Harabar makarantar cike take da hayaniyar yara suna ta wasa da ciye ciye sakamakon sports day din da sukayi da yake ranar juma’a ce. Yan red house sune team din uncle Mukhtar kuma su suka cinye. A gajiya ya samu wuri ya zauna sannan ya dauki ruwan gefen sa ya fasa yana sha idan sa akan daliban.
Lokaci lokaci
daliban sukan wuce ta gaban shi su masa hi sannan su wuce. Murmushi ne ya kubce
masa ganin yadda malamtar dai da aka raina tafi komai jawowa mutum farin jini a
wajen yara in ya yi ta yadda ya kamata. A yanzu yaran har kallonsa suke yi a
matsayin abun kwaikwayo. Hakan ya sa ya ji son yaran da koyarwar ya kara shigar
sa sosai. Jin su yake kamar kannensa ne.
Yana kallonsu
ne idonsa ya fada kan wani yaro dan ss1 Umar Sadiq ya kifa kan shi a kan gwiwar
sa. Yaron dama sam bei cike walwala ba da surutu kuma komai nashi shi kadai
yake yi. Ganin kowa yana tare da yan team din sa yau shi kuma ya ware ya sa uncle
Mukhtar jin babu dadi. A hankali ya taka inda yake ya dafa kafadar sa.
“A minute?” Ya
tambaya, yana kallon yadda idon yaron ya yi ja duk da ba kuka yake ba. Ba musu
ya bishi.
Mukhtar ya
gyara murya. “You can trust me.” Ya fadawa yaron wanda yanzu yake kallonsa da
alamar shakku a ranshi. Ajiyar zuciyarsa kawai ya ji sannan ya dan yi shiru ya
ce.
“Failure has
always been my identity. Na san saboda a yellow house nake shi ya sa muka
fadi…” Mukhtar ya zuba masa ido cike da mamaki da rashin sanin abun cewa.
Ya dafa shi.
“Why do you think so?”
Umar ya daga
kafada sama sannan ya tabe baki. “Babana ne ya gaya min. Kuma it’s true. Ko
fifth position ma ban taba yi ba. Whenever i want to focus, my whole attention
freezes. Sai na ji ba zan iya ba. Ko yau ma ina tsoron gaya mishi we failed.”
Mukhtar ya
rufe fuskarsa da tafin hannunsa yana nazarin ta inda zai soma. Shi malami ne
kuma his opinion matters. Yara suna kallon malaman su tamkar iyayen su ne kuma tun
da uban wannan yaron ya sanya wa yaron gwiwa, shi ne in a good place ya
karafafa masa gwiwa.
“Yadda nake
gani ni kuma shi ne your future is bright. I wish dama ni ne kai, all qualities
of perfection ka hada su you just need a little push. Ka san waye zai yi
pushing dinka?”
Ya girgiza kan
shi. “Kai ne. Kai za ka gayawa kanka za ka iya because no matter what, sai ka
fara yadda da kanka za ka iya cimma wani abu. Ka sani na yarda za ka iya, all
teachers ma na ji suna zancen ka rannan a staff room. They all wish sune kai
saboda yadda kake daban a dalibai. Ba hayaniya, ba surutu, just goodness.”
Yaron ya yi murmushi
ya gyada kai. Uncle Mukhtar ya ci gaba. “Baba kuma yana gaya maka hakane saboda
yana so kafi shi.”
Umar ya zare ido.
“He’s a great man fa. Major general ne.”
Mukhtar ya ce,
“wow, he’s pushing you to do better in his own language.”
Umar ya ji dadi
ya ce, “I will try. But please don’t tell anyone not even him akan maganar mu.”
“You have my
word.” Mukhtar ya ba shi amsa sannan yaron ya mike da fara’ar sa. Daidai
lokacin mahaifin Hafsah ya shigo school din.
Yara da yawa
suka je suna gaishe shi. Malamai ma duk suka je suna gaishe shi yana amsawa.
Mikewa Mukhtar ya yi cike da jin nauyin mutumin ya taka har inda yake sannan ya
russuna yana mika masa hannu su gaisa.
“Yauwa uncle
Mukhtar dama saboda kai na shigo. Gashi ma lokacin masallaci ya yi. In ba
matsala, ka bini zuwa masallacin, akwai maganar da nake so muyi.” Mukhatr ya
daga kai ya kalle shi saboda yaga ko mene dalilin neman sa amma ya rasa. Gaban
shi ya fadi, Allah ya sa ba wani abu ya yi ba.
“Yes sir. Let
me round up.” Da nauyin zuciya ya juya ya nufi staff room inda shi kuma
mahaifin Hafsah ya shiga zaga school din yana jin dadin yadda komai yake
tafiya. Shi mutum ne mai son farantawa jama’a. Mutum ne me kaunar taimako.
**
Bilkisu ta
jima tana kallon Hafsah kafin ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi. ba ta taba
ganin Hafsah a damuwa makamancin wannan ba. Duk sai ta ji rashin dadin zuwan ta
yau. Da ta nutsu ai tuntuni za ta zo ta yi wa Hafsah jaje ta kuma ba ta baki.
Sam banu
walwala a tattare da ita. Babu wannan kuzarin da surutun da take ciki kullum.
Duk yadda Bilkisu take tunanin abun ya wuce nan da ta zo ta ganta a haka.
Kwallar idonta ta goge sannan ta sake kallon Hafsah wadda fuskarta ce kadai a
waje inda sauran jikinta yake lullube da bargo.
“Haba besty…”
ta soma amma Hafsahn ta katse ta.
“Ni don Allah
ki kyale ni da zancen makarantar nan. Dama can ba sonta nake yi ba.” Ta juya
kanta ta fara hawaye
Duk yadda suke
da Bilkisu haka ta yi ta yi Hafsah ba ta kula ta ba har ta gaji ta tafi gida
ganin magariba ta taho.
Baccin da ya
sace Hafsah me nauyi ne hakan ya sa ta kai kusan isha ba ta farka ba har sai da
mummy ta shigo tana buga filonta.
“Sannu
isasshiya. Wato ma bacci kike maimakon ki tashi ki fara biitar course din da
kika fadi ko?”
Cike da kunci
Hafsah ta juyo. Kafin ta yi magana sai ga Yaya Sadiq nan ya shigo dakin. Ganin
sa ya sa ta ji dadi ba sai ta amsa mummy ba.
“Allah dai ya
shirya mana.” Mummy ta fada tana ficewa da bacin ran da take ji ya fi ma na
Hafsah din. Yarinya sam baudaddiya. Ana nuna mata gabas kullum tana kallon
yamma. Badon kamanni ba sai ta ce canjo mata ita aka yi a asibiti don duk wanda
jinin ta yake yawo a jikinsa kamata ya yi ko ba duk ba, ya dauko wani abun a
halinta. Ko Sadiq ma yana da wasu dabi’unta amma Hafsah? Hnmm.
“Hey…” Sadiq
ya fada bayan mummy ta fice. Hafsah ta mike zaune tana kallonsa ta gaishe shi
muryarta a dashe.
“Wai duk carryover
dince ta mai da ki haka?”
Ta tabe baki.
“Damuwar yadda zan gyara tafi yawa da yadda ba zan sake disappointing dinku ba.
Kowa a gidan nan is perfect. Kalli Bilkisu ma. Ni kuwa komai nawa takes its own
shape duk yadda naso na tsara shi ba ya yi.”
Ya kalle ta cike
da tausayinta ya rungume ta. “You’re different shi ya sa. Kuma don dai wannan
daya, ki kalle shi da positivity watakila Allah ya boye miki wani abu babba ne
a karkashin lamarin. Ke dai kawai embrace it with good faith, okay? Ki dauke
shi a matsayin jarabawa da kuma albarka… ko da kuwa ke baki fahimci menene
hikimar ba…”
Hafsah ta
gyada mishi kai. “Shi ya sa nafi son ka. Your wife is one lucky girl.” ya yi dariya
kadan.
Hafsah ta turo
baki ta ce, “Amma only when you’re not bossy like…”
Ta kalle shi
ta kumbura fuska da murya irin yadda yake yi.
“Ke Hafsah,
kawo min ruwa kuma in kin zo ki ajiye ki juya.”
Duk suka sa
dariya sannan suka fara hira har ma ya ja ta waje suka fita suna hira.
***
Tun da ya dawo
yake tunanin offer din da aka ba shi na koyar da Hafsah ranar lahadi. Zuciyarsa
har tsalle take yi saboda murna. A gefe guda kuma tunanin yadda yanzu zai zama ba
shi da wani isasshen lokaci ne yake masa yawo. Kannensa mata ne kuma suna
bukatar idonsa ko da yaushe musamman ma Hajara da yaga duk fadan sa ba zai
chanja mata ra’ayi ba.
Juyi yake a
kan katifar amma ya kasa yanke shawara. Yana so ya taimaki Hafsah amma yana
duba gidansu. Family first, family over everything. Ganin dai duk yadda zai yi
ba zai iya shawara shi kadai ba ya sa ya nufi dakin kannensa. A karon farko da
zai tambaya shawararsu ba ta Inna ba.
Saboda ya san
Inna cewa zatayi kawai ya yi.
Zaune ya same
su suna hira ko wacce ta amsa sallamarsa. Fitilar kwan da ke ci ya kalla yaga
hasken babu yawa sannan ya ce.
“Fitilar ma
sai an gaya muku kun kunce ku wanke kwan ko?”
Juwairiyya ta
kada kai. “Ai wankin Hajara ne kasan kuma duk sanda ta dauka sai ta fasa.”
“Wallahi yaaya
karyane. Ita ce fa ta fasa dayan.” Ganin za su fara musu ya sa ya daga hannu.
“Duk ba wannan
ba. Ni kawai shawara nake baku ku zama masu tsafta kafin kuje gidan ku.
Musamman ma Hajara da naga Garban nata dan gaye ne…”
Hajarah ta
sunne kai kasa ita kuma Juwairiyya ta kwashe da dariyar tsokana. “Tab Yaya
wannan garan? Kayan miya yake tsaidawa fa…”
Hajarah ta
harare ta.
“Bar ta Hajarah
ai ita ko mashinshini babu.” Hajarah ta kwashe da dariya sannan ta mata gwalo ta
ce,
“Sana’a sana’a
ce dai. Kuma gonar ma tashi ce a wajen sa da yawa suke sarar kayan miya. Ko ba
komai ba zan kwana da yunwa a gidan sa ba. Ehe…”
Kallon da
Mukhtar ya musu ne ya sa ba wadda ta kara cewa komai. Nan ya shiga gaya musu
yadda sukayi.
“Maganar karin
dubu ashirin akeyi amma kunsan kasancewa tare da ku ya fi min dubu ashirin.”
Suka yi murmushin jindadi sannan suka ce.
“Mu ma muna
son ka.”
“Amma Yaya
babu komai ka karba kawai in da wata matsalar daga baya ba sai ka ce ka fasa
ba?” Juwairiyya ta fada.
Hajarah ta yi
shiru sannan ta ce, “Ni dai kar aje a siye mana yaya. Kasan masu kudinnan.”
Sukayi dariya
sannan ya mike.
“Toh zan dai
yi tunani.”
Da haka ya bar
dakin ya koma nashi ya kwanta. Kaso me yawa ya tafi ga karban aikin a ransa
inda ragowar kason yake makale da family dinsa…
Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.