In kin Karanta ki yi sharing please
"Aifa dole kaya su dinga koɗewa, haba a ce sawa ɗaya sai an wanke kaya, su kaya ba wani na azo a gani ba" Inna da ta fito daga ɗaki riƙe da ɗan likidiri ta ce da Muktar wanda ke ta faman cuɗa kaya, ɗagowa ya yi yana murmushi daga sunkuyen wankin, "ai Inna kayan ne sam ba sa mun daɗi in nasu su da ɗauka ko yaya maiƙon jikina ya taɓa kayan na fiso kan in kuma sawa in wanke"
Murmushi inna
ta yi, "ai iyawa ne bakai ba, in ka dawo ka cire kayan sai ka baza su a
inuwa su sha iska kafin ka mayar adaka"
Murmushi ya yi
ba tare da ya ce komai ba, inna tasan halin abin ta, tun da ya yi murmushin nan
cewa bazai yi bane kawai ba zai ba anma bazai yi yadda ta ce ɗin ba, kwafa ta yi "ai
shike nan kayan ka" ta faɗa
kafin ta yi zaure har ta kai ta tsaya ni na shiga gidan Harira in ka gama kan
kaje in da za ka ka daure ka shigo ka duba Malam ɗazu
Fiddausi da ta shigo siyan taliya take cemun jinin nasa ya yi tsanani"
"Tom shike
nan a masa sannu kanin zo" Inna ba ta ce komai ba ta fice daga gidan
tabarshi yana shanya.
Sai da ya gama
komai sannan ya fito, yana ƙoƙarin ɗaure
ƙofar
gidan da wayar kebir ya ji muryar juwairiyya na faɗin yaya kar ka kulle, sakin ƙofar
ya yi tare da juyawa Juwairiyyar ya gani ɗauke
da katuwar Kula tare da Hajara wadda ke sanye da uniform ɗauke itama da ƙatuwar
kular kamar kullum in ta taso saga makaranta sai ta fara zuwa ta ɗauko kula inda Juwairiyya
ko Ummi ke zama da abinci kafim ta tawo gida, bai ce musu komai ba ya tsallaka
kwatar da ta raba tsakiyar layin nasu ya shiga gidan su Harira da sallamar sa.
daga zaure suka haɗa ido da Bahayura wadda ke gefen tabarmar da
su Inna ke kai tana gurza kuɓewa
murmushi ta sakar masa, lah yaya shigo mana ta faɗa
lokacin da ta jawo turmi miƙo masa ta yi zauna daga bakin zauren ya zauna dan tsakar gidan
ya tushe, a nutse ya gaida su ya musu ya mai jiki kafin Bahayura ta gai she da
shi, "yaya ya aikin?, Jiya nazo ai baka nan"
"Aiki
Alhamdulillah, eh jiya naje lesson da nakewa yara da na dawo na biya ta
majalisar mu sai dare na shiga gida"
" Haba
nifa in ce har gidan su Yaya Salisu naje bakanan"
Murmushi ya yi
" towo Allah ya sa ba ba shin ki naci na manta da shi ba" sai da kowa
ya yi dariya kafin Umman su Bahayuran ta ce " ai ko ba shin ne ta ƙyaleka
ka sarara.
Aje kuɓewar ta yi kafin ta miƙe ta
mika hannu saman kusa da jakun kunan su ke rataye daga ɗan inda rufi ya zubo, takardu ta ciro "
ka gani Badawi ne ya kawo min tana nufin saurayin ta wai form ne na school of
hygiene, ya sai mun to daga ni har shi muna tsoron mu cike ba dai dai ba"
cike da annashuwa ya amsa " amma Badawi ba ƙaramin kyautawa ya yi ba gaskiya miko
biro in cike miki yanzu in ya so ko gobe sai in miƙa miki in jiyo mai da me
zakuyi."
"Anma
yaya da ka kyautamin walllahi don ni ya ce in kai da kaina gashi na kashe kuɗin motar da yaban."
Tsaf ya cike
mata kafin ya mike "bari in leƙa in gaida malam ɗin," sosai ya tausayawa yadda Malam ke
jin jiki, a kasalance ya bar gidan kasancewar yau lahadi ranar da suke ɗaukan karatu ya sa da ya
fito daga gidan littattafan sa ya ɗauka
kafin ya wuce masallaci.
Ko da ya dawo
dakyar ya samu bacci ya yi awon gaba da shi sabida tunane tunane haka kawai ya
rasa mai ya sa da ya zauna sai Hafsa da ‘yar hirar rakin su mara tsayi ke dawo
masa wani zubin takaicin kan sa ya kamashi wani zubun ya saki murmushi, bai san
mai yake ji kan yarinyar ba kuma zai iya cewa maine ba ya san dai ba sabo bane
ba kuma so bane cikin tunanin da son gano mai ne ya samu bacci ya yi gaba
dashi.
Washe gari da
wur wuri kamar kulluum ya shirya bayan ya cika gidan da ruwa, fitowar da ya yi
daga kama ruwa ya tarar an zuba masa abincin karin sa yau a langane har ya ɗauka ba tare da dubawa sai
kuma ya buɗe kosai da
faanke ne, "an gama toya wainar nan kuwa?" ya tamaba.
Umma ta ce
"towo yau kai ke tambayar waina ina kafison fanke?" Murmushi ya yi abokin
aikina ne rannan da kika zubamin ya ji daɗin
ta shi ne nace bari yau in kai masa.
"Hajara ɗibar masa a ta gidan Malam
Hassan in ya so sai ki zuba musu wata" Inna ta faɗa da ɗan
ƙarfi.
"Ta ɗari biyu zaki zuba" shi
ma ya faɗa
Koda ta miƙo msa
amsa ya yi ya sa a langar da ke hannun sa kafin ya zaro ɗari biyun ya miƙa mata, juyawa ta yi ta ce da Inna "
kinga ya bada kuɗin"
Da hanzari
inna ta ce " wanne kuɗi
ba shi abinsa kaji ka mene dan an baka ta ɗari
biyu ka bawa wani?" "A'a inna abin fa siyarwa ne, sai na dawo"
ya faɗa tare da saka
kai ya fice ba tare da ya amshi kuɗin
ba.
**
Yau tana tashi
ta hau zuba kayan ta a ‘yar ƙaramar akwatun ta, itakam wannan hutun semester ɗin ba za ta iya yin sa guri
guda ba takaicin first papar ɗin
su sai ya ishe ta sai da ta ɗebi
duk abin da tasan za ta buƙata kafim ta shiga wanka tsaf ta shirya kafin shida ta kammala
komai ta fito riƙe da jakar ta sam batayi niyar faɗawa Momy za ta wani gurin ba, tafi so sai ta
je ta bugo mata waya wannan ya sa take so kafin Mom ɗim ta fito falo takai kayan cikin but ɗin mota.
Cak ta tsaya
lokacin da ta ji Muryar Mum ɗin
"ke Hafsa ina zaki da wannan fagon kayan?," Daurewa ta yi tare da
tattara kwarin gwiwar ta guri guda kafin ta jiyo fuskar ta ɗauke da murmushin ƙarya
" Momy yanzu nake son in kai kayan sai in zo in fada miki daga Flourish
gidan Gwaggo zan dinga wucewa acan zan hutun"
"Ba inda
zaki da wannan damunar zaki tafi wannan gidan ga uban sauro da raɓa"
"Allah
Mum ba raɓa, sauron ma
ni ba jin sa nake ba" Hafsa ta fada a shagwaɓe.
"Nadai faɗa miki ba in da zaki, kin
san ba iya aikin gidan nan zan ba ni kaɗai
in kin tafi"
"Please
Mum ki tallafa ki barni in tafi, walllahi ina missing ɗin gwaggo"
Harar ta Mum
ta yi bayan ta zauna " ai kin san dai duk yadda kike missing din su ba
kamar ni da suka haifa ba, ba inda zaki"
Abba da ya
fito ne ya ce "Hajiya Hansatu kai kayan ki mota" cike da murna ta
fice sannan ya juyo kan Mum wai dan Allah Hadiza mai ke damun ki ne, kibar yara
suyi zumunci mene ciki dan ta je ta yi sati biyu.
Yatsina fuska
Mum ta yi " ni karka min sharri Abban Farida ina ga satin da ya wuce ta je
gidan, ni bance kar ta je ba kwana ne, uban sauron da ke gidan nan ta je zazzaɓi ya rufe ta kadai san dai
Hafsa ba lafiya ta cika ba."
Dariya Abba ya
yi " kema dai kinsan duk yadda Gwaggo zatai ba za ta bari sauro ko wani
abin ya cutar da Hafsa ba ki kyale ta taje" shiru kawai ta yi ba tare da
ta ce komai ba.
Kalil ne ya fito
yana sosa ido hango Abba da ya yi ne ya sa shi rugowa da gudu yana murna Abba
ya rungume shi "a'a Khalilullahi an tashi?" Gyaɗa kai ya yi " Good
morning Abba, ta shi na yi da wuri Aunty Hafsa ta ce in ban tashi da kaina ba
yau ba za ta ba ni cake ba"
Dariya Abba ya
yi "Morning my boy, wato kwadayi ya tashe ka kawai maza jeka ta shirya ka,
kuyi sauri kar mu makara"
Har Khalil ya
ruga ya tsaya cikin daga murya irin ta yara ya ce "Good morny Mum"
murmushi ta yi ganin ya yi gaba abin sa.
Juyowa Abba ya
yi ya kalle ta "wai yaushe zaki mayar musu da yaran su karfa yaron nan
yacire kunya ya zo amsar su"
"Mayar ya
kuma? Ai na amso su ke nan ta faɗa
tare da barin wurin" girgiza kai kawai Abba ya yi yana darya shikam bai taɓa ganin inda uwar mata ke
iko da jikokin ta ba sai kan matar sa, shafa kansa ya yi "Hadiza ta akwai
rikici"
Dariya ta yi
tare da juya idanu
Tun da aka
buga ƙararrawar
fitowa break ya hanzar ta dan zuwa ganin Hafsan tun da ya shigo makarantar ya
ji yana son ganin ta sai dai kasancewar ba dabi'ar sa ba ce zuwa aji gun malami
ya sa ya daure zuwa a fito break ɗin.
Annurin fuskar
sa ne ya ɗauke hango
wurin wayam ba kamar yadda ya saba daga nesa zai hango kanta alamun tana zaune
a sanyaye ya karasa ya zauna lokacin lokaci yana duba agogo da hanya ko zai
ganta tayo wajen sai dai babu alamar ta duk son sa da fanke yau kasa ci ya yi
ji ya yi duk ya gundure shi, rufe langar ya yi tare da miƙewa
sakamakon buga ƙararrawar da akai ta komawa aji har ya yi hanyar office da
zummar aje langar sa sai kuma ya yi ajin da aka bawa Hafsan primary 2 ne
teacher per class ne, gaban sa ke dukan uku uku dan bai san mai zai ce mata ba
har ya ƙarasa
bai iya tsaida abin da zai ce ba ya juyo muryarta na faɗin "lah Uncle ina kwana?"
Juyowa ya yi
fuskar sa ɗauke da
murumushin da bai san ya iya irin sa ba ya ce " lafiya ƙalau,
Aunty"
"Kaga
baka ganni ba ko?, Abubuwa suka sha min kai walllahi"
Murmushi ya yi
"aifa na ce yau wannan sarkin mallake kujera ko lafiya kinga na ma kawo
miki waina baki fito ba ya miƙo mata" amsa ta yi tare da faɗaɗa murmushin ta kai amma Na gode walllahi kamar
kasan ban karya ba shirya Kalil ke makarar dani.
Murmushi ya yi
bari inje kar mu shiga lokacin ɗalibai
tom ta ce ya yi gaba cike da kwarin gwiwa sam bai za ta zai iya yin jarumtar
nan ba ko da yake da ba ta leƙo ta ganshi ba har ta masa magana sai dai
ya juya.
Juyuwar da ya
yi yaga ta koma ya sa shi sauke ajiyar zuciya sannan ya ci gaba da tafiya.
Tafe yake a
nutse, lokacin da aka tashi zuwa titi mota ce ta tsaya gefen sa har ya yi gaba
ya ji muryar ta na faɗin
uncle ina kayi?"
Juyowa ya yi
" cikin gari na yi, kamar ba hanyar mu ɗaya
ba"
Murmushi ta yi
"yau ƙoƙi zani
gidan kakan ni na sai mu saukeka a hanya shigo"
Buɗe gidan gaba ya yi ya shiga
suka gaisa da Malam Musa driver, sai dai ku saukeni a school of hygiene zan yi
submitting form din ƙanwa ta," "tom" Hafsa ta ce, komai ta tina kuma
ta ce " ina ne unguwar ku, form din kawai za ka miƙi?"
" Dala
ne, eh shi kawai zan bayar" ya faɗa
a takaice
"Ah tun
da hanya ce Malam Musa sai mu jira shi ya bada ko?" Ta faɗa tana mai mayar da
hankalin ta kan Malam musa, wanda ya gyaɗa
kai tare da jan motar....
Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.