Ticker

6/recent/ticker-posts

Inason Addu'o'in Ruqyah

TAMBAYA (34)

Assalamu alaikum warahamatullahi ta'alah wabarajatuhu. Malam barkada warhaka yakokari Allah yataimaka. Dan Allah malam ayoyin ru'uya nikeson agayamin.

AMSA:

Anason wanda zai yi ruqya din ya zamo mutum mai addini wanda aka yarda da nutsuwarsa. Gwargwadon imani da ikhlasin sa gwargwadon tasirin ruqya din a jikin mara lafiyan. Zai fara da:

Auzu billahis sami'il alim, munash shaidanir rajim, min hamzihi wanafkihi, wanafsi

Sai ya karanta:

1) Hasbiyallahu lailaha illa huwa, alaihi tawakkaltu, wahuwa rabbul arshil azim (Sau 7)

(Sunan Abu Dawud)

2) Suratul Fatiha

(Sahihul Bukhari)

3) Ayatul Kursiyyu (Suratul Baqara ayata 255)

(al- Hakim)

4) Amanar rasulu (Suratul Baqara ayata 284-286)

(Sunan at-Tirmidhi)

5) Falaqi, Nasi & Ikhlas

(Sahihul Bukhari)

Annabi SAW yaga wata yarinya fuskarta ta canza kala a cikin gidan Ummusalma (RA), sai ya ce: "Kuyi mata ruqya saboda ta kamu da kambun ido ne"

(Sahihul Bukhari)

An rawaito daga Nana Aisha (RA) ta ce duk lokacinda Annabi SAW yana cikin yanayin rashin lafiya yana karanta Surori 3 (Falaqi, Nasi & Ikhlas) ya tofa ya shafa a jikinsa mai albarka. Sai tace: "A lokacinda yana rashin lafiyar karshe (kafin wafatinsa) ya kasance yana tofawa a jikinsa amman lokacinda jikinnasa ya yi tsamari sai na dinga karantawa ina tofawa a hannayensa saboda albarkarsu"

(Sahihul Bukhari)

Haka kuma Nana Aisha (RA) ta rawaito hadisi cewar duk sanda wani a cikin iyalinsa yana rashin lafiya, yana karanta wadannan Surori guda 3 ya tofa ya shafa musu

(Sahihu Muslim)

Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana nema wa Hassan da Husain tsari da wannan addu'ar (Harma ya ce babanku {Annabi Ibrahim AS} yana yiwa yayansa {Annabi Ismail da Ishaq} ga addu'ar kamar haka:

أُعِيذُكُمَا بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّة، مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ، وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لاَمَّةٍ.

"O'eezukuma bikalimatil-lahit-tammah, min kulli shaytanin wahammah, wamin kulli 'aynin lammah"

Bi ma'ana: "Ina neman muku tsari da kalmomin Allah cikakku daga dukkan shaidan da wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani mai kambun baka, mai cutarwa"

(Sahihul Bukhari hadisi mai lambata 3371)

Idan kuma mutum ya ji ciwo, misali: kamar cizon kunama. Zai karanta

Bismillah (Sau 3)

Auzu billahi wa qudratihi min sharri ma'ajidu wa uhadhiru (Sau 7). A shafa a wajen

(Sahihu Muslim 2202)

Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya ziyarci mara lafiya sai ya ce masa;

لاَ بَأْسَ طَهُورٌ إِنْ شَاءَ اللهُ .

La ba asa tahoorun in sha'al-lah.

(Sahihul Bukhari)

Ba komai, tsarkaka ce in Allah ya yarda.

Akwai kuma;

أَسْأَلُ اللهَ الْعَظِيمُ، رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيكَ .(سبع مرات)

Asalul-lahal-'azeem rabbal-'arshil-'azeem an yashfeek (Sau 7).

(Sahih Tirmidhi)

Ina rokon Allah mai girma, Ubangijin Al'arshi mai girma, ya warkar da kai. (sau bakwa).

Manzon Allah, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya ce; "Babu wani bawa Musulmi da zai ziyarci mara lafiya wanda ajalinsa bai riga ya zo ba, sannan ya fadi wannan (addu'a) sau bakwai face ya sami lafiya".

Wadannan sune wasu addu'o'i daga cikin Qur'ani da hadisai wadanda Annabi SAW ya koyar ga wanda za a yiwa ruqya

Sannan kuma anason a danne jijiyoyi guda 2 dinnan da suke a hannun mai Aljanun (inda ake saka agogo), idan an kammala ruqya din sai a ce "ukhruj ya aduwallah" bi ma'ana "ka fice daga jikinta yakai maqiyin Allah" sai a saki jijiyoyin da sauri. In sha Allahu za a samu waraka (Saboda ansha gwada hakan sosai). Dalilin da ya sa ake hakan shi ne: saboda hadisin da Annabi SAW ya ce: Lallai shaidan yana yawo a jikin dan Adam kamar yanda jini yake yawo a jijiyoyi

(Sahihayn)

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

 (addu'a) sau bakwai face ya sami lafiya".

Wadannan sune wasu addu'o'i daga cikin Qur'ani da hadisai wadanda Annabi SAW ya koyar ga wanda za a yiwa ruqya

Sannan kuma anason a danne jijiyoyi guda 2 dinnan da suke a hannun mai Aljanun (inda ake saka agogo), idan an kammala ruqya din sai a ce "ukhruj ya aduwallah" bi ma'ana "ka fice daga jikinta yakai maqiyin Allah" sai a saki jijiyoyin da sauri. In sha Allahu za a samu waraka (Saboda ansha gwada hakan sosai). Dalilin da ya sa ake hakan shi ne: saboda hadisin da Annabi SAW ya ce: Lallai shaidan yana yawo a jikin dan Adam kamar yanda jini yake yawo a jijiyoyi

(Sahihayn)

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments