In kin Karanta ki yi sharing please
Tun da aka rubuta exam din farko hankalinta bai kwanta ba. Ganin yadda exam din ta yi mata ya saka ta hana idonta bacci ta dage da karatun sauran courses din. Sam ta cire wasa da ba ta lokaci a abubuwa marasa muhimmaci ta mai da hankalinta completely kan karatun. ba ta son failure a rayuwarta musamman ma ta fannin karatun.
Pencil take
fikewa wanda zatayi practicing zanen kifi da shi mummy ta shigo falon.
“Hafsah dai ta
ba ce bat. Wannan bamu san wacece ba.” Mumy din ta fada tana jawo kujerar kusa
da Hafsahn ta zauna sannan ta dubi kan table din inda anan Hafsah take wuni.
“Mummy sannu
da dawowa.” Haka kawai ta ce sannan ta ci gaba da zanenta.
Kallonta
mummyn ta yi sannan ta yi murmushi. “Allah ya bada sa’a. Daman so nake kije
gidan su Hidaya ki karbo min wani lace da na siya.”
“Mummy dan
Allah. Exam fa nake. Hidayan ta kawo miki mana.” Ta turo baki sannan ta juya.
Sabanin yadda
suka sabayi, mummyn ta ce, “Toh shike nan Allah ya bada sa’a. Da a ce komai na
rayuwarki haka kika ba shi muhimmanci ai da ba haka ba. Ni na koma daki. Na
dafa abinci ma in zaki zuba.”
Yadda Mummy ta
yi laushi ya sa Hafsah ta ji babu dadi ta kalle ta. “Mummy kinsan zan karbo
miki ko?”
Murmushi ta yi.
“Bakomai. Good luck.” Da haka ta bar wurin.
**
Yau ma ta je makarantar
don haka ta yi saurin zuwa kujerarta ta zauna. Tana ta duba takaardun hannunta,
fuskarta cike da damuwa fal wadda ta mamaye fuskartata tun ran farko.
A hankali ya
tako, hangota da ya yi ya saka ya ji wani abu da ba zai kira shi da walwala ba.
Kawai he felt something.
Ko da ya
karaso, Hafsah taso ta yi kamar ba ta ganshi ba don yau ba ta son yin magana
amma sai ta kasa.
“Hi.” ta ce sannan
ta matsa mishi ya zauna. Murmushi ya yi ya ajiye flask din hannunsa a tsakanin
su sannan ya zauna.
“Hello.” Ya
amsa mata sannan ya zauna. Sun jima ba su ce komai ba har sai da yaga ba zatayi
magana ba sannan ya ce,
“Bismillah:
wainar gero.” Ta dago ta kalle shi da alamun tambaya ya yin da shi kuma yake
kokarin buɗe flask
din. Nan take kamshin geron ya cika mata hanci ta ji tana son ci. Sai a sannan
ta tuna da rashin jin abincin safe da ta yi a ranar.
Amma da yake
ba ta taba ci ba sai kawai ta kalle shi har ya doni kulikuli ya kai bakinsa. Hankalinsa
kwance yake taunawa.
“Ban taba ci
ba.” Ta amsa shi tana dora indanuwanta akan shi. Duk da tension din karatun da
take ciki sai da ta ji wani abu ya amsa a zuciyarta. ba ta san da me za ta kwatanta
shi ba. Kawai dai in an matsa mata za ta ce yana burgeta.
Da mamaki ya
kalle ta sannan ya yi murmushi wanda ba ta gani ba saboda dauke kanta da ta yi
daga kan sa.
“Yau zaki
fara. Da dadi.”
Ta kai hannu
ta gutsuri kadan sannan ta doni kuli kulin. Sai da ta dan kalli piece din
hannunta ta kalla taga baya kallonta sannan ta kai bakinta. Taunar farko, ta
gaskata maganar sa sai gashi ba tare da ta ce komai ba ta kai hannu ta sake
dauka. A haka suka cinye ba tare da kowa ya ce komai ba. Ruwa ya mika mata, ba
musu ta karba da murmushinta ta sha. Daidai sannan aka kada kararrawa.
“Thanks. Kuma
da dadin sosai.”
Ya murmusa. Wa
ya gaya mata daman girkin Innarsa girkin wasa ne. “Inna ta ce take yi.” Ya fada
cike da nuna jin dadin sa a fili.
Ta gyada kai.
“Five star.”
Mikewa ya yi yana
kallon yaran da suke guje gujen komawa class.
“Thanks for
lunch.” Ta sake maimaitawa wanda a daidai lokacin Mukhtar ya sake jin wani abu
ya shiga zuciyarsa game da Hafsahn. Kalmar dai daya ce, ta burge shi.
Ba tare da ya
ce komai ba ya mata murmushi, ta mayar masa. A daidai wannan lokacin wata alaka
ta shiga tsakaninsu. Alakar da babu wanda zai iya mata suna a cikinsu.
Kallon bayansa
ta yi har ya ba ce mata da gani sannan ta mayar da hankalinta kan takardun ta
tana sake jinjina dadin wainar gero din. ta yi mata dadi kuma za ta fadawa
mummy don ta koya mata.
**
Bayan kwana
biyu an yi exam fiye da rabi, Hafsah tana zaune tana kallo mummy ta shigo
falon. Sannu ta yi mata sannan suka ci gaba da kallon su. Karan kiran da ya
shigo wayar mummy ne ya ratsa shirun da sukayi. Mummy ta dauka tana dariya ita
kada
“Ke dan Allah?
Kai kai kai amma nayi murna wallahi.” Iya abun da Hafsah ta iya jiyowa ke nan
kafin mummyn ta tashi ta bar falon. Ko kadan ba ta ci gaba da tunanin ba ta ci
gaba da kallon fim din indiyan da ake haskawa a tashar. ta yi nisa gun kallon
sai ga mummyn ta dawo.
“Kin san
Hajiya Deenah wadda muke sarar laces a wajen ta da na gaya maki rannan?”
Hafsah ta kalle
ta, “Matar nan ta Abuja?”
Mummy ta
murmusa. “Dadi na da ke baki da mantuwa. Ita ce ta zo Kano in fada miki
wallahi. Gobe za ta zo mu gaisa. Toh kin san dai bai kamata na ji kunya ba.
Maza maza ki je drawer ta ki nemo leshin da zaki kai a rage miki…” Hafsah tana
jin haka ta juya tana kunkuni.
“Yau dai daya
ba zan saurareki ba. Wannan umarni ne.” Mummy ta sha kunu wanda ya sa Hafsah ta
yi saurin mikewa don ita barin wajen ma zatayi kafin mummy ta tuno wani abun ta
sake saka ta dole. Har ta taka mummy ta dakatar da ita.
“Sannan ki
kira Hidaya tazo. Ko kuma bar shi ma zan kira mamanta. A nan za ta kwana. Zaku
je shopping ne ku siyo kayan girke girken da za a mata gobe. A nan za ta yi
lunch.” Ita dai Hafsah ba ta tanka ta ba. Sai da mummy ta sake daga murya cike
da fada.
“Baki ji ni
bane!”
“Na ji mummy.”
Da sauri ta bar falon tana jin wani haushi yana cika ta. Ita sam ba ta son
kalar rayuwar nan kuma ba ta san me ya sa Abba baya hana mummy ba bayan su
kullum a cikin yi musu nasiha yake kan kar su dauki rayuwa da zafi.
Mummy kuwa a
take ta kira Farida ta sanar mata da kawarta za ta zo daga Abuja. “Mummy ki aro
chef din Hajiya Maryam mana ta taya su.” Ta bada shawara wadda ta saka mummyn
nishadi. Nan da nan ta ajiye wayar ta kira Hajiya Maryam wata business partner
dinta ta yi sa’a kuma chef din is available. Bayan nan ta kira gidan su Hidaya
sannan ta aika driver a dauko ta.
Account
balance dinta ta duba taga ba ta da matsala ko da kuwa nawa za ta kashe ba tare
da ta taba jarinta ba. Wannan opportunity ne babba a wajen ta. Ta dade tana son
kawance da manyan mata ko dan connections da kuma business. Duk kawayen ta
kaman ita suke bab wata babbar hajiya da duniya ta san da ita. Cike da zumudi
ta tashi ta tafi dakinta tana binciko kayan da ya fi ko wanne tsada a kayanta
wanda beifi sau daya ta taba sakawa ba.
Drawer gwal
dinta ta buɗe ta ciro
wanda daman saboda irin wannan ranar ta tanade shi.
Ranta fari tas
ta fara shirye shirye da goge gogen gidan.
**
Kamshi ne yake
ta faman tashi a kitchen din inda chef Roy ta dage wajen nuna bajintar ta ta
iya girki sannan kuma tana nunawa Hafsah da Hidaya wasu dabarun girkin.
“Duk sanda
kike bukatar wani dandano na musamman a tattare da girkin ki musamman ma nama,
marinate it first. Taste din na daban ne. Ki masa hadi sannan ki diga mai sai
ki rufe shi na wasu awanni. The resulting aroma is fantastic.” Ta fada musu
tana saka marinated minced meat din a fridge don ya fi tsimuwa.
Hafsah ta tabe
baki ta ce, “girki akwai wahala wallahi.”
Chef Roy ta yi
murmushi. “Amma akwai faranta ran jama’a musamman ma masoyan ka. Ai girki yana
da tasiri sosai akan mutane. In fact hanya mafi sauki wajen janyo hankalin
mutane gareka shi ne ta hanyar abinci me dadi. My advice? Ki daure ki koya.”
“Gaya mata
dai.” Hidaya ta mara mata wadda tasa Hafsah ta yi shiru don ta gaskata maganar
su. Abinci me dadi yana shiga zuciya ya yi abubuwa da dama. ba ta manta wainar
geron da taci ba, ba ta manta dadinta ba, ba kuma tajin za ta taba manta wanda
ya ba ta din.
Da haka suka
ci gaba da girke girken main dishes sannan suka fara rolling sheets na samosa.
“Zan iya zuwa
koyan girki wajen ki?” Hafsah ta tambaya ba tare da ta dago ba.
“Of course, ko
yaushe.” Chef ta amsa.
Hidaya ta
kurawa Hafsah ido alamun tambaya sai dai ba ta samu damar cewa komai ba mummy
ta shigo.
“Dan Allah
kuyi sauri. By now ya kamata a ce kun fara jera abuncin nan a table. Chef kar
ki biye wa yaran nan.”
“Yes ma’am.”
Ta russuna sannan mummy ta fice directly zuwa dakinta inda za ta shirya. Su
kuma suka ci gaba da sarrafa snacks din cikin sauri.
***
“She’s amazing
gaskiya.” Hafsah ta fada tana gutsirar samosa tana sake yabawa girkin chef din
wadda har ta gama gyara wurin da suka ba ta ta tafi.
Su Hafsah ma
sunyi wanka ke nan sunyi kyau sosai sannan suka zauna ciye ciye.
“Ku zo ku
gaishe ta. Kuma dan Allah Hafsah kija ajinki.”
“Toh mummy.”
Ta amsa don ta gaji da wannan warnings tun jiya. Jikinta ma duk ya yi sanyi
saboda ta rasa me zatayi don ta burge mummy. Ita she’s not a good actress akan
irin abubuwan nan. Da sai ya fi ma in mummyn ba ta nuna tana nan ba.
A hankali suka
fito daga dakin Hidaya ta rike mata hannu kamar tana guiding dinta. Sai da suka
isa falon, fuskarsu a sake sannan Hidaya ta radawa Hafsah.
“Banda dariya,
jin kunya and too much talks.” Saura kiris Hafsahn ta yi tsaki.
Cike da nutsuwa
suka karasa sannan suka durkusa suka gaida Hajiya Deena.
“Ma sha Allah.
Ya kuke?”
Hafsah za ta amsa,
Hidaya ta rike hannunta a boye sannan ta amsa in a classy way don ita gwana ce.
“Ya sunan ku.”
“Ni Hidaya and
?”
“Hafsah. Sannu
da zuwa aunt.” Hafsah ta fada cike da murmushin da ya sa kumatun ta ya fara
ciwo. A haka ta saci kallon mummy taga fuskarta. And it showed ba ta kwafsa ba.
“Wannan ita ce
Asma, diya ta ce amma ba ta gani.”
“Ohhh.. I’m so
sorry.” Su dukka suka furta a tare suna nuna rashin jin dadinsu a fuskarsu
sannan suka kalle ta. A take Hafsah ta ji tausayin yarinyar ya cika ta har sai
da ta yi kwalla. Da kyar ta kalle ta again tace. “Hi.”
Suna kallo
Hajiya Deena ta kama hannun yarta. “Go with them habibty.” Da haka suka kama
hannunta suka fita daga falon jikinsu ya yi sanyi sosai. Har suka isa daki ba
wanda ya sake magana inda suke ta tunanin ta inda za su soma yi mata hira.
“Hi, sunana
Asma AbdoulJalal. I was born blind. Ban san meye kala ba. And I’m happy.”
Hafsah ba ta san sanda ta rungume ta ba sannan ta runtse nata idanuwan. Duhun
da ya mamayeta ya saka ta fara hawaye. She couldn’t imagine life a makance. ba
ta san ta inda za ta soma ba.
“Kowa sai ya
dinga jin tausayi na, saboda ban san kalar komai ba. Not even Mamma.” Ta fada
sadly amma da murmushi a fuskarta.
Duk sai suka
zama bebaye suka kasa magana.
“Amma all the
same, the world ia equally beautiful. Komai sai dai nayi imagining. The only
thing i am missing is colors. Duhu kawai na sani so komai a duhu nake ganinsa.
A duhu nake tunanin sa. Ance I’m beautiful haka ne?”
Da ido suke ta
binta tana ba su mamaki. Yadda take ta surutu freely. Su kuwa sai faman goge
hawayen su suke. Cike da karfin hali Hafsah ta amsa mata.
“Kina da kyau.
Ba kadan ba. Kina da mugun kyau. I don’t know how to describe it for you.”
Shiru Asma ta
yi wanda ya bawa Hafsah daman tashi ta tafi bandaki tana kukan rashin godewa
Allah akan dukkan ni’imomin da ya mata. Rashin kula cewa idon ta da ya bar mata
ma wata babbar kyauta ce da rahama sa a gareta….
Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.