In kin Karanta ki yi sharing pls
Har sun wuce
Salisu ya riƙo
shi "Please ka zo muje yau ɗaya
dai"
Kallon agogo
Muktar ya yi " na faɗa
ma so nake in kwanta da wuri"
Tsaki Salisu ya yi " kwanciya at this time kofa magariba ba ai ba, ko kuma baka sallah ne yau?"
Haushi ne ya
kama Muktar "kaifa ɗan
iska ne wallahi, to wanki nake son inyi in maka short test ɗin da na musu and ina son
duba Google"
Watsa hannu
Salisu ya yi " ba zancen iskanci na sani ko ka fara al'ada ne, yanzu muje in
mun dawo zan taya ka wankin"
Dafe kai
Muktar ya yi " wai ana dole ne?, ni kasan sam bans son sabgar ‘yan
mata wallahi, bare ma ƙaramar yarinya irin Maryam ba in da zani"
Jan sa Salisu
ya fara "wallahi sai kaje" jin ya rantse ya sa Muktar kawai bin sa s
baya rai a ba ce, shi in za ai komai kar asashi sabgar mata.
Tsaye suke ƙofar
gidan su Maryam ɗin
Muktar ya harde hannun sa a yalwataccen ƙirjin sa, fuska a ɗaure, Salisu ne ya matso "dan Allah Malam
ka taimaka ka saki ranka karka tsoramun ita" hararar sa Muktar ya yi,
fitowar Maryam ya sa shi fasa faɗar
abin da zai ce, ya ɗan
saki fuskar sa kaɗan.
Fuskar ta ɗauke da fara'a ta ɗan rissina " lah Malam
yau da kai aka zo ina wuni?"
Kafin ya amsa
Salisu ya yi caraf ya ce " eyye mai nake son gani wato idaniyar ba ni suka
fara gani ba wato to walllahi kishi nake"
Dariya ta yi
"Haba Masoyin Maryam kaima kasan kai na fara gani wai in fara girmama shi
matsayin baƙo"
ta faɗa cikin salon
tata yaudarar, "anma ka yi haƙuri bari inkuma fitowa" ta faɗa kamar za ta juya .
Murmushi ya yi
" ai na san ni kika fara gani" taɓo
Muktar ya yi wanda ya yi saƙaro yana kallon su, kallon da bazaka iya cewa na mamaki bane
ko na jin haushi " Malam tana gaida ka ka yi tsit"
Murmushi
Muktar ya yi " ba shiru na yi ba jira nake ku gama soyayyar sai in
amsa" kunya ce ta rufe Maryam ko da Muktar bai koyar da ita ba a secondry
shiɗin bai da kalar
raini bare kuma malamin ta ne.
"Koma dai
mene ni karka sa ta dena magana zo ka tafi," Salisu ya faɗa yana ɗan ƙoƙarin tura shi.
Murmushi ya yi
"dadai ni na kawo kaina shi ne za a koren, Malama Maryam mu kwana
lafiya" ya faɗa
kafin ya bar gun.
Har ya wuce ya
dawo duda gari ya fara duhu amma hakan bazai sa ya kasa gane ɗaya cikin ƙannen
sa ba duk inda ya ga wani, Hajara ya hango lafe jikin dutsen dala inda ya raba
layin da gidaje ya yin da Garba ke tsaye jikin gidan yana kallon ta kwatar da
ta raba siririn layin ta musu tsakani dariya kawai take da alamu hirar ko abin
da ya faɗa ma ya mata
daɗi.
Rai ɓace Muktar ya ƙarasa
sam ba ta ankara da shi ba lokacin da yake tawowa sai muryar sa ta ji
"Uban me kike ana" a tsora ce ta bar gun da ɗan gudun ta ba tare da ta tsaya ba shi amsa
ba.
A fusace ya
juyo ya kalli Garba wanda ya yi tsuru tsuru "yanzu in ƙanwar
ka ce za ka ji daɗi
wani kato ya jawo ta zance wani gurin ba ƙofar gidan ku ba?"
Sosa ƙeya
Garba ya hau yi " wallahi ba cutar da ita zan ba nifa auren ta
za..""
Ɗaga
masa hannu Muktar ya yi "zaka aure tan ka kasa jurewa a baka damar zuwa
gida zance, malam ka fita sabgar ta tun kan ‘yan sanda suyi mana iyaka" fuuu ya
bar gun
Ita kuwa
Hajara tana zuwa gida ɗaki
ta shige hankali tashe sam batayi tsammanin ganin yayan nata a hanyar ‘yan
Kado ba tun da tasan sam baya yin area ɗin
shi ya sa ma ta ce su dinfa haɗuwa
da Gaban anan.
"Ke
Hajara!!!" Ya faɗa
cikin hargowa lokacin da ya shigo gidan "kina ina ne ko sai na fito da ke
na tattataki ki"
Jiki a saluɓe ta fito gaban ta na faɗuwa sam ba ta son abu ya haɗata da yayan nata bare irin
wannan, cikin faɗa
yake magana " wato da na ce ki fita sabgar yaron nan shi ne kika koma
binsa wani gurin ko, wato ke ba zaki iya maraicin ki ba"
Cikin rawar
murya ta ce " wallahi yaya Inna ce ta aikeni ‘yan kado gurin Musa mai
kilishi shi ne nagan shi tsayawa ta ke nan mu gaisa ka zo gun Allah" ta faɗa tana ɗaga hannu sama.
Tsaki yaja
" nidai shawara zan baki da ki ɓata
sunan ki gwanda ki ce ya fito a aurar da ke kowa ya huta" ya faɗa tare da shiga ɗaki ba tare da jiran amsar
taba.
Inna ce ta
kalle ta " Gaskiya ya faɗa
miki gwanda ki ce ya fito kowa ya huta, ni da ki jaza min masifa a gari, ƙarim
wani zagin a unguwar na ban muku tarbiyya ba gwamma ko ba shi ne in ɗauko inmiki kayan
gado"
"Allah
inna kawai gaisawa za muyi yaya yazo..." Harar ta kawai Inna ta yi ta kasa
karawa.
** ****
Yes shigo ya
faɗa lokacin da take
buga ƙofar
Hafsa ce rike da riguna kala biyu ta shigo ɗakin
wanda baka jin komai sai ƙamshin air freshener mai sanyaya zuciya ɗan ta shi zaune Usman ya yi
daga kwanciyar da ya yi ya dube ta " to sarkin damu mene kuma, kinsan dai
ba ɗin ki nake ba
ko?"
Murmushi ta yi
" kai yaya Usman nima ba ɗin
ki na kawo ma, tayani zaɓa
wanne zai fi mun kyau za mu je ɗan
wani outing ne."
Zaro ido ya yi
" what are you mad ke da waye" dariya ta yi "kalli fuskar ka to
ni da Hidaya da Bilkisu ne" ajiyar zuciya ya yi ta wasa "oh na ɗauka keda wasu ƙatti ne
yanzu mutun ya jawowa kansa"
Dariya tasa
mai ƙarfi
" kaji Yaya Usman da kuri sai ka ce za ka iiya wana abu"
Kwafa kawai ya
yi " Allah yarinyar nan kin rainani walllahi, wannan ta fi kyau" ya
nuna ta hannun daman ta.
Kallon ta ta
yi na sakanni " No wannan ta fi" ta faɗa
kafin ta fice girgiza kai ya yi wannan yarinyar da matsala take da tasan wadda
take so za ta zo damun sa.
Bai gama tunanin
ba ta dawo "baka ban gudunmawa ba, jiya naje gidan yaya Sadik ya ba ni nasa
saura kai" ta fada tana miƙa hannu.
"Ni mai
zan baki?, Shi ai rich man ne ni kinsan am broke, Lecturers are not rich"
"please joke aside miƙo
sauri nake" ta faɗa
tana miƙa
hannu
Hannu ya sa a
aljihu ya ciro kuɗi
kan ya ce wani abu ta amsa Thank you Yaya" ta faɗa tare da yin waje murmushi ya yi tare da miƙewa ya
rife ƙofar
sa kafin ta zo ta ce shi zai kai su.
Ta yi kyau
sosai zakai tsanmanin biki zasu, a nutse take sakkowa daga bene " Mum na
tafi" ta faɗa
lokacin da ta leƙa ɗakin
Mum ɗin," ina
kuma zaki?"
Murmushi ta yi
" tunfa last week nake ce miki za mu ɗanje
cin abinci da su Hidaya jiyama na faɗa
miki"
Fitowa Mum ɗin ta yi " kuma
ahaka" ta faɗa
tana kallon ta
Kallon kanta
Hafsa ta yi alamun mai na yi.
"Yanzu ke
sai ki fita da tsunmokaran nan?"
"Lah Momy
tsummokara fa, waɗan
nan ɗin?"
Banza Momy ɗin ta mata tare da yin sama
hakan ya sa Hafsan bin bayan ta wasu kayan ta canja mata sanadin tana sauri ya
sa ta kasa musu ta karba ta canja tare da yin waje suka nufi gidan su Bilkisu,
Umman su ta fara tozali da ita a falo cike da fara'a ta amsheta suka gaisa
kafin ta wuce ɗakin su
Bilkisun.
Ƙanwar
Bilkisun na kan gado tana kallo a system ta shiga tana ganin ta ta hau murmushi
suka gaisa "kardai ki cemun ba ta kintsa ba?"
Murmushi Ummi
ta yi "yanzu ta shiga wanka" mita Hafsa ta fara " lallaima matar
nan da kinsan baki shirya ba shi ne zaki yi ta azazzala ta"
Shigowar
Bilkisun ya sata sake sabuwar mita ya yin da Bilkin ta mata shiru, kamar minti
goma ta tsaya gaban ta to ai saiki shiru na shirya taso mu tafi daga nan suka
wuce gidan su Hidaya, ko gidan ba su shiga ba ta fito dan duk ta fisu son a
fita.
Sosai sukai
yawo sun sha hotuna kamar ba gobe, sunci har sun ture shi kansa driver din nasu
sai da ya samu nasa rabon dan har guziri ya yi, guri wurin huɗu sukaje kafin su yanke
shawarar komawa gida, a ƙofar gidan su Hidaya ma dakyar suka rabu sabida sabuwar hira
da ta ɓarke.
Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.