𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Idan Mace Tana Cikin Haila, Shin Ya halatta Mijinta Yayi Amfani Da Condom Yasadu Da Ita?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗
To ɗan’uwa bai halatta ka sadu da mai haila ba ko da kuwa ka sanya Condum. saboda Allah Ya haramta saduwa da mai haila, kuma ya kira jinin haila a aya ta 222 a suratul Bakara da kazanta:
وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ ۖ قُلْ هُوَ أَذًى فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي الْمَحِيضِ ۖ وَلَا تَقْرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطْهُرْنَ ۖ فَإِذَا تَطَهَّرْنَ فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللَّهُ ۚ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ الْمُتَطَهِّرِينَ ٢٢٢
Kuma suna tambayar ka game da haila Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakewa. (Suratul Bakara: 222)
Ba namiji ne kaɗai haila take iya cutarwa ba, idan ana saduwa da mace mai haila mahaifarta za ta takure sai jini ya barke mata, wannan sai yake nuna cewa: ba za a sadu da mace mai haila ba ko da an sa Condum .
Imamu Suyidi rahimahullah ya ce: ( Babu ban-banci tsakanin saduwa da condom da saduwa batareda condom ba) Ish-tibah wannaza-ir ( 458).
Malamai sun Nassanta haramcin saduwa damai haila koda da condom ne.
Yazo acikin Tuhfatul- Muhtaaj ( 1/390)
Haramunne saduwa damai haila koda da condom ne. Babu saɓani tsakanin malamai wajan nassohinsu a kan haramcin saduwa damai haila koda da condom ne.
Bai halatta saduwa da mai haila ba, da condom ne ko bada shiba, wajibine a kan duk wanda ya aikata hakan yatuba yanemi gafarar Allah, da kulla niyyar ba zai sake aikata hakan ba, bai halatta ga mace ta amsawa mijinta idan yanemi hakan agareta, Idan yaci gaba daneman saduwa da ita tana haila tana da hakkin tanemi saki awajan Alkali, Babu biyayya ga abun halitta wajan saɓon mahalicci.
Dan haka dai babu ban-banci wajan saduwa da mai haila da condom kobada condom ba wajan haramci, haka haramunne mace ta amsawa mijinta a kan wannan, Allah yatsaremu dakoyi da yahudawa wajan nunawa Allah wayo cikin Abun da ya haramta musu.
WALLAHU A’ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.