Ticker

6/recent/ticker-posts

Taƙaitaccen Tarihin Waɗansu Makaɗan Baka

Idris Ɗangiwa Zuru da Mamman Sarkin Taushin Katsina daga Rini ta Bakura suka fito. Jatau Kamba daga Kanoma ya fito domin Jikan Sarkin Makaɗa Kada Kanoma ne, zuriyar su ɗaya da Makaɗa Mamman Tsogo Kanoma.

**

Musa Ɗanƙwairo Maradun daga Ɗankadu ta Ƙasar Bakura suka koma da zama a Maradun, a lokacin mulkin Sarkin Ƙayan Maradun Ibrahim I ( Sarkin Ƙaya Iro) wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1903 zuwa 1923.

**

Sa'idu Faru Ɗan Makaɗa Abubakar Mai Kotso (Abubakar Kusu) Ɗan Makaɗa Alu Mai Kurya kuma Ɗan Faru ta Ƙasar Maradun ne, anan aka haife shi a shekarar 1916.

**

Ibrahim Gurso Mutumen Mafara ne. Ibrahim Narambaɗa mutumen Tubali ta Gundumar Galadi a Masarautar Shinkafi ne.

**

Salihu Alasan Jankiɗi Ɗan Alasan Ɗan Tigari mai abun Kiɗi kuma mutumen Rawayya ta Ƙasar Bunguɗu ne.

**

Muhammadu Ɗankyana da Daɗi Jibiya da Auta Daɗi da Isah Ɗan Makaho da Makaɗa Kabsha duka yan Dolen Moriki ne dake Masarautar Moriki ta Jihar Zamfara duk zuriyar su ɗaya. Jikokin Makaɗa Bara Dolen Moriki ne.

**

Makaɗa Mamman Amali Mutumen Sububu dake Masarautar Maradun ne. Makaɗa Sani Sabulu mutumen Kanoma ta Masarautar Maru ne. Abu Ɗankurma duk da yake zuriyar su Makaɗa Gurso Mafara ne, a Maru ne aka haife shi.

**

Garba Mai Tandu shi da Garba Ɗan Duddu daga Shinkafi suka fito. Abubakar Amadu Kassu daga Kadawa Gundumar Magarya ta Masarautar Zurmi ya fito.

**

Makaɗa Muhammadu Dodo Mai Taushi da Ɗan shi Ɗan Dodo Alu Mai Taushi (Kundumi Magajin Ɗan Ɓaidu) da Amadu Mai Launi da Garba Mai Nakada da Musa Ɗan Biri da Bawa Yarkofoji da Abdun Inka Yarkofoji da Makaɗa Siddi da Garba Ɗan Diga Tumba da Makaɗa Dumbuje da Makaɗa Ɗungum duka Mutanen Kasar Bakura ne.

Makaɗa Garba Ɗan Wasa da Ɗan shi Zayyanu da Sani Ɗan Aino Gyalange da Buda Kaiwa da Musa Mai Komo Gayari mutunen Gummi ne.

**

Ɗan Shu'aibu Tungar Rini da Yahaya Sahunu da Magajin Zambuna da Ɗan Balade Morai da Abdu Ɗan Gunduwa Kagara mutunen Mafara ne.

**

Makaɗa Kutub'u Kawaye da Ƙanen shi Ƙwazo da aka fi sani da Kwazo Bagega da Sani Ɗan Baldo mutanen Anka duk da yake shi Sani Ɗan Baldo asalin shi daga Bakura ne.

**

Ibrahim da Musa da  Abubakar Ɗangulbi da Jibo Na kwakwai da Ibrahim Ɗan Tsuga mutanen Gwaram/Jangebe ta Ƙasar Mafara ne.

**

Ibrahim Ɗanƙurji Dosara /Mada, Hassan Wayam, Ɗan Zaki Ƙaya mutanen Maradun ne.

Makaɗa Buwai Shemori, Kaka Dawa da ɗiyan shi Sani da Babangida da Aliyu Gadanga (Kaftin) da Burgediya Tambai da Lawali Waziri da Tambai Shatan Duma da Makau Makaɗin Tauri da Husaini Sarkin Kotso da Sani Marafan Kiɗi Wanke da Mande Marafa mutanen Masarautar Gusau ne.

**

Makaɗa Ɗan Bawa Ƙaura, Makau Ƙaura, Dama Magizawa, Na Mai Kiɗi Magizawa da Murtala Dan Ali Banga, Ziti Kasuwar Daji daga Ƙaura Namoda.

**

Ibrahim Na Yankwale Tsanu, Ɗan Gusau Madobiya, Mamman Na Ta Ukka, Mande Sangamawa daga Zurmi.

**

Barau Na Dauran, Wakkala Gidan Kaso, Baban Daftan Nasarawa Mailayi, Dogo Nasarawa Mai Layi, Mai Turu, Bokan Marafa, Roƙo Torawa Makaɗin Yan Tauri, Makaɗa Sule, Mamman Mai Banga daga Birnin Magaji.

Daga Zauren:

Makaɗa Da Mawaƙa

Post a Comment

0 Comments