Ticker

6/recent/ticker-posts

Ko da So... (Kashi na 22)

“Sabbin kaya za su iso nan da sati daya saboda haka ya kamata muyi clearance sales don mu rabu da tsofaffin.” Hajiya Hadiza, mahaifiyar Hafsah ta gayawa me kula da boutique din nata.

Matashiyar ta amsa. Sannan ta dora da, “how many percent off, ma?”

Hajiya Hadiza ta danyi shiru tana ajiye biron hannunta. “Zan yi lissafi.”

Da haka ta ci gaba da dudduba kayan tana jotting din abun da ya kusa karewa da abun da ya fi yawa. Taku take daidai tana jin dadin nasarar da ta samu a kan kasuwancin nata. Duk abun da ta saka a gaba ba ta kyale shi sai ta cimma nasara.

Kiran waya ne ya katse mata tunani ya sa ta dubi wayar sannan ta tabe baki kafin ta dauka.

“Lafiya, ina boutique ne. Toh shike nan.” Ta fadi sannan ta kashe wayar ta jefa ta cikin jaka. Abun da aka fada ya sa ta juya za ta tafi don anyi mata ba zata. Matar uncle din Hafsah ce ta haihu shi ne maman Hidaya ta kira ta fada mata suje barka anjima.

“Wani abu ya taso min. Zan shigo da safe.” Ta fadawa Saratu sannan ta fice tana nufar motar ta tare da tunanin wacce irin shiga zatayi. ba ta son shigar da za ta jawo mata raini.

**

Babban gida ne sosai da ban garori da dama. Ko da mummy ta faka motar ta a harabar gidan sai da ta tsaya tana tunanin ko ta yi kyau ko batayi ba. Karshe dai ta hakura ta cire mukullin sannan ta fito. Kofar ban garen Amina me jegon ta yi tana taku a hankali. Tana budewa sanyin kamshin turaren wuta ya bugi hancinta.

Ta kalli corridor din da za ta kaita main parlor din taga yadda aka yi masa ado da frames kala kala. Ga runner carpet nan har karshe. Ta cire takalmin ta ta saka a rack din da aka ajiye a wurin.

Sama sama take jin hirar su har ta karasa da sallamar ta. Cike da takama da nuna ita ma ta isa ta samu wajen zama sannan suka fara gaisawa da mutanen wurin. Dukkan su dai facaloli ne.

Maman Hidaya ta kalle ta ta murmusa. “Hadiza leshin ki ya yi kyau wallahi.” Kanta ya kumbura, amma sai ta basar kamar ba wani abu ne mai muhimmanci ba ta ce,

“Kuma kawai na siya ne randomly saboda shan iska.”

Ta kyalla ta kalli leshin jikin Amina taga babba ne sama da nata. Haushi ya cika ta wato ita Amina za ta nunawa sutura. Ai kuwa dai babu abun da mijinta ya fi nata.

“Yayi kyau kuwa.” Aminar ta fada itama tana yabawa. Hajiya Hadiza ta yi yake tana ganin kamar magana kawai Aminar take so ta yaba mata.

Ta dan kau da kai sannan ta ce, “ina babyn?”

“Yara sun dauka. Ai ita kam wannan yayyin ta sune iyayenta.” Suka kwashe da dariya.

Maman Hidaya ta ce, “toh abunka da kalan hanji.” Aka sake yin dariya. Amina ta maze duk da ba ta dauka da komai ba. Tun da ta samu cikin ake nata tsiya kala kala wai ta tsufa. Da farko ma taso ta cire likitan ya ce mata babu wani risks sosai.

“Daga ita na kulle dai balle a samu nayi.” Ta fadi sannan suka shiga wata hirar daban.

***

Ganin a kwana biyu Bilkisu tana ta boye matsalar da take ciki ya saka Hafsah yanke shawarar take gidansu. Ko da ta shirya za ta tafi mummy ba ta ce komai ba hakan ya sa ta ji dadi ta kama gabanta.

A dukkan tsananin mummy ba ta takura mata idan wajen Hidaya za ta je ko wajen Bilkisu. Ta yarda dasu da mu’amalar su da Hafsah din.

Tana isa gidan ta yi sa’a ba ta tarar da kowa ba ta wuce dakin Bilkisu. A kwance ta same ta ta kurawa sama ido hawaye nata fita daga idanunta a gefe kuma wayar ta tana ta ringing.

Hafsah ta yi sallama sannan ta zauna gefen ta ta daga wayar taga Tariq ne.

“Ki barshi kawai.”

Bilkisun ta fada tana tura bakin haushin sa da ta kasa boyewa. Hafsah kuwa daukar wayar kawai ta yi ta ce masa ya zo yanzu. Tana sauke wayar, Bilkisu ta kalle ta ta fashe da kuka.

Muryarta na karyewa ta shiga bawa Hafsah labarin yadda sukayi. Ko da ta gama maimakon ta ji Hafsah ta fara rarrashinta, dariya ta mata.

“Ke yanzu abun da kike wa kuka ke nan?”

Bilkisu ta juya. “Kema ba carryover kika gama yiwa zazzabi ba.”

“Bakiga yadda ta yi mishi bane and he didn’t stop her.”

Hafsah ta ce, “yo ke babu class ma sam a lamarin ki. Nice ke ta ruwan sanyi zan rama. Amma duk ba wannan ba gaskiya Tariq bai kyauta ba.”

Bilkisun ta gyada kai. “Toh kin gani. Yanzu ya zan yi.”

Hafsah ta yi shiru sannan ta yi tafi. “Ina da wani tsari amma gaskiya sai kin goge hawayen nan. Kuma ji be ki. Je ki yi wanka mu shiga kitchen.” Kamar mutum me rimot haka ta tashi ta fada wanka, ba ta jima ba ta fito.

Sai da ta daura robe a jikinta sannan Hafsah ta ce, “zabo kaya kala biyu muje mu tambayi Ya Iftee wannan ya fi dacewa ki saka.” Bilkisu ta kalle ta alamun ba ta amince da plan din ba.

Hafsah ta tashi da kanta ta nemo kayan sannan taja ta har dakin Ya Iftee. Sukai sa’a tana zaune tana zana jagira da alama fita zatayi.

“Hi Ya Iftee! Dama Tariq ne zai zo shi ne muke so ki taya mu zaban kayan da ya fi kyau.” Hafsah ta daga mata kayan. Tana kallo Ya Iftee ta ba ta rai amma ta basar.

“Eh Ya Iftee. Wanne zan sa? ya ce na mishi kwalliya.” Ta sake tabe baki tana tunanin yadda zatayi.

“Ke yanzu saurayin kike wa wannan rawar jikin?” Ta tambaya tana yatsina fuskarta saboda ta kasa boye bacin ranta.

Hafsah ta yi kwafa ciki ciki. Kamar Bilkisun ba zatayi magana ba ta ce, “Ni ba komai bane a wajena. We love each other so much.”

Hafsah ta ji dadin amsar ta ce ita suke jira ta yi musu zabi. Tsabar takaici ma ya sa ta kasa magana har sai da suka gaji suka bar dakin. Suna fita ta yi wurgi da jagirar tana tsaki me cin rai. Ta tashi bazar bazar ta nufi bandaki inda zatayi ihu ba tare da an jiyo ta ba.

Ko da suka koma daki, ajiye kayan sukayi sannan suka tafa. “Kinga fuskarta kuwa?”

Hafsah ta ce, “ai haka akeyi daman. Ke in kika zauna ranki ne zai baci.” Suka dara sannan suka tafi kitchen.

Meatpie kawai sukayi sai zobo da suka dafa. Sanda Bilkisu ta gama kwalliya sannan Tariq ya iso.

Tare suka fito fuskarta dauke da fara’ar da Hafsah ta ce mata ta makala. Suka zauna sannan suka gaishe shi.

“Kawarki ta guje ni. Na rasa dalili.”

Hafsah ta kalli Bilkisu alamun ba ta san komai ba. “She didn’t say a word.”

Da mamaki ya kalli Bilkisu. “Babu komai kawai wayar ce kwana biyu bana taba ta. We’re good. Na zuba ma lemo?” Ta tambaya fuskarta cike da murmushin gaske. Har mamaki take yadda ma ta sake da shi har haka ta ji haushin nasa yana ba cewa.

Ya kalli lemon. “Kuma ba poison a ciki?”

Hafsah ta yi dariya. “In ma akwai sai dai poison din love ta saka ma.” Ya kalli Hafsah sai kuma ya dauke kai da sauri yana kallon Bilkisu.

Ta zuba masa lemon ta mika shi kuma ya kalli zobon da aka ajiye ya ce shi zai sha. Ta zuba masa tana kallonsa. Da kyar ya sha duk da dadin da ya masa.

“Wallahi babu wani abu tsakanina da Iftee.” Ya fada. Hafsah ta yi wani boyayyen murmushi.

Bilkisu ta girgiza kai. “Yayata ce fa. Me ya kawo zancen ta? Nace ma wani abu ne?”

Ya jijjiga kai. Hafsah ta saci kallonsa taga duk ya rasa yadda zai yi sai ta mike ta ce,

“Dama fita za muyi. Na baku aron minti biyar..” da haka ta bar wajen sannan ta koma cikin gidan ta nemo wayarta.

Ko da ta dauko tunowa ta yi ashe ba ta da number din uncle Mukhtar. A lokacin ji ta yi kamar ta kira Abba ta tambaye shi ya bata.

Zama kawai ta yi tana tuno yadda yake kallonta. Lokaci yana cika ta koma ta hango su suna dariya. Har ranta ta ji dadin yadda suka dinke. Hakan ya sa ta sulale ta bar gidan cike da farin cikin ganin Bilkisu a farin ciki.

Sai bayan sallahr isha Bilkisu ta kira ta mata godiya. Cike da jin dadi ta mata fatan alheri. Har ta kwanta bacci ta tuna da assignment dinta duk da ta yi.

Daukowa ta yi ta sake dubawa ta gani ko ya yi. Ta mayar ta koma ta kwanta amma ta ji kewa ta cikata. Ko baccin ma ya gudu.

Tashi ta yi ta fita tsakar gida inda suka zauna. Ta zauna a wurin ta daga kanta sama tana kallon taurari tana murmushi.

Rubutawa

Aeshakhabir

Fadimafayau

Soyayya
Credit: LuckyTD

Post a Comment

0 Comments