Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Saduwa Ta Dubura

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam.. Dafatan kana lpia tare da iyalai baki daya. Allah ya saka da alheri a kan gudummuwar da kake bamu akoda yaushe. Allah ya saka da alheri yasa Aljanna ce tukuici ameen. Malam wata Qawata ce jiya da dare ta kirani wai dan Allah in taimaka mata tana cikin mawuyacin hali. Wai shekararta 4 da aure yanzu Amman mijinta yana saduwa da ita ta dubura dan ta gaya man ko ranar daren farko ma wlh ta nan ya sadu da ita. Tai masa magana meye dalili ya ce haka nan. Toh yanzu har ta kaiga tana zudda ruwa ta wajen. Wai idan zaiyi ta nan gabanta yakanyi lapia lau Amman idan ta dubura ne sai yasa condom.

Kuma wai ko tana jinin al'ada yana saduwa da ita. Ta barsa ne saboda San da take masa. Wai ya zatayi na bata shawara. Wallahi na rasa mezan ce mata. Malam dan Allah kaiman voice note sai na aika mata dan suji tsoran Allah tun kamin dare yai masu. Wassalam

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Da farko dai ki gaya mata cewa ba'a saɓa ma Allah don neman yarda ko soyayyar miji. Domin Manzon Allah  ya ce "BABU BIYAYYA GA WANI ABIN HALITTA CIKIN SAƁAWA MAHALICCI".

Saduwa ta dubura haramun ne. Kuma Qazanta ce wacce ko dabbobi basu yinta. Allah Maɗaukakin Sarki ya gaya wa muminai game da saduwa da iyali, ya ce :

 فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللَّهُ ۚ

  "KUZO MUSU TA WAJEN DA ALLAH YA UMURCEKU (WATO TA FARJINSU)". (Suratul Bakara: 222)

Manzon Allah   ya fadi haramcin yin wannan aikin kuma ya ce Allah ya tsine wa masu yinsa.

Hadisi daga Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (R.A) ya ce Manzon Allah   ya ce "ALLAH BA ZAI YI DUBA BA, (WATO KALLON RAHAMA) GA MUTUMIN DA YA SADU DA NAMIJI, KO KUMA MACE TA DUBURARTA".

Tirmidhiy da Nisa'iy da Ibnu Hibban ne suka ruwaitoshi.

 

Acikin wani hadisin kuma daga Sayyiduna Abdullahi bn Amru (rta) Manzon Allah  ya ce "QARAMIN LUWAƊI NE - WATO NAMIJI YAZO WA MATARSA TA DUBURARTA".

Imamu Ahmad da Bazzar ne suka ruwaitoshi.

Imam Tabaraniy kuma ya ruwaito wani hadisin ta hanyar Sayyiduna Uqbatu bn Aamir (rta) ya ce Manzon Allah  ya ce "ALLAH YA TSINE WA MASU ZUWA MA MATAYE TA DUBURARSU".

Imam Abu Dawud ma ya ruwaito wani hadisin ta hanyar Sayyiduna Abu Hurairah ya ce Manzon Allah  ya ce "ALLAH YA TSINE WA MUTUMIN DA YA SADU DA MATARSA TA DUBURARTA".

To kinga koda anan aka tsaya duk wani mai imani dole ne ya tsorata ya guji aikata wannan Qazantar domin tsinuwar Allah ba abar wasa bace. (Allah shi kiyayemu).

To bayan haka kuma akwai hadisan dake nuna cewa duk wanda ke aikata wannan mummunan aikin to lallai ya riga ya kafirta (Allah shi kiyayemu).

Daga Abu Hurairah ((R.A) daga Manzon Allah   ya ce "WANDA YAKE ZUWA WA MATA TA DUBURARSU TO YA RIGA YA KAFIRTA".

(Imam Tabaraniy ne ya ruwaitoshi acikin Mu'ujamul Ausat).

To ki gaya mata taji tsoron Allah ta dena biye wa mijinta suna saɓa ma Allah. Domin hakika itama tsinuwar nan zata afka mata mutukar dai bata hanu daga yin hakan ba. Tayi masa wa'azi ta gaya masa cewa Allah ya haramta. Idan ya hanu shikenan idan kuma bai hanu ba, to gara ta nemi manya su shigo cikin al'amarin.

Shigowar tasu yana da muhimmanci tunda gashi kin fara kamuwa da chuta ta dalilin hakan. 

Kuma kada ta sake barinsa ya sadu da ita yayin da take cikin jinin haila. Shima Allah yayi tsinuwa ga masu yin haka. Kuma akwai yiwuwar kamuwa da miyagun chutuka ga duk ma'auratan dake yin haka.

Allah yasa su gane, su tuba, su koma ga Allah  kafin fushinsa ya abka masu.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments