Sarkin Zamfaran Zurmi Alhaji Muhammad Bello Sulaiman

    Sarkin Zamfaran Zurmi Alhaji Muhammad Bello Sulaiman
    "Sarkin Zanhwara na Zurmi yac ce Shaho ya gurgusa ba shi iyawa" 
    In ji Makaɗa Abubakar Kassu Zurmi a taken ɗan tauri Ibrahim Shaho. Wannan shi ne Sarkin Zamfaran Zurmi  mai ci, wato Alhaji Muhammad Bello Sulaiman. Sai dai ban san wane Sarkin Zamfaran Zurmi bane ya yi zamani da Shaho.

    Haƙiƙa Honorable Alhaji Abdulaziz. Da Mahaifin wannan Sarkin ne Shaho ya yi zamani, watau Sarkin Zamfaran Zurmi, Suleimanu Muhammadu Sambo. Ya yi sarauta daga shekarar 1951 zuwa rasuwar shi a shekarar 1971/72.

    Bayan rasuwar shi sai aka naɗa ɗan shi(Ƙanen /Kanin wannan mai ci yanzu) Kabiru Suleiman Muhammadu Sambo wanda Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun ya yi ma Waƙar nan mai amshi "Kabiru jikan Muhammadu, ya ci fansar yan Uba... Bayan an cire Sarki Kabiru a shekarar 1975 /1976 sai aka naɗa Ƙanen /Kanin Mahaifin su, Muhammadu Mainasara ɗan Muhammadu Sambo wanda shi ma Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun ya yi mashi Waƙa mai amshi " Sarkin Zanhwara Mainasara, Ɗan Mamman namijin duniya", bayan rasuwar shi a cikin shekaru 2000 sai aka naɗa Ƙanen shi /Kanin shi Alhaji Abubakar Atiku Muhammadu Sambo wanda Garba Musa Ɗanƙwairo Maradun ya yi ma Waƙar da ban iya kawo ta, an cire shi a cikin 2022 sai aka naɗa wannan ɗa nasu mai ci yanzu, Alhaji Bello Suleiman Muhammadu Sambo.

    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
    Ɗanmadamin Birnin Magaji
    Imel: birninbagaji4040@gmail.com
    Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.