Kukan da Khairi ke ta faman zabgawa Momy ta faman lallashin ta ya sa Usman da ke zaune yana faman duba takardun ɗaliban sa miƙewa, falon ya fito a nutse ya ɗauki yarinyar Momy ba ta ce komai ba zaton lallashin yarin yar zai yi ɗakin Hafsa ya nufa inda ya fito riƙe da hannun Khalil wanda ke ta wasa abinsa.
Tsallen murna
yaron yake ya biyo Usman ɗin
a baya yana tsalle suka fice a baya ya sanya Khairin shi ma Khalil kusa da ita
yaja ya zauna inda Usman ya hau mazaunin driver ya ja motar Khalil ya leƙo gaban
motar "Uncle unguwa za mu?"
"Gida zan
mayar da ku" abin da kawai Usman ya ce ke nan Kalil ya koma lakwas rai ɓace, a dai dai ƙofae
gidan yayar tasa ya faka motar ko ciki bai shiga ba ys buɗe ya fito tare da saɓo Khairin a faɗa Khalil ya biyo bayan sa
bugu guda Mai gadi ya buɗe
ganin Usman ya sa shi matsawa gefe alamar ya shigo sai da suka gaisa sannan ya
yi cikin gidan.
Farida na
zaune tana kallo ya shigo da gudu Khalil ya ƙaraso ya rungume ta, ta cafe shi tana faɗin ɗan lele na " ɗazun nake cewa zani ganin ku ashe kun
tafe" aje Khairi Usman ya yi, ta ko zunduma ihu ba za ta zauna na Usman ya
miƙawa
Farida ita, ta kuma maƙale shi, "kin gani ko kawai kik ɗauki yara kik kai wani wuri jibi tama manta da
ke" ya faɗa
lokacin da yake ƙokarin sauke Khairin.
Hararar sa
Faridan ta yi "gidan iyayen nawa ne wani wuri?"
"Nidai
koma mene yaran nan takuramin suke ko jiya inason in bacci Khalil ya zo ya
takuramun sai dai muyi game, to ni ba Hafsa bane"
"Eyye
sannu issasshe kaine ma wa na, ka shigon gida ba ko gaisuwa ka hauni da faɗa,"
Murmushi ya yi
"ayi haƙuri
Hajiya Aunty Farida, Ina wuni?"
Harar sa ta yi
ka ɗauki yaran nan ku
koma, tumma kan Baban su ya dawo, dangwarar da khairin ya yi tare da yin waje
da gudu, tsaki taja tare da ɗaukan
wayar ta ta hau kiran Momy.
Momy na zaune
tana hutawa kiran Farida ya shigo da murmushi ta ɗaga
" Momy kece kika sa Usman ya kawo su Khalil"
Miƙewa
Momy ta yi tamkar tana kallon Faridan " gida kuma nifa ɗaukan ta ya yi zai
lalllashe ta bar in sa Hafsa ta zo ta tawo da su"
"Yawwa
Momy kisa ta zo yanzu, kafin Abban su ya dawo yama gansu"
Katse wayar
Mum ta yi tare da yin ɗakin
Hafsa zaune ta same ta gefe guda takar du ne, ba tare da ta zauna ba ta ce "ince
kodai baki faɗawa
Hidaya kina da CO ba, jiya Sam mantawa na yi bamuyi Maganar ba, na ce karki faɗa mata"
Fuskar Hafsa
ta tuna ƙarara
ba ta son batun CO ɗin
murya aɗan dashe ta ce
"ai bama maganar result da ita, nata ma gunki na ji" ajiyar zuciya
Momy ta yi.
"Yawwa
kinga wai Usman ne ya ɗauki
su Khalil ya mayar gida shi ne nake so ki je ki dawo da su,"
"Towo shi
ma dai yaya Usman, yaran da ba shi ke kula da su ba,"
Kwafa Mum ta
yi basshi zai zo ya samen maza jeki ki dawo dasu"
Hafsa ba ta ce
komai ba ta miƙe kasancewar ta kullum a kintse yasata maya fi kawai ta zara
ta yo farfajiya inda suka ci karo da Abba." Yawwa Hajiya Hansatu ai gwanda
ki cire damuwar haka ki yi walwalar ki, ina zaki haka"
"Gidan
yaya Farida zani wai yaya Usman ya mai da su Khalil shi ne ta ce azo a ɗauko su"
Murmushi Abba
ya yi irin nasu na manya "ho Usman sarkin rikici, ai ya kyau ta da mayar
musu da yaran su, muje ciki ya faɗa"
Binsa a baya
Hafsa ta yi tana murmushi dan sam ba ta son zuwa gidan Aunty Farida a tsukun
nan tasan damun ta za ta yi kan course din da ta fadi. Momy naganin sun shigo
tare ta tsuke fuska, "ya kika dawo kuma?"
"Abba ne
ya ce ba inda za ta tun da an mai da su sai ki bari wani hutun in sun ra'ayi sa
kawo miki, kayan su kuma in Usman din ya dawo ya kai musu" sin sin Hafsa
ta shige ɗaki Mum ta
hau faɗa Haba Abban
Farida kana fa ji nace na ɗauko
su ke nan" murmushi ya yi tun da dai ya riga ya mayar su shike nan bacin
haka ke waye ya ɗauke
miki naki yaran ki bar musu yaran su wurin su yadda za su shaƙu da
abinsu.
Kwafa ta yi
tare da miƙewa
tabar wurin, shi Usman ɗin
zaizo ya samen ne"
Da ɗan ɗaga Murya Abba ya ce "haba rabin ran ko
kin manta da ɗan
tsohon naki ne ya mayar miki da su ba, abin cin nawa fa"
Juyawa ta yi
zuwa dining area ta haɗo
abincin ta aje masa ta juya za ta tafi, Haba masoyiwa ki zauna abincin zaifi daɗi badai Usman bane zan miki
maganin sa"
Murmushi ta yi
ta dawo ta zauna tare da ɗora
motar ta, ya yi murmushi ya hau cin abincin sa.
***
Tun da sukai
batun koyawa Hafsan ya kasa tsaida shawara gashi gobe lahadi, sam baya son
tunanin da zuciyar sa take kan yarinyar, yana son kuɗin da za a biya shi yana son koyawa Hafsan sai
dai take taken zuciyar sa ya sa yake tsoron tusa kansa kusa da ita yana tsoron
kamuwa da son ta, a hankali ya fito tsakar gidan su ajiyar zuciya ya yi, ya sani
yarinyar talaka ma ba lallai ta so shi ba, bare irin su Hafsa, yanzu sa a ce tana
son ka, kai za ka iya riƙe ta? Tambayar da zuciyar sa ta masa ke nan.
Fitowar da ya
yi a ƙofar
gida ya zauna yau sam baya son zuwa wurin su Salisu baya son damun sa da suke
batun budurwa, Juwairiyya da ya hanga ɗauke
da kula ne ya sa shi miƙewa ya ƙarasa inda take "kawo ya ce"
"Akwai
wata can yau Hajara kanta ke ciwo nace ta bari in kawo sai in zo in ɗauki ɗayar ta jirani"
"Ok kar
ki bar gidan ba kowa bari in ƙarasa gangaren"
"tom"
kawai ta ce ta yi gida shi kuma ya ƙarasa daga ɗan
nesa ya hangi Hajara sanye da Uniform zaune kan tebur gaban ta kuma kula ce,
take zuciyar sa ta ce mai kake jira dubu ashirin fa ba wasa ba ce, kana buƙatar
samun kuɗi da yawa ko
dan ƙannen
ka su daina zuwa cikin maza haka suna yini.
Jiki a saluɓe ya ƙarasa
wurin, Garba ne ya riga shi ƙarasowa tare da ɗaukan kular ta shi muje ya ce ta miƙe
dakyar sai dai ganin Muktar ɗin
ya sa taja ta tsaya fuskar ta cike da tsoro cikin rawar murya ta ce
"wallahi yaya ba ni na kira shi, kawai ganin sa nayi"
Muktar bai ce
komai ba ya ƙarasa
tare da sa hannu ya amshi kular, ya kan naki ya ce a nutse lokacin da ya ɗan kalli gefen da take. A
hankali ta ce a Alhamdulillah har suka zo gida ba wanda ya yi magana a tsakar
gida ya dire kular ya zari buta dan yin alwalar magariba.
Ana idar da
Salla fanadol ya soya gun Mahadi chemist, Garba na hango shi ya fito dags
chemist ɗin ya ƙaraso
da sauri, ganin sa ya sa Muktar tsayawa.
Ɗan
rissinawa Muktar ya yi kan ya gaishe shi, shiru sukai ns sakanni kafin Muktar
ya ce "ka tsaidani?"
Sosa kai Garba
ya yi kan ya ce "dama rokon alfarma zan yi, dan Allah karka yima Hajara faɗa walllahi ba ita ta kirani
ba"
Murmushi Muktar
ya yi "Karka damu da zan mata da tuni nayi, shike nan"
A'a sai kuma
roƙon
dan Allah ko sau ɗaya
a wata ne yaya ka taimaka , kabari ina zuwa taɗi,
walllahi zan jira har sa'adda za ta gama karatun kuma bazan hana ta ci gaba da
karatun ba, ni kaina bana jin daɗin
yadda sai dai in dinga binta hanya"
Tsai Muktar ya
yi da idanun sa kan Garba na sakanni numfashi ya furzar, zan kiraka" ya
fada a takaice kafin ya ƙarasa cikin gida, ajiyar zuciya mai nauyi Garba ya furzar
Allah ya sani yana masifar shakkar Muktar din duda in zai girmeshi baifi da
shekaru kaɗan ba.
Maganin da ya
siyo ya bawa Hajara tare da kara yi mata sannu, ya shige ɗakin sa wayar sa ya ɗauka ya rubutawa Alhaji Ba
shir saƙon
accepting offer din kafin ya ɗauki
wasu Physics test book ɗin
sa ya hau dubawa duda ya manta maine akeyi a electricity and magnetism na lvl
one, anma ya san dole akwai da yawa cikin littatafan da yake dubawa.....
Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.