Ko da So..... (Kashi na Goma Sha Huɗu 14)

    In kin Karanta kiyu sharing please

    Faka motar da Malam Musa ya yi cikin harabar school of hygiene ya sa Muktar buɗewa ya fito, ɗan sunkuyowa ya yi bakin tagar "ina zuwa yanzu zan miƙa in fito" murmushi kawai Hafsa ta yi ya yi gaba, yadda zuciyarta ta kasa yadda cewar wannan Makaranta ce ta gaba da secondry ya sa ta buɗe motar ta fito, a nutse take tafiya tana bin tsirarin daliban da ke kai kawo, zagaye makarantar ta yi duka makarantar a idanun ta ba ta fi Faculty ɗin su ba, sai da ta gama yawon ta sannan ta dawo riƙe da alawar madara da ta gani gurin wata ɗaliba ta siya, Hango Muktar tsaye jikin mota ya sa ta yin sauri ta karaso.

    "Lah har ka dawo, Na bar ku kuna ta jira ko?"

    Murmushi ya yi "a'a nima yanzu na fito" ya faɗa tare da matsawa daga jikin ƙofar motar bayan ya buɗe ta shiga shi kuma ya buɗe ƙofar gaba Malam Musa ya ja motar sukai gaba.

    Kasancewar za su sauke Muktar a Dala ya sa Malam Musa bi ta cikin gari, ganin an biyo ta kasuwar kurmi ya sa Hafsa tunawa sunyi da Hidaya za su so kamar ta ce su tsaya sai kuma ta tuna da halin Hidaya in ta ji ta zo ita kaɗai akwai rikici, adai dai ‘yan Kado suka sauke Muktar yana ta faman zuba godiya kafin su wuce.

    Hangar Malam da Hafsa ta yi yana alwala lokacin da suka shigo layin yasata faɗaɗa murmushin ta tamkar ta matso kusa da shi.

    Cike da fara'a ta ƙarasa inda ya ke alwalar, shi ma murumushin yake, rissinawa ta yi ta gai da shi kafin ta ce " yau zuwan nawa a sa'a na yi tun da ns fara tozali da rabin raina"

    Dariya yi "assha ashema rabin rai ne abu bai yi daɗi ni da nake son fadar duka" itama dariya tasa a'a inna saka duka ran ina zan kai su Abba?" Karasowar Malam Musa riƙe da Jakar ta ya sa ta amsa ta yi gaba tare da barin su suna gaisawa.

    Kai tsaye gidan ta nufa, ƙarami ne ba can ba ya fi rabin fuloti anma baza'a ce fuloti bane ginin ya yi kyau sosai dai dai misali ginin siminti ne ba shi da gate anma ba za ka kira shi gidan talakawa ba, gidan masu rufun asiri ya fi dacewa da shi, da Sallama Hafsa ta shiga lokacin da ta wuce zauren farko, "a'a muryar waye nake ji kamar Muryar Bebilo" Gwaggo da ke zaune kan ‘yar ƙaramar kujera ta mata tana wanke wanke ta faɗa" turo baki Hafsa ta yi lokacin da ta shiga riƙe da Jakar ta " Ni sai in koma, kurum dan mutun ya tsufa sai ya dinga faɗamin sunan tsoffi"

    Dariya Gwaggo ta yi " kajimin ja'irar yarinya Ba sai ki koma ba, ai kinfi ni sanin hanya tun da ta ita kika bi kika shigo"

    Malam da ya shigo riƙe da buta ne ya ce "koma kinji Hafsatu na, kyale ta kishi take"

     murmushi Hafsa ta yi kamar dama da gaske komawar za ta yi kafin ta ce "to ba inda zani tunds dai wanda nazo gunsa yana maraba"

    Dariya suka sa dukkan su sannan suka soma tambayarta mutanen gida.

    “Duk suna lafiya. Ina kawu Halipha?” Ta tambaya tana shigar da akwatin ta dakin Goggon. Kamshin turaren wuta ya doki hancinta har ya sa ta rufe idonta. Son kamshi a jinin kakarta da mamanta yake amma ita ba ta wani damu ba. Tana yabawa da kamshi in ta ji sai dai bai dameta har ta saka da kanta ba.

    Da akwatin ta a baya ta karasa shiga ɗakin wanda yake matsakaici ne. Gefen wardrobe ta hanga inda za ta saka akwatin nata. Kamar ta tuna wani abun ta daga kai ta kalli jerin tukwane da tangaren da suke saman wardrobe din. A kullum burgeta sukeyi saboda babu inda ta taba ganin irinsu banda wajen Goggon. Kallon jeren take yi, girma girma kuma samfuri daban daban ya sa ta soma kirga su.

    Tana kirgen ne Goggo ta daga labule ta shigo ta tarar da ita. “Bebilo…” ta kira tana katse Hafsah wanda ya sa ta buga kafa.

    “Oh Allah, Goggo kin katse ni.” Goggon ta yi dariya.

    “Seti goma ne dani in fada miki domin ni yar gata ce. Daga baya na saida me ros da me bakin les dina. Ke har kumbo gare ni me sha biyu.” Goggon ta fada tana zama a gefen karamin gadon ta da yake kusa da babban gadonta wanda Hafsah take so.

    “Ni ba ganewa nake ba fa Goggo. Wannan gadon naki ne dai nake so ki ba ni na tafi da shi gida kin ki.” Ta fada tana danewa kai gami da kwanciya a kan filon.

    Goggon ta murmusa. “Sai randa kika bar mun miji zan baki.”

    Hafsah ta tabe baki. “Toh me zan yi da mijin ki duk furfura? Kan shi ma duk sanko. Ni kuwa wanda zan aura in kika ganshi sai kinyi kishi.”

    “Bebilo ke nan. Allah ya nuna min ranar nan.” Goggon ta tashi ta fita.

    Da yake Goggon ta jima da fita, hakan ya bawa Hafsah damar yin tunani akan maganar da sukayi. Wanne irin miji take so? Shin ita za ta taba yin aure kuwa? Ba ma wannan ba, ita ba ta taba soyayya da kowa ba kuma finding her spec was the biggest challenge ever. Sau da dama Hidaya tana hada ta da mutane amma tana rejecting da taga hotunan su saboda sam basuyi mata ba. Ko saurayin Hidayan ma sam inda ita ce ko kalle bai isheta ba shi ya sa ma ba ta son kalar hirar da ita.

    A wannan tunanin ta tuno da Bilkisu wadda hakan ya sa ta danna mata kira.

    **

    Zaune suke a tsakar gidan. Fili ne fetal an kawata shi da shukoki masu ban sha’awa da dain kallo. Wasu a cikin su suna da fure me kamshi sosai musamman ma da daddare. Daga gefe guda kuma wata yar rumfa ce haddadiya da aka yi ta da itaciyar bambu. Idan mutum ya zauna a rumfar zai iya hango kwalliyar gidan nasu. Sau da dama Bilkisu ta kan fito nan ta zauna ta yi karatu iska me dadi tana kada ta.

    Hakan ya sa da aTariq ya ce zai zo ta gayya ce shi nan. A zuwan sa na biyu wanda shi ne yau ya saka ta tanadi karamin kafet da ta shimfida kasan teburin wurin.

    Lemon da ta zuba masa ya dauka ya sha sannan ya ajiye yana hamdala. “Wannan hadin da su Baba sukayi tamkar amsar addu’ata ne. Ko nace Allah ya amsa min addua ta ta hanyar su. Beel, you’re everything i ever wanted in a woman.” Ya furta mata kan shi tsays duk da yana dan hin kunya. Abu na farko da ya sa ita ma Bilkisun ta ji ta daina jin zafin abun game da shi. Duk inda kamala take ya cika ta sannan kuma a waye yake. Wayewa ta ilimi da expressing kan sa.

    Kunya ta lullube ta ya sa ta rasa abun cewa. Tun zuwan sa na farko yake lullube ta da kalaman da ba yadda zatayi sai yi musu masauki a zuciyarta.

    Ya saci kallon ta, kunyar tana burge shi ya ce, “Alhamdulillah. Ni kam nayi sa’ar auren hadi. Na samu me sona…”

    Bilkisu ta dago ta kalle shi, fuskarsa cike da murmushi. “Nace ma haka?” Ta fada da yar murya.

    Ya murmusa. “Haka zuciyata take gaya min. ba ta yi min karya.”

    Jin haka ya sa ta rasa abun cewa. A daidai lokacin kiran Hafsah ya shigo wayarta. A zuciyarta har hamdala ta yi saboda escape din da ta samu.

    “Heyy…” ta fada tana kara wayar a kunnenta.

    “Nayi fushi wallahi tun da lafiya kike sai anjima.” Hafsah ta fada.

    Bilkisun ta kalli Tariq taga hankalinsa ma ba kanta yake ba sai ta sake yin kasa da murya. “Haba besty na. He is here. Ki bari zan kira ki…”

    “Iyyeh??? Lallai ma! Ke video call zan kira kuma wallahi ki mika masa wayar tun kafin…”

    Bilkisu ta katse ta. “Na ji.” A haka sukayi switching sannan ta kalli Tariq wanda shi ma ya kalle ta da murmushi.

    Ganin murmushin Bilkisu ya sa Hafsah ta saki baki sannan tace. “Sheep in love! Kalle ki dan Allah.”

    Tariq ya yi dariya sannan ya ce, “wacece ta katse mana lokacin mu?”

    Mamaki ya kama Hafsah. Wannan wani irin abu ne? Shin dama love at first sight da ake cewa da gaske ne? Don wallahi tana jin muryar Bilkisu ta ji ta chanja. Ganin fuskarta cike da farin cikin da take kokarin boyewa ya sake ba ta mamaki. Shi love din haka yake daman? Lokaci guda sai ya kama mutum ya mai da shi wani abun daban.

    A wani tunanin kuma take mamakin yadda duk kusancin su da Bilkisu saboda shigowar wani cikin rayuwarta ya saka har suka dauki kwana biyu ba su yi magana ba and Bilkisun was genuinely happy with that. It shocked Hafsah to bones.

    Bata fuska ta yi don ta nuna how unhappy she was with him sannan tace. “Billy ki ba shi wayar.” Fuskarsa tana bayyana a gaban screen din Hafsah ta hade girar ta.“And who are you? Kasan wacece ita a gare ni kuwa? Cikin kwana biyu kake nema ka maye gurbi na?” Ta tambaya da dukkan gaskiyarta wadda ya sa shi dariya.

    “Tariq Aliyu. You must be Hafsah. Yanda ta fada haka kike and I’m so thrilled to let you know i have snatched your friend. Na sace ta, tawa ce dukka.”

    Hafsah ta sha kunu sannan ta daga muryarta yadda Bilkisu za ta jiyo. “Billy ki karbi wayar. Ina da case da ke…”

    Bilkisu ta karba. “Besty na don’t mind him.”

    “Hnmm.” Kawai Hafsah ta ce sannan ta harari Bilkisu. Bilkisu na ganin fuskarta tasan yanzun za ta fado wata maganar da za ta sa ta ji kunya hakan ya sa ta yi saurin yi mata sallama ba tare da ta jira me zatace ba ta kashe wayar.

    “Hafsah ce…” ta kalli Tariq.

    Ya jijjiga kan sa da murmushi. “A drama queen i guess.”

    Tayi murmushi. “You absolutely have no idea. Rigimarta tafi karfinta.”

    Shiru suka dan yi ko wannen su yana tunanin makomar rayuwarsu.

    Rubutawa

    Aeshakhabir

    Fadimafayau

    Soyayya
    Credit: LuckyTD

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.