𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam, don Allah zan iya ɗaukar Alqur'ani izifi sittin a halin ina
cikin rashin tsarki kuma ga shi za ni Islamiyya muna yin hadda ne. Kuma malam
wata rana malaminmu ya kan ce ka miqo mai Alqurani kuma ba ka da tsarki ya za
ka yi saboda wasu sun ce wai ba a son wanda ba muharraminka ba ya san ba ka da
tsarki, don Allah a taimaka mana Allah ya qara basira ya kuma shirya mu a bisa
tafarkin addini.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salam, ya halasta mai haila ɗalibar Alqur'ani ko malamar Alqur'ani su
taɓa shi a lokacin da suke
kan darasi ko suke hanyar zuwa ɗauko
darasi gwargwadon buqatarsu ko don wata maslaha, ko da kuwa izu sittin ne.
Haka nan duk hadasin da malamai suka ce yana hana ɗaukar Alqur'ani saboda shi, to ana ɗaga wa ɗalibai da malaman Alqur'ani qafa musamman
a lokacin da buqatar darasinsu ta taso masu, ko wata maslaha da ta tilasta masu
taɓawar musamman a fahimtar
Mazhabarmu ta Malikiyya.
Duba Assharhul Kabeer ko Háshiyatud Dasuqiy
(1/125, 126).
Amma idan ba ɗaliba mai koyon karatu ba ne, kuma ba
malama mai koyar da karatun ba ne, to bai halasta su taɓa Alqur'ani a halin janaba ko haila ba a
fahimtar mafi yawan malamai.
Allah S.W.T ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/EbkKRXdFzNu4F8aQZbZ1Vx
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.