Ticker

6/recent/ticker-posts

Fajaruddeen (Kashi na 9)

Da dabara irin tasu ta manya umman fajar ta gane Fa'iza ba ta da wani saurayi hasalima ta fiskanci yarinyar tafi mai da hankalunta zuwa ga karatun ta hakan ya sa yau ta kudiri niyar yima fajar maganar.

 Zaune suke fajar nacin abinci yayim da ummansa ke ninke kaya yayi yayi ta bari ya kammala cin abincin ya ninke taƙi hira suke sosai irinta ɗa da uwa ummansa ta ce Deeni yadda ta kira sunan nasa ya sa ya san abu mai mahimmanci take san su tattauna hakan ya sa ya janye hannunsa daga kwanon abincin ya mai da hankalinsa gabaki ɗaya ga umman tasa.

 Na gaji da ce maka kafito da mata kana zuzzuƙewa hakan ya sa na nemo maka da kaina yanzu bawai shawara nake baka ba ina san dole a ‘yan tsukunnan kayi aure nida mahaifinka muna ɓuƙatar ganin jikokinmu indai baso kake kuma se mun mutu ba tukun kayi auren.

 Sosa ƙeya yai kafin ya ce wallahi mami ba haka bane inaso in ƙarasa phd ɗina lokacin albashina yaƙaru yadda zan iya ɗawainiyar matar da ku na ji aure dole kayi da yawa basa samun yadda kake samu sa'annan ɗawainiyar su tafi taka haka sukayi auren kaima haka zakayi arayuwa in ka ce se ka samu yadda kake so to kuwa abubuwa da dama za ka tsufa bakayi su ba komai daki daki ake binsa umarni nake baka ba shawara ba inma tsoron gurin zama kake ga ɗakimka nan dana mahaifin ka inma yai muku kaɗan se ku haɗa da ɗakin fatima inyaso ita se ta dawo nawa falon da kwana ku zauma kaida matar kafin Allah ya hore maka naka.

 Anman umma....bata bari ya ƙarasa ba ta ce anman me kaga na sani yarinya ce baka samu ba ni nasamo maka yarinya mai hankali nida mahaifinka mun yaba da tarbiyyar ta gabansa ya yanke ya faɗi shi ke nan angama da shi ya san halin ummansa cikin ‘yan ƙauyensu ta je ta samo masa mata shida ko ‘yar birnin ba kowacce yake ganin zai zaman aure da ita ba.

 Kamar tasan me yake tunani ta ce faiza ɗalibar ka na zaɓar maka na yaba da hankalunta ina san ka je ku daidai ta a tsorace ya kalle ta umma wace faizan kana da wata ɗaliba faiza da na sani ne anman umman yarinya ce fa yarimyar ni wallahi kallon ɗiya nake mata umma tasa salati faizan ce yarinya kaga katuwar budurwa ka ce kana mata kallon ɗiya tafa yi candy kai ina ka haifi kamarta.

 Na ji koma kallon me kake mata seka dena ka maidashi kallon mata kana ji na ka je ka sameta ku dedai ta na faɗa maka to umma ya ce ya ci gaba da cin abincinsa badan yana masa daɗi ba sai dan ya san in ya tashi yabarshi umma za ta masa faɗa.

 Yana gama ci ya shige ɗakinsa rai duk a tunkushe shi ta ina ma zai iya tunkarar faiza da sunan soyayya tabbas wannan umarnin na ummansa akwaishi da nauyi.

 ******

Faruk ne tsaye ƙorar shagon da ke kallon mai awararsa kamar kullim yauma ɗim ba ta fito ba ya dubi mai shagom bayan ya amshi ledar da ya miƙo masa ya ce pls in tambaye ka man ina jin ka inji mai shagon faruk ya nuno masa inda fatiha ke suya pls yarinyar can gurinfa address ɗinta nake nema mai kantin yai ɗan shiru kamin ya ce ehto gaskiya ban sani ba da yake ni ba ɗan unguwar bane anman ai tana fitowa da daddare ok inji faruk na gode yai gun motarsa da zummar zai dawo anjima ɗin.

*******

Ita kuwa Fatiha gabaki ɗaya hankalinta yayi makaranta dan satinsu guda da komawa ta dawo ta tarar babansu ya zo Allah ya temaketa bai ce daga ina take ba zatonsa ta je gun suyarta ne sedai yau satinsa guda kenan yaƙi tafiya tasan karatu tuni yai nisa ga wayarta ta lalace balle ta ji ko ana karatum dan yanzu ta amshi numbobin wasu Yan ajinsu da suke ɗan gaisawa dan babu wanda za ta ce tai sabo da shi ko ita.

 ba ta da ikon fitowa koda tsakar gidane yanzu zai hauta da faɗa bare kuma ta ce za ta makaranta indai ba suyar awara ba shi ma inbe ganta da kayan ba ba ta isa ta fita ba.

 Addu'ar ta kullin Allah ya sa ya tafi ko ta samu ta je makaranta dan tasan intai kuskuren tafiya yana nan yasamu labari tas zai koreta daga gidan dan yai rantsuwa kan cewar in ya sake ganin ta je makaranta seta bar gidan ta rasa me ya sa dan dai tasan bawai dan baya san boko bane tun da yayyenta da ƙannenta suna zuwa be hana ba inma dan ita mace ce ai shi yakai asiya da kansa tama kuɗi yake kuma biya mata komi.

 Kiran dataji ya kwala mata yasata saurin goge hawayen fuskarta tai saurin ficewa gami da isa gunsa ta durƙusa tana faɗin gani Baba dan tsabar iskanci kina jina inata kiranki kikai banza wato ga ɗan iska ko mahaukaci na ihuu.

 Dan Allah Baba kayi haƙuri tsaki yaja jibeta kamar wata ta kwarai hannu ya miƙa mata ta kalle shi alamar me ki je duk kuɗin sana'ar nan taki ki kawom zatai magana ya daka mata tsawa jiranki nake ina sauri tai saurin miƙewa ta kawo masa bai ko irga ba ya tusa a aljihu yaja mashin ɗinsa ba tare da ko yima umman su fatihan sallama ya kaɗa kansa yai waje.

Fatiha ta share hawayenta duda ƙasan ranta na mata ɗaci sedai farin cikin tafiyarsa yafi yawa.

 Ummanta ke ba ta haƙuri ta share hawayenta karki damu umma ni wallahi ko kaɗan banji haushin kwacen kuɗi da baba yai ba inda ina da wanda yafi haka duk zan iya ba shi ba tare da damuwa ba sabida mahaifina ne yamin gata ya haifoni ta hanya me kyau wasu sunanan suna so ace suma sunada uba koda kuwa kullin komai suka samo se ya amshe ni abu guda ke damuna yake kuma sani takaici shi ne tsanar da baba yake nunamin.

 Hawayen da ya tawo mata umma tasa hannu ta goge karki damu ki cigaba da haƙuri da yimasa addu'a Allah ya ganar da shi insha Allahu zai dena yanzuma ya fahinci abubuwa bai baine

💞 Don't forget to vote, comment and follow 💞

 Umma yau bazani gurin awara ba inji fatiha Ibrahim ya ce to inji umma da ban markaɗo ba ai gabaki ɗayama yau an haƙura a'a gwanda dai yaje ɗin ko kya samu kuɗin zuwa makaranta goben kedai ki kintsa sosai tun da kince karatum safe gareku to umma ta shige ɗaki.

 Kayan da za ta sa ta ɗebo dan wankewa dan tun da babansu ya zo ba ta samu tai wanki ba dan yanzu ya ce ta jiƙa gida ya hauta da faɗa.

 Washe gari tsaf ta shirya sai makaranta koda suka fito daga morning lecture gurin zaman ta ta nufa wani ta hanga zaune a gurin ta baya ta biyo hakan ya sa ba ta gane ko waye ba kamar ta koma tadai ƙarasa yayanta fajar ta gani nanta taɗaɗa murmushinta ta ƙarasa.

 Sallamar ta ce ta dawo da shi daga tunanin da ya tafi shi ma murmusawa yai suka gaisa yaɗan gyara ta zauna.

 Kinsan harnai fishi taɗan waro dara daran idanunta masu ƙara mata kyau tana faɗin towa Allah dai ya sa badani akai fishin ba yaɗan haɗe rai to dawa ye kuwa inba dake ba ta kuma waro ido ni kuma me nayi ace adawo hutu sati biyu ki ƙi zuwa ta ce lah wallahi nazo satin farko to anji satin da ya wuce me ya sa bakizo ba tai shiru dan ba ta da amsar ba shi ya kuma cewa kuma kika kashe waya.

 Sai asannan ta ce wallahi wayar ce ta samu matsala ban samu nakai ta gyara ba shike nan anmiki uzuri anman karki kuma fashi ta ce insha Allahu ya miƙe bari ni in wuce yabar gurin.

 Azahiri ya zo gurin ne dan su tattauna abin da ke damunsa ko za ta ba shi shawara dan ya rasa ta yadda waishi zai iya zuwa gurin faiza bema san me zaice yajeyi ba saidai yadda yaga fatihan duk ta rame murmushin ma da take ya kasa ɓoye damuwar da take ciki ya sa shi basarwa dan yana ganin indai mace yarimya Kamar fatiha za ta iya ɓoye damuwarta har tayi dariya ina gashi namiji.

 *******

Faruk bai samu ya koma unguwar su fatiha ba sai yau sabida ayyuka da suka sha masa kai duda kuwa hankalinsa kaff yana kanta saidai yau ɗin ma baiyi sa'ar samunta ba saidai ya samu Ibrahim yana ƙoƙarin kunna wuta da alamu yanzu ya fito suka gaisa faruk ya zauna gefen bencin dake gun za a iya cewa karo na farko kenan da faruk ya taɓa zama a irin wannan gurin.

 Adabarance yake jan Ibrahim da hira duda ya kula yaron miskili ne bai cika san magana ba sai da yaga ɗan saki jiki da shi yake ce masa kwana biyu bakwa fitowa da rana? Ibrahim ya ce eh ai kasam an koma makaranta bamu da lokaci ayya har yayar taka eh shiyasa yauma na fito dan ta gaji da ta dawo Allah sarki ka ce makarantar tasu da nisa?.

 Eh ai kasan Buk new site ai da nisa sosai makam akwai nisa anan area din take karatun eh a buk ɗin take cike da mamaki faruk ya ce buk Ibrahim ya ce eh kafin faruk ya kuma magana Ibrahim ya ce ta nawa zan zuba maka ta ɗari uku ok ya ce ya zuba ya miƙa masa faruk ya amsa yabar gurin ba tare da ya tambayi abin da ya kawoshi ba wato address ɗin su ba dan ya kula yaron ya ƙosa ya tafi.

Koda ya koma gida mamaki yai tayi yadda ya san ɗaliban jami'a da ɗan bamzan girman kai musanman hausa fulani bai taɓa zaton za a samu bahaushiya yar jami'a na talla ba ya san dai sauran yare akwai sosai anman dai hausa sai yake jin da wuyar samu tuni yarinyar ta kuma birgeshi ashe shiyasa idanunsa suke mata kallon ƙima ashe shi ya sa yake ganinta a nutse ashe shi ya sa yake ganin ba ta masa kama da ‘yan talla ba ashe da illiminta tabbas me illimi a ko ina daban yake.

 Shiko fajar tin randa sukai maganar faiza da ummansa ya dena zama hira agidan kai zaman gidanma sai ya dena shi duk dan kar ta taso da batun.

 Yau ya samu ummansa tana lazimi sosai yaji daɗi dan ya san ba ta magama se ta kammala ya ce da Fatima ta ce mata ya fita har yakai zaure fatima ta fito da sauri tana faɗin yah kazo inji umma saida gabansa ya faɗi ya daure ya shiga ɗakin.

 Saida ta idar da addu'ar sannan ta dubeshi ka kuwa je gurin yarinyar nam in ka je ya kukai yadda yake wani sun sunkwi da kai yana shafa sumar sa ya sa ta gane be jeba ka je ne ta kuma tambaya dan tabbatar wa cikin rawar murya yake faɗin daman bari nai.....bata bari ya ƙarasa ba ta ce shi ke nan Deeni tun da ban isa da kai ba ban isa insa kayi ko karka yiba.

 Shi ke nan karkaje kayi yadda kake so tai ficewarta yai saurin binta a baya yana ba ta haƙuri tai masa banza dan Allah umma ki yi haƙuri zan je karma ka je wallahi zan je yau inna dawo daga aiki shi ke nan tun da ka ce za ka na haƙura anman wallahi nasamu labarin ba ka je ba karka nefi afuwata.

 Murmushin dole yai zani ma shike nan jeka Allah yai albarka ya ce amin ya miƙe yabar gidan ta bi shi da addu'a can ƙasan ranta batasan takura masa saidai ta fahinci inba haka taiba ba zai yi aure ba ba ta san ya rasa faiza dan tana ji a jikinta yarinyar za ta zame masa alkairi.

Rubutawa

Faɗima Fayau

Fajaruddeen

Post a Comment

0 Comments