Hafsa na zaune a falo tana kallo Momy ta shigo riƙe da leda gefen Hafsa ta ajiye, ya yin da Hafsan ya ɗago ta kalle ta kafin ta ce "Momy sannu da zuwa" ta faɗa tana ƙolarin buɗe ledar.
"Yawwa, sannu" kin dawo ashe itama ta tambaya.
"Eh tun ɗazu ma, kuma mai Umman su
Basman ta samu?"
Zama kan
kujera Mum ɗin ta yi
tare da taɓe baki,
mace ce, sai wani firiri ta tame wai ita tasa leshin da ya fi nawa"
Murmushi kawai
Hafsa ta yi kan ce Momy waye ya baki alkaki?, kamar kinsan kwaɗayi nake ji walllahi"
"Hajiya
Babba ce ta baki har na fito ta ce in kawo miki nama ce mata gobe zaki je ganin
babin ta ce adai kawo"
Murmushi Hafsa
ta yi "woo ni Hafsa mai kakanni" dariya Mum ta yi yo waye baida su ai
sai dai in mutuwa sukai, wayar Hafsa da ta yi alamun an turo saƙo ya
sa ta dubawa Yaya Usman ne, Momy ta kalla tare da yin murmushi.
"Lafiya
kike kallona kina wani dariya?," Wayar da ke hannun ta, ta dan haskawa
Momin wadda ta Karanta Momy na falo kuwa abin da Usman ɗin ya ce ke nan.
Rai Momy ta haɗe tare da cewa "cene
masa bama na gidan," Ba musu Hafsa ta rubuta tare da miƙewa ta
shige kitchen tabar wayar jikin Momy tana ta sheƙa dariya so take in ya zo yaga wayar gun
Mum ɗin ya yi tsammanin
ita ce ta masa reply.
Daga ɗan nesa ta laɓe tana hangen falon har ya
shigo ganin Momy ya sa shi ƙoƙarin juyawa ta ce "Kai Usman zo nan"
Jiki ba ƙwari
ya matso Hafsa ta fito kamar ba ita ke dariya ba ta matse "lah yaya ka
dawo?"
Watsa mata
harara ya yi ta yi kamar ba ta ganshi ba ta hau lalube "Mum ina
wayata?"
Ɗago
wayar Momy ta yi daga cinyar ta, ta miƙo mata, ta amsa tare da zama gefen Momy
wadda le faman faɗan
mayar da su Khalil da Usman ɗin
ya yi, ɗagowa ya yi
rai cinkushe ya ce "anma fisabilillahi nida gidan shike nan sai akawo wasu
jarirai su takura mun?"
"Eyye sannu
issasshe, gidan ku ai ka ce ba gidan ka ba," Momy ta katse shi.
Langwaɓar da kai ya yi tamkar wani
ƙaramin
ya ro, "aiko tafkar su zan koma tun da dole sai an kawo su"
Hafsa ce ta ɗago " Kai yaya dan
Allah, kai lokacin da kake zuwa gidan Gwaggo ko Hajiya Babba kana takura musu
ai b wanda ya tafke ka, su da gidan Kakan nin su"
Miƙewa ya
yi a kufule "na fahinci ke kike zuga Mum kan ya rannan"
Momy ce ta ɗaga masa hannu "Malam
dakata, ba wanda yake zugani, tun da abin naka haka ne ka fito da mata ka yi aure
ka bar yara su huta ai dama kana da abinyi, in kuma kaƙi zan nemo ma koma wace
in haɗa ka da
ita"
Dariya ya sa Haba
Hajiya Momy sai ka ce a lokacin da ai ko Yaya Sadik da ya haƙura da
auren dolen da kika masa dan shi ɗan
da ne"
Tsuke fuska
Mum ta yi " kana wasa ko to mu zuba" ta faɗa tare da miƙewa tabar wurin Hafsa ta yi saurin bin
bayan ta tare da shigewa ɗaki.
Faɗawa jikin kujera ya yi yana
dariya Finally faɗan
da yake gudu dai sun haɗu
da momy ya sha shi.
Washegari da
wuri Hafsa ta shirya zuwa makaranta, lectures ɗaya
sukayi ta safe sai kuma ta 2 to 4 da Malamin ya mayar 12-2 ana fitowa daga
Morning lectures ɗin
kasan benen ASN suka nufa ita da Bilkisu domin siyan takardun da aka bayar
sunyi sa'a babu mutane sosai wannan ya sa suna zuwa aka sallame su, har sun
wuce gaban exam office suka dawo ganin tabarmar shinfide ba kowa suna zuwa
Hafsa ta faɗa kai tana
faɗin kai har na ji daɗi, ya yin da Bilkisu ta
mike ta hau duba fuskar ta jikin madubin da ke manne jikin bango.
"Gaskiya
wanda ya sa madubin nan ba karamin technology ya kawo ba" inji Bilkisu da
ke faman kamar fuska tana goggogewa.
Dariya Hafsa
ta yi tare da tashi zaune ta ja jakar Bilkisu ta ciro janbaki tare da miƙewa,
"To Hajiyar Janbaki walllahi baki isa ba ba ni abuna da tsada na siya."
"Koma
nawa kika siya, walllahi sai na sa" ta faɗa
tare da fara shafawa tana mita "mutun sai rowar tsiya haka rannan nayi
nayi kiban ruwa kika ƙi sai ledar kika ban kawai ƙyale ki na"
Dariya Bilkisu
ta yi "yo daga wasa shafe shi ma duka Hajiyar Mita"
Shabiyu saura
minti biyar suka nufi ajin su Malin chemistry ɗin
na tsaye jikin bene idanun sa na kallon ajin lokaci lokaci yana kallon agogo da
alamu jira yake 12 ɗin
ta yi ya rufe, ganin yadda duk wanda ya hawo keɗan
yo gudu ya shiga ya sa sums yin gudun, suna shiga ya bi bayan su ya rufe.
Ganin Ibrahim
zaune kujerar su ya sa Bilkisu yin baya ya yin da Hafsa ta ja ta tsaya kan sa
tana faɗin wurin mune,
mursisi ya ƙi
tashi, cikin fushi ta ce za ka tashi ko sai na girgiza kujerar"
Kamar dutse yaƙi
motsawa sam Hafsa ba ta son zaman baya wannan ya ba ta kwarin gwiwar gaza jin
tsoron malamin da ya tsura mata idanu tun bayan goge allo da ya yi ya juyo
yaganta shi bai ce ta zauna ba, bai kuma ce ta fita ba da alamu mamakin karfin
halin ta yake dan wanda ta tsaya kan nasa ya girme mata, ganin yadda Malamin ya
tsura musu ido ya sa Ibrahim tashi Hafsa ta yi kwafa tare da zama.
Ajiyar zuciya
Malamin ya yi ya juya har ya fara rubuta ya juyo " Abin da akwai maza masu
tsoron mata ba sai yau"
Aka sa dariya,
duban Hafsa ya yi Hajiyar rikici fatan dai yau ba zaki mun bacci a aji
ba," kunya ce ta kama Hafsa dama Bilkisu ta faɗa mata ya san kowa suma ya san su gashi kuwa
ya san kullum baccin ta take a class in nasa musanman in Khadija da suke surutu
tare ba ta zo ba, dan ita Bilkisu in ana lectures to mantawa take suɗin aminai ne mai da hankali
take sosai ba ta surutu.
Sai wurin biyu
da rabi ya fita duk Hafsa ta gaji idanun ta tun da ya fara batun course ɗin suka fara lunshewa sai
ta yi kamar zatai bacci sai ta ɗago
ta kalle shi ta fasa.
Sai da suka
biya ta coke village suka sayi shawarma dan tun jiya Hafsa keson cin ta coke
village ɗin a mota
suka ci abinsu aka sauke Bilkisu inda Hafsa ta wuce gida, ta yi niyar daga
makaranta za ta wuce gidan Hajiya Babba taga babin Ummi sai dai gajiyar da ta
yi ya sa ta bari sai anjima da yamma kawai ta je.
**
Kasancewar
litinin ce ta ƙarshen wata ya sa Muktar tun da ya tashi suka gaisa da Inna
yake faɗa mata
"in ayi alba shi zai wuce gidan Rashida na ji rannan kince da na faɗa miki zaki aika mata da
sako."
"Towo
kaima dai Muktar da rashin azanci kake, tun jiya ba sai ka faɗamun ba, yanzu in ka makara
fa"
Shafa kansa ya
yi ai "abin da sakon zai ɗauki
lokaci ba, ki in bari sai gobe naje"
Mikewa Inna ɗin ta yi bari muga ta shiga
madafar su, daga inda yake yana juyo burun burun ɗin
ta na taɓa kwanuka,
kamar minti uku ta fito rike da buhun samo, dana bakko, gashi tsaki ne da su
kuka da garin tuwo da na ɗan
wake, "kace mata kanwar tana da zafi dan karta zabga ta ɓata mata abinci."
Tom ya ce mata
ya ɗauki kayan ya
fice, aransa yana jin daɗi
aikin nan nasa ba wai iya ɗebe
masa kewar zama wuri guda yake ba har ‘yar uwarsa ya taikama tun da ada kuɗin zuwa gunta ma ba shi
dashi.
Koda aka tashi
siyayya dai dai gwargwado ya mata ya hau mota daga Hotoro zuwa Mariri, adai dai
lokon su aka sauke shi ya saɓi
buhun da ya haɗe kayan
duka a kafaɗa zuwa
gidan Rashidan, yau baiyi katarin haɗuwa
da yaran Rashidan ba duda kuwa tarin yaran da ke ta wasa a lokon.
Tun daga zaure
yake jiyo Hayaniya mutan gidan ya yin da kukan yara ke tashi, sallama ya hau yi
ba wanda ya tanka masa daurewa ya yi ya shiga kamar kullum yauma gidan kaca
kaca, riƙe
take da kwalar rigar mijin nata wanda ke faman faɗin
ta sakar masa riga.
Ganin yayan
nata ya sa ta sakin sa ta fashe da kuka, "yaya ni gaskiya na gaji ka tafi
dani dan Allah
Ajiya zuciya ya yi muje daɗi kai kuma lallashi yaran,
ya faɗa suka shiga ɗaki da Rashida wadda keta
faman kuka.
Sai da ya bari
ta sha kukan ta sannan ya ce ta taimaka ta yi shiru, wanda dakyar ta yi.
"Mai ya
faru? haba Rashida kin ban kunya abin da rashin mutuncin naki har yakai ki iya
riƙe
kwalar mijin ki ba kina faɗin
maganganu marasa daɗi"
Kuka ta kuma
sawa "yanzu yaya kaima goyon bayan sa kake"
Girgiza kai ya
yi kema kin san ko zan goyi bayan kowa ke zan goyi baya tun da kece jinina,
kawai sa kema kin san baki kyau ta ba, ita kuma gaskiya in ban faɗa miki ba, abin da wanda
zai faɗa miki ba"
Cikin shessheƙar
kuka ta ce yaya sam Mutumin nan bai san daraja ta ba, baya tausayi na, baisan
cina ba baisan sha na ba, sai dai in ciyar da shi abin da kawai ya sani shi ne
ya hakke mun na gaji nayi nayi ya sake ni yaƙi.
Leƙowa
Nura ya yi ya ce "ba wai kawai naƙi sakin ta bane dan ta ce cikin da ke
jikin ta za ta zubdane ina sakin ta ta sake aure, ni kuma har ga Allah ina son abin
da ke cikin, shi ya sa naƙi sakin ta tun da sai na sake ta za ta zubar"
Salati Muktar
ya sa "zubda ciki Farida, dan sunna ɗin?
Yo ko na zina ne ai ba kya yi kisan kai ba"
Kuka ta rushe
da shi, "ni nagaji ga uwar yunwa, ga wahalar cikin nan nagaji, walllahi
nagaji"
Dakya Muktar
ya samu ya lallashe ta ta haƙura ya haɗa
su ya yi ta musu Nasiha, ya ba su kayan da ya kawo, sai yamma liss ya tafi gida
dan sai da ya tabbatar sun shirya abin mata da miji kan ya tafi sai wasa da
dariyar su suke, Nura ne ma ya kwaɓa
ɗan wake ya jejjefa
musu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.