, tare da matsalar gaza fahimta ko ganewa daga iyaye!

Da farko cutar rashin haihuwa iri-iri ce:

(1) Akwai wacce ake yin maganinta a wurin likitoci a asibiti, saboda asalinta matsala ce da ta shafi rashin lafiyar wani sashe daga cikin sassan jiki da ke kula da al’amuran haihuwa.

(2) Akwai wacce sai a wurin malamai masana harkar ruquya ta Sunnah ake samun maganinta, domin cutar tana da alaqa ce da shaiɗanun aljanu da mutane. Don haka, duk yadda aka yi bincike a asibiti da wuya a iya gano matsalar ma, balle a san maganinta.

(3) Sannan kuma akwai matsalar da dalilinta ba rashin lafiya ba ne. Haka nan kawai Allaah Ta’aala ya halicci wannan mutum: Allaah bai ƙaddara masa samun haihuwa ba. Ita dai maganinta sai a yawaita addu’o’i da tawali’u da ƙan-ƙan-da-kai ga Allaah, kamar dai na sama da ta gabata.

Haka kuma matsalar rashin ƙarfi: Ita ma akwai ta asibiti wacce idan likitoci suka bincika suna iya gano musabbabinta kuma su bayar da magunguna. Daga baya kuma a samu waraka da izinin Allaah Ta’aala.

Akwai kuma matsalar da sai malaman ruquya suke iya gano ta kuma su bayar da maganinta. Kuma in aka dace sai ka ga an samu waraka, da izinin Allaah Ubangijin Halittu.

Idan aka gano matsalar kafin aure, wajibi ne a sanar da mai nema ko wacce ake nema tun nesa-da-ƙofa, don kar ya zama an yaudare shi an cuce shi. Idan kuwa aka ƙi yin hakan, to daga baya alƙali na iya ɗaukar matakin horo ga wanda ko waɗanda suka ɓoye wannan irin aibun, suka cutar da musulmi.

Amma idan ba a san da matsalar ba sai a bayan aure, kamar irin wannan matsalar (ta rashin ƙarfin iya biyan buƙatar mata), to abin da ake yi a sharia, in ji malamai shi ne: Sai alƙali ya bai wa mijin damar neman magani na tsawon shekara guda. Idan aka dace shike nan, idan kuma ba a dace ba to sai a raba auren kawai, idan abokin zaman auren ya yarda. Haka Abdur-Razzaaq da Ibn Abi-Shaibah suka riwaito daga Ibn Mas’uud (Radiyal Laahu Anhu) kuma Al-Albaaniy ya inganta shi a cikin Al-Irwaa’u: 1911 , sannan kuma ba a san wanda ya saɓa masa daga cikin Sahabbai ba.

Sai dai wannan yana ga mijin da ba ya iya saduwa ne kwata-kwata. Amma wanda ya ke da matsalar rauni ko rashin ƙarfin gaba, ta yadda yana iya saduwar amma dai ba ya iya gamsar da matar ce, a kan wannan malamai irin su As-Shaikh Ibn Al-Uthaimeen (Rahimahul Laah) sun ce, shi ba daidai ya ke da wanda ba ya iya saduwar kwata-kwata ba. (As-Sharhul Mumti’u)

Don haka, wajibin iyaye a nan shi ne: Su kalli girman matsalar da damuwar da ’yarsu take ciki, ba irin abin da suke tsammanin aukuwarsa na faɗuwar girma ko zubar mutuncin gidansu ba. Su ɗauki matakin taimaka mata, gudun kar ta faɗa a cikin hallaka. Su zurfafa bincike a cikin wannan al’amarin da idanun basira: Idanun da suka goge a cikin fahimtar yanayin rayuwar matasan yau da hikimominsu da dabarbarunsu. Idan an gano gaskiyar matsalar, cewa mijin ba ya iya saduwa da matarsa, to babu wani laifi a shari’a idan manya suka zauna suka warware wannan auren, kamar yadda da ma can zama suka yi suka ɗaura shi.

A nan ba sai an kai ga shiga kotu ba, balle wani ya ji ko ya ga an tozarta shi, ko an wulaƙanta shi, sai dai in ya zama dole.

Sannan ita kuma matar aure wajibinta shi ne: Ta yi taka-tsantsan da duk abin da ya shafi miji ko iyayenta. Kar ta yi gaggawar bijire musu, da ɗaukar matakin saɓa musu. Yawanci wannan ba ya haifar da ɗa-mai-ido.

Ta bi su a hankali cikin hikima da ladabi da biyayya da addu’a har Allaah ya sa su fahimce ta, kuma har buƙatarta ta biya. Sai a lokacin da alamuran suka kai Laa haula Walaa Quwwata ne, ko kuma suka zama Maa laa budda ne, sannan ake ɗaukar matakin rabuwa. Ko a nan ɗin ma iyayen ne dai suke wucewa gaba.

Sannan kuma ta sani cewa: Ba duk abin da mutum yake tsammani ne yake zama daidai ba. Me yiwuwa matsalar rashin gamsuwa da mijinki da kike kuka da shi, ba daga mijin ba ne, daga wurinki ne. Kuma bincike ne kawai zai iya tabbatarwa.

Me yiwuwa kuma babu laifin komai daga wurinki ko daga wurin mijinki. Tunanin zuciya ne kawai ke hana samun natsuwar rai da samun gamsuwar.

Dole ki amince cewa: Samun cikakken natsuwa da farin ciki da jin daɗi da gamsasshiyar biyan buƙata ga musulmi sai a Gidan Aljannah. Wannan wataƙila shi ne manufar iyayenki a irin matsayinsu da suka ɗauka. Don haka, ta yi haƙurin rage ƙarfin ƙiyayyar da ta shiga cikin zuciyarta dangane da halin mijinta. Ta amince da shi idan aka samu maganin da ya warware matsalarsa. Domin kamar yadda suke cewa ne: Da sabon gini gwanda yaɓe !

Yanzu idan kika rabu da wannan mijin ba da dalili ƙwaƙƙwara na sharia ba, wane yaƙinin kike da shi cewa wani mijin da za ki aura a bayansa ba zai zama mai irin wannan matsalar ba ne, ko kuma mai matsalar ma da ta fi ta wannan ɗin?!

A taƙaice dai, wajibi ne matasan musulmi su riƙa juriya da bin abubuwa a cikin rayuwa sannu-sannu cikin natsuwa da lura, tare da ɗaukar shawarwarin manya daga cikin iyaye da malamai da sauran masana a cikin al’amuransu, don taimakawa ga samun ingantattun hanyoyin warwarewa ga matsalolinsu.

Allaah ya taimake mu. Ya ƙara gyara mana gidajen aurenmu.

 WALLAHU A'ALAM

Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments