Kamar wasa son uncle Mukhtar ya kama zuciyar Hafsah amma ta kasa ganewa. In tana zaune shi kadai take tunani. In ta na bacci mafarkan hirar su kawai take. Son shi ya ma ta kamun da ba za ta iy guduwa ba.
A karo na
farko da ta aminta da cewar tana son burge shi ya sa yau ta ji tana so tayi
kwalliya don ya yaba. Ya saba yaba yanayin fahimtar ta kuma hakan yana sanyaya
mata zuciyarta. Yau so take yi ya yaba da kwalliyarta.
Hoda ta dauko
ta shafa a fuskarta sannan ta nemi lipstick ta shafa. ba ta so tayi wata
kwalliya me hayaniya ba kuma taso yau din ta fito yadda ta saba.
Ta kalli
yatsunta ta ji tana sha’awar tayi musu lalle ko dan ya ce tayi kyau.
Tashi tayi ta
debo littafan ta sannan ta bar dakin. Ko da ta fito ba kowa a falo hakan yasq
ta nufi wurin fulawowin ta ajiye littafan ta sannan ta koma ciki don dauko
madaidaiciyar carpet din da take shimfida musu. Ta duba ko ina ba ta ganta ba
sai ta nufi dakin mummy. A hankali ta murda handle din taga mummy bacci take.
Sadaf sadaf ta
shiga ta fara neman ta amma ba ta ganta ba.
“Me kike nema
a nan duk kin hana ni bacci.” Ta tsinci muryar mummy kamar daga sama. Har fa
minshari ta ji mummyn tana yi ya akayi ta ji motsinta.
“Mummy carpet
din lesson din mu.” Ta fadi fuskarta ba yabo ba fallasa sai dai haka kawai ta
ji wani nervousness yana lullube ta, ta fara wasa da yatsunta ganin yadda
mummyn take kallonta.
Mummy ta mike
zaune sannan ta daga labulen gefenta tana kurawa Fuskar Hafsah ido wadda tana
gani tasan yau anyi mata kwaskwarima.
Mummy tayi
kwafa ciki ciki sannan ta daga girarta. “Carpet din soyayya dai ko?”
Hafsah ta zaro
ido. “Mummy…”
“Rufe min baki
a nan! Wato kun mayar dani shashasha ke da babanki ko. Ya ce za a dakatar da
lesson din amma cigaba ma kukayi ko? Toh daga yau na soke wani abu waishi
lesson.”
Hafsah ta
yarfa hannu. “Mummy carryover fa?”
Mummy ta danyi
wata dariya da ba ta da alaka da nishadi sai dai ta nunawa Hafsah cewa ba ta
isa ba. “ta zama spill over ma. Fice min a daki!”
Hafsah ta
tsaya a wajen da take kamar an dasa ta. Ta kasa gane fushin mummy na menene da
kuma dalilin da za ta ce ta soke lesson dinsu. Ita fa ba son shi take yi irin
son soyyaya ba kawai tana son shi ne saboda yana da kirki kuma yana birge ta.
Ta rasa abun cewa amma ta sani a zuciyarta cewa ba za ta fita daga dakin ba har
sai ta fahimci wani abu.
“Mummy me
nayi?”
Mummyn tayi
tafi. “Tambaya ta ma kike yi me kikayi ko Hafsah?”
Hafsah ba ta
gane ba. “Toh shi uncle Mukhtar din me yayi?” Ta tambaya tana ware idanuwa akan
mummy wadda shock ma ya sa ta kasa magana.
“Mu…”
“Kinga fice
min a daki kuma wallahi kar na ji labarin ya shigo min cikin gida. Ba ma wannan
ba…” sai mummyn ta mike da sauri ta bude drawer kusa da ita ta dauko wani
mayafi ta yafa. Ta ja hannun Hafsah ta kaita dakinta sannan ta janyo kofar tana
huci.
Kai tsaye ta
tafi gate ta sami me gadi. Ya russina ya gaisheta. “Wannan yaron, kar ka sake
barinsa ya shigo min gida. Duk yadda zakayi, kayi amma kar nuna umarni ne daga
mutanen gidam.”
“Toh Hajiya in
sha Allahu. Allah ya kara girma.” Ya fada yana jaddadawa har sai da mummy ta
bar wurin.
Ta wuce ta
inda Hafsah ta ajiye littafanta. Ta kallesu tayi tsaki sannan ta shige cikin
gida.
***
Wasa wasa
zazzabi ya kwantar da Mukhtar don tun da ya dawo daga aiki ranar juma’a ba inda
ya sake fita. Kwance yake a kasan bargo yana jin yau da dama dama kamar zai iya
fita. Ko kadan baya son yaki zuwa koyawa Hafsah karatun ta na yau.
Ya mike zaune
yana ta gumi, kanshi yana ta sarawa kamar zai tsage gida biyu. Ya dafe kan
nashi da hannu bibbiyu sannan ya koma yq kwanta.
Kwanaki shida
ya ke yi kafin ya saka Hafsah a iso yaji wannan karan sun masa nisa. Yau din
cike yake da kewarta gashi zazzabi yaki barin jikinsa. Ji yake kamar in ya
tashi ya watsa ruwa zaiji dama dama ya leka. Ko bai samu nasarar yi mata karatu
ba ya dai ganta ko dan zuciya da ruhinsa zasu samu nutsuwa. Domin a yanzu ko
ina ciwo yake
masa.
Ya sake
yunkurawa zai tashi. Inna ta daga labule ta shigo sannan ta yi sallama wadda da
kyar ya amsa, hakan yana kara tabbatar masa da cewar ba zai iya fitar ba.
“Kaqi ka sha
magani. Shi zazzabin nan naci ne dashi.” Innar ta fada tana mika masa kwanon
hannunta. Ya leka yaga wani koren ruwa yaji kamar ya ture amma ganin yadda Inna
take ta fama ya sa ya kafa kai ya sha kadan ya mika mata.
“Sannu.” Da
kai ya amsa mata sannan ya koma luu ya kwanta jikinsa sam babu kwari. Innar ta
kalle shi cile da tausayinsa sannan ta tashi ta fita tana jinjina irin kamun da
zazzabin ya masa.
Ko da Inna ta
fita, bacci ne ya dauke shi har lokacin zazzabin sam bai bar jikinsa ba. Kwana
uku yana yawo da shi a jikinsa don kan shi ciwo yayi tayi a satin sai ya dauka
kawai pressure aiki ne da hayaniyar yara. Ko panadol bai sha wa ciwon kan ba
shiyasa zazzabin yayi masa mugun kamu har ya kwantar da shi.
Inna ta leko
ta gan shi yana bacci. Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta koma gaban wuta tana
dama masa kunu da zai sha in ya tashi. Ta lura ba iya zazzabin bane yake
damunsa. Akwai wani abu da yake boye mata. Ko an kore shi ne ba ta sani ba tun
da gashi tun ranar Jumu’a ya kwanta, yau lahadi amma jiki yayi tsamari.
Sauki kawai
take so yaji ta ga me yake damunsa a zuciya. Hakan ya sa ta fita wajen abokinsa
me kemis ya zo bayan magariba ya ba shi magani da allura.
***
Kallon
question paper din dake hannunta Hafsah tayi sannan ta soma amsa test din.
Allah yaso tayi karatu irin yadda uncle Mukhtar ya koya mata. Ya gaya mata tun
kafin a sanya lokacin test za ta dinga bin courses din tana karantawa don in
lokaci yayi revision kawai zatayi.
Jiki ba kwari
ta gama test din duk da ta iya komai amma ba ta ji wani farin ciki ba. Ko da ta
fito ba ta tsaya jiran kowa ba ko direba ba ta kira ba ta hau bus. Har suka isa
old site tana zaune tayi jigum abun tausayi.
Tsakanin jiya
da yau yanayin ta ya chanja akan rashin ganin uncle Mukhtar kuma jin cewa bai
zo ba jiya sam ya kara saka ta a damuwa. Ga mummy da gaba daya yau ko
gaisuwarta ba ta amsa ba har sai da tayi ta naci sannan ta ce mata ta dawo
lafiya.
Adaidaita sahu
ta hau ta fada masa address din makarantar. In ba ta je ba, ba za ta iya bacci
ba. Kawai so take ta ji ko lafiya lau yake har ma yaki zuwa jiya.
Tana isa ta
ciro kudi ta sallami me adidaitar wanda ko chanji ba ta karba ba tayi cikin
school din. Kujerar su ta je taga baya nan. Ta kalli time taga one ma ba ta yi
ba. Watakila yana class ta ayyana a ranta sannan ta shiga staff room tana gaida
malaman da ta tarar.
Sama sama ta
ji ana cewa baida lafiya.
“Kuma gashi ba
ni da wata number din shi bayan wannan balle mu tambayi address dinsa. He
really looks sick.” Uncle Mas’ud ya fada wanda shi yafi kusanci da shi. Dayar
malamar ta girgiza kanta.
“Allah sarki.
Allah ya ba shi lafiya.”
Hafsah tana
jin haka ta matsa kusa da fara’arta ta karfin hali ta tambaya.
“Uncle Mukhtar
ne ba lafiya wallahi. ya zo da safe amma sai sick leave principal ya bashi.”
Taji kamar ba
gaske ba. Hafsah ta sake kallonsa taga dai maganar da ya fada bai wai gizo ko
mafarki take yi ba. Take ta ji kafafuwanta sunyi mata nauyi.
Da kyar tayi
musu sallama ta tafi. Tana isa dakinta itama zazzabin ya rufe ta. Taja bargo
tana rawar dari hawaye masu zafi suna zuba daga idanta. Allah sarki uncle
Mukhtar. Ashe bai da lafiya. Ko waye zai kula dashi? Ko waye zai ce masa sannu?
Tunaninsa kala
kala ya cika mata kai. ba ta ankara ba itama zazzabi mai zafi ya rufe ta.
Dukkan sassan jikinta ya dauki zafi da ciwon kewar uncle Mukhtar.
**
Ko da ya koma
gida allurar aka sake mishi hakan ya sa yaji dama dama. Sune zaune a tsakar
gida shi da Inna ta gyara zama. “Ince dai komai lafiya a wajen aikin?”
Mukhtar ya
matsar da kwanon abincin da ko rabi bai ci ba ya ce, “lafiya lau inna. Sun ma
ce na huta na kwana biyu sannan na dawo.”
Ta kalle shi
ta ji alamar ba karya yake mata ba. “Toh Allah ya kara sauki.”
Mukhtar ya
amsa da ameen sannan ya mike ya tafi dakinsa. Ya kwanta yana jin wani irin
sanyi da emptiness yana eloping dinsa. Zazzabin ya sauka.
Jikin da
sauki. Amma zuciyarsa da ruhinsa cikw suke da ciwo. Ciwon so. Ko shakka baya
yi.
Son ta yake
yi. Kuma son ya mishi wata iriyar damka. Ko kadan zuciyarsa ba ta mishi adalci
ba. Ko kadan bayajin zai iya jarumtar cinye wannan yakin da zuciyarsa ta ballo
masa. Ya juya, sai yaji kamar muryar Hafsah a kunnensa.
“Uncle
Mukhtar, ina kewarka.” Ya san ba gaskiya bane. Ya furta a hankali.
“Zuciya da
ruhi suna kukan rashin jinki Hafsah.” Ya furta.
Juwairiyya ta
zaro ido cike da tsoro sannan ta karasa inda yake ta kwallawa Inna kira.
“Wallahi
sambatu yake yi. Innalillahi, Inna cewa fa nayi Yaya Mukhtar ya jiki amma yake
kirana da Hafsah… mun shiga uku! Allah ya sa ba aljanu bane.”
Inna ta ja ta
tsaya, tabbas ta san akwai wani abu a kasa. Zuciyarta ta yi missing beat.
Maimakon ta shiga dakin sai taja da baya ta koma tana alhinin wannan jarabawa
da ta kama Mukhtar.
Tasan ba
zazzabi ne kawai ba.
Ciwon so ya
kama shi!
**
Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.