Cike da ɗoki Hafsa ta tashi, kaya kala biyu ta ɗauko in da ta shirya ta saka doguwar abayar ta golden ne kalar ta, a falo ta tarar da Momy tana ta famar mitar jikokin ta da aka mayar da alamu har lokacin Usman bai yadda sun haɗu ba wannan ya sa Hafsa saurin wucewa Dinning area ta zubo abincin ta tare da komawa ɗakin ta dan ba ta son taka sawun ɓarawo tasan kure kaɗan zatai Momy ta hau ta da faɗa.
Tana zaune
tana duba wasu formulas dan ba ta son in Muktar ya zo ya tambaye ta basic
abubuwa na course ɗin
ta hau zare ido, Sallamar Hidaya ya sa ta mai da littafin tare da sakin
murmushi, "yanzu nake mita a raina kinƙi zuwa bayan na faɗa miki in uku ta yi inada abinyi"
Duban agogo
Hidaya ta yi kafin ta ce " ai ban makara ba, tashi muje Allah dai ya sa
Bilkisun ta shirya"
Maya fin ta da
ke gefen gado ta naɗa
a kanta kafin ta ce "amin dai" Sallama suka yiwa Momy suka fice.
A ƙofar
gate ɗin su Bilkisu
suka tsaya ko minti uku basuyi ba ta fito, sai da suka hau titi sannan Hafsa ta
ce " gidan Gwaggon za mu fara zuwa ko kuwa kasuwar kurmin?"
Hidaya ce ta
ce "no it's better mu fara zuwa kasuwar in ya so ko irin munga wani abin
ma yi mata tsaraba"
Murmushi Hafsa
ta yi Haka ne kuma ta faɗa
kafin ta mai da kallon ta ga Bilkisu wadda ta mai da hankalin ta sosai ga bakin
hanya tana tunani.
Hafsa ce ta ce
" Maddam mai ke damun ki tun da kika shigo ina kule da ke you are not on
your usual self"
Murmushi ta yi
tare da ƙara
kallon gefe, kafin ta ce ba komai kawai banjin daɗi
ne"
Shiru Hafsa ta
yi sai kuma ta ce "Tariq ne?"
Ɗan
kallonta ta yi kamar za ta ce eh sai kuma ta kalli Hidaya wadda idanun ta ke a
kanta, girgiza kai ta yi "no kawai banjin daɗi
ne"
Kafun Hafsa ta
ce wani abu Hidaya ta yi caraf ta ce " tun da dai sabida ni ba zaki faɗi damuwar ki ba sai ki dawo
normal in mun rabu kya ci gaba da damuwar"
Hafsa ce ta yi
dariya " No badan ke bane dan Malam Musa ne, kar ya ji ta mato kan
namiji" dariya sukai Har Malam Musan wanda ya ce "ah in dan nine sai
in toshe kunnuwa" ya faɗa
yana ƙokarin
faka motar suka fito zuwa kasuwar shi kuma ya fito ya samu tebur ya zauna.
Sosai sukai
siyayya kusan rabin kayan na Hidaya ne sabida makaranta da za ta koma, ya yin
da Hafsa da Bilkisu kusan kayan girki ne sai akushi da ya burge su suka siya,
Bilkisu ta fara siya sabida Tariq nason har kar gargajiya tana gani ta tuna da
shi in ya zo wannan satin ciki za ta zuba masa abinci abin da ta fara ayyanawa
a ranta ke nan.
Kusan sai
wurin ɗaya suka bar
kurmi suka wuce gidan Gwaggo tun da suka baro kasuwar Hafsa ke duba agogo ba ta
son uku ta mata a waje kar Muktar ya zo ba ta nan ya zama stranded dan tasan
Mum ba lallai ta wani yi welcoming din sa ya ji normal ba.
Tun da ta
hango kofar gidan ba tabar Malam ta ji daɗi
dan shi ne kawai zai tsayar da ita ya ce sai sun tsaya sunci abincin rana kan
su tafi ganin ba tabarmar tasan bayanan.
Hannun ta rike
da kayan da ta sayo musu gefen ta Bilkisu ce Hidaya na daga ɗan bayan su, a hankali ta
ce "kin ƙi dai faɗan
meke damun ki ko?"
Itama shigen
irin yadda ta yi maganar ta kwata " za muyi waya anjima," ta faɗa tare da yin sallama sakamakon
zauren da suka shiga.
Halima na tuƙa tuwo
Gwaggo na yanka alayyahu da alamu na miyar tuwon ne, suka shiga "lale
maraba da ‘yar
gudun hijira" Gwaggo ta fada tana murmushi.
Murmushi Hafsa
ta yi ba tare da ta ce komai ba ta aje ledar Hannun ta ta shige ɗaki Halima ta ce "to
walllahi karki mun ta'adi", ta faɗa
cikin ɗan ɗaga murya.
"Kaya na
kawai zan ɗauko"
ta faɗa daga ɗakin, ya yin da Hidaya da
Bilkisu suka zauna gefen Gwaggo suna gaishe ta fuskar su ɗauke murmushi.
Fitowa ta yi
rike da adakar ta ta ɗan
rissina ta gaishe da Gwaggo kafin ta ce zaman mai kukai na faɗa muku sauri fa nake"
Hidaya ce ta
ce ni gaskiya tuwon nan ya burgeni sai na ci"
Hararar ta
Hafsa ta yi "ki ci me, kin taɓa
ganin inda mutun yaje gidan mutane rana tsagal tsagal ya ce zaici abinci ba su sa
da shi ba, Please taso mu tafi"
Gwaggo ce tasa
salati " ungo nan Bebilo, wato gidan namu ne gidan mutane ko?"
Dariya Bilkisu
tasa "Hajiya Bebilo sai ki yi haƙuri muci tuwon nan"
Hararar
Bilkisu Hafsan ta fara yi kan ta ce " kaji Gwaggo da ku aljanu ne?"
Girgiza kai
kawai Gwaggo ta yi tana murmushi " in ba zaki ci ba ke kya iya
tafiya" inji Halima.
Turo Baki
Hafsan ta yi "ai walllahi da akwai abin da zan faɗa miki na fasa"
Rufe tukunyar
tuwon Halima ta yi tare da faɗin
"ai zanzo har gida inji komene"
Sai da suka ci
tuwon sannan suka baro gidan, tuburewa Hafsa ta yi ita za a fara kaiwa wannan
ya sa sai da aka sauke ta sannan Malam Musa ya wuce da su Hidaya.
Tana shiga
gida Sallah kawai ta yi, ta shiga kitchen simple abinci ta yi da nemon abarbar
da ta sayo ta sanya a fridge kafin ta faɗa
banɗaki ta yi wanka.
Kayan ɗazu da ta ciro ta ɗauko ta sa a jikin ta suma ɗin dai doguwar riga ce sai
dai wannan na atamfa ne, sun mata kyau sosai sai da ta yi sallar la'asar sannan
ta ɗebi littattan ta
ta yo farfajiya can kasan bishiya ta samu wuri ta zauna ta fara duba wani novel
lokaci lokaci ta duba kallon bakin gate.
Shi kuwa
Muktar Bayan ya kammala wankin Inna kayan sa yau dubawa kusan duk kayan da yake
sawa yau da kullum ba su masa ba wannan ya sa shi buɗe akwatun da yake sanya kayan da sai Friday ko
ɗaurin aure yake sawa,
rasa na zaɓa ya yi
kafin can idanun sa su faɗa
kan wasu sabbin shaddar sa sky blue da kuma milk tsai ya bisu da ido bayan ya
fito da su dakyar ya iya yanke shawarar blue ɗin
zai saka duda a goge suke da ya ware su yaga sun ɗan
cukurkude wannan ya sa shi ɗauka
ya yi tsakar gida.
A ruwan sitati
ya tsoma su sai da ya shanya sannan ya fice, daga gidan ba shi ya dawo ba sai
wurin biyu ya tarar sun bushe Allah ya taimake shi da wuta ya goge abinsa
sannan ya shiga wanka.
Sosai ya yi
kyau tun kan ya sanya hula a kansa kyansa da cikar kamalar sa suka fito, sai da
ya ci abinci sannan ya bar gidan zuwa Gidan su Hafsa.
Ya kusa minti
biyar a ƙofar
gidan zuciyar sa na tunane tunane kafin ya daure ya iya bugawa, kamar jira Baba
Bala yake ya buga kodan Hafsa ta sanar da shi zuwan Malamin nata oho, ya buɗe a mutunce suka gaisa ya
ce "Malam Hajiya Hafsa ko?"
"Eh"
Kawai Muktar ya ce yana murmushi.
Nuno masa inda
take ya yi a nutse ya fara takawa, kamshin turaren sa ne ya sanar mata da
dosowar sa wurin ta tun kan gangar jikin sa ta ƙaraso cike da annurin fuska ta miƙe
sukai sa'ar saka idanun su cikin na juna, da hanzari Muktar ya cire nasa domin
faduwar gaban sa ne ya ƙaruwa lokaci guda lallausan murmushin da ke ɗauke fuskar Hafsa ya narkar
masa da tunani.
Cikin hanzari
ya tunatar da kansa ba ajin su guda ba, karatu ya zo koya mata neman kuɗi ya kawo shi ba soyayya
ba, wannan ya ba shi kwarin gwiwar ƙarasawa tare da yin murmushi.
A nitse cike
da girmamawa Hafsa ta gaishe shi tare da faɗin
ina zuwa ta faɗa kafin
ta yi ban garen da zai sada ta ga falon su, dadduma ta ɗauko tare da lemo da snacks ta fito ɗakin Momy ta leƙa ta
faɗa mata Malamin nata
ya zo sannan ta koma farfajiyar.
Can gefe
tsakiyar fulawoyi ta shinfida musu dardumar ya tada Sallar la'asar dan tun yana
hanya aka yi sallar ita kuma ta koma ta ɗebo
takardun ta kan kujerar da ta taso.
Sai da ya idar
suka kuma gaisawa "kinsan tun jiya nake ɗokin
inzo mu ga juna, kwana biyun da mukai bamu haɗu
ba duk ba daɗi"
Murmushi ta yi
cike da zumuɗi ta ce
"ashe ba ni kaɗai
ba, duk sai nake jin kamar mun shekara da sabawa" ko mai suka tuna oho sai
kowa ya shiga mutsu mutsu insa ta hau ƙoƙarin zuba lemo shi kuma ya hau bubbuɗe takardun da ta ajiye.
Lemon ta aje
masa gaban sa sannan ta ce "ga lemo" ta faɗa tare da turo masa farantin da snacks ɗin suke.
Murmushi ya yi
"kinsan Allah a ƙoshe nake."
Dariya ta yi
"to ba abinci bane ai dan haka gaskiya sai ka ci"
Dariya ya yi
" kinsan wani abu da karatu bama fa iya Physics ba, no koma mene, sai kin
sa aranki you can do it, kin cire tsanar sa aranki shi ne zaki iya gane shi
yadda ya kamata" ya faɗa
a niyar sa na kawar da batun cin abin da ta kawo.
Murmushi ta yi
" tab Physics din zan so, over my dead body"
Dariya ya yi
tare da tsare ta da ido "Hafsa kalle ni" ya ce
Duban sa ta yi na ɗan sakwanni tare da saurin ɗauke idanun ta dan gani ta
yi ya mata kwarjini sosai "dole kiso Physics in har kina son in koyar da
ke dan magana ta gaskiya ba zanzo ina koya miki abu kina jin haushi na nida shi
ba"
Dariya ta sa
" ah ai bazanji haushin ka ba, kawai I can't like the course,
gaskiya"
Iska ya furzar
kafin ya ce "kisa to nine physic in ko kuma wani da kike so, let say your
boyfriend ya faɗa"
can ƙasan
ransa wani abu ya soke shi sauri ya yi ya daure "in kika sa wanda kike so
ne zakiyi kokari ki so shi, asannu in kin fara sonsa everything about the
course zai zamar miki simple"
Ɗan ɗaga girar ta ta yi kamar
mai tunani sai kuma ta yi murmushi "tom shike nan zan yi yadda ka ce baka
sha lemon ba" ta faɗa
tare da matso masa da shi kusa.
Hoo Hafsa
rikici ya daɗa tare da
kurɓar lemon wanda
sanyi da daɗin sa ya
daki kwanyar sa baima san lokacin da ya kuma kurba ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.