Ticker

6/recent/ticker-posts

Ko da so... (Kashi na 2)

Jiki ba kwari Hafsa ta bi shi da kallo lokacin da ya bar ajin,idanunta ta mai da kan takardar da sunayen masu neman aikin ke kai Muktar ta kuma mai-maitamana, murmushi ta yi kafin ta ja biro jikin sunan nasa kamar yadda ta yiwa matashiyar matar ɗazu alamar ya ci interview ɗin.

Ahankali ta miƙe tana duba agogo kafin ta miƙawa Malamin da suke interview ɗin tare, wanda ke kusa da ita bari in je gun Abba, karɓa kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba, ba ta damu da rashin maganar tasa ba ta bar ofishin.

Har ta wuce ta dawo, fuskar ta ɗauke da murmushi "lah Anti ina kwana?" ta faɗa cikin har shen turanci matar ma murmushi ta mayar mata, "kya ce ina kwana mana, anya Hafsa? a ce tun da kukai candy ko a ɗan leƙowa a gaisa," matar ta mayar cikin turanci.

"Kai Anti wallahi abububuwa sukai yawa, kuma gani na na yi in nazo ai duk kuna aji zan ɗauke muku hankali, anma ai ina cewa Abba ya gaisar mun da ku."

"Eh fa ya na faɗe wataran, bari in je sauri nake Hafsa ta faɗa"

" nima kin ga aji zan shiga" matar ta fada kafin ta yi gaba.

Abba na zaune yana duba takardu Hafsa ta shigo da Sallamar ta, ɗagowa ya yi yana kallon ta kafin ya ce "to sarkin rikici badai nufin ki anan zaki zauna ba?," girgizar kai ta yi a'a tafiya ma zan yanzun nan naga an mana fixing class 2-4 gwanda in je.

"Towo class kuma gashi ni yanzu ina som mu tattaunawa da team ɗin da sukai interview ɗin, dan mu samu mu a turawa waɗan da suka samu nasara sakon kar ta kwana zuwa gobe su fara zuwa, musanman wanda zai ɗauki Physics ɗin nan."

"Tom shike nan kawai ba ni kuɗin ɗan sahu da na ƙara masa 200 a kan normal price zai kaini, dan innace sai driver ya zo kaini zan makara."

Dubu Uku Abba muƙo mata "Allah ya bada sa'a," murmushi ta yi "Amin sunma yi yawa ai, Allah ya saka da alkairi" ta faɗa kafin ta wuce.

A nitse Muktar yake tafiya tun da ya baro ɗakin gwajin ya kasa tunanin hukuncin da mutanen za su yanke tsaf ya tsaya dan naƙaltar su sai dai fuskokinsu ba su nuna sun yi maraba ko akasin haka da jawabin da ya gudanar ba, duda cewa shi a ransa yana jin kwarin gwiwar ya yi abin da ya da ce ko da bai samu Malamin senior ba to su ɗauke shi a matsayin malamin primary.

Har ya wuce mai lemon ya dawo soyayyar Umman sa da lemo mai ɓawo ya san ya bazai iya ganin lemo ya wuce bai sai mata ba, Ɗari biyun sa ke nan, "na ɗari za a bani" ya faɗa a takaice, Baba Yakubu ne ya yi miƙo masa bakar ledar kai dai Muntari kana son siyan lemon ɗari naga randa za ka sai na du ɗari biyun.

Dariya Muktar ya yi, " adai ci gaba da tayamu da addu'a wataran na dubu zan siya," Allah dai ya sa ai nima zan so haka.

A kishin giɗe Innan take tana jin radiyo ganin shigowar Muktar ya sata gyara zama, yanayin fuskar ta ya nuna ɗoƙi da son jin labari mai daɗi na an ɗauke shi aikin, ajiyar zuciya ya yi kafin ya zauna kusa da ita ledar lemon ya miƙo mata kafun ya ce "wanne shirin suke?"

"Kaji dai shirin Muda likita nake son ji, ta yau ‘yan siyasa sun siye filin shi ne nake saurara, ya aikin kuma fatan an dace.,?" Iska ya ɗan furzar "to gashi nan dai sunce zuwa dare za su turo mana sako," ya faɗa jiki ba kwari.

"To Ai shike nan, ai mutun baya wuce ƙaddarar sa in ba a dace ba sai mu ci gaba da jarrabawa" Umman ta faɗa ga. Shiru kawai sukai kowa da abin da ke zarya a ransa ya yin da sautin Radio ke ta shi a tsakar gidan.

*****

Sam Hafsa ta gaji da ajin na farko ba son Physics take ba sabida ba ta ganewa, na biyu malamin da ke koya musun yada ya wani haɗe rai ya sa duk haushi ya cikata, ga kuma haushin kanta da take ji tun ɗazu da take tawowa idanun ta sun gaza goge mata hoton mutumin ɗazun ita a yanzu ba za ta iya faɗin asalin mai take tunani akan sa ba.

Kamar jira take Malamin ya fi ce zumbur ta miƙe, riko tan da ta ji an yi ya sa ta juyowa Bilki su ce, tare sukai secondry school yanzu kuma suke aji guda a Jami'a, "Hajiya ina zuwa haka cikin gaggawa Bilkisun ta tambaya tana kallon ta.?"

Ɗan wawwaigawa Hafsa ta yi taso mu tafi kar" yamma ta yi," dariya Bilkisun ta yi "wato da a ce ban ruƙo ki ba kina nufin tafiya zakiyi ki barni ko me.?"

Dariya Hafsa ta yi "no da ba tafiya zan ba kawai zan ɗan fita ne in shaƙi fresh iska,"

"ok jeki ki shaƙa bari in nuna ma Ummi wannan abun"

"ok" kawai Hafsa ta ce har ta kusa bakin ƙofa ta ce "dan Allah karki barni ina ta jira waya ta babu caji na san da Abba yaga biyar ta yi tun da na ce masa four ne zai ta kira in bai same ni ba hankalin sa zai ta shi."

Tana tsaye jikin karfen benen tana bin bishiyun gun da kallo tare da tsuntsayen da ke kai kawo daga wannan bishiya zuwa waccan ji take tamkar kar ta bar gun wannan ya sa ma ba ta kuma leƙawa ta dan cewa Bilkisun ta fito ba.

Kafaɗar ta Bilkisun ta taɓa "zo mu tafi" kamar jela ta bi bayan bilkisun, sai da suka fara zuwa Masallaci sukai sallah kafin su nufi wurin da za su shiga mota.

Har ƙofar gida aka kai Hafsa in da ta sauka tana ɗagawa Bilkisu hannu kafin ta fara kwankwasa kofar gidan su, minti kaɗan Baba mai gadi ya ta so ya buɗe ganin ta ya saki washe baki "a'a Hajiya karama a dawo?" dariya ta yi "eh walllahi na dawo ya aiki?" ta tamtabaya.

"Aiki Alhamdulillah ai tun ɗazu da naga Alhaji ya dawo shi kaɗai na ce araina yau ba ni da abokiyar hira sai kim kai yamma,"

" ka bari kawai Baba ai Malaman nan ba sa kyautawa bamu san da aijin ba ɗazu aka sanya da na san da shi ai da ban bi Abba ba duk na gaji."

"Assha sannu, Allah dai ya sawa karatun albarka," "amin" ta ce kafin ta yi gaba, gaban ta ne ya hau faɗuwa lokacin da ta ɗora idanun ta kan Momin su wadda ke saman bene tana faman watso mata harara, tasan ba komai bane fa ce dan kawai ta ga tana magana da Baba, a hankali jiki ba kwari ta nufi kofar da za ta datar da kai asalin falon gidan.

Da sauri ta yi ƙoƙarin shigewa ɗaki dan karma Momin ta sassko ta mata faɗa, sai dai saurin nata bai idda ita ga shiga ɗakin ba ta ji Muryar Momin, "sannu issasshiya wato zaki iya cewa wancan mutumin kin dawo ni ban isa ki zo ki ce mun kin dawo ba?."

Ajiyar zuciya ta yi a hankali kafin ta jiyo, "No momy kawai ina san aje jakata ne sai in hauro saman," taɓe baki Momin ta yi, yanzu fisabilillahi Kalle ki, kin kyautawa mahaifin ki ke nan?" kallon kanta Hafsa ta hau yi, tana son gano aibun ta gaza gano hakan ya sa ta cewa Momy "mai nayi?"

"Eh kya ce mai kikai zaku je makaranta inda mahaifin ki keda alfarma a ce duk kayan ki ki rasa wanda za ka sa sai wannan jemammiyar rigar..?"

Dariya Hafsa ta yi "kai Momy wannan fa sabuwa ce last week na saya 17k fa" tsaki Momin ta ja, "ai walllahi lefin Abban naku ne ni ai bazan ta fi da ke a haka ba," dariya kawai Hafsa ta ce "shike nan Mum karki damu in za mu fita tare sai abin da kika zaɓar min zan sa but banda takalmi mai tudu."

"Ni in tafiya da ke a'a kawai ki je ki bada ni cikin manyan mutane," dariya Hafsa ta yi "mai aka dafa? yunwa na ke ji" ta faɗa tana shiga ciki.

"in sai na faɗa miki zaki ci ki kwana da yunwa," Momin ta faɗa tana ƙokarin zama, Hafsan ba ta dena dariya ba ta nufi in da kwanunakan abin cin suke.

***

Muktar na zaune cikin abokan sa kamar kullum bayan sun yi mangariba zuwa isha kafin ya wuce gida wayar sa ta yi ƙara alamar saƙo ya shigo, tun ɗazu yake duba wayar shiru ba kira ba saƙo wannan ya sa har ya banzatar da wayar sai kuma ya ɗauko ya duba _"muna ta ya ka murnan samun aiki na koyar da Physics bisa gwajin da ka zo ɗazu, za ka iya fara zuwa aiki daga gobe, gaza zuwa cikin wannan satin na nufin baka amshi aikin ba, Mun gode Hukumar Makaranta" _

Zumbur ya miƙe bayan kammala karatun saƙon Umman sa kawai ya tuna ita ya dace ta fara jin labarin nan, "ina za ka ne?, ai 8:30 batai ba" ɗaya cikin abokan sa ya faɗa cikin ɗaga murya.

Shi ma cikin ɗaga murya ya ce "mu haɗu gobe kawai, zan ma bayani," gudu gudu sauri- sauri yake har ya ƙarasa gida sallamar ma tare da kiran Umma ya haɗa ta, cikin sauri ta fito "kiran da yake mata ya sa ta kasa amsa sallamar lafiya dai kake mun wannan kira?"

Wayar sa ya hau nuna mata kallon sa ta yi " yo banda abin Muntari ni me zan gane a waya mai ya faru?' sun ɗauke ni aikin ya faɗa cike da murna ɗo.

"Kai Alhamdulillah, Allah ya ƙarawa annabi daraja ya sa a fara asa'a, ayiriri!" ta sa buɗa, daɗi ya kuma rufe Muktar a duniya yana son ganin farin cikin Innan sa, "yau she kuma zaku fara zuwa ta tambaye shi?."

"Go be in sha Allah" ya ce

"Allah ya sa muna da rai" ta faɗa

"amin Inna, bari in amso Omo gun Musa in zo in wanke kayan da zan sa gobe, gwanda in fara zuwa a mutunce," dariya ta yi "tom sai ka shigo" ya fice...

Rubutawa

Aeshakhabir

Fadimafayau

Soyayya

Credit: LuckyTD 

Post a Comment

0 Comments