Ticker

6/recent/ticker-posts

Ko Da So (Kashi na 20)

In kin Karanta ki yi sharing please

Zumudin da Mukhtar yake ciki ya saka sau biyu yana farkawa daga bacci kafin asuba ta yi. Sai da ya yi sallahr asubah ne ma ya tuna ashe lahadi ce ba litinin ba. Duk da haka, farin cikin da yake ciki ba mai misaltuwa bane. Ko da ya sanar da Inna sai yaga farin cikinta ya fi nasa yawa hakan ya sa ko kokwanto kan aikin baya yi. Aiki ne da koyar da Hafsah zai kaishi gidan ba wani abu daban ba. Abun da yake ta jaddadawa kansa da zuciyarsa ke nan musamman ma da ya rasa dalilin tsananin dokin da yake ciki.

Cike da walwala ya karasa inda Inna take wanki ya gaishe ta wanda ya sanya ta tsura masa ido kafin ta yi ajiyar suciya mai nauyi.

“Inna?” Ya kira sunan ta yana jin tsoro kar dai ta chanja shawara ne amma ganin nisan kiwon tunanin da ta yi ya saka ya fara tunanin wani abun ne daban da bai shafi aikin sa ba. Ganin ba ta ji ba ya sa shi ma ya zuba mata idon yana kokarin karantar ta.

Murmushi yaga ta yi sannan ta goge wani hawaye da ya fito daga idonta kafin ta mai da shi. Ta sake murmushi wanda Mukhtar yake gani sam ba na farin ciki bane.

“Yau da ka fito dinnan ka sa min hannu ya tuna min da sanda ina amarya. Allah ya ji kan mahaifin ku.” Ta fada, tana sauke ajiyar zuciya cike da kewa da son mijin nata da ya tafi ya barta shekara da shekaru.

Mukhtar ya sake jinjina son da ke tsakanin iyayen sa amma mutuwa da ba ruwanta sai da ta raba su.

“Ameen.” Ya amsa, a take yana sake nazarin yadda shi kuma tashi rayuwar za ta kasance. Zai so a ce shi ma su shimfida makamanciyar soyayyar nan a gidansu shi da matarsa.

Inna ta tsame hannunta ta mike daga durkuson da ta yi. “Nayi ciki.”

Ko da ya ji hakan sai da kwalla ta zo idanunsa. Ya san yadda irin wannan ranakun suke kasancewa Inna. Haka za ta wuni a daki cike da alhini da kewa. Ba za ta cika magana ba, ranar ma ba za ayi abincin sayarwa ba.

Wankin ya ci gaba da yi zuciyarsa tana masa nauyi. Ana cewa soyayyar yara da iyayensu tafi ko wacce girma amma shi sai yake gani kamar Innar su tafi su san Baban su. Ko dan tafi su dadewa ne da shi bai gane ba. Watakila ita ta fi su iya nunawa ko kuma sabon da ke tsakanin su ya zarce tunanin kowa. Tunani yake yi kala kala game da mahaifin nasa yana kwatanta yadda zai yi ya zama kamar sa ga matar sa da yayan sa. Tabbas shi ma ya san mahaifin sa mutum ne mai kirki da son kyautatawa iyalansa. Ko iya wannan ne halinsa nagari, ya ci a yaba masa.

Shi ma hawayen ne ya fara zarya a kumatun sa sanda ya fara tuno irin sabon da sukayi, da sunan fulatancin da yake kiransa, da wasan da suke yi tun suna kanana. Ya share hawayen tare da addua sannan ya fara gaggauta dauraye kayan saboda ranar da ta kwalle a kansa.

***

Idan ta yi kyau, dukkan jiki ya yi kyau. Idan ta baci, dukkan jiki ya baci. Wannan aba mara qashi da ake kira zuciya ita ce a kirjin ko wanne dan Adam da take bugawa, take rinjayar al’amura da ra’ayoyin mutane. Rashin qashin nata ya sanya soyyayar Tariq ta kama Bilkisu har ta manta da cewar soyayyarta gare shi haramtacciyar abu ce a gareta a gidan su.

Bata ji, ba ta gani. Domin ta daina jin maganganu da habaice habaicen yan gidan nasu. Ta dena ganin zunde da hararar da ake mata. Tariq take ji, Tariq take gani.

Zaune take a kasan kafet din wajen tana zuba mishi shinkafa da ta dafa da kanta ta ji takun takalmi yana karasowa gareta.

Daga kan da zatayi taga Ya Iftee tana takowa cikin wata doguwar riga da ta kama ta tsam ta bayyana dukkan adon jikinta. Fuskarta fayau take sai man lebe. A bayan ta yar aikin gidance take binta da tray. Suka karaso da murmushi a fuskarta.

Ta kalli Bilkisu sannan ta kalli Tariq. “Hello Tee.”

Ya kalle ta cike da mamakin ganinta don tun da yake zuwa bai taba sanin nan ne gidan su ba. Ba kuma su taba haduwa ba tun bayan rabuwarsu. Jami’ar Legas sukayi tare har sukayi soyayya suka rabu kafin ma su kammala karatun su.

Ifteesam ta kau da kai don tasan kallonta yake.

Bilkisu ta hadiye wani abu da ya tsaya mata a wuya yaki wucewa. Ta rasa abunyi sai ta rufe flask din. Daidai sannan Ya Iftee ta kalle ta da fara’arta.

“My treat, sis. A sha soyayya lafiya.” Sannan ta yi wa me aikin alama da ta ajiye abincin suka ta tafi.

Da dukkan karfin halin ta da danne zuciya Bilkisu ta amsa. “Ki zauna mana sis.”

Kamar me jira, taja kujera ta zauna. Tariq ya kalle su su biyun sannan ya murmusa.

“Ban taba sanin Iftee yayar ki ce ba. Tare mukayi level one.” Ya gayawa Bilkisu wadda karfin hali kawai take yi.

Tayi murmushi. “Allah sarki. Bari na baku space ku dan yi catching up.” Da haka ta mike tana kiran Hafsah a waya wadda daman ta kirata ba ta dauka ba kuma take da niyyar kiranta bayan Tariq din ya tafi.

Nesa dasu ta yi amma zuciyarta tana ingiza ta da ta kalle su. Ta kai minti biyu tana kokawa da zuciyarta amma sai da ta kalle su. Idanunta na sauka kansu ta ji tamkar an watsa mata ruwan dalma. Dariya suke yi sosai wadda takai ga sai da Ya Iftee ta buge shi a kafada.

Ta kafe su da ido, zuciyarta tana suya. Huci take yi kamar hayaki zai fita daga hancinta. Kafarta ta yi mata nauyi sosai ta ji kamar an dora mata nauyin dutse a kanta. A hankali ta soma jan kafarta zuwa kofar da za ta kaita cikin gidan.

Iftee kuwa da yake komai a lissafe take yi tana yi tana kallon Bilkisun tana harararta. A yanzu ba wai tana son Tariq bane kuma shi ma yanzu ya tabbatar mata da hakan. Kawai ba yadda za ayi Bilkisu ta same shi ne.

Ba za ta bari ba.

***

Hafsah tana zaune a falon Abba suna kallon labarai wayarsa ta haska alamar sako ya shigo. Da yake wayar tafi kusa da Hafsah sai ta dauka za ta duba. Ya murmusa sannan ya ce,

“Bani waya ta nan.”

Tayi dariya ta mika masa.

“Na dauka zakiyi gardama ai. Don na san yanzu sai kice kina taya mamanki kishi.” Cike da tsokana yake maganar saboda kawai so yake ya ji yanayin rayuwarta a fannin soyayya don gashi ta doshi shekara ashirin kuma ko da wasa bai taba ji ance masa ta kawo wani gida ba. Ba wai abun ya dame shi bane, kawai so yake ya fahimce ta. Ya san in ya bar Hafsah da mamanta akan zancen ba zai ji komai ba sai mitar yadda suka barke da fada a karshe.

Hafsah ta tabe baki. “Tabb toh wai kai Abba wace ma za ta so ka tsofai tsofai da kai. Nice ma mummy ko damuwa ba zan ba.”

Yayi dariya har cikin ransa sannan ya karanta sakon da ya shigo wayarsa. Sai kuma ya lura da wanda ya shigo tun jiya da daddare bai gani ba. Sakon Mukhtar na amsa offer din da ya yi. ya ji dadi sosai ya fadada murmushin sa.

Hafsah ta zuba masa ido. “Yanzu Abba da gaske kake?”

Ya daga gira. “An gaya miki ni din wasa ne?”

Ta sheke da dariya har da tafi. “Tabbdi…” ta fada sannan ta mike tsaye.

“Ai kuwa sai na gayawa mummy.” Ya janyo ta ta dawo ta zauna sannan shi ma ya sake dariyar.

“Kiga yarinya za ta kashe min aure! Rufa min asiri kar kisa a fara min kulle a gidan nan. Don mamanki ai ba ta da ta biyu.”

Kafin ta amsa ya kara da zancen da yake son yi wanda ya jayo duk wannan tsokanar. “Haka kawai ina zaman lafiya zaki jawo min. Gara ma na nema miki a abokai na ki bar gidan kan ki batan gida.”

Hafsah ta yi dariya. “Abba abokin ka fa? Tab ai ni wasa nake wallahi ba wata mommy da zan gayawa.”

“Toh in a kya son abokina ki kawon wani.”

Ta danyi shiru. “Toh ni Abba ba wanda yake sona ai. Ko Bilkisu ma ta yi miji banda ni.”

Yadda ta langwabar da kai ya sa ya ji babu dadin yadda ya dauko zancen. Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi yana kallon yar tasa da ta banbanta da kowa a cikin gidan. In aka ce masa zai yi irin wasan da yake yi da Hafsah da yar cikinsa sai ya musa amma sai gashi a hakan yake tafiyar da ita. Dama ance ko wanne da da kalar irin iyayen sa a gida daya ma kuma sai yanzun yake gani. A yaran sa, ko wanne yadda yake haka ake tafiyar dashi. Zai iya cewa a cikin sa iyaye biyar ne. Uban su Farida, Sadiq da Usman daban yake da uban Hafsah. Abun har mamaki yake ba shi.

“Mukhtar zai fara miki lessons. Ki saka ranar da ta miki.” A take fuskarta ta haska da farin ciki. Ta kasa boyewa sai da ta yi tsalle. Ba tare da ta mishi sallama ba ta fice tana ta murmushi ita kadai har ta isa dakinta.

Ta fada gado sannan ta janyo filo ta rungume tana ta murna. A karo na farko da take jin irin wannan yanayin game da wani. Ta rasa murnar ma ta me ce ce. Ta rabuwa da carryover ko ta haduwa da uncle Mukhtar? Ta sake juyawa tana tuno fuskarsa me cike da annuri da kwarjini. Farin ciki ya sake maimaye zuciyarta.

Ta mike ta koma falon Abba.

“Thanks so much Abba.” Ta furta sannan ta fice ganin mummy na harararta.

**

Rubutawa

Aeshakhabir

Fadimafayau

Soyayya
Credit: LuckyTD

Post a Comment

0 Comments