Hausar ‘Yan Lakum (Masu Tallen Magani) A Garin Gusau

    Kundin Digiri Na Farko (B.A HAUSA) Wanda Aka Gabatar A Sashen Nazarin Harsuna Da Al’adu, Tsangayar Fasaha,  Jami’ar Tarayya Gusau, Jahar Zamfara, YULI, 2023

    NAZARIN HAUSAR YAN LAKUM A GARIN GUSAU

    Na

    SABITU SANI

    Contact: 08038510879 


    AMINCEWA 

    Wannan kundin Bincike na SABITU SANI mai Lamba 1820104005, ya cika ƙa’idojin da aka shimfiɗa dangane da neman takardar shedar digirin farko (B.A Hausa) a Sashen Nazarin Harsuna da Al’adu  Jami’ar Tarayya Gusau.

     

    SADAUKARWA

    Na Sadaukar da wannan aiki ga mahaifana, Alhaji Muhammadu da Malama A’isha da kuma Malama Marwanatu Shehu da kuma Matata Malama Aina’u Suleiman, da Alhaji Mustapha Mudassir (Per-Master) da dukkanin sauran ‘yan uwana.

     

    GODIYA

    Dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijinmu mahalicci, Maɗaukakin Sarki, wanda shi ne ya ba da damar gudanar da wannan bincike, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) fiyayyen halitta da iyalan gidansa da sahabbansa da kuma magabata, tare da mutanen kirki da suka duƙufa wurin ba da ilimi ga al’umma.

    Ina amfani da wannan damar domin miƙa godiyata ga mahaifina da fatar Allah ya jiƙansu da Rahama, haka kuma ina mika godiya ta ga malamina kamar Dr. Adamu Rabi’u Bakura da Malam Abu Ubaida Sani, da Muhammad Arabi, da Malam Isa Sarkin Fada, da Mal. Musa Abdullahi da sauran ɗaukacin malamaina tun daga ajin farko har zuwa na ƙarshe. Ina kuma godiya ga dukkanin waɗanda suka ba da gudummawa a wurin karatuna da kuma wannan aiki, musamman maigidana Alh. Mustapha Mudassir (Per-Master) wanda ya taka rawa ta musamman a wannan karatu nawa.

    Daga ƙarshe ina miƙa godiya ta ga abokanan karatuna kamar Hajiya Rukayya Yusuf S/Fada, Zainab Abdulkadir da Muhammad Yahaya da sauran su, da fatar Allah ya sa wannan karatu ya amfani al’umma baki ɗaya.

     

    TSAKURE

    A duk lokacin da aka samu waɗansu mutane sun keɓe kansu a wani muhalli na daban, akasari a kan samu wanzuwar wani karin harshe na rukuni wanda ya keɓenta ga waɗannan mutane kawai. Duba da wannan ne ya sa aka gudanar da wannan bincike na Nazarin Hausar ‘Yan Lakum a garin Gusau. Wannan bincike mai taken Nazarin Hausar ‘Yanlakum bincike ne da ya zaƙulo sabbin kalmomi da jimloli da “Yanlakum suka samar a rukuninsu. Sannan binciken ya gano hanyoyin da ‘Yan Lakum suka yi amfani da su yayin samar da waɗannan kalmomin nasu. Baya ga wannan bincike ya kawo wasu daga cikin dabarun da ‘Yan Lakum suke yi a lokacin da suke aiwatar da aikinsu na sana’ar Lakum. Sannan daga ƙarshe aka zo da shawarwari ga ɗalibai da masana da attajirai da ma ɗaukacin al’umma gaba ɗaya.

     

    ƘUNSHIYA

    i. Amicewa   -- iii

    ii. Sadaukarwa  -- -- iv

    iii. Godiya -  -- - -- v

    iv. Tsakure-  -- - -- vi

    v. Ƙunshiya -- -- viii

     

    BABI NA ƊAYA: Gabatarwa

    1.0 Shimfiɗa -- -- 1

    1.1 Manufar Bincike --  -- - -- 4

    1.2 Farfajiyar Bincike - -- 5

    1.3 Hasashen Bincike --  -- - -- 5

    1.4 Matsalolin Bincike --  -- - -- 6

    1.5 Muhimmancin Bincike --  -- 8

    1.6 Hanyoyin Gudanar da Bincike  10

    1.7 Ra’in Bincike --  -- - -- 11

    1.8 Naɗewa -  -- -- 13

    BABI NA BIYU: Bitar Ayyukan da Suka Gabata

    2.1 Bitar Ayyukan da suka Gabata  14

    2.1.1 Bugaggun Littafai --  -- 15

    2.1.2 Kundayen Bincike--  -- 19

    2.1.3 Muƙalu da Mujallu --  -- 28

    2.2 Hujjar Cigaba da Aikin Bincike  39

    2.3 Naɗewa -- -- 44

    BABI NA UKU: Fashin Baƙi a Kan Ma’anonin Shafi Taken Bincike

    3.0 Shimfiɗa--  -- - --  -- 45

    3.1 Ma’anar Nazari    -- - -- 45

    3.2 Ma’anar Kalmar Hausa --  -- 46

    3.3 Ma’anar Kalmar Lakum ko ‘Yan Lakum -  -- -- 50

    3.2 Kashe – Kashen ‘Yan Lakum - -- 51

    3.3 Wasu Daga cikin Dabarun ‘Yan Lakum  --  -- - -- 53

    3.4 Badali  -- -- - -- 54

    3.5 Amayo Allurai da fyatosu ta hanci   -- -- 54

    3.6 Tayar da Hayaƙi   -- - -- 55

    3.7 Yanka Wuƙa a jiki--  -- - -- 55

    3.8 Tayar da Wuta --  -- - -- 56

    3.9 Naɗewa -- -- 58

     

    BABI NA HUƊU: Hausar ‘Yan Lakum a Garin Gusau

    4.0 Shimfiɗa -- -- 59

    4.1 Taƙaitaccen Tarihin Garin Gusau  59

    4.2 Hausar ‘Yan Lakum A Garin Gusau -  --  -- -        - -- 65

    4.3 Sunayen Kuɗi a wurin ‘Yan Lakum -  --  -- -        - -- 65

    4.4 Kalmomi ta hanyar ƙirƙira       - -- 67

    4.5 Kalmomi ta hanyar kwatance da siffantawa-  ---- 68

    4.6 Kalmomi ta hanyar aro    -- -- -       - --  -- 70

    4.7 Kalmomi ta hanyar gusar da ma’ana -  --  -- -        -- 72

    4.8 Jimlolin ‘Yan Lakum-- - -- 74

    4.9 Naɗewa--  -- -       - --  -- 76

    BABI NA BIYAR : Sakamakon Bincike

    5.0 Shimfiɗa--  -- -      - --  -- 77

    5.1 Sakamakon Bincike --        -- 77

    5.2 Shawarwari--  -- -      -- - -- 79

    5.3 Naɗewa--  -- -      -- - -- 81

    Manazarta    -- - --  -     -- - -- 84


    GABATARWA

    1.0 SHIMFIƊA

    Wannan aiki mai taken “Nazarin Hausar ‘Yan Lakum a Garin Gusau” bincike ne da ya yi ƙoƙarin binciko yadda ‘Yan Lakum (Masu Wa’azin Turmi) a garin Gusau su ke yin Hausar su domin sadarwa a tsakanin su da juna.

    Wannan nazari ne da ya danganci ilimin walwalar harshe, kuma zai mayar da hankali a kan Karin harshen rukuni, wanda ya shafi Hausar ‘Yan Lakum ta fuskar sara a wajen mu’amala ta sadarwa tsakaninsu da juna ko da sauran jama’a.

    Wannan gabatarwar ita ce fitila wadda ta haskaka dukkan abin da ya wakana a cikin wannan kundin bincike, domin ita ce ke ɗauke da dukkan tubalan ginin wannan aiki.

    Domin samun sauƙin gudanar da wannan aiki, an tsara wannan aiki a kan tsarin babi-babi, tun daga babi na ɗaya har zuwa babi na biyar.

    A babi na ɗaya an yi tsokaci a kan manufar wannan bincike da farfajiyar bincike da hasashen bincike, da matsalolin bincike, da muhimmancin bincike da hanyoyin gudanar da bincike, da ra’in bincike, sai kuma aka zo da naɗewa a ƙarshen babin.

    A babi na biyu, mai kanun bitar ayukkan da suka gabata, bayan an yi shimfiɗa, sai bitar ayukkan da suka gabata, am fara da rubutattun littafai, sai kundayen bincike da aka rubuta a matakai daban daban na ilimi, sai kuma maƙalu da mujallu, duka dai masu nasaba da kuma alaƙa da wannan bincike, sai kuma hujjar cigaba da bincike, daga ƙarshe aka zo da naɗewa.

    Babi na uku, mai kanun fashin baƙi a kan ma’anonin da suka shafi taken bincike, bayan an yi shimfiɗa, an kawo ma’anar kalmar Hausa, da ta Lakum da kuma ‘Yan Lakum, sannan an kawo kashe kashen ‘Yan Lakum daga nan kuma aka zo da wasu daga cikin dabarum ‘Yan Lakum sai kuma naɗewa.

    Babi na huɗu, mai kanun Hausar ‘Yan Lakum a garin Gusau, an fara da shimfiɗa, taƙaitaccen tarihin Garin Gusau, Hausar ‘Yan Lakum a garin Gusau, an kawo kalmomin da ‘yan Lakum suka samar a wannan rukuni nasu, an kasa kalmomin ta la’akari da dubarar da aka yi amfani da ita ko hanyar da aka bi yayin samar da waɗannan kalmomi na ‘Yan Lakum, bayan nan aka kawo yankunan jimloli, da kuma jimlolin Hausar ‘Yan Lakum daga ƙarshe aka zo da naɗewa

    A babi na biyar, mai kanun sakamakon bincike, bayan an yi shimfiɗa, sai aka kawo sakamakon bincike, daga nan kuma aka zo da shawarwari, sai kuma jawabin naɗewa da kuma manazarta.


    BABI NA ƊAYA

    1.0 SHIMFIƊA

    Wannan babi na ɗaya za a yi magana a kan manufar wannan bincike, da farfajiya ko kadadar bincike, da hasashen bincike, da matsalolin bincike, da muhimmancin bincike da hanyoyin gudanar da bincike da ra’in bincike, sai kuma daga ƙarshe a zo da naɗewa.

     1.1 MANUFAR BINCIKE

    A rayuwa babu wani abu da za a aiwatar ba tare da wata manufa ba, saboda haka wannan bincike ko nazari an gudanar da shi domin cimma wasu manufofi kamar haka:

    1)      Zaƙulo keɓantattun kalmomin da 'Yan Lakum suka ƙirƙira kuma suke amfani da su a zantukansu na yau da kullun.

    2)      Gano hanyoyi ko dabarun da suke bi ko amfani da su yayin ƙirƙira waɗannan kalmomi nasu na fannu.

    3)      Zaƙulo sabbin jumloli da kuma yankunan jimlolin da suka samar daga waɗannan kalmomi nasu kuma suke amfani da su a lokacin sadarwa tsakaninsu.

    1.2 FARFAJIYAR BINCIKE

    Kasancewar harshen Hausa yana da manyan rassa uku na nazari waɗanda suka kunshi:

    a. Adabi (literature),

    b. Al’ada (culture)

    c. Da kuma harshe (language).

    Wannan bincike an gudanar da shi ne a ɓangaren harshe, wanda ya kebanta a fannin ilimin walwalar harshe.  Hasali ma an keɓance binciken a cikin  garin Gusau kacokam, musamman yankin birnin ruwa a Gundumar Mayana inda nan ne yawancin masu wannan sana’a ta lakum su ka fi yawaita.

     

    1.3 HASASHEN BINCIKE

    Kasancewar kusan kowane rukunonin al’umma sukan keɓanta da Karin harshensu, domin sadarwa a tsakaninsu, ana hasashen su ma rukunin masu sana’ar lakum ya amsa sunansa na rukuni, ya zamana suna da:

    v  Kalmomi nasu na fannu da suka ƙirƙira kuma suke amfani da su tsakaninsu da juna.

    v  Hanyoyi ko dubaru da suke bi ko amfani da su wajen samar da waɗannan kalmomi nasu.

    v  Jimloli da kuma yankunan jimloli da suka ƙirƙira sanan kuma suke amfani da su yayin sadarwa da junansu.

     

    1.4 MATSALOLIN BINCIKE

    A kowane irin al'amari na rayuwa da ake gudanarwa ba a rasa cin karo da 'yan matsaloli nan da can ba, musamman a lokacin da ake gudanar da shi. Don haka, a yayin aiwatar da wannan binciken an haɗu da wasu 'yan matsaloli da ƙalubalai. Kaɗan daga cikinsu akwai:

    «  Matsalar masu gida rana (kuɗi)

    Babu shakka, wannan matsala ta kuɗi babbar matsala ce da take ci wa al'umma tuwo a ƙwarya musamman mara sa ƙarfi (talakawa) kasancewar wannan zamani komai sai da kudi. Lalle wannan matsalar ta kawo cikas sosai yayin gudanar da wannan bincike, musamman ga dalibai irin mu da ba su da isasshen lokacin neman na kansu, sannan ga shi komai ya yi tsada.

    «  Rashin isassun kayan aiki

    An samu matsalar rashin littatafai da maƙalu da kuma kundayen bincike waɗanda suka yi magana kai tsaye a kan Hausar masu sana'ar lakum (wa'azin turmi) a wani gari, bisa ga dukkan alamu wannan ne karon farko da aka fara gabatar da bincike a kan wannan ɓangaren hakan ya haifar da wahalhalu masu tarin yawa wurin samun bayanai.

    «  Rashin samun haɗin kan waɗanda bincike ya shafa.

    Wannan ma wani babban ƙalubale ne da aka fuskanta, yayin tattara bayayanan wannan bincike, domin waɗansu mutanen ba su bayar da amsa idan an tambaye su, saboda suna tunanin za a ɗauki sirrinsu a yaɗa wa duniya. Wannan matsalar ta kawo tarnaki ainun a lokacin da ake gudanar da wannan bincike.

    A takaice dai, waɗannan su ne kaɗan daga cikin matsalolin da aka samu a yayin gudanar da wannan bincike.

    1.5 MUHIMMANCIN BINCIKE

    Alal haƙiƙa harshe  abu  ne  mai  muhimmancin gaske  a  rayuwar  ɗan'Adam,  kasancewarsa  ɗaya  daga  cikin abubuwan  da  ɗan'Adam  ya  fi  buƙata  a  rayuwarsa.  Harshe  ne  tubalin  ginin  fannonin ilimi  daban-daban,  ana  amfani  da  harshe  musamman  ma  harshen  Hausa  wajen  harkokin addini  da  sana'o'i  da  tattalin  arziki  a  tsakanin  al'umma.  Saboda  haka  ne  wannan  binciken yake  ganin  nazarin  abin  da  ya  shafi  harshe  a cikin al'umma  yana  da  muhimmanci  sosai  saboda waɗanda  za  su amfana  da  shi  ta fuskoki  da  dama kamar:

    v  Wannan bincike zai taimaka wa jami'an tsaro lokacin gudanar da binciken da ya danganci 'Yanlakum da abokan hulɗarsu.

    v  Wannan bincike zai taimaka wajen sanin ma'ana a zantukan 'Yanlakum.

    v  Wannan bincike zai taimaka wajen ƙara samun abin nazari ga masu bincike musamman a fagen ilimin walwalar harshe.

    v  Nazarin  sara  muhimmin  fage  ne  a  fannin  ilimin  walwalar  harshe, wannan  ne  ya  sa manazarta  ilimin  walwalar  harshe  za  su  amfana  da  wannan  nazarin  sosai,  domin  za  su ƙara  fahimtar  tagomashin  da  harshen  Hausa  yake  da  shi.

    v  Zai taimaka ga bunƙasa rumbun kalmomin Hausa.

    v  Ɗalibai  masu  nazarin  halayyar  zaman  jama'a  da  walwalarsu  (sociology)  za  su  amfana da  binciken a  matsayin madogara  wajen  fasalta  maganar Hausawa  da  harshen Hausa.

    v  Zai  taimaki  masu  ilimin  tsara  ƙamus  da  manazarta  ta  hanyar  ba  su  gudummuwa  wajen samun sababbin  kalmomi  da  ma'anarsu.

    v  Wannan bincike zai taimaka wa malaman addini yayin aiwatar da wa'azinsu.

    v  Wannan  bincike  zai  taimaka  wa  mutanen da ke hulɗa da 'yanlakum ta hanyar naƙaltar  yadda  'yanlakum  ke  sarrafa  harshe, hakan zai sa su fahimce su daidai gwargwado.

    v  Wannan  binciken  zai  taimaki  gwamnati  ga  tsare-tsarenta  game  da  harsunan  Nijeriya  ta hanyar killace  salon maganar wasu rukuni a  cikin al'umma.

    1.6 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

    Domin haƙa ta cimma ruwa, kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu. A yayin gudanar da wannan bincike an yi amfani da manya kuma sanannun hanayoyin gudanar da bincike. Wannan bincike an tsara shi ne domin a nazarci Hausar 'yanlakum ta fuskar sara a cikin lafuzansu. Hanyoyin da  aka bi wajen tattara bayanan wannan bincike, an same su kai tsaye ne,  wasu kuma sai da aka  kai ziyara  duk  inda  ya  dace  tun  daga  ɗakunan  karatu, da ziyartar shafukan yanar gizo da  wasu  hanyoyi da dama domin zaƙulo abubuwan da suka shafi wannan nazarin. Hanyoyin da aka bi wajen tattara bayanan wannan nazarim suna da dama daga cikin waɗannan mashahuran hanyoyi da aka bi ko aka yi amfani da su sun haɗa da:

    a. Bitar ayyukan da suka gabata,

    b. Ganawa ko zantawa da masu wannan harka,

    c. Ziyarar shafukan yanar gizo,

    d. ziyarar ɗakunan karatu mabambanta

    d. Sa ido da kuma lura (Observation).

     

    1.7 RA'IN BINCIKE

    Wannan nazarin an ɗora shi  ne  kan  ra’ain  da  ake  kira ra'in fage  (field  theory) na Lehrer (1969). Ana amfani da wannan ra’in ne  domin  fayyace irin canje-canjen da ake samu a cikin harshe,  da yadda  ma’anar  kalma  kan  iya  canzawa  gaba  ɗaya  daga  ma’anar  da  aka  san  ta.  A kan  yi amfani da wannan ra’i wajen kwatancen harsuna kasancewar  bambancin  da  ake  samu  a harsuna  a  sarari  suke  tun  daga  azuzuwan  kalmomi, da muhallin da ake samun kowace kalma. Kamar kalmomin da suka danganci yanayi na zafi, da muƙami, da kaloli, da sunayen sassan jiki, da dabbobi da kayan marmari, da sauransu.

    Field theory by Lehrer (1969) that field theory can be used to illustrate language change. The way semantic   carved up and realized in lexical items changes. It can also be used in contrastive analysis of different   languages.  To illustrate how a given semantic area is sub-divided similarly or differently in different languages. Languages often differ even in apparently  quite  basic lexical division,  and field such as temperature  terms, kinship terms,   colour terms, part of  the  body  and divisions  of animal vegetable world will divide the  semantic  space  differently  and reflect this in the  vocabulary  items covering  those field.  Malmljar, K. (1991).

    Wato  wannan  ra’i  ne  na  rarrabe  ma’ana  a  tsakanin  kalmoni  domin  su  dace  da  muhallin  da  aka same  su  sannan  a  gano  irin  sauye-sauyen  da  aka  samu  a  cikin  harshe  da  kuma  yadda  suka taimaka  wajen  haɓaka  harshe. Har  ila  yau  wannan  ra’i  na  nuna  dangantakar  da  ke  tsakanin kalmomi  ta  fuskar  ma’ana.  An yi  amfani  da  wannan  ra’i wajen  nazarin  Hausar  ‘yanlakum domin  a  ga  irin  canje-canjen  da  ake samu na  kalmomi a cikin harshe sakamakon yunƙurin masu wannan sana’a  ta  Lakum.

    Har ila yau wannan ra’in ya samu karɓuwa ga waɗanda  suka  bi  wannan  ra’i  irin  su Gumperz,  (1962),  da  Lyons,  (1970),  da  Hudson  (1980),  da  Wales (1989),  da Ahmed  (2015). Har aka  gangaro  zuwa  yanzu  da  wannan  bincike  ya  ɗauki  ra’in  domin  amfani  da  shi  wajen gudanar da  wannan bincike.

     

    1.8 NAƊEWA

    Wannan babi da ya gabata, wato babi na ɗaya, babi ne da aka tattauna game da abubuwa da dama, kamar manufar wannan bincike, ko kuma dalilin aiwatar da wannan bincike, sannan an tattauna akan farfajiya ko kuma a ce kadadar bincike, sai hasashen bincike, da matsalolin bincike, da muhimmancin bincike, da hanyoyin gudanar da bincike, da ra’in bincike, daga ƙarshe aka zo da naɗewa.


    BABI NA BIYU

    2.0  BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

    Hausawa na cewa waiwaye adon tafiya, kuma da na gaba ne ake gane zurfin ruwa. Don haka a wannan babi na biyu mai taken bitar ayyukan da suka gabata, babi ne da yayi waiwaye a kan ayyukan da suka gabata waɗanda masana da manazarta da dama suka gudanar a shekaru mabambanta. Haka zalika, a karkashin bitar ayyukan da suka gabata, an tattauna a kan abubuwa uku zuwa huɗu waɗanda suka haɗa da; duba bugaggun littattafai da kundayen bincike da kuma maƙalu, da mujallu waɗanda hannu ya kai gare su. Kafin nan an taɓo ma'anar harshe, karin harshe, karin harshen rukuni, da kuma dangantakar harshe da al'umma. Ko shakka babu, wannan babi zai ƙara haska mana fitila a kan wannan bincike da ake ƙoƙarin aiwatarwa.


    2.1 BUGAGGUN LITTATAFAI

    An yi ayyuka da dama na wallafaffu ko bugaggun littatafai da masana da manazarta da kuma masu bincike suka wallafa masu alaƙa ta kusa da ta nesa da wannan aiki ko bincike kaɗan daga cikin irin waɗannan wallafaffun littatafai akwai:

    Salihi, T. M. (2012) a cikin littafinsa mai suna "Sakace A kan karin Harshen Hausa", marubucin littafin ya rubuta abubuwa da dama, inda ya yi bayani a kan ma'anar harshe da ma'anar karin harshe, da bambanci tsakanin harshe da karin harshe.   Haka kuma ya tattauna a kan matakan da ake bi wajen fito da bambancin harshe da karin harshe da dai sauransu.

    Bugu da ƙari, a cikin littafin ya yi magana a kan tsarin matsayi a cikin al'ummar Hausawa, karin harshen zamantakewa ko matsayi, da kare-karen harshe na matsayi na sana'a wanda a nan ne ya kawo ire-iren Hausar masu sana'a kamar haka:

     

    1. Hausar masu gyaran Wayar Salula.

    2. Hausar Mahauta.

    3. Hausar masu Gurasa.

    4. Hausar ‘Yan Karta.      

    5. Hausar Ɗalibai.

    6. Hausar ‘Yan tasha.

    7. Hausar ‘Yan caca.       

    8. Hausar Maƙera. 

    9. Hausar Yan sanda.

    10. Hausar Teloli.

    11. Hausar Manoma.

    12. Hausar Yan daba, da kuma

    13. Hausar Direbobi.

    Salihi, (2012).

    Saboda haka, wannan littafin yana da alaƙa ta ƙut-da-ƙut da wannan bincike domin an yi tsokaci a kan Hausar rukunin al'umma da dama. Saboda haka suna da alaƘa da juna kasancewar dukkaninsu sun yi magana a kan Hausar wasu rukunan al'umma a cikin Hausawa.

    Yakasai, S. A. (2012) a cikin littafinsa mai suna "Jagoran Ilimin Walwalar Harshe" wanda ya rubuta a tsarin babi-babi inda ya rarraba littafin har babuka ashirin (20). A cikin littafin, marubucin ya yi tsokaci a kan harshe da al'ada, da ma'ana da nau'o'in jinsi. Ya yi magana a kan yanayi da tsarin sadarwa da dai sauransu. A babi na takwas (8) na littafin mai taken "Dangakatar Harshe Da Rukunan Jama'a" marubucin ya yi magana a kan yanayi da tsarin rukunin jama'a, salo cikin dangantakar harshe da rukunin jama'a da harshe. Marubucin ya kawo nau'o'in Hausa kamar haka;

    1. Hausar Kasuwanci.

    2. Hausar Mawaƙa.

    3. Hausar Sarakuna.

    4. Hausar Malamai.

    5. Hausar Dattijai.

    6. Hausar Matan aure.

    7. Hausar Gidan Magajiya

    8. Hausar wurin zaman makoki.

     Yakasai, (2012).

    Saboda haka, wannan littafin yana da alaƙa da wannan bincike. Dalili a nan shi ne, a cikin littafin an yi magana a kan nau'o'in Hausa na wasu rukunan jama'a.

    Fagge, U. U. (2001). Ya rubuta littafi mai suna"Ire-iren Karin Harshen Hausa na Rukuni" wanda shi ma wannan littafin yana da nasaba da wannan aikin sai dai, ba irin sa ba ne. A littafin, an yi tsokaci a kan nau'o'in Hausar rukuni da dama da kuma sauran abubuwa da dama. A littafin, marubucin ya yi tsokaci a kan nau’o’in Hausar rukunin jama’a da dama. Wannan ne ya nuna ayyukan suna da nasaba sosai da sosai.


    2.2 KUNDAYEN BINCIKE

    Salihu, N. A. (1987) ya rubuta kundin bincike mai Taken "Code Switching among University of Sokoto Hausa English Bilingual". An yi shi ne harshen Ingilishi wanda yake magana a kan Ingausar Hausar da ɗalibai ke yi a yayin da suka fara yin magana da Harshen Hausa amma daga ƙarshe a ƙarasa da Harshen Ingilishi inda ya kawo misalai kamar haka;

    Misali:

    (a). Gaskiya i don't like abun da kake yi man.

    (b).  Akwai wata close friend ɗinmu, we are family friends'...."

    (c).  Gaskiya abin da Umar ya yi is not good at all.

    (d).  Muna da exams tomorrow.

    Dangantakar wannan aikin da binciken Salihu ita ce, dukkan su an yi su ne a kan Hausar rukuni na wasu jama’a kuma ɓangaren harshe.

    Yahaya, S. (1998) a cikin kundin digirinsa na farko wanda ya gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Najeriya a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato mai taken "Hausa a Jami'a".

    A cikin wannan kundin bincike, manazarcin ya kawo misalan Hausa a jami'a kamar haka;

    ƊALIBAI MAZA.

    (a). ƘWARO:

        Yana nufin ɗalibi mai ƙwazo.

    (b).  JIRGI:

        Yana nufin Risho(Stove) na dafuwar abinci.

    (c). WANKI:

        Satar amsa ko juya aikin wani kalma zuwa kalma.

    (d).  AHLUL KITAB:

    Ɗalibin da a kodayaushe yake tare da abin karatunsa yana karatu.

    (e). FARIN-WATA:

        Na nufin samun wata ‘yar matashiya game da abin da zai fito a wajen  Jarabawa.

    ƊALIBAI MATA.

    (a). MALAM MAI JAR HULA:

         A wajen mata yana nufin jinin al'ada.

    (b). ADAMA:

         Na nufin mace mai yawan tsegumi.

    (c). FARFAƊIYA:

         Na nufin mace mai yawan faɗuwa, ma'ana mai yawan zina.

    (d). B.Z (widow):

         Ana nufin bazawara, wato wadda ta yi aure ta fito.

    (e). B.G.Z (Ballegaza-Disorganise woman)

    Suna nufin mace marar kimtsi da kamun kai da dai sauransu.

    Akwai alaƙa ta ƙut-da-ƙut a tsakanin aikin Yahaya (1998) da wannan bincike, dalili kuwa shi ne dukkaninsu sun keɓamta a ɓangaren harshe, kuma an yi nazarin su ne a kan Hausar rukuni na wasu mutane.

    Muntari, H. (2008) A binciken da ta gudanar mai taken "KarinHarshe Na Rukuni A Hausa: Nazari A ƙasarZazzau". Kundin Digiri Na biyu. Sashen Harsuna   Da Al'adun Afrika Zariya:  Jami'ar Ahmadu Bello. Ta fara ne da kawo tarihin ƙasar Zazzau a taƙaice da kuma bayanin karin harshen rukuni da dalilan da suke kawo karin harshen. Ta duba rukunoni da dama na masu sana'o'i mabambanta a ƙasar Zazzau, ta nazarci Hausar Asibiti da Hausar ‘Yan acaɓa da Hausar Fada da Hausar Kotu da Hausar Mahauta. Ta kawo misalai na kalmomin da aka ƙirƙira ga kowanne rukuni su ke amfani dasu, waɗanda suka keɓanta ga wannan rukuni kawai.

    Binciken nata ya yi kama da wannan domin ta kalli rukunin wasu masu sana'a ne, da yadda suke samar da kalmomi da jumloli sababbi a harshe. Haka ma wannan yana ƙoƙarin bayanin yadda masu sana'ar lakum ne, ke samar da kalmomi da jumloli domin bunƙasa harshen Hausa.

    Ahmad, H. ( 2015) A cikin kundin neman digirinsa na biyu da ya gabatar a Sashen Nazarin Harsuna Da Al'adun Afirika, Tsangayar Fasaha, Jami'ar Ahmadu Bello Zariya. Mai taken karin harshen rukuni, nazarin Hausar masu sana'ar kayan gwari a garin Zariya. A cikin aikin nasa ya kawo tarin kalmomi da wannan rukuni na masu sana'ar kayan gwari suka ƙirƙira da waɗanda suka faɗaɗa ma'anarsu.Ga  misalin wasu daga cikinsu kamar haka:

    Kalma Ma'ana

    v  Ƙwara --  -- Albasa mafi  kyau

    v  Gwarama --  -- Mutum mai rigima da yawan cin bashi.

    v  Fiya -- ƙaramin buhun Zuba tattasai.

    v  Solo -- Babban buhu mai cin Kwando ashirin.

    v  Gwalagwaji -- Ruɓaɓɓen tumatir ko tattasai.

    Wannan bincike da ake gudanarwa yana da alaƙa da binciken Ahmad, H. dalili kuwa shi ne dukkaninsu an yi su ne a kan abin da ya shafi harshe na rukunin wasu mutane masu aiwatar da wata sana'a a cikin Hausawa.

    Yero, Z. S. (2017). A cikin kundin digirinta na biyu da ta gabatar a Sashen Nazarin Harsuna Da Al'adun Afirika, Tsangayar Fasaha, Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya. Mai taken Hausar yaran mota a garin Zariya, a cikin aikin nata ta yi bayanin yaran mota da ayyukansu da kuma abokan hulɗarsu, sannan ta kawo kalmomin da suka samar a rukuninsu, tun daga waɗanda suka ƙirƙira da na aro da waɗanda aka faɗaɗa ma'ana da dai sauransu. Ga misalin wasu daga cikinsu:

    Kalma     Ma'ana

    v  Garau --  --  -- Tsohuwar mota.

    v  Awiizoo--  -- wasa da mota kan titi.

    v  Fyau --  --  -- Sabuwar mota.

    v  Kaco --  --  -- Ɗan kwaya.

    v  Garau-garau-- Sabuwar mota.

    v  Gudubale --  -- Babbar mota mai buɗaɗɗen baya.

    Bayani

    v  Garau:  yaran mota na kiran tsohuwar mota da garau. Kuma kalma ce  da  suka ƙirƙira domin amfani da ita a tsakaninsu.

    v  Awizo:  kalma  ce  da  yaran  mota  suka  ƙirƙira  kuma  suke  amfani  da  ita  wajen irin wasan  ganganci da direbobi ke  yi da  mota a  kan titi.

    v  Fyau:  kalma  ce  da  yaran  mota  suka  ƙirƙira  kuma  suke  amfani  da  ita  wajen  kira ko nuna  cewa  kuɗi sabon  fitowa  daga  Banki ne  ko  lanƙwashewa  bai  yi ba.

    v  Kaco:  suna  ne  da  suka  ƙirƙira  suna  kiran  wanda  ke  shan  ƙwaya  da  sunan Kaco.

    v  Garau-garau:  suna  ne  da  suka  ƙirƙira  suna  kiran  tsohuwar  mota  wadda  ba  a morar ta  sosai.

    v  Gudubale:  suna  ne  da  yaran  mota  suka  ƙirƙira  suna  kiran  babbar  motar  ɗaukar itace.

    waɗannan kalmomin da  suka  gabata, kalmomi  ne  waɗanda  yaran mota  suka  ƙirƙira  suke kiran wasu abubuwa  waɗanda  suka  danganci sana'arsu, ko dai ta  la'akari da  sifar abun ko kuma ta  la'akari da  halayyarsa, ko kuma don  kawai suna ganin sunan da  ya  dace  da  su kenan.

    Waɗannan ayyuka biyu suna da dangantaka sosai da sosai, domin dukkaninsu sun shafi ilimin walwalar harshe kuma an yi su ne a kan Hausar wani rukuni na wasu mutane a cikin Hausawa.

    Abdulƙadir, M. (2018) A cikin kundin bincikensa na neman digiri na farko mai taken "Hausar Rukunin 'Yan Banga A Garin Gusau" wanda ya gabatar a Jami'ar Tarayya Gusau, Sashen Nazarin Harsuna Da Al'adu. Shi ma wannan kundin binciken yana da alaƙa da wannan binciken. Kasancewar dukkaninsu an yi su ne a kan harshe kuma a ɓangaren ilimin walwalar harshe wanda ya shafi Hausar rukuni. A cikin kudin bincikensa, manazarcin ya kawo Hausar yan banga kamar yadda za mu gani a nan;

     KALMOMI.MA'ANA

    v  Sabce:Na nufin kayan sata a wajen yanbanga.

    v  Sabci-faɗi:  Bulalace irin ta dorina.

    v  Tambaya:   Na nufin maganin tsarin jiki ko buwaya. 

    v  Mugu:A wajen yanbanga yana nufin ɓarawo.

    v  Makuba:    A wajen 'yanbanga ana nufin wurin zaman 'yan daba ko  masu aikata laifi.

    Dangantakar wannan kundin binciken da wancan kundin binciken ita ce dukkansu suna a ɓangaren harshe, kuma ko a ɓanagren harshe duk sun shafi Hausar rukuni na wasu al’umma waɗanda ke zaune ko suke rayuwa a Gusau.

    Tukur, A. (2020) a Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al'adu, Jami'ar Tarayya Gusau. Mai taken: "Hausar masu sana'r waya a garin Gusau". Manazarcin ya yi bayanai masu tarin yawa, kamar ma'anar wayar salula, ire-iren waya, wuraren da ake sayar da waya na da da na yanzu a garin Gusau, da dai sauran abubuwa da dama. Sannan ya kawo kalmomin da masu sana'ar waya suka ƙirƙira kuma suna amfani da su ga kaɗan daga ciki:

        -- Kalma --  --  -- Ma'ana

    1)      Ƙetare      --  -- Kada ka sayi waya.

    2)      Kilin     Waya mai kyau.

    3)      Guduma        Ƙatowar waya.

    4)      Jagwal   -- waya marar lafiya.

    5)      Sumuni Dubu ɗari.

    6)      Ƙundu Bandur na kuɗi.

    Wannan kundi yana da alaƙa sosai da na Tukur, A. (2020) domin kuwa duk suna magana ne a kan Hausar rukunin wasu al'umma ne a cikin garin Gusau.

    2.2.1  Muƙalu Da Mujallu

    Abubakar, I. A. (2001) ya rubuta muƙala a kan Hausar gardawa a cikin birnin Kano da kewaye. Gardawa su ne almajirai da suka girma suka kai lokacin gardanta. Wato bayan shekara 28 sun haddace Alƙur'ani tare da iya rubuta shi. Ya kawo misalai na kalmomi da ma jumloli da suke amfani da su domin sadarwa. Akwai alaƙa sosai tsakanin aikin Abubakar da wannan aiki da ake yi. Domin duk sun yi tsokaci a kan Hausar wani rukuni na jama'a.

    Fagge, U. U. (2002:99-101), ya bayyana cewa akwai wani salon magana da zawarawa suke yi. Binciken ya nuna cewa su dai zawarawa a sanadiyar lokutan da suka ɗauka a gida kafin su samu damar yin wani aure shi ne yake haifar da ire-iren karin harshen da ake samu a tsakaninsu. Ga wasu misalansu kamar haka:

    Kalma    -- Ma'anar yau da kullum   Sabuwar ma'ana

    v  Ɗan-birni -- wayayye        Matashin saurayi

    v  Kwasa    --  -- Ɗibar wani abu    Aure

    v  Ƙarfe     --  -- Ƙarfe --  -- Marowaci

    v  Tulu       --  -- Abin zuba ruwa       Mai ƙaton ciki

    Haƙiƙa, akwai abubuwa da dama da karin harshe ya haifar ga wannan rukunin na Hausawa. Kaɗan daga cikinsu akwai, azanci wanda ya bai wa zawarawan damar sarrafa harshen Hausa ta ɓangarori daban-daban, wanda yin hakan kan jawo sanya wa wani abu suna, kuma ma'anar ta dace, kuma ta zauna daram ba tare da haifar da wata matsala ba a harshe. ko shakka babu waɗannan ayyukan biyu suna da dangantaka sosai.

    Musa, A. (2011:273) ya gabatar a kan Karin harshen Hausar niga ya fara da bayar da ma'anar Hausa-Niga inda ya bayyana cewa wani rukuni ne na matasa Hausawa masu haɗin gambiza na al'adu biyu Watau, al'adunsu na Hausa da na aro na Nigan Amerika, wanda suke gani a fina-finan sinima da satilayi (dish) da bidiyo. Ya cigaba da cewa bayan al'adunsu na asali. Hausa-Niga sun ƙirƙiri sababbin kalmomi na sadarwa a tsakaninsu. Kuma waɗannan kalmomi suna yin tasiri a tsakanin sauran matasa, kuma har suna samun karɓuwa da bunƙasa. Ya yi nuni da ɗabi'un Hausa-Niga da cewa aske kai ƙwalkwabo yana ƙyalli. Amma suna da shiga ta asali ta Hausawa.

    Akwai kuma shigarsu ta Amerika-Niga Watau, T-shat marar hannu mai kama da singileti ko shat da wando jins koɗaɗɗe ko mai jiki duk faci ko wanda yake kira cinos mai aljihu barkatai daga sama har ƙasa, ga yin zanzaro, da ƙaton takalmi sawu ciki (but), ko waje ko kambas. Wani lokaci Niga kan sa sarƙa da ɗankunne. Hausa-Niga sun ƙirƙiri kalmomin sadarwa waɗanda suka keɓanta da rukuninsu na matasa. Misali:

    Kalma     --  -- Ma'anar asali --      Ma'ana wurin Hausa niga

    v  Tsami       -- Ɗanɗano mai tsami       Rashin wayewar kai

    v  Haɗuwa      -- Gamuwa    -- Yin ado

    v  Sharewa    -- Kauda datti  --  -- Mantawa/ Ƙyalewa

    v  Mai tsada     Marar sauƙi       ƙyaƙƙyawa

    v  Django Suna        Mahaifi

    Waɗannan  Ayyukan biyu sun yi kama da  juna domin dukkaninsu nazari ne  a kan Hausar wani rukuni na al 'umma, sannan kuma suna ƙirƙira kalmomi da jumloli da suke amfani da su a cikin rukuninsu.

    Munnir  (2010)  ya  yi  nazarin  Hausar  'yan  tasha  a  garin  Gusau  da  ke  cikin  jihar  Zamfara.  Ya nazarci  yadda  suke  faɗaɗa  ma'anar  kalmomi,  da  yadda  suke  juya  guraben  haruffa  a  cikin kalma  ba  tare  da  ma'anar  kalma  ta canza  ba. Wannan aikin  yana  da  dangantaka  da  wanda  za  a yi  kasancewar    duk  a  kan  sarrafa  harshe  ne.

    Yakasai, S. A. (2010) ya yi nazarin dangantakar harshe da muhallin magana.  Ya  nazarci  yadda  ake magana  ko  taɗi  a  al’adar  Hausawa  da  kuma  tsarin  da  ake  bi  wajen  aiwatar  da  maganar  ko taɗi.  Ya  bayyana  abubuwan  da  kan  zo  a  zuciyar  mutum  a  duk  lokacin  da  zai  yi  magana  ko taɗi, ko bayar da  umurni. Waɗannan abubuwa sun haɗa da:

    v  Darajar mai sauraro a idanun mai magana.

    v   Abin da ake magana ko hira a kai.

    v   Wurin da ake gudanar da hulɗoɗi.

    Wato ba haka nan kawai ake yin magana ba.  Kowacce magana tana da zubi da tsari. Wannan ya nuna cewa akwai zumunta tsakanin waɗannan ayyuka biyu.

    Azare, Y. M. (2011:224) ya bayyana cewa mata na amfani da wasu nau'in kalmomin harshe domin sadarwa a tsakaninsu, ta yadda ba kowane mutum kan fahimci ma'anar da suke nufi ba. Ya kalli rukunonin mata da dama, daga matan aure masu ilimi (boko ko mahammadiya da marasa ilimi, sai mata marasa aure wato, 'yan mata masu ilimi na sakandare da 'yan jami'a da 'yan islamiya da kuma marasa ilimi kamar 'yan talla, sannan zawarawa da kuma karuwai. Kasancewar kowane rukuni na da irin Hausar da suke amfani da ita domin sadarwa a tsakaninsu. Misali:

    Kalma/Yankin jimla --  -- Ma'anarta a wurin matan

    v  Sayar da manja       Jinin al'ada.

    v  Rijiya gaba dubu     Mace mai yawan aure.

    v  Daƙiƙi Ragon namiji.

    v  Sandar girmaAl'aurar namiji.

    v  Burodi Audugar al'ada.

    v  Wancan magana     Jima'i/ saduwa.

    A ƙarshe, ya nuna cewa ko tantama babu domin kuwa a kan sami sauyi a harshe ta la'akari da yanayin hulɗoɗin al'umma, wanda kan haifar da ƙirƙirar harshe, wato karin harshe domin ya dace da hali ko yanayin da ake ciki. Wannan kan haifar da samuwar sababbin kalmomi waɗanda daga baya sukan koma ga al'umma. Watau, al'umma su zaɓi waɗanda za su rika amfani da su, su kuma yi watsi da wasunsu. Alaƙar wannan aiki da wanda ake gudanarwa ita ce, sun kasance suna magana game da karin harshen rukuni. 

    Adamu, S. (2022) ya rubuya muƙala mai taken kalmomin teloli a garin Gusau a cikin aikin manazarcin ya kawo ma'anar tela da kashe kashen teloli ta fuskar kayan aiki da kuma ta fuskar muhallin da suke aiki, baya ga wannan kuma ya kawo wasu kalmomi da suka ƙirƙir kuma suke amfanin da su a ɓangaren maza da na mata ga misalin wasu daga cikinsu kamar haka:

    NA MAZA

    Sace: Babbar riga ce ta sarakuna da manyan mutane (dattijai da attajirai). Ana yi mata shuggai irin na Yar-shara.

    Gare: Ita ma babbar riga ce wadda mafi akasari matasa kan sa. Shigganta a jirge ake yanka su, sama ya fi ƙasa faɗi.

    Shakwara: Wannan ma babbar riga ce wadda ake yanka shiganta faɗi ɗaya daga sama zuwa ƙasa.

    Yar-Bunguɗu: Wannan babbar riga ce wadda ake ɗinkawa da ƙoran saƙi, na saƙar hannu.

    Wuyan-Wundi: Nau'in ɗinki ne da ake yi wa babbar riga zagayayyen wuya, mai aiki ko maras aiki. Duk nau'o'in manyan riguna ana iya yi musu wuya wundi.

    Yar-Shara: Nau'in rigar maza ce wadda mafi akasari guntuwa ce zuwa guwayyu, tana da shiggai amma ba ta da hannuwa.

    Ɗan-itori: Wando ne wanda ake yi wa ƙarin hantsa daga wannan idon sawu zuwa wancan.

    Tsala mai bulala: Wando ne wada ake yi wa ƙarin hantsa daga guiwa zuwa guiwa. Kuma ana yi masa taki gefen aljifai daga sama zuwa ƙasa wanda ake kira fitsarin bajini.

    Na Annabi ya zo kasuwa: Nau'in ɗinki ne wanda ake yi wa riga aljifai guda biyu hagu da dama, kuma aljifan wajen rigar ake manna su.

    Sardauna a ofis: Nau'in ɗinki ne wanda ake lanƙwaso wani ƙyalle a yi masa tsini a wuyan hannun riga a take shi da ɗinki.

    NA MATA

    Buba: Rigar mata ce mai zagayayyen wuya, wadda ba a yo wa kwalliya. Mafi akasari tsofaffi suka fi saka ta.

    Agwada: Babbar riga ce ta mata mai zagayayyen wuya, ana take gefen hamata zuwa ƙasa kaɗan na hagu da dama. Wasu kan yi mata kwalliya wasu kuma ba sa yi.

    Amaliya: Babbar riga ce, amma iyakacin ta bakin guiwa.

    Amburela: Nau'in rigar mata ce mai shan bance, kuma gajeruwa ce ƙwarai ba ta kai guiwa ba, amma ƙasanta yana da faɗi. Hannuwanta ƙanana ne, an yi ma wuyan zugen atamfa ko barnina.

    Baba na isa aure: Riga ce gajeruwa mai wuya mai faɗi da kan bayyana sassan nonuwa.

    Zura hannunka masoyi: Riga ce wadda hannunta ba ya rufe hamata kuma gajeruwa ce.

    Umar, M. M. & Abbas, N. I. (2020). Sun rubuta wata mujalla mai taken Nazarin Hanyoyin Samar da Hausar Wasu Rukunan ‘Yan Kasuwa a Cikin Garin Sakkwato a cikin aikin nasu manazartan sun yi bayanin Hausar kasuwanci inda suka ce "Hausar  kasuwanci,  Hausa  ce  da  take  ƙunshe  da  kalmomin  fannu  waɗanda  suka  shafi  kayayyakin  da  'yan  kasuwa ke  sayarwa,  da  yadda  suke  gudanar  da  hulɗar  kasuwanci  tsakaninsu  da  masu  sayen  kaya  da  sauran  'yan  kasuwa.  A taƙaice,  ana  iya  cewa  Hausar  kasuwanci  karin  harshen  rukuni  ne  na  musamman  da  ya  keɓanta  ga  'yan  kasuwa  da  masu sana'o'i  wadda  ke  bayyana  yadda  suke  amfani  da  Hausa  a  sadarwarsu  ta  yau  da  kullum.  Misali,  da  zarar  'yan  kasuwa  sun yi  wa  juna  irin  wannan  Hausa  za  ka  ga  sun  san  abin  da  suke  nufi.  Fagge  (2004)  ya  ce,  “Bisa  ga  al'ada  'yan  kasuwa  kan  yi amfani da  wani nau'in  harshe  a  tsakaninsu  don  tafiyar  da  hankulan  masu  sayen  kaya.” Hanyoyin Samuwar Hausar Wasu Rukunan ‘Yan kasuwa a Cikin Garin Sakkwato.

     

    1.  Faɗaɗa  Ma’anar  Kalmomi

    v    Faɗaɗa  ma’anar  kalmomin  asali

    v     Faɗaɗa  ma’anar  kalmomin  aro

     2.  Ƙirƙira

    v  Ƙirƙira  daga  kalmomin  asali

    v  Ƙirƙira  sabuwar  kalma  da  babu  ita  a  da  a  harshen  Hausa

    v  Ƙirƙira  ta  haɗin  gambizar  kalmar  asali  da  ta  aro

    3.  Sarrafa  Kalmomin Aro

    v    Sarrafa  kalmomin  Larabci

    v    Sarrafa  kalmomin  Ingilishi

    Kalma -- Ma'ana --  -- Ma'ana ta asali

    v  Takalmi    -- wurin aza ƙafa na babur -- Abin kare tafin ƙafa daga rana ko ƙaya.

    v  Katawa     babur wanda ya tsufa       -- Tarkon ƙarfe na kama ɓera.

    v  Haɗi Canja wa ƙaramin babur inji      Gauraya wani abu da  wani.

    v  Kura Dillalin dake ƙayyade  --  -- Dabbar daji.   kuɗin la'ada

    v  Baƙoo       Mai sayen kaya --  -- Mai ziyara ko sabon abu.

    Waɗannan ayyuka biyu suna da alaƙa ta kut-da-kut, domin suna magana ne a kan karin harshen rukunin wasu mutane.

    2.2.2  Hujjar Cigaba Da Bincike

    Idan aka yi duba ga bayanan da suka gabata, a inda muka yi tankade da rairaya a kan ayyukan da aka aiwatar, a kokarinmu na kwatanta kudurin wannan nazarin da abin da magabata a fagen nazari suka aiwatar, za mu fahimci cewa, har zuwa yanzu ba a ci karo da wani bincike da aka gudanar dangane da Hausar 'yanlakum, ko da a wani gari saɓanin garin Gusau ba. Wannan dalili ne ya tabbatar muna da cewa, an bar wani babban giɓi da ke bukatar cikewa, musamman a ɓangaren ilimin walwalar harshe.

    Littafin Salihi (2012). Yana da alaƙa taƙut-da-ƙut da wannan bincike domin a cikin littafin an yi tsokaci a kan Hausar rukunin al'umma da dama. Ayyukan suna da alaƙa da juna kasancewar dukkaninsu sun yi magana a kan Hausar wasu rukunan al'umma a cikin Hausawa. Haka kuma, sun bambanta da juna domin a littafin ba a yi magana a kan Hausar 'Yanlakum ba, amma, shi wannan binciken an yi shi ne a kan Hausar 'Yanlakum a garin Gusau.

    Haka zalika littafin Yakasai (2012). Shi ma yana dangantaka da wannan bincike sosai da sosai, kasancewar dukkaninsu sun yi tsokaci a kan Hausar rukunin wasu al'umma. To amma sun sha bamban, saboda shi wannan bincike an yi shi ne a kan nazarin Hausar 'Yanlakum a garin Gusau kawai.

    Bugu da ƙari, littafin Fagge (2001) shi ma yana da alaƙa da wannan bincike na nazarin Hausar 'yanlakum saboda dukkaninsu sun yi magana a kan Hausar rukunin wasu mutane a cikin Hausawa. Sai dai abun da ya bambanta su shi ne fagge bai yi magana a kan Hausar 'yanlakum ba kamar yadda wannan bincike ya yi.

    Alaƙar binciken Salihu (1987), da wannan binciken ita ce dukkansu an yi su ne a kan Hausar rukuni na wasu jama’a kuma a ɓangaren harshe. Abin da kuma ya bambanta su shi ne, wancan aikin an yi shi ne a kan Ingausar Hausar da dalibai ke yi a Jami’a. Yayin da wannan aikin an yi shi ne a kan Hausar masu sana’ar lakum a Gusau.

    Akwai alaƙa ta ƙut-da-ƙut a tsakanin aikin Yahaya (1998) da wannan nazari, dalili kuwa shi ne, dukkaninsu an yi su a ɓangaren harshe, kuma an  gudanar da su ne a kan Hausar rukuni na wasu mutane.

    Amma wurin da suka farraƙa kuwa shi ne, a wancan kundin binciken an yi nazari a kan Hausar ‘Yan Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sokoto. A wannan kundin binciken kuma, ana nazari ne a kan Hausar 'Yanlakum a garin Gusau

    Binciken Ahmad, H. (2015) bai zo daidai da wannan ba, domin   an yi shi ne, a kan Hausar masu sana'ar kayan gwari a zariya, shi kuma wannan aiki ana aiwatar da shi a kan Hausar masu sana'ar Lakum a garin Gusau.

    Aikin Zainab, S. Y. (2017) ya bambanta da wannan domin aikin Zainab an yi shi a kan Hausar yaran mota a garin Zariya. Wannan kuma ana gudanar da shi a kan Hausar 'Yanlakum a cikin garin Gusau.

    Haka zalika, abun da ya bambanta aikin Abdulkadir (2018) da Wannan shi ne, Abdulkadir yayi aiki a kan Hausar Rukunin ‘Yan Banga a garin Gusau. Yayin da shi kuma wannan binciken an yi shi ne a kan ‘’Hausar Rukunin 'Yanlakum a garin Gusau’’.

    Kundin Tukur, A (2020) ya sha bamban da wannan, domin wannan ana yin shi ne a kan Hausar 'Yanlakum a garin Gusau shi kuma wancan an yi shi ne a kan Hausar masu sayar da waya a garin Gusau.

    Aikin Abubakar (2001) ya bambanta da wannan nazari domin shi ya yi nasa aiki a kan Hausar gardawa a garin kano.

    Fagge (2002 : 99-101) ya yi aiki a kan salon maganar zawarawa.

    Musa (2011 : 273) ya yi bincikensa a kan Hausar Hausa-niga.

    Munir (2010)  ya yi aiki a kan Hausar 'yan Tasha a garin Gusau.

    Yakasai (2010) ya yi nazarin dangantakar harshe da muhallin magana.

    Azare (2011: 224) ya yi aiki a kan Hausar rukunin mata daban-daban daga matan aure, zawarawa, 'yan talla, da sauran su.

    Adamu, S. (2022) ya rubuta muƙala mai taken "kalmomin teloli a garin Gusau.

    Umar, M. M. & Abbas, N. I. (2020), sun rubuta wata mujalla mai taken "Nazarin Hanyoyin Samar Da Hausar Wasu Rukunan 'Yan Kasuwa a garin sakkwato.

    Idan aka yi la'akari da bayanan da suka gabata za a fahimci cewa, bincike a kan"Nazarin Hausar 'YanLakum A Garin Gusau" yana da hujjar da za a ci gaba da gudanar da shi. Saboda bitar ayyukan da magabata suka yi, da kuma sauran ayyukan da suka gabaci wannan bincike, su suka tabbatar da hakan.

    Saboda duk da cewa an yi ayyuka da dama da suka gabaci wannan aiki masu alaƙa da shi ta kusa da ta nesa, to amma ba a samu wani aiki da zo daidai da wannnan bincike ba, na nazarin Hausar 'yanlakum musamman a garin Gusau.Wannan dalili ne ya zaburar da wannan bincike domin cike gurbi ko giɓin da masana da manazarta da ɗalibai 'yan'uwa suka bari domin amfanin al'umma baki ɗaya.

    2.2.4  NAƊEWA

    A wannan babi na biyu bayan an yi shimfiɗa, an tattauna a kan muhimman abubuwa da dama kamar bitar ayyaukan da suka gabata da kuma hujjar ci gaba da bincike. A ƙarƙashin bitar ayyukan da suka gabata, an yi tsokaci a kan abubuwa uku zuwa huɗu kama daga bayanai daga bugaggun littattafai da kundayen bincike. Daga ƙarshe kuma, aka yi bayani a kan wasu muƙalu da mujallu masu alaƙa da wannan kundin bincike, domin samun tudun dafawa.


    BABI NA UKU

    FASHIN BAƘIN MA'ANONIN KALMOMIN

    DA SUKA SHAFI LAƘABIN BINCIKE

    3.1 SHIMFIƊA

    A wannan babi na uku mai suna fashin baƙin kalmomin da suka shafi laƙabin bincike, za a duba ma'anonin kalmomin da suka fito a cikin laƙabin bincike domin fahimtar abin da suke nufi, sannan za a duba kashe-kashen 'Yanlakum da kuma wasu daga cikin dabarun da suke yi a lokacin gudanar da wannan sana'ar tasu domin karɓar kuɗi a wurin al'umma, daga karshe a zo da naɗewa.

    3.2 MA'ANAR  NAZARI

    Nazari zai iya ɗaukar ma'anar ayyuka dabam - dabam da da ake aiwatarwa da manufar samun sani (ilimi), ko fahimtar wani batu, ko kuma shiri domin gwaji ko jarabawa. Nazari yana bukatar aiki tukuru da lokaci da lura sosai domin samun nagartattun bayanai, da bunkasa kwarewa, ko kuma zurfafa fahimta a wasu ɓangarora na rayuwa da ake da buƙatar yin hakan.

    Sau da yawa ana dangantaka nazari da ilimin boko inda ɗalibai da Malamai da masana suke bibiyar wasu batutuwa na ilimi a makarantu da kwalejojan ilimi da jami'o'i domin gano ainihin haƙiƙanin yadda waɗannan batutuwa su ke. Ta hanyar karatun littatafai, tambayoyi, ƙwanƙwance bayanai, tattaunawa, bitar ayyukan da suka gabata, da kuma tattara bayanai wuri ɗaya.

    A wata mahangar kuma idan an ce nazari to ana nufin zurfin tunani da hangen nesa domin gano hanyar shawo kan wata matsala, ko kuma sanin wani abu da ya shige wa mutane duhu.

    3.3 MA'ANAR KALMAR HAUSA

    Masana da dama kuma a shekaru mabambabanta sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma'anar kalmar Hausa, kaɗan daga cikinsu akwai:

    Zarruƙ  da  Wasu  (1986:l6)  sun  bayyana  "Hausa  kamar  haka: “Koda yake  can  farko,  akwai  ƙabilar  Hausa.  Duk  da  haka  a  yanzu  wannan  suna  ya zamana  harshe,  ba  na  ƙabila  ba.  Domin  idan  aka  ce  ƙabila,  ana  nufin  al'umma  mai asali  ɗaya  da  yare  ɗaya  da  ƙirar  jiki  kusan  iri  ɗaya  da  al'adu  iri  ɗaya  da  falsafa  ko ra'ayin  zaman  duniya  iri  ɗaya.  Bayan  haka  kowa  cikin  alummar  zai  riƙa  alfahari shi  ɗan  ƙabilar  ne.  Hausawa sukan ce su ƙabila ne.  To  amma  idan  ka  matsa tambaya,  za  ka  ji  haifaffen  ƙasar  Hausa  ya  ce  maka  asalinsa  shi  Bafilatani  ne,  ko Babarbare  ko  Banufe  ko  Buzu  ko  dai  ɗan  wata  ƙabila  daban.  Ga  shi  kuma  a wannan  ƙabilar  bai  san  ko  sannu  ba.  Bayan  haka  wannan  kalmar  Hausa  a  wurin Bahushe  ma'anarta  "harshe.  Idan  aka  yi  magana  da  wani  harshen  daban, Bahaushe  yakan  ce  yana  ji  ana  wata  Hausa.  Wato  a  nan  ka  ga  Hausa  sunan  harshe ne  ba na  ƙabila. 

    Al'ummomin  da  suka  taru  suke  yin  magana  da  wannan  harshe  su ne  Hausawa.”  Idan  ka  bibiyi  wannan  bayani  na  Zarruk  da  Wasu  (1986)  za  ka  gane cewa Hausa  dai harshe  ne,  masu  yin  magana da harshen kuma sunansu Hausawa.

    Adamu  (1997:  48)  cewa ya yi “Hausa  suna  ne  na  harshe,  kuma  masu wannan  harshe  su  ake  kira  Hausawa,  domin  su  al'ummar  Hausawa  ba  su  ɗauki kansu ƙabila ba, don kuwa a gurinsu duk wanda ba Bahaushe ne ba, to shi suke ce wa ƙabila, ko kuma bagwari, wato kamar yadda dai Larabawa suka ɗauki duk wanda ba Balarabe ba da cewa Ajami ne”.

    A ɗaya hannun kuma Adamu (1997: 48-49) ya nuna cewa “Idan mutum ya bibiyi ma'anar ƙabila sosai zai ga cewa Hausawa sun shiga daidai wa daida. Misali bisa ga bayanan marubuta sun ce ƙabila al'umma ce mai asali ɗaya da yare ɗaya da kamanni kusan iri ɗaya da al'adun gargajiya iri ɗaya da ra'ayin zaman duniya (wato falsafa) iri ɗaya da dai sauransu, kuma lallai ne cikin wannan alumma kowa ya zama yana da'awar shi ɗan ƙabilar ne yana kuma alfahari da ita (wannan ya yi daidai da bayanin da Zarruƙ da Wasu (1986) suka yi dangane da ƙabila). Sai ya ƙara da cewa “Idan mutum ya tarar da Hausawa kafin canzawar zamani da cuɗanya zai ga cewa komai na wannan bayani ya yi daidai da su, don haka ashe bisa wannan ma'ana, Hausawa ƙabila ne. Shi kuwa Amfani (2012: 4) cewa ya yi “Hausa harshe ne, kuma tana ɗaya daga cikin harsunan ɗan'Adam waɗanda ake samu a nahiyar Afirka. A lissafin ko ƙididdiga irin ta masana ilimin kimiyyar harshe, harshen Hausa yana cikin wani babban rukuni na kason harsunan duniya wanda ake kira Afroasiatic. Shi ma wannan babban rukuni yana da 'ya'ya kuma kowane ɗa, shi ma ƙaramin rukuni ne mai ɗauke da harsuna. Ƙaramin rukunin da Hausa ke cikinsa shi ake kira gidan harsunan Cadi. Wasu harsunan 'yan gidan Cadi, waɗanda 'yan'uwan Hausa ne, su ne Angas da Bole da Ron”.

    3.4 MA’ANAR KALMAR LAKUM

    Kalmar ta samo asali ne daga kalmar larabci wato (لكم) mai ma’anar naku a zahiri, yayin da a wannan rukuni ta ke da ma’anar Malam, saboda masu wannan sana’a sukan shiga rigar malanta su fake ta hanyar shiga irin ta malamai da kuma samun wasu addu’o’i da za a haddace, saboda yaudara barazana da kuma burga, wani lokacin har da Ƙur’ani da tazbaha, ko da yake akasarin su suna da ilimin addinin musulunci dai- dai gwargwado.

    Ma’ana ta isɗilahi kuwa tana nufin sana’ar wa’azi da sayar da magani da ba da laƙani ko laya da kuma duba (Istihara). Galibi sukan yi amfani da amsa amo (speaker) yayin gudanar da wannan sana'a, kuma suna aiwatar da sana'ar ne a cikin unguwannin birane da ƙauyuka, da safe ko da dare, ko kuma da rana a kasuwanni da wuraren taruwar jama’a.

    3.5 MA'ANAR 'YANLAKUM

    ‘Yanlakum (masu wa’azin turmi) rukunin jama’a ne da ke wa’azi da sayar da maganin gargajiya ko na musulumci ko bayar da wani laƙani ko guru ko laya, bayan sun kammala wa’azi. Wannan rukunin jama'a, galibi sukan gudanar da wannan sana'a tasu ne da safe ko da dare a cikin unguwannin gari da ƙauyuka. Wani loton kuma da rana a kasuwanni ko masallatan juma'a da sauran wuraren taruwar jama’a. Akasari sukan yi amfani da amsa-amo (speaker) wadda suke azawa a kan mota ko wani gini ko bishiya (itaciya) da ke kusa da su domin jiyar da al'umma.

    3.1 KASHE-KASHEN ‘YAN LAKUM

    ‘Yan lakum sun kasu zuwa gida uku manya kamar haka:

    a . ‘Yanɗaiɗai,

    b. Sunƙuru,

    c. Rufani.

    a. ‘Yan Ɗai-ɗai

    Wannan kaso na ‘Yan lakum shi ne kason da ke sayar da maganin lalurori iri daba-daban, ɗaya bayan ɗaya kamar matsalar sanyi, zahi, ciwon daji, ulsa da makamantansu. A nan bayan ɗan lakum ya gama addu’o’i da gabatarwa da tambihi sai ya tsunduma cikin tallar magani daki-daki, wato bayan ya yi tallar maganin sanyi kimanin mintuna goma zuwa sha biyar sai ya ko ma na Basir daga nan kuma sai na olsa haka dai zai yi ta yi har lokacin da zai tashi, sannan yana yi yana rage farashin maganin. Su ma sun kasu kashi biyu akwai ‘yan-siba wato masu aiki kasuwa-kasuwa da rana, akwai masu aikin safe da dare acikin unguwanni su kuma waɗannan ba su cin kasuwanni.

    b. Sunƙuru

    Wannan kaso na ‘Yanlakum, su ma suna sayar da magani amma su ba kamar ‘yan-ɗai-ɗai ba. A nan marar lafiya zai zo ya yi masu bayanin duk abun da ke damuwarsa da tsawon lokacin da ya ɗauka yana fama da wannan lalura, sai a haɗa masa magunguna a ce ya ba da naira kaza, saɓanin 'yan dai-dai da ke sayar da magani ɗaya bayan ɗaya kuma kowanne ƙulli da nashi farashi, amma kuma wani lokacin ‘yan daidai sukan yi sunƙuru idan sun fahimci wanda ya zo neman maganin yana da ƙiri (kuɗi) wato yana da  abun hannunsa.

    c. Rufani

    Wannan kaso na ‘yanlakum babban aikin su shi ne duba wato istihara idan wani abu ya ɓace ko an sace shi za su yi istihara domin gano inda abun yake, ko kuma wanda ya sace shi, wai an ce  suna amfani da rufanai dalilin da ya sa ake kiransu ruhani ke nan, daga cikinsu akwai masu ruhanai na gaskiya, akwai kuma na ƙarya, duk da yake kashi casa’in da tara cikin ɗari (99/100) su ne na ƙarya, wato waɗanda ba su da rufanai, kawai suna amfani da dubaru da hikimomi da kuma mamare ne.

    3.2 WASU DAGA CIKIN DABARUN ‘YAN LAKUM

    Kira da Riƙe Mutane Kada su Watse: A nan idan ɗan lakum zai fara sana’arshi ta lakum yana amfani da wasu dabaru domin jawo hankalin mutanen da ke nesa kusa, da kuma riƙe na kusa gare shi kada su watse, ta hanyar faɗar wasu kalamai kamar:

    Duk masoyin Annabi (S.A.W) da ke kusa ya samu wuri ya natsu, wanda yake nesa kuma ya matso kusa don jin maganar ɗan gata Rasulullahi, Shi kuwa munafuki yanzu ka ga ya kakkaɓe rigarshi ya ƙara gaba.

    Sannan wani lokaci za su ce, za su nuna wani abin ban al’ajabi, wanda faɗin hakan zai sa na nesa su matso, su haɗu da na kusa, su kasa su tsare, domin ganin wannan abu na ban al’ajabi, amma daga ƙarshe ba su nuna komai, dama sun yi ne kawai domin tara mutane da kuma hana su watsewa.

    3.3 BADALI

    Idan an ce badali a nan ana nufin duk wata dabara ko waibuwa da za su aiwatar yayin gudanar da sana’arsu da nufin baddalar da jama’a, wato su sauyar da tunanin jama’a idan sun aikata wani abu na ban al’ajabi sai jama’a su ɗauka da gaske ne, alhali ba gaskiya ba ne, abu ne da kowa zai iya yi idan yasa kansa ba wani abun mamaki ba ne wanda sai wane da wane, daga cikin dabarun na badali akwai:

    3.4 AMAYO ALLURAI DA KUMA FYATO SU TA HANCI

    ‘Yan lakum sukan ɓoye allurai a cikin bakunansu ko a cikin hantunansu a lokacin da za su gudanar da aiki, da nufin amayo su ko fyato su a gaban jama’a a yayin da suke aiwatar da sana’arsu. Idan hakan ta faru jama’ar da ke wurin za su yi tunanin cewar sun amayo su ne ko sun fyato su ne daga cikin ciki ko kai, wanda a zahirin gaskiya sun ɓoye su ne a cikin baki ko hanci.

    3.5 TAYAR DA HAYAƘI

    ‘Yan lakum sukan yi amfani da fankon ashana sai su ciro wurin da ake ƙyasta kan ashana sai su juya shi su goge shi ya koma lafai-lafai sai su shanya ya sha iska su aza wannan abun da suka goge a birkice a kan cokali, sai su kunna masa wuta idan ya ƙone zai bar maski a kan cokalin, sai su shafo wannan maskin a kan yatsunsu, to da zarar sun murza yatsun sai hayaƙi ya tashi a kan yatsun.

    3.6 YANKA WUƘA A JIKI

    Anan kuma ‘Yan lakum sukan yi amfani da wuƙa mai kaifi biyu sai su koɗa (wasa) ɗayan ɓangaren ya yi kaifi sosai, ɗayan ɓagaren kuma su dallasar (da kusarwa) da shi ta hanyar goga shi a kan kwalba. Sukan fito da wannan wuƙa a lokacin da suke gudanar da sana’arsu, su yanki wani abu take kaga ya rabe biyu, sannan sai ku ga kamar sun juya ɗayan ɓangaren wuƙar amma a zahiri ba su juya ba, su sake yankan abun sai ka ga ya sake rabewa biyu, a ganin jama’a kowane gefe yana da kaifi amma a zahiri gefe ɗaya ne ya ke da kaifi, wato wanda suke amfani da shi yayin yankan wani abu, amma idan za su yi gwaji a kan jikinsu sai su yi amfani da gefen da ba ya da kaifin ma’ana dakusasshen ɓangaren. Su kan yi haka ne don nunawa jama’a cewa su ba hakanan suke kara zube ba, a shirye suke, alhali kuma ba haka abun yake ba, dabaru ne da hikinkimu wanda kowa ma zai iya yi.

    3.7 TAYAR DA WUTA

    'Yan Lakum musamman 'yan rufani suna amfani da wani abu da ake kira mai kwalli da ake sayar wa a wurin 'yankoli da kuma sinadrin gilasirin sai a sa a takarda a naɗe su wuri ɗaya  sai a samu wuri a ɓoye naɗin ko ƙullin, a duk lokacin da wani mai wata lalura ya zo da matsalarsa sai su ce suna buƙatar ƙasar sawun ƙafarsa, sai a ce ya cire takalminsa ya taka ƙafarsa a ƙasa sai su ɗebi ƙasar sawun tafin ƙafar tasa su naɗe shi a takarda tamkar yadda suka naɗe waccen takardar ta mai kwalli da sinadrin gilasirin, daga nan sai su kaikaici Idanun mutun su musaya takardar da suka naɗe ƙasar tafin ƙafar mutum da takardar da suka ɓoye, wadda suka naɗe da sinadrin gilasirin da maikwalli, a lokacin da suke riƙe da takardar da suka naɗe da gilasirin da maikwalli  a hannunsu  sai su yi wata burga da barazana ta yin addu'a su aje ƙullin ƙasa,  sai su umurci mai matsalar da ya taka wannan takarda da suka aje kimanin sakan (second) biyu zuwa uku, to dama wannan haɗi na gilasirin da maikwalli nauyi kaɗan kuma na ɗan lokaci ƙalilan yake buƙata wuta ta tashi, da zarar ya taka kimanin sekan biyu zuwa uku yana ɗauke ƙafarsa sai wuta ta tashi, sai su faɗi masa cewa akwai babbar matsala domin akwai masu son su ga bayansa, a gaya masa yana da tarin maƙiya da mahassada a kewaye da shi saboda haka sai ya tashi tsaye, amma yanzu za a ba ka taimako wanda idan ka kiyaye  amfani da shi to sai dai ta Allah ba dai mutun ba. Sai su haɗa masa magani su karɓi kuɗi masu tsoka a hannunsa. A tunanensa ƙasar tafin ƙafarsa ce da aka ƙulle a takarda ta kama da wuta bai san an musaya ta da wani ƙullin na gilasirin da maikwalli ba.


    3.8 NAƊEWA

    Wannan babi na uku da ya gabata mai kanun fashin baƙin ma'anar kalmomin da suka shafi taken bincike babi ne da ya yi bayanin ma'anar kalmomin nazari, Hausa, lakum, da kuma 'yan lakum, sannan an yi bayani game da kashe kashen 'Yanlakum da kuma wasu daga cikin dubarun da suke yi a lokacin gudanar da sana'arsu daga ƙarshe aka naɗe babin.


    BABI NA HUƊU

    HAUSAR 'YAN LAKUM A GARIN GUSAU

    4.0 SHIMFIƊA

    Wannan babi na huɗu babi ne mai matuƙar muhimmanci a wannan aiki domin a ciki ne aka kawo takaitaccen tarihin garin Gusau, Hausar 'Yan lakum a garin Gusau, an fara kawo kalmomin da 'yan lakum suka samar a wannan rukuni na su, an kasa kalmomin ta la'akari da dubarar da aka yi amfani da ita, ko hanyar da aka bi yayin samar da waɗannan kalmomi na 'Yan lakum, bayan nan aka kawo yankunan jumloli da kuma jumloli na 'Yanlakum, daga ƙarshe aka zo da naɗewa.

    4.1 TAƘAITACCEN TARIHIN GARIN GUSAU

    Garin Gusau gari ne da aka kafa a shekara ta dubu ɗaya da ɗari takwas da sha ɗaya (1811) a hasashen kundayen bincike, wato bayan tasowa daga Yandoto a shekarar (1806).

    Gusau na ɗaya daga cikin manya-manyan garuruwan tsohuwar jihar Sakkwato, kafin garin ya zama babban birnin jihar Zamfara a shekara ta (1996). Kamar yadda kundin bayanin tarihin ƙasa na shekarar (1920) ya nuna, garin Gusau yana kan babban titin Sakkwato zuwa Zaria, wato kilo mita ɗari biyu da goma (210) tsakaninta da Sakkwato, kilo mita ɗari da saba'in da tara (179) tsakaninta da Zaria. A ɓangaren gabas Gusau ta yi iyaka da ƙasar Katsina da Kwatarkwashi, daga Arewa kuma, ta yi iyaka da ƙasar ƙaura-Namoda. A ɓangaren yamma kuma, Gusau ta yi iyaka da Bunguɗu. A ɓangaren kudu, Gusau ta yi iyaka da ƙasar Ɗansadau da Tsafe. (Gusau, 1912:7).

    Zuwan almajiran malam Shehu Usmanu Ɗanfodiyo wato malam Sambo ɗan'Ashafa ya kafa garin Gusau tare da sauran jama'arsa. Malam Sambo ɗan'Ashafa da almajiransa malamin addinin Musulunci ne, don haka, babu ruwan su da bautar iskoki, da tsafi da duk abin da ya shafi imanin Bahaushe na gargajiya da dukkanin camfe-camfensu.

    Duk irin bautar iskokin da Hausawa ke yi kafin zuwan addinin Musulunci malam Sambo ɗan'Ashafa da almajiransa ba sa yin su kuma a lokacin da ya zo Gusau bai samu irin waɗannan abubuwa na bautar iskoki a Gusau ba. Don haka, a wannan lokacin garin Gusau ba ya da tarihin Jahiliyya. Hakan ya sa duk al'adun Gusau al'adu ne irin na addinin Musulunci. Hakazalika, shigowar wasu mutane baƙi a Gusau bai sa garin ya gurɓace ba kuma Waɗannan kyawawan al'adun ba su lalace ba. Dalili a nan shi ne mafi yawan baƙin mutanen da ke shigowa a Gusau malamai ne na addinin Musulunci da kuma almajirai.

    Bugu da ƙari, Fulani da wasunsu kan zo garin Gusau domin samun tsira da addininsu, mutuncinsu da kuma dukiyoyinsu. Wannan ita ce shimfiɗar da al'adun Gusau ke kwance a kai kuma suke gudana a kan koyarwar addinin Musulunci da kyawawan al'adu irin na Fulani da Hausa waɗanda ba su ci karo da tsarin shari'ar addinin Musulunci ba.

    A Zamanin Mulkin Sarkin Katsinan Gusau wato Malam Muhammad Modibbo (1867 – 1876) aka samu kwararowar baƙi da ƙungiyoyin mutane daban-daban. Zuwan waɗannan baƙin ya sa garin ya samu bunƙasa a cikin ƙanƙanen lokaci. Haka kuma, a wanman lokaci ne aka samu sukunin gudanar da harkokin addinin Musulunci waɗanda suka shafi karatu, karantarwa, da kuma harkokin ibada ba tare da wata takura ko tsangwama ba. Bugu da ƙari, akwai cikakken tsaron rayukan mutane da dukiyoyinsu. Don haka, a wannan lokaci babu abin da ya sha wa mutanen Gusau kai face harkokin karatu, noma da kuma kasuwanci.

    Zuwan Turawan mulki mallaka a ƙasar Hausa da tasirin karatun boko ya sa wasu al'adu tsiruwa. Ana cikin haka sai ga shari'ar Musulunci ta sake kawo kai. An samu canje-canje da dama a wannan lokaci, domin an samu mutane da suka shahara da gudanar da tafsiri masallatan Jumu'a da wasunsu a garin na Gusau. A yanzu dai, garin Gusau yana da masarauta ɗaya rak, babban sarki ɗaya wato emiya (Emir). Wakilai ko uwayen ƙasa goma sha uku (13), yan majalisa goma sha takwas(18), sarautun fada kuma akwai akalla ɗari ɗaya da goma (110).

    Daga lokacin da aka kafa garin Gusau ya zuwa yanzu, an tabbatar da cewa an yi sarakuna da dama a lokuta daban-daban kimanin Sarakuna goma sha biyar (15), wato daga shekarar (1806) ya zuwa shekarar dubu biyu da ashirin da uku (2023). Saboda haka, Sarakuna da dama sun Jagoranci masarautar Gusau da mutanen garin Gusau. Don haka, ga jerin sunayen Sarakunan da suka yi mulki a masarautar Gusau daga shekara ta dubu ɗaya da ɗari takwas da shida (1806) zuwa shekara ta dubu biyu da ashirin da uku (2023) kamar haka;

    1. Malam Muhammad Sambo (1806-1827)

    2. Malam Abdulkadir (1827-1867)

    3. Malam Muhammad Modibbo (1867-1876)

    4. Malam Muhammad Tuburi (1876-1887)

    5. Malam Muhammad Gide (1887-1900)

    6. Malam Muhammad Murtala (1900-1916)

    7. Malam Muhammad (1916-1917)

    Akwai wasu sarakunan da suka yi sarautar Gusau bayan wadannan Sarakuna wadanda ba 'ya'yan wancan gidan na farko ba. Don haka, wadanda suka yi Sarautar masarautar Gusau ba daga gidan malam Sambo ba sun hada da;

    8. Muhammad Ummaru Malam (1917-1929)

    9. Muhammad Mai-Akwai (1929-1943)

    10. Usmnan Dansamaila (1943-1945)

    11. Ibralhim Marafa (1945-1948)

    12. Muhammad Sarkin Kudu (1948-1951)

    13. Alhaji Suleiman Isah (1951-1984).

    Waɗannan su ne suka yi sarauta waɗanda ba ya'yan malam Sambo ba. Bugu da ƙari, bayan wani lokaci, sarauta ta dawo gida. Sarakunan da suka yi mulki bayan sarauta ta dawo gidan sun hada da;

    14. Alhaji Muhammad Kabir Danbaba (1984-2015)

    15. Alhaji Ibrahim Bello (2015-ya zuwa Yau). (Wikipedia Masarautar Gusau).

    A takaice dai, waɗannan su ne Sarakunan da suka mulki masarautar Gusau daga shekarar (1806) zuwa shekarar (2021). Haka kuma, wannan shi ne takaitaccen tarihin Gusau ta malam Sambo.

    4.2 HAUSAR 'YAN LAKUM A GARIN GUSAU

    Kasancewar ‘Yan lakum rukuni ne na jama’a masu gudanar  da hulɗoɗinsu da  al’amurransu na yau da kulln a cikin al’ummar Hausawa, sannan ga su da dubaru da hikinkimu na karɓar kuɗi hannun mutane ya tilasta su samar da nasu karin harshen rukuni wanda idan ba cikinsu ka ke ba, ko sun yi magana a gabanka to da wahalar gaske ka iya fahintar abun da suke nufi. Sun ƙirƙiri kalmomi da jimloli masu tarin yawa domin sadarwa a tsakaninsu, ga wasu daga cikin irin waɗannan kalmomin nasu tare da ma’anarsu a daidaitacciyayar Hausa.

    4.2 SUNAYEN KUƊI A WAJEN ‘YAN LAKUM

    Kalma --  -- Ma’ana

    1. Kamsa  --  -- Biyar
    2. Gunza  --  -- Goma
    3. Muri  --  --  -- Ashirin
    4. Kamsuna  --  -- Hamsin
    5. Ata  --  --  -- Ɗari
    6. Ata da kamsa --  -- Ɗari da biyar
    7. Ata da kamsuna      --  -- Ɗari da hamsin
    8. Ataini --  --  -- Ɗari biyu
    9. Ata kamsa  --  -- Ɗari biyar
    10. Zugun --  -- Dubu
    11. Zugun wahid  -- Dubu ɗaya
    12. Zugun kamsa --  -- Dubu biyar
    13. Zugun ashara --  -- Dubu goma

     

    4.3 KALMOMI  TA  HANYAR ƘIRƘIRA

    Kamar sauran hanyoyin samar da kalmomi, Zarruk (1993) ya bayyana ma’anar ƙirƙirar kalma da ƙago wani laƙabi ko wata magana don bayyana wata baƙuwar ma’ana. Haka kuma ya raba ƙirƙirar kalma zuwa gida biyu kamar haka: (i) ƙirƙirar bazata, da (ii) ƙirƙirar takanas. A nan za a yi bayanin wasu daga cikin kalmomin da ‘Yan lakum ke amfani da su a cikin mu’amalarsu ta yau da kullum wadda yanayin sana’arsu ce ta sa suka samar da kalmomin kuma suke amfani da su a cikin harkokinsu. Wato ƙirƙirar kalmomin su ka yi, sannan alamu sun nuna cewa sun samu kalmomin ne ta hanyar ƙirƙirar bazata. Waɗannan kalmomin sun haɗa da:

    Kalma -- Ma’ana

    1. Asawa --  -- Mahaifi/tsohuwa   
    2. Asawanya   -- Mahaifiya/ tsoho
    3. Ɗarani --  -- Mashin
    4. Ɗan-gwabso -- Ɗan-daga
    5. Ɗan-tanko --  -- Mai shan taba
    6. Ɗanwara --  -- Ɗangiya
    7. Fariguza --  -- Rago
    8. Gulamin-ta-sulaiman --  -- Memori
    9. Guza --  --  -- Gaban namiji
    10. Kwasasshe -- Maikuɗi
    11. Kanɗa --  --  -- Sha
    12. Ƙiri --  --  -- Mai kyau
    13. Kiɗima        -- Ɗaki
    14. Mago --  --  -- Magani
    15. Magori --  -- Mai magani --
    16. Mani --  --  -- Gaban mace
    17. Natuta --  -- Talaka
    18. Nazauran --  -- Bazawara
    19. Sogaye --  -- kaya
    20. Sunƙi --  --  -- Ɗaki
    21. Sunƙin mai duka -- Masallaci
    22. Sogan na sheɗan -- kayan kallo
    23. Sogayen nakare -- Takalmi
    24. Sogayen amalu -- Kayan aiki
    25. Takaka-- Bindiga
    26. Takakoki --  -- ‘Yan bindiga
    27. Sagin mai duka     -- Hadari
    28. Samaka       -- Mahaukaci
    29. Ta-baba-alula -- Keke
    30. Ta-sulaiman-- Waya (hanset)
    31. Watu --  --  -- Abinci
    32. Watun yarima --  --   -- Tuwon masara
    33. Watun risi --  -- Tuwan shinkafa
    34. Watun kwoc -- Tuwon dawa

    4.4  KALMOMI TA HANYAR KWATANCE KO SIFFANATAWA

    A nan ‘Yan lakum sukan yi amfani da dabarar kwantance ko siffantawa yayin laƙabawa wani abu suna a rukuninsu, ta hanyar danganta wannan abun da wata ɗabi’a ko halayya ko yanayin halitta ta wani mutum ko wata dabba ko wani abu da ya ke da wannan ɗabi’a ko kuma yake yawan aikata ta, misali

    Kalma     --  -- Ma’ana

    1. Dage  --  --  -- Faɗa
    2. Fara --  --  -- Tunkiya
    3. Jaa --  --  -- Akuya
    4. Kwata --  -- Jini
    5. Mai ƙafon tsumma     -- Mai gari
    6. Na-kasa  --  -- Barci/kwana
    7. Na-shanshani -- Ƙafafu
    8. Na-jaki  --  -- Duka/bugu
    9. Na-tunku --  -- Kashi
    10. Kwaɗo --  -- Fitsari
    11. Na-auduga --  -- Dariya
    12. Na-maraya --  -- Kuka
    13. Na-amarya --  -- Kunya
    14. Na-zomo --  -- Gudu/Sauri
    15. Na-kura --  -- Tsoro
    16. Na-lawan --  -- Rago
    17. Na-kahu --  -- Karatu/Ilimi
    18. Na-giwa --  -- Girma
    19. Na-gyaɗa --  -- Fetur
    20. Na-kujeri --  -- Ɗuwawu
    21. Na jiyamu       --  Ido
    22. Santal   -- Gaskiya/Naƙwarai
    23. Sansiro --  -- Sanyi
    24. Ta-manzo --  -- Sadaka
    25. Tatalmizu       -- Sadaka
    26. 'Yar gabas --  -- Sallah

     

    4.5 ARO (BORROWING)

    Rufa’i (1979) ya bayyana ma’anar aro a harshe da hanya ce da harshe ke aro kalmar wani harshe ya sauyata zuwa harshensa. Wannan bincike ya lura da cewa akwai kalmomin da ‘yanlakum suka samo kuma suke amfani da su ta hanyar aro daga sauran harsuna musamman harshen larabci, da kuma kaɗan daga wasu harsuna. Misali:


    Kalma --  --  -- Ma’ana

    1. Aƙalu --  --  -- Hankali
    2. Ainu --  -- Ido
    3. Badawi--  -- Gari
    4. Baɗalu --  -- Ciki
    5. Dari --  -- Gida
    6. Gulami --  --  -- Yaro
    7. Gulama        --   -- Yarinya
    8. Istoma --  --  -- Ciwon olsa
    9. Jasadun      --  --  Jiki
    10. Ju’i --  -- Yunwa
    11. Ƙauli --  -- Magana
    12. Lahamu --  --  -- Nama
    13. Lailu --  -- Dare
    14. Labanu --  --  -- Nono
    15. Lasuwaki --  --  -- Kasuwa
    16. La  --  -- Ba (Nagation)
    17. Maridanci --  --  -- Rashin lafiya
    18. Ma’i --  -- Ruwa
    19. Nari   --  -- Zafi/ Wuta
    20. Naka --  -- Kwana
    21. Siyam --  -- Shekara
    22. Rijalu --  -- Babban mutun
    23. Ra’asu --  --  -- Hula
    24. Sayyara --  --  -- Mota
    25. Sariƙu --  --  -- Ɓarawo
    26. Sariƙai --  --  -- Ɓarayi
    27. Sha'aru     -- Gashi
    28. Ta’allaƙa --  --  -- Laya

     

    4.6 KALMOMI TA HANYAR GUSAR DA MA’ANA DA JUYAR DA GAƁOƁIN KALMA

    A nan ‘yan lakum suna ɗaukar wasu kalmomi na Hausa sai su sauya ma’anarsu, wato su ba su wata sabuwar ma’ana koma bayan wadda aka san su da ita ta ainihi ko asali. Haka kuma sukan ɗauki kalma sai su juyar da furucinta wato gaɓar farko ta koma ƙarshe ita kuma ta ƙarshe ta dawo farko, wanda ake kira (metathesis) a harshen Ingilishi da harshen Hausa kuma ana ma shi  lakabi da rawar 'yan mata.

    Misali:

     

    Kalma --  -- Ma’ana

    1. Bututu    -- Lasifika
    2. Duƙowa --  -- Zuwa
    3. Hita --  --  -- Ƙyale
    4. Isa  --  --  -- Wanda bai jin Hausar
    5. Jewa  --  --  -- Wani wuri
    6. Ƙashi  --  -- Ɗan-Sanda
    7. Kattafawa --  -- Haɗawa
    8. Kafan --  -- Fanka
    9. Katako --  -- Soja
    10. Liman --  -- Aure
    11. Naɗewa --  -- Kamawa
    12. Saukewa --  -- Yi
    13. Saukewa --  -- Bada wani abu
    14. Sirba --  --  -- Basir
    15. Turba --  -- Batur
    16. Tuta  --  --  -- Rashi/Babu
    17. Tsamaku --  -- Iskoki
    18. ‘Yankanɗe-kanɗe -- Shaye-shaye
    19. Zubawa/Zubairu  --  -- Tafiya

    4.6.1 Jimlolin ‘Yan Lakum

    Baya ga kalmomin da ‘yanlakum suka ƙirƙira sai kuma jimlolin da suka ƙirƙira kuma suke amfani da su a harkokinsu na yau dakullun. Sun ƙirƙiri waɗannan jimloli ne ta hanyar harhaɗa waɗannan kalmomi nasu domin su ta da jimla mai ma’ana, ga wasu daga cikin su:

    4.6.2 Hausar ‘Yan Lakum  --  -- Daidaitacciyar Hausa

    1. Magon magorin nan santal ne -- Maganin mai maganin nan na gaskiya ne.

    2. Zan zuba in sauke ‘yar gabas. -- Zan tafi in yi Sallah

    3. Laja la ƙiri. --  -- Ba kasuwa

    4. La sauke gulami  -- Ba haihuwa

    5. Ana sauke gulamai suna bajewa. Ana haihuwa yaran na mutuwa.

    6. Hita da shi.  --  -- Ƙyaleshi

    7. Maridanci ya naɗe ni. --  -- Rashin lafiya ta kama ni.

    8. Ɗaranin asawana ne. -- Mashin ɗin mahaifina ne.

    9. Kattafa mani ta’allaƙa --  -- Haɗa mani laya.

    10. Tsamaku sun nake mata ga baɗalu   Aljanu sun mata kwance ga ciki

    11. Mu zuba kawai. -- Mu tafi kawai

    12. Ga ni nan duƙowa -- Ga ni nan zuwa.

    13. Kwata la duƙowa -- Jini ba ya zuwa

    14. La na-kahu  --  -- Jahili/ ba ilimi

    15. Jalabce --  --  -- Zauna

    16. Ɗanka mai ƙiri -- Budurwa mai kyau.

    17. Na faɗa da ɗankar nan --  -- Budurwar nan ta burge ni

    18. Sauke man ata kamsa. --  -- Bani ɗari biyar.

    19. Asawan abokina ne ya baje -- Mahaifin abokina ne ya rasu.

    20. Yana dari yana naka. --  -- Yana gida yana barci

    21. Naɗo shi a ta-sulaiman. --  -- Kirashi a waya.

    22. Hita da gulamin nan --  -- Kyale yaron nan.

    23. Na hita da ɗankar nan  --  -- Na ƙyale budurwan nan

    24. Ɗankar nan ta naɗo ni --  -- Budurwan nan ta kira ni

    25. Gulamin nan ya zuba --  -- Yaron nan yatafi.

    26. Rijalun nan ya baje -- Mutumin nan ya mutu.

    27. Jalabce ka yi watu  -- Zauna ka ci abinci.

    28. Ɗankar nan la nakahu --  -- Budurwar nan jahila ce.

    29. Ka sauke ‘yargabas? --  -- Ka yi sallah.

    30. Maridanci ya naɗe asawana -- Babana ba ya da lafiya.

    31. Zuba kawai ga ƙashi nan duƙowa  Tafi kawai ga ɗan sanda nan

     zuwa.

    32. Tarani --  --  -- Na gane.

    33. La tarani --  -- Ban gane ba.

    34. Na Kwaɓe --  -- Na bari

    35. Siyam wahid --  -- Shekara daya

    36. Siyam salasa --  -- Shekara uku

    37. Siyam hamsa --  -- Shekara biyar

    38. Naka Wahid --  -- Kwana ɗaya

    39. Naka arba --  -- Kwana huɗu

    40. Naka sitta --  -- Kwana shida

    41. Badalta --  --  -- Ɓoye

    42. Kurantar da shi -- Tsoratar da shi

    43. Amalus subhi --  -- Aikin safe

    44. Amalul laili --  -- Aikin dare

     

    4.6  NAƊEWA

    Wannan babi wato na huɗu babi ne da kusan ya tattauna ilahirin aikin ɗungurungum, domin bayan an yi magana a kan taƙaitaccen tarihin garin Gusau. Sai kuma aka kawo Hausar 'yanlakum a garin Gusau, an fara kawo kalmomin da 'yanlakum suka samar a wannan rukuni nasu, an kasa kalmomin tala'akari da dubarar da aka yi amfani da ita, ko hanyar da aka bi yayin samar da waɗannan kalmomi na 'yanlakum, bayan nan aka kawo yankunan jumloli da kuma jumloli na 'yanlakum, daga ƙarshe a ka zo da naɗewa.

    BABI NA BIYAR

    SAKAMAKON BINCIKE

    5.0 SHIMFIƊA

    A wannan babi na ƙarshe mai kanun sakamakon bincike babi ne da zai yi magana akan sakamakon bincike da kuma bayar da shawarwari ga ɗalibai da sauran manazarta. wannan bincike mai taken "Nazarin Hausar 'Yan Lakum A Garin Gusau" Bincike ne da aka gudanar da zummar gano manufa da kuma ma'ana a cikin zantukan 'yanlakum musamman na garin Gusau an tsara binciken a kan tsarin babi babi tun daga babi na daya har zuwa na biyar kowanne babi yana dauke da muhimman bayanai masu amfani ga al'umma musamman ɗalibai da manazarta.

    5.1 SAKAMAKON BINCIKE

    Sakamakon wannan bincike ya yi daidai da maƙasudi ko manufar binciken domin kuwa an samu nasarar:

    v  Zaƙulo wasu daga cikin kalmomin da ‘yanlakum suka ƙirƙira kuma suke amfani da su a zantukansu na yau da kullun kamar yadda ya gabata.

    v  Zaƙulo ‘yankunan jumloli da kuma jumloli da suka ƙirƙira daga waɗannan kalmomi nasu na fannu kamar yadda ya gabata.

    Sannan idan an lura da kyau a cikin gundarin aikin, za a fahimci cewa daga cikin dabarun da 'Yanlakum suke amfani da su ko suke  bi wajen samar da kalmomin su akwai:

    v  Ƙirƙira: Wato su ƙirƙiri wata sabuwar kalma wadda babu ta kwatakwata a harshen Hausa  domin ambaton waɗansu ababe.

    v  Aro: (Borowwing) 'yanlakum sun ari kalmomi masu yawan gaske musamman daga harshen Larabci zuwa Hausar rukuninsu.

    v  Kwatance da Siffantawa: Sannan sukan yi amfani da dabarar kwatance da siffantawa wajen laƙaba wa wasu ababe suna misali nakasa (bacci), na shanshani (ƙafafu) na maraya (kuka)

    v  Gusar da Ma’ana: Baya ga wannan sukan ɗauki wata kalma ta Hausa sai su sauya ma’anarta da wata ma’anar ta daban saɓanin wadda ɗaukacin mutane suka sani.

    v  Sauya Gurabun Gaɓar Kalma: (metathesis)  rawar ‘yan mata wato na gaba ya koma baya inda ake ɗaukar gaɓar kalma ta farko amayar da ita baya a ɗauki ta baya a mayar da ta ta farko. Misali turba (batur), sirba (basir) da makamantansu.

    5.2 SHAWARWARI

    ko shakka babu harshen Hausa harshe ne  mai tagomashi da kwarjini a idon duniya, harshe ne da Allah (S.W.A) ya azurta da hikimomi masu tarin yawa da kuma al'umma masu kaifin basira da zalaƙa. Saboda haka ya zama wajibi ga al'ummar Hausawa masana da su dukufa wajen rubuce rubuce cikin harshen Hausa a fannona daban daban na ilimi tun daga ɓangaren kimiyya da fasaha da ƙere ƙere da ma sauran fannoni na ilimi domin bunƙasa da ci gaban harshen Hausa a duniya. Domin kowace al'umma ita ke ɗaukaka harshenta ta hanyar girmama shi da darajanta shi, haka ita ke durƙusar da harshenta ta hanyar wutaƙanta shi da tozarta shi. Don haka ya zama wajibi gare mu Hausawa wajen ƙara azama da ƙoƙari don ganin wannan harshe mai albarka ya ciri tuta a duniya.

    Da farko dai muna kira ga ɗalibanmu na wannan lokaci su yi ƙoƙari su rika zaɓar harshen Hausa a matsayin abin da za su yi nazari akai idan za su tafi makarantun gaba da sakandare, wannan shi zai kara bunƙasa harshen.

    Sannan  masu gudanar da bincike musamman ɗalibai, idan za a yi nazari ko bincike a kan wani abu daga sassa ko rassan Hausa guda uku wato Harshe, da Adabi, da kuma Al'ada, ya kamata a tsaya tsayin-daka a natsu tare da bin ingantattun hanyoyi domin gudanar da bincike mai inganci da nagarta.

     

    Bayan haka yayin gudanar da bincike a riƙa yin amfani da harshe mai sauƙi domin samun sauƙin fahimta.  

    Kira ga ɗalibai 'yan'uwa gaba ɗaya musamman masu nazarin harshen Hausa da su ƙara faɗaɗa karatu idan an samu dama.

    Haka kuma, a na ba da shawara zuwa ga malamanmu na wannan sashe mai albarka, wato sashen nazarin harsuna da al'adu, da su ƙara azma da ƙoƙari a kan wanda suke yi domin ganin samun nasarar ɗalibansu da su kansu kamar yadda suka saba.

    Daga ƙarshe, muna ba da shawara zuwa ga masana, da masu ruwa da tsaki, da kuma masu sha’awa da harshen Hausa su riƙa ɗaukar nauyin wasu ɗalibai suna tura su jami'o'i daban-daban na gida da na waje domin nazarin harshen Hausa, da kuma ɗaukar nauyin buga littattafai da rarraba su zuwa makarantu da ɗakunan karatu na makarantu daban-daban.

    5.3 NAƊEWA

    Hausawa na cewa Karshen tikatika tik kuma komai nisan dare gari zai waye sannan komai nisan jifa ƙasa za ta faɗo, haƙiƙa komai ya yi farko to shakka babu zai yi ƙarshe, cikin iyawar mai kowa mai komi a nan muka zo ƙarshen wannan bincike mai taken Nazarin Hausar 'Yan Lakum A Garin Gusau

    A babi na ɗaya, an yi tsokaci a kan manufar wannan bincike da farfajiyar bincike da hasashen bincike da matsalolin bincike da muhimmancin bincike da hanyoyin gudanar da bincike da ra'in bincike sai kuma a ka zo da naɗewa a ƙarshen babin.

    A babi na biyu, mai kanun bitar ayyukan da suka gabata. Bayan anyi Shimfiɗa, sai bitar ayyukan da suka gabata, an fara da rubutattun littatafai, sai kundayen bincike da aka rubuta a matakai daban-daban na ilimi, sai kuma muƙalu da mujallu duka dai masu nasaba da kuma alaƙa da wannan bincike, sai kuma hujjar ci-gaba da bincike, daga ƙarshe a ka zo da naɗewa.

    Babi na uku mai kanun fashin baƙi a kan ma'anonin da suka shafi taken bincike, bayan an yi Shimfiɗa, an kawo ma'anar kalmar Hausa, da ta lakum, da kuma 'Yan lakum, sannan an kawo kashe-kashen 'yan lakum, daga nan kuma aka zo da wasu daga cikin dabarun 'yan lakum, sai kuma naɗewa.

    Babi na huɗu, mai kanun Hausar 'Yan Lakum a Garin Gusau. An fara da Shimfida, takaitaccen tarihin garin Gusau, Hausar 'yan lakum a garin Gusau, an fara kawo kalmomin da 'yan lakum suka samar a wannan rukuni nasu, an kasa kalmomin tala'akari da dubarar da aka yi amfani da ita, ko hanyar da akabi yayin samar da waɗannan kalmomi na 'Yan Lakum, bayan nan aka kawo yan kunan jumloli da kuma jumlolin Hausar 'yan Lakum, daga ƙarshe aka zo da naɗewa.

    A babi na biyar, mai kanun sakamakon bincike. Bayan an yi shimfiɗa, sai aka kawo sakamakon bincike, daga nan kuma aka zo da shawarwari sai kuma jawabin naɗewa da manazarta.

     


    MANAZARTA

    Abdulkadir, M. (2018). “Hausar Rukunin Yan Banga a Garin Gusau.” Kundin Neman Digirin Farko A Jami'ar Tarayya Gusau.

    Abdulƙadir, Z. (2013). “Karin Harshen Rukuni: Nazarin Hausar Kan Titi”.Unpublished M.A Thesis. Zaria, Ahmadu Bello University.

    Abubakar, I. A. (2001). “Dangantakar Harshe Da Addini: Nazari Akan Karin Hausar Gardawa a Birnin Kano da Kewaye”. Maƙala da aka Gabatar A taron ƙarawa Juna Ilimi Tsakanin Malamai da ɗalibai. Kano: Jamiar Bayaro. (Unpublished).

    Adamu, A.U. (2008). “Salon Ta ɗin Mata Hausawa a cikin Garin Kano.” Kundin Digiri na Biyu,Sashen koyar da Harsunan Nigeriya. Kano; Jamiar Bayero.

    Adamu, M.T (1997). Asalin Hausa da Harshensu. Kano Dansarkin Kura Publishers, 1997.

    Amfani A.H (2012). “Hausa da Da Hausawa: Jiya da Yau da Gobe, in Amfani, H.A, et al (eds.) Champion of Hausa Cikin Hausa.” Zaria Ahmadu Bello University Press, 2012.

    Azare, Y.M.(2011).  “Language  In  Diversity:  A  Look  At  The  Role  Of  Women  Towards Language  Development  In  Hausa  Socio-Lingustics  Setting”.  In Studies In Hausa Language, Literature and Culture.  The 6th Hausa International  Conference.  CSNL, Kano:  Bayero University.

    Babanzara,  M. H.  (2006).  “A  Typology  Of    Hausa  Jargon”.  In  Journal  Of  Humanities Vol.3.No.4, Fuculty  of Art and  Islamic  Studies, Kano: Bayero Universty.

    Bunza, A. M. (2017). Dabarun Bincike. Zaria, Ahmadu Bello University press Limited.

    Dawakin Tofa, M. I. (2005). “Karin Harshen Mahauta.” Kundin Digirina Biyu, Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya Kano: Jamiar Bayero.

    Fagge,  U. U. (2002). “Zaurancen Zaurawa a Birnin Kano Da Kewaye”.  In  Algaita  Journal  Of Current Research  In Hausa.  Vol.2  No.1.

    Fagge, U. U. (1999). “Tasirin Karin Harshe na Rukuni wajen ƙirƙirar Sababbin Ma’anoni a Hausa”. Takardar Da aka Gabatar a taron ƙara wa Juna Ilimi. Sashen koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jamiar Bayero.

    Fagge, U. U. (2001). Ire-iren Karin Harshen Hausa Na Rukuni. Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Rufa’i, A. (1979). "Principal Resources of Lexeme – Formation in Hausa.” Harsunan Najeriya. Kano. Bayero University.

    Zarruƙ da Wasu. (1986). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa. Ibadan University Press Limtied.

    Zarruƙ, R. M (1993) Aro da Kirƙira A Harshen Hausa. Institute of Education. Zaria. Jami’ar Ahmadu Bello.

    https://www.amsoshi.com/2022/03/hausar-rukunin-masu-sanaar-waya-garin.html?m=1

    https://www.google.com/amp/s/docplayer.net/amp/54653968-Karin-harshen-rukuni-nazarin-hausar-masu-sana-ar-kayan-gwari-hamisu-ahmed-ma-arts-16486.html

    Muntari, H. (2008). “Karin Harshe Na Rukuni A Hausa: Nazari A ƙasar Zazzau. Kundin Digiri na Biyu”. Sashen Harsuna da Aladu na Afirka Zariya: Jamiar Ahmadu.

    Musa, A.  (2011).  “Hausa-Niga:  Nazari  A  Kan  Walwalar  Harshe  Da Zamantakewa  Tsakanin Rukunin  Matasa  Maza  Hausawa  A  Yau”.  In Studies of Hausa Language,  Literature And  Culture.  The Sixth Hausa International Conference. CSNL.  Kano:  Bayero University.

    Salihi, T. M (2012). Sakace A kan Karin Harshen Hausa. Absur Comprint. F. C.E, Kano.

    Salihu, N.A (1987). “Code Switching among University of Sokoto Hausa-English Bilingual”. Kundin binciken digirin farko a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya: Jami'ar Usmanu Danfodiyo Sokoto.

    Sani, A. & Sani, A. U. (2023) “Daga Hausar Rukuni Zuwa Boyayyiyar Al'ada”: Kebabben Nazari A Kan Hausar Telolin Garin Gusau. Journal of Language, Literatire And Culture: Publication of the Department of Languages and Cultures, Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria.

    Tukur, A. (2020) “Hausar Rukunin Masu Sana'ar Waya A Garin Gusau.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna Da Al'adu, Jami'ar Tarayya Gusau.

    Umar, M. M. & Abbas, N.I. (2020) “Nazarin Hanyoyin Samar da Hausar Wasu Rukunan ‘Yan Kasuwa a Cikin Garin Sakkwato”. Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University Sokoto, Nigeria

    Yahaya, S. (1998). “Hausa a Jami'a. Kundin Neman” Digirin Farko A Jam'ar Usmanu Danfodiyo Sokoto.

    Yakasai,  M.G.  (2004).  “ Yanayin  Karin  Sojoji  A  Barikoki”:  Nazari  a  kan  Barikokin  Bukabu Da  Na  Jan-Guza”.  Kundin Digiri Na Biyu. Sashen Koyar da Harsuna Nijeriya.  Kano: Jamiar Bayero.

    Yakasai,  S.  A  (2005).  “Aro  Ko  Ƙirƙira:  Nazrin  Samuwar  Sababbin  Kalmomin Hausa” A Jamia  Da  Kuma  Garin  Sakkwato.  Takardar  Da  Aka  Gabatar  Wajen  Taron  Ƙara  Wa Juna  Sani. Sakwwato:  Jamiar Usmanu Ɗanfodiyo.

     Yakasai, S. A. (1988). “Verbal Honorifics in Hausa:  A Sociolinguistics Analysis”. Phd Theseis. Kano: Bayero University.

    Yakasai, S. A.  (2010). “Dangantakar Harshe da Muhallin Magana:  Nazari Kan Magana Tsakanin Hausawa”. In Harsunan Nijeriya Volume XXII.  Center For the Study of Nigerian Languages. Kano: Bayero University.

    Yakasai, S. A. (2012).  Jagorar Ilimin Walwalar Harshe. Sokoto:  Garkuwa Media Services LTD.

    Yero, Z. S. (2017) “Hausar Yaran Mota”: Nazarin Ma'ana Da Ginin Jimla. Kundin Digiri Na Biyu. Sashen Koyar Da Harsuna Da Al'adun Afirika: Jami'ar Ahmadu Bello Zaria.

    https://ha.m.wikipedia.org/wiki/Masarautar Gusau.

    WAƊANDAAKAZANTADASU:

    1.      Malan Sanusi Muhammad (Malan Muhammadu) dan shekara 35, Ranar Lahadi 8/1/2023

    2.      Malan Umar Ibrahim shekare, ɗan shekara 25, Ranar Litinin 9/1/2023.

    3.      Malan Usman Malan Ibrahim Kagane, ɗan Shekara 40, Litinin 9/1/2023.

    4.      Doctor Sulaiman Shala Gusau, ɗan shekara 38, Ranar Talata1 0/1/2023.

    5.      Malan Sule Tsoho Gusau, ɗan shekara 27, Ranar Alhamis 6/7/2023.

     www.amsoshi.com

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.