In kin Karanta ki yi sharing please
Tun da dare ya raba Khairi ta dasa kuka, gajiya da rarrashinta da Mum ta yi ya sa ta ɗauke ta takaiwa Hafsa wadda ke bacci, kukan Kairin ya tashe ta, Mum ta ɗora mata ita a cinya tare da ficewa daga ɗakin.
Ko dan Hafsan
ce ta ɗauko ta daga
gidan Kakannin ta oho anma Hafsan na kunna fitila ta kalle ta sai ta yi shiru
wannan ya sa Hafsan miƙewa ya haɗo
mata abincin ta sannan ta ba ta ta goya ta, ta jima tana jijjigata kafin ta yi
bacci, kwantar da ita ta yi kafin ta samu itama ta kwanta.
Huɗu saura Khairi ta tashi ta
hau kuka, Hafsa na hanma ta miƙe ta kuma ba ta abinci sannan ta goya sa
sai dai taƙi
bacci, haka ta sauke ta yarinyar ta hau wasanta ya yin da Hafsan ke gyangyaɗi.
Gari na wayewa
Hafsa ta shirya itakam ba za ta iya ba gidan Yaya Sadik za ta ta yi Bacci,
wanka ma a toilet din falo ta yi dan khairi na Bacci ba ta son ta tashi Mum ta
ce ba za ta ba.
*****
A kwance ya
same ta tana daddana waya. Kamar ba zai magana ba, har ya wuce sai dai hango
tulin kayan abincin da suka ci jiya da daddare akan dining table har yanzu ba
ta ɗauke ba ballantana
a yi batun wankewa ya sa shi kallon Lokaci cike da takaici, uku saura idanun sa
suka gane masa. Sake kallonta ya yi yaga yadda tasha kwalliya kamar ba gobe,
jewelries dinta ma duk sunyi matching da kayan da tasa, A kallon farko ta yi
bala’in burge shi don son kwalliyarta na daga dalilan da ya sa ya aure ta,
wannan ya sa bacin ransa game da kwanukan ya yi sauƙi.
“Ameerah!” Ya
faɗa muryar sa cike da
emotions din da ba ma zai tantance me yake ji a lokacin ba. A hankali ta dago
ta kalle shi kafin ta mai da hankalinta kan wayar.
“Haba Ameerah,
this is not right. Kalli gidan ki fa!” ba ta fuska ta yi a ranta tana cewa
yanzu zai fara wannan faɗan
nasa mara amfani yabi ya cika min kunne.
“Oh
sweetheart…” ta fada a shagwabe lokacin da take ƙoƙarin ta shi zaune duk da ba ta ajiye
wayar ba amma hankalinta na kan shi.
Sai da taga
yana kallon ta sannan ta haɗe
hannu. “Ban san me ya sa kai baka fara kallon abu me kyau ba kafin ka nemo
lefi. Look at me, duk kwalliyar nan taka ce! Da a ce na tsaya wani wanke wanke
i would have wasted alot of my time… wannan kwalliyar sam ba zan samu lokacin
yinta ba.”
Cike da rashin
sanin abun fada ya shafa fuskarsa sannan ya nemi wajen zama.
“You can
always manage your time Ameerah. Idan kika tashi da wuri ki ka gama da aikin
gidan kikayi kwalliyar you have all the day to press your phone. Wallahi ana
shigowa falon nan tsamin miya ake ji.” Ya fada yana mikewa don da ganin yanayin
fuskarta ma ba za ta ba shi amsa me dadin ji ba.
Dining din ya
nufa ya kwashe kwanukan sannan ya yi kitchen dasu. Ko da ya shiga kitchen dinma
sai ya ji kunya ta kama shi saboda kurar da ya yi ga wani wari da yake tashi
sama sama. buɗe fridge
ya yi ya ga vegetables din ciki sun rube. A take ran sa ya baci sosai. Ya
tsaya, ya zaga, ya juya, ya tsaya ya rasa ta inda zai kamo lamarin. Sai kawai
ya yi tsaki ya fita.
“Okay okay ki
taso muyi aikin nan don wallahi saura kadan dai gidan nan ya zama bola. Ki zo
muyi aikin, i have something for you. Very special!” ya yi winking a karshe
yana kakaro murmushin karfin hali ya yaba a fuskar sa. Tana magana kasa kasa ta
taso ba da son ranta ba.
Rahina fa za
ta zo ta yi anjima…” bai tsaya jinta ba yaja hannunta sukayi kitchen din. nade
hannun rigaarsa ya yi, inda ya kaɗa
kumfa, malama ina wankewa kina ɗaurayewa,
ya faɗa lokacin da hau
kiciniyar wanke kofi, tsai kawai ta yi da idon ta kansa ita kam ba ta shirya taɓa ruwa yanzu ba amma tasa
in ta yi magana faɗa
zai yi, wayarsa da ta yi ringing ya da shi jan tsaki hannun sa ya fara gogewa
da towel kafin ya zaro ta.
“Toh.” Kawai
ya ce sannan ya nufi kofa ta bi shi da ido cike da murnar Allah ya cece ta ba
zatai wanke wanken nan ba.
Bai jima ba
sai gashi sun shigo da Hafsah wadda ke faman surutu "ashe ma kana gida ai
Allah ne ya ci dani da har nace bazanzo yanzu ba sai dare momy ta
takuramun" kallon ta ya yi tare da watsa mata ‘yar ƙaramar
harara aiko fita zan yi kima sa a ranki baki ganni ba, haka kawai sai yarinya ƙarama
ta dinga damfara ta, ya faɗa
da sigar wasa" hirar da suka shigo suna yi ke nan, Ameerah na hango Hafsa
fita a guje ta rungume ta.
“I miss you so
much Hafsy!” Ta fada tana murmushi.
Hafsahn ta yi
dariya. “ Anya kuwa Anti Amira ni kikai missing?" Hafsan ta faɗa tana dariya.
"Koma dai
mai zaki ce ni na san ke na yi missing, yanzun ma Allah ne ya debe ni ya san na
yi missing ɗin ki ya
turo min ke, yayan ki bai son cin abincin Rahina Please ki taimaka kan ki tafi
ki dafa masa yau ban jin daɗi"
Amira ta faɗa tana ƙasa da
murya kmar mara lafiyar gaske.
"Yo to
mene marabar abincin nata da na Rahinar duk ƙazanta ce" Sadiq da ya fito da
alamar fita zai yi motsa jiki ya faɗa.
Dariya Hafsa
ta yi " eh na ji kuma yau dole a ci ƙazan tar ba, ni zuwa nayi ma in yi Bacci
wallahi Khairi ce ta hanani sukuni, ni ban kama da Maman ta ba, anma ta maƙale
mun" lakuce mata hanci ya yi " ba dole, au danma tana son ki, kike faɗar haka kamar a kunnen Yaya
Farida, in za ta tafi ki ɗauko
mata kuɗi a envelope a
saman drawer ya faɗa
kafin ya fice"
tsayawa Hafsah
ta yi tana kallon Ameerah sannan ta ce, “ba zaki je ki raka shi ba? Ke dan love
dinnan ma baki iya ba?”
Harara
Ameerahn ta watsa mata kafin ta yi wajen itama. Da kallo Hafsahn ta bi gidan
tana jin tsami tsami yana tashi sannan ta tabe baki amma still ba ta ga laifin
Ameerahn ba.
Kawai dai tana tunanin Ameerahn ta gaji ne. Tana
zaune, sai gashi ta shigo.
“Yauwa ko
kefa? Haka ake yi ai. Ko dan ki mallake yayana.” Ta fada cike da tsokana.
Wuri Ameerah
ta samu ta zauna sannan ta ce, “hnmm haushinsa fa nake ji. Duk jikina ciwo yake
saboda aikin gidan nan na samu daƙyar ya bari Rahina ke zuwa tayani shi ma
ya ce sai randa bazai wuni a gida ba, girki kuwa duk sanda ta yi sai ya gane ya
yi ta fada na rasa ya ake yake ganewa”
Da mamaki
Hafsah ta kalle ta. “Wai dama kana jin haushin wanda kake so? How is that
possible?” Ta tambaya saboda ita a ganinta in dai tana son mutum sosai ba za ta
taba jin haushin duk abun da zai yi mata ba musamman ma in kyakkyawa ne.
“Ke yarinya ce
har yanzu.” Inji Ameerah.
“Kai
Anty." Dariya Amira tasa "Umman mu ta ce za ta bawa Momy zaƙo nama
za ta shi kika kawom?"
"Au kinga
zan manta dalilin zuwan" Hafsa ta zaro ledar ta miƙa mata kafin ta miƙe mai
zan girka muku?"
Jingina sosai
Ameera ta yi da kujera "yau kitchen ɗin
naki ne ai kin ka fini sanin abin da yake so" ta faɗa lokacin da take ƙoƙarin saka pin ɗin wayar ta.
**
A gajiye ya
dawo ya tarar ba kowa a gidan saboda haka kawai duba bokitan da robobin ruwan
gidan ya yi yaga ba ruwa. Ya san yaran nan suna sane suka wuce islamiyya ba su cika
ba saboda Inna ta cika da kan ta. Haka ya shiga jan ruwan har sai da ya cika su
duk sannan ya debi ruwan wanka. Zafi ake sosai shi ya sa bai damu ma sai ya
kunna wutar dafa ruwan ba.
Ko da ya fito,
mai ya shafa sama sama, sai da ya ci ɗanwaken
sa da ya tarar an rufe masa a ɗakin
sa, sannan ya saka kayan sa ya fice don sunyi da abokan sa za su hadu a gidan
su Salisu. Kai tsaye gidan su Salisun ya nufa. Daga bakin kofar gidan Baban su
Salisun yana zaune da almajiransa suna ta karatu.
“Baba ina
wuni, ya kokari?” Ya gaishe shi yana durkusawa. Da fara’ar sa Baban ya amsa.
“Ya mutan
gidan Mu’utar?” Ya tambaya yana sake yaba hankalin yaron.
Bayan sun
gaisa ya nufi cikin gidan da sallama saboda Salisun ma dakinsa a cikin gida
yake ba a soro ba.
Umman su ce
zaune tana tankaɗe
garin tuwo. Ko da ya gaishe ta ba ta amsa ba.
“Umma ina
wuni.” Ya sake gaidata. Amma ta yi biris dashi. Jikinsa ya yi sanyi sai kawai
ya fice ya tsaya daga kofar gidan. Yana kallo Baban ya taso yana tambayarsa.
“Baba dama
wajen Salisu nazo.” Ya fada yana sosa keya. A boye Baban ya yi murmushi saboda
yana ganin yadda Mukhtar din ya yi ya san me dakinsa ce ta koro shi da hali.
Har yau abun dariya yake ba shi saboda yadda take kishi da mahaifiyarsu Mukhtar
din har ma da yaranta saboda kawai Baban ya taba nuna yana son Innar inda Innar
taki yarda da auren sam. Shekaru sama da goma ke nan amma ta kasa cire kishin
nan a ranta.
Shigewa Baba
ya yi ba tare da ya ce komai ba. “Sa’a sarautar mata, ta mallam Gambo!” Ya fara
mata kirari tun da ya lura da yanayinta.
Ganin cewa
watakila Salisun yana jin su ya sa ya daga murya, “kai Salisu, Mu’utar na jiran
ka a waje.” Ya fada yana daukar buta ya zagaya yana jinjina kishin matarsa duk
da sun tsufa.
Mukhtar ya yi nisa
a tunanin yadda zai ci gaba da harkokin sa tun da ya samu aikin nan Salisu ya
fito yana ta baza kamshin turare don kamshin ne ma ya dawo da Mukhtar hayyacin
sa.
“Haka dai,
kullum cikin tunani.” Abun da ya fara cewa ke nan wannan ya sa Mukhtar din
murmushi.
“Dan malam
yaki halin malam. Wannan kwalliyar fa?” Muktar ɗin
ya faɗa lokacin da ya ɗora idanun sa kan Salisun
Juyawa Salisun
ya yi alamun shi ya hadun nan sannan ya ce, “haba dan Allah kullum ka zo sai ka
tsaya anan kamar wani barawo sai ka ce baka san ɗakina
ba a cikin gidan.”
Mukhtar bai
amsa masa ba suka fara tafiya cikin layin.
“Toh ya ake
ciki ne mutumina. Ya aikin?” Ya tambaya bayan yaga alamar ba zai samu amsa ba.
“Komai normal,
Alhamdulillah ana ta ƙoƙari dai.”
“Toh Allah ya
taimaka amma ni kam Allah ya kiyaye nayi teaching kuma a private degree ne fa
dakai na BUK kuma. Kamar ni dai a ce nike da result ɗin a ce ina teaching Ina? Nooo…” inji Salisun
ya fada yana saka hannunsa a aljihu.
Murmushi
Muktar ya yi. Kai ai ɗan
gata ne kana da uba, ni kuwa wasu ke jira in samo in basu, ƙannena
fa huɗu aƙa
yanzu duk mata, in ban ba su ba ai bana ce su za su ban ba"
“Nima ɗin ai ba shi Malam ke min
komai ba kaima ka sani” Salisun ya faɗa
lokacin da yaɗan haɗe rai.
"Amma dai
shi ke ciyar ka ko?"
Banza Salisun
ya masa tare da yin gaba, iska Muktar ɗin
ya furzar kafin ya ɗan
ƙara
sauri ya taddo shi.
Shiru sukayi saboda kowa da kalar tunanin da
yake yi har suka isa majalisar tasu. Kamar ko yaushe in daya ya bawa daya
haushi sai su chanja wajen zama. Suna zama kuwa sauran abokanan nasu suka lura.
“Oh ku dai ba
kwa girma.”
Mukhtar ya ba
ta rai. “Bar sokon mana. Matar sa ta gamu da wahala, tun da har yanzu ya gaza
hankali ya gane a Nigeria ko me ka samu za ka haka za ka yi indai ba haram
bane”
Fusata Salisu ya
yi, " waye maras hankalin ai kai kasan ba hankali ka fini ba, ko dan kawai
mutane na fade kana da nutsuwa kake tsanmanin da gaske suke?"
Dafa shi
Muktar ya yi "sorry my guy wasa nake, yo banda abun ka ai abokin ɓarawo ɓarawo ne, abin da ya ni shi
ya yi ka, ko me nace kamar akaina nake faɗa"
Hararar sa
Salisu ya yi "Karka raina mun hankali fa"
Dariya Muktar
yasa, nan Salisu ya kuma ƙuluwa
Ibrahim ne
wanda ya ce “Haba guys, ya kuke mana haka ne? Please Muktar ka dena dariyar
haka" An danyi shiru ana tunanin topic din magana ke nan Mukhtar ya leka
gefen Salisu cike da zolaya ya ce,
“Kuma fa ka yi
kyau yau mutumina. Ya kamata Maryama taga kwalliyar nan ta yaba.”
Banza Salisu ya yi kaman bai ji ba.
Miƙewa
Muktar ya yi bari in je gida inason kwanciya da wuri sabida tashin safe, har ya
yi nisa ya ji Muryar Salisu tsayani zan je Gidan su Maryam suka jera tare suna
tafe suna hira tamkar ba sune sukai rikici ɗazun
ba ko da yake dama Salisu ne sarkin ruko shi Muktar da ya fahinci abin zai zama
faɗa zai mayar wasa in
kuma ya zama da anyi shike nan ya wuce.
Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.