In kin Karanta ki yi sharing please
Ruwan da aka tafka jiya da daddare zuwa asubahin yau ya sa kayan da Muktar ya wanke ba su bushe ba, takaici da ɓacin rai duk yabi ya cika shi sam baya son saka ƙananan kaya gashi kaf manyan kayan jiya ya wanke su, cike da ɓacin rai ya buɗe jakar bakkon da ke gefen katifar sa wadda yake sa ƙananan kayan sa shi bama zai iya tuna yaushe ya sanya su ba.
Rai a cinkushe
ya shirya ji yake tamkar bai sanya kaya ba, ruwan da aka maka ya sa Inna ta
makara batai kosai ba, sai fanke tuni an zuba masa nasa ɗauka ya yi ya musu sallama ya nufi titi.
Sai da ya fara
kai abincin sa office ɗin
su sannan ya wuce ajin da yake da shi wato SS 2, kamar kullun da yawa sun riga
shi zuwa musan man da yake yau ya ɗan
so ya makara yana shiga suka sa ihun uncle yau kaine da ƙananan kaya, banza ya
musu, ya gaida su suka amsa tare da yin ƙananun maganganu ƙasa ƙasa,
girgiza kai kawai ya yi yahau rubutu bisa allo, Khadija da ta doso bakin ƙofar
ajin ne ta tsaya turus riƙe da baki tsayawa ya yi da rubutun cikin harshen turanci ya ce
"Hajiya kin makara mai makon ki zo ki fara kwafar aiki kin wani tsaya
anan"
Ƙarasowa
ciki ta yi tana dariya kafin ta ce " class ku faɗamin ba dai dai nake gani ba, anya uncle
Muktar ne?," Girgiza kai ya yi Kadija da Fatima ba sa ji sam ya san dama ɗaya cikin su sai ya yi
magana. Mustapha ne ya ce ai bari mukai a gama class din mu tambaye shi anya ba
twin in uncle Muktar bane.
Fatima da
Khadijah ta hango na tawowa ya sa ta leƙawa tare da yi mata alamar ta yi sauri,
tana shigowa tasa salati kamar wani babban abu ya faru takaici ya cike Muktar,
dakyar ya samu suka zauna, sam bai so yau yake da SS 2 ba gashi dai ya fi son
yaran anma sun fi ko wanne aji takura masa, ko dan yanzu ya fara sabawa da ɗabi'un yaran makarantar na
rashin hayaniya sam mutsi mutsin surutun ‘yan SS 2 din ya fara damun sa saɓanin da da yake ganin sa ba
komai ba.
Yau kusan dai
ajin nasa ba su wani gane shi ba dan duk ya ƙare a kan batun kayan da ya sako tamkar
wani wanda ya sako kayan da ba su taɓa
gani ba, alla alla yake akada ya fice ana kaɗawa
ya bar ajin ta taga suka leƙo Allah uncle ka yo kyau " murmushi kawai ya yi tare da
yin gaba.
Ko office
baije ba ya wuce SS1 su ba su da kula ko damuwa da mai malami yake ciki kamar
SS 2 wannan ya sa lafiya ya gama koyar su ya fice lokacin da aka buga break,
tana tsaye tana duba wasu takardu da ta amso wurin Abban ta, idanun ta suka
wulga caraf suka faɗa
kansa tsai ta tsayar da idanun kansa ya yin da wani abu ke yawo a ranta yar
take ji da sauri ta ɗauke
idanun ta lokacin da ta fahinci ya gane kallon da take masa.
Jiki ba kwari
ya ƙaraso
dama a tsarge yake ga kuma uban kallo da ta zuba masa duk sai ya kuma tsarguwa
daf da ita ya tsaya har yana iya jiyo ƙanshin turaren ta da bai tashi sosai a
nutse ta ce "uncle ina kwana?"
Murmushi ya yi
" lafiya ƙalau, yau kin rigani fitowa break?"
Itama
murnushin ta yi " ina ta kallon ka ko? Yi haƙuri dan Allah kawai gani nayi ka yi kyau?
A ɗan hanzance ya kalle ta
yana murmushi haka kawai ya ji kalmomin nata sun masa daɗi, cikin hanzari bayan ta tuna katoɓarar da ta yi ne ta ce
cikin rawar murya " kawai yau da nagan ka da kayan da ban saba ganin ka da
su bane naga ka yi daban"
Murmushi ya yi
" karki damu ai nima na san nayi kyau, duda dai ban kama ƙafar
ki ba" ya faɗa
tare da yin gaba dan sam kalmomin fun ƙarfin bakin sa sukayi suka fito.
Tsuru ta yi tana
kallon sa har ya kule mata samun kan ta ta yi da kasa zuwa kujerar da suka saba
ta juya kawai ta yi ajin ta, shiɗin
ma kasa fitowa ya yi a office ɗin
ya ci fanken sa.
Ko da aka
tashi kamar ranar Juma'a yau a bakin gste ta jira shi ya shiga suka tafi yau
hirar kusan da Malam Musa sukayi ta dan Hafsa ba ta jin daɗi, gane hakan da Muktar ya
yi ne ya sa shi juyowa ya ce "Aunty lafiya dai naga kinyi shiru" tun
kan ta yi magana yanayin fuskar ta ya nuna murya kasa kasa ta ce bana jin dadi
ne.
Sannu tun da
suka tawo yake juyowa lokacin lokaci yana mata yadda ya nuna kulawar sa duk sai
ta ji mutuncin sa ya ƙaru wurin ta, a kwanar Dala suka sauke shi ya mata Allah ya
sawwake kafin ya tsallaka suka ja mota sukai gaba.
Jiki ba kwari
Hafsa ta shiga gidan Gwaggo, Gwaggon na tsakar gida inda Halima ke gefen ta da
tana cin abinci da alamu yanzu itama ta shigo dan kayan makarantar ta na school
of health technology na jikin ta, sannu da hutawa tama Gwaggo ta shige daɗi, cikin ɗan ɗaga murya Gwaggon ta ce "Bebilo lafiya
dai ba haks kika fita ba"
Halima ta ɗan taɓa "ɗan leƙa kiga
ko lafiya, turo Halima ta yi kafin ta miƙe ta shiga ɗakin
Hafsa ta gani tana ta faman fito da kaya tsayawa ta yi tana kallon ta kafin ta
ce Hajiya Hansatu mai kike haka?
Ɗan ɗagowa Hafsa ta yi ta harare
ta Allah Aunty Halime banson sunan nan"
"na ji
bakya so, mai kike nema haka?" Dafe kai Hafsa ta yi cike da takaici sai
yanzu ta tuna a kan drawer ta bari, rai a cinkushe ta ce pad ɗina na mance wallahi,"
dariya Halima ta yi hardai yau Hansatun nan ba za ta girma shi ne na tashin
hankali haka, ina zuwa" ta faɗa
tare da fita minti kamar goma sai gata ta shigo da ita.
Amsa ta yi
tare da yin ajiyar zuciya dan yanzu da ta fita siyowa gwanda ta tattara ta koma
gida.
Zaune suke
tana cin abinci Halima na rubutu uncle Zahraddeen ya shigo riƙe da
leda, yana ganin ta ya faɗaɗa murmushin sa "kaga
manyan ‘yan
mata saukar yaushe?"
Dariya ta yi
bayan ta ture kwanon yau kwanana uku, ina zuwa kai na fara tambaya ai Gwaggon
ta ce baka nan" guri ya samu ya zauna gefen Hafsan bari kawai munje
seminar ne yau ɗinma
dakyar suka sallame mu."
Bari in zubo
ma abinci ta faɗa tare
da miƙewa
Halima ya kalla, tare da cewa mutun sarkin ƙiwa yanzu da ke ce ko na roka da mita za
a zubo"
Dariya ta yi
itama na ɗoki ne waye
zai ɗauki hidimar ka,
kullum kai dai ka ce ayi, harar ta ya yi kafin ya ce in kin gama rubutun ki
sarrafa mana kifin nan.
Gwaggo ce ta
ce ita da take rubutu Bebilon ta yi dafa mana, a hankali ya ce tab ina Hafsa
ina girki kema kinsan Aunty Hadiza ba lallai tana bari Hafsa ta yi komai a gida
ba.
Hafsa da ta ƙaraso
ce dauke da kwanon abinci da kofin ruwa ta aje masa, tare da ɗaukan ledar kifin aikam na
ji ka wato ban iya komai ba kake nufi, ta fada da ɗan tsuke fuska.
Dariya ya yi
ah haba "ni na isa ince baki iya ba, kawai banso ki wahala girki a kurfoti
ba sauƙi,
ki ajiye Halima ta dafa kinji Bebilon Malam," yar harar wasa ta watsa masa
"ai fa ba zakamin wayo ba girki na yau dole za ka ci gidan nan"
Gwaggo ce ta
sa dariya "Dan Allah ka barta gwamma ta girka yau ɗinnan Malam ya ci ƙarni ya ishe shi ya canja
shawara"
Yiri ri! Hafsa
ta ɗanyi dariya gami
da shewa aikam Gwaggo ki fara haɗa
kayan ki dan cewa zai bai sanki ba sabida daɗin
girki na" ta faɗa
tana shafawa kifin lemon tsamin da ta yanka, ya yin da takaici ya ishi
Zahraddeen tunanin asarar kuɗin
kifin sa kawai yake ji yake tam kar yaje ya make Halima wadda taƙi zuwa
ta amshi kifin hannun Hafsa.
Kiran sallar
la'asar da aka yi ya sa shi fita bayan ya yi alwala, tare suka shigo da uncle
Mansur yaya ne ga Zahraddeen shi yake bin Umman su Hafsa tuni ya yi aure sai
dai baya kwana uku bai zo gidan ba.
Tun daga zaure
uncle Mansur ya ce a'ah yau girkin ‘yan gayu ake haka a gidan kamshin da ya
daki hancin su ya sa ya faɗi,
Hafsa da ke juya miya ta saki murmushi, ai yau girkin nan ko ta fada tare da ɗan yin karamar kwafa.
Gwaggo ce ta
ce ai dai abari aci tukunna ba ƙamshin ba ɗan
ɗanon suks sa dariya,
hira suke sosai kafin Uncle Mansur ya tashi zai tafi dakyar Hafsa ta roƙe shi
ya ce zaije ya dawo ya ci.
Kamar yadda
al'adar gidan take tabarma suka baje a madai daicin tsakar gidan can gefen taga
fitilar ‘yar
sola irin wadda yara ke haɗawa
suna siyarwa ce ta haske tsakar gidan ya yin da Hafsa ta ɗauko food flasks ɗin da ta juye abincin ta
ajiye gaban Gwaggo.
Kallon ta
Gwaggon ta yi "mai zan da shi?" Ta tambaya
Murmushi Hafsa
ta yi "zubawa"
Halima ta
kalla " ki aje wannan karatun kizo ki zuba, dan kin yi sa'a yau an ɗauke miki girkin shi ne
wato komai sai dai ayi?"
"Anma
Gwaggo nida ba ni na yi aikin ba ai ban san kan sa ba"
Zahraddeen ne
cikin kufula ya ce "zaki zuba ko sai na make ki?"
Tana ƙunƙuni
tana zubawa ta miƙawa kowa, tun da aka miƙawa Zahraddeen Hafsa ke kallon sa so take
ta ji mai zaice, sam bai kula da yadda take kallon sa ba, ya nutsu yana cin
abincin sosai ya masa daɗi
bai ta ɓa tunanin
yarinyar ta iya girka ba bare ts sarrafa kifi ya zama ba ƙarni.
Ganin bazai
magana ba ta ce "Uncle baka ce komai ba?
Tsotse ƙayar
hannun sa ya yi kafin ya ce " eh to abinci dai gashi nan kamar dusa
dusa"
Dariya tasa
"ai da dusar ne da farantin nan naka bai zama ba komai kai ba"
Kallon
farantin ya yi sai kuma ya sa dariya dan baima san ya cinye ba, Malam ne ya ce
ai wannan abincin ko a otel albarka"
Gwaggo da take
suɗe hannu ne ta ce "a'ah
dai Malam kawai kana tsoron tane" suka sa dariya duka.
Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.