Ticker

6/recent/ticker-posts

Ban Taɓa Gamsuwa Da Mijina Gaba Da Gaba Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Aslm Alaikum, Malam Ina cikin Matsala Dan Allah Meye Mafita, yanzu Inada shekara 4 da Aure Yayana 2 Amma Mijina Bai Taɓa Gamsar Dani  ba Ta Gaba da Gaba Sai yayi Wasa Dani da Hannu yasa Hannu a Yan tsakana sannan nakawo, Kuma Yanzu Malam Wlh banason ya ce zai kusance, da yazo min da Buqatar Hakan Sai Narinqa Jin Qunci sosai da ɓacin rai. Wallahi Malam Ina Jin Bazan iya Rayuwar Aure da shi ba, Gashi Kuma Har mun Haihu biyu. Wallahi banason ya ce Zai kusanceni, Nidai Malam Inaji kamar A raba auren.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Tabbasss akwai kunci da damuwa wajen rashin gamsar da mace a shimfida, kuma ba shakka yaana sanya mace tsanar mijinta da yi masa komai akan larura ba dan rai yanaso ba.

Toh amma akwai abubuwa 2 da yakama ki sani ita halittar mata kala kala ne, wata mace sam in za a kwana ana saduwa da ita bazata taɓa kawowa ba amma ana mata wasa da dan tsakanta zata kawo, su irin wanan mata saduwa bata gamsar dasu sai idan mijinsu Yana da qaton gaba wanda ya haɗa kauri da tsayo toh shine idan yana saduwa dasu gabansa zai dinga gogar ɗan tsakansu sai yasa su gamsu, amma idan aka samu akasi bashi da qaton gaba mai kauri da tsaho toh dole sai dai adinga yi mata wasaani sosai tare da wasa da ɗan tsakanta ta hakanne zata gamsu, toh mutuqar dai mijinta zai  iya yi mata duk wata hanya da zata gamsu toh anan baza'aga lefinsa ba domin iya abin da zai iya kenan a tsarin halittarsa .

Sabida haka kenan indai har mijiinki yana iya gamsar dake ta hanyar wasanni toh tabbasss ya fita haqqinki , kece zakiyi haquri da yadda Allah ya halicceki da kuma yadda  Allah ya halicci shi domin indai na fahimta dai dai toh mijinki bashi da lefi kuma kema baki da lepi sai dai kowa ya iya bakin qoqarinsa yadda wani bazai shiga haqqin wani ba.

Shi mijinki ya zama wajibi akansa yabi hanyoyin da zai gamsar dake ta hanyar wasanni kafin saduwa, ke kuma kidinga bashi haɗin kai duk sanda ya buqaceki tare da sanar da shi yadda zai gamsar dake kafin saduwa tunda ke ta hanyar wasa kike gamsuwa.

Aqarshe inna mai baki haquri da ki kwantar da hankalinki ki zauna da mijinki ku fahimci juna domin Wallahi idan dalilin Rashin gamsuwa ne zaki rabu da aurenki toh zakiyi dana sani , wato yanzu akasarin maza maganar gaskiya basu da  qarfin da suke iya gamsar da matansu , wasu sanyi da basur ya cinyesu, wasu kuma rashin isasshen hutu da nutsuwa yasa basa ma sha'awa balle  su gamsar da mace, wasu kuma halittarsu ce haka, wasu kuma sakaci ne da rashin gyara ke kashesu, wasu rashin saduwa da matansu akai akai shike mai dasu ragoye, sai dai fatan Allah ya rufa mana asiri amma na tabbatar miki idan kinji matsalar wasu ma'aura sai kinji ke yar Aljanna ce akansu. Sai fa ka tarar da wacce mijinta yana wata ɗaya bai kulata ba, wasu shakara 2, har shekara 3 zuwa 5.

Lallai dai inna shawartar yan'uwana maza ku kula da kanku da lafiyarku, akula da haqqin da Allah ya dora muku , kuma ku nemi magani dan gyaran aurenku domin Wallahi wanann zamanin ya wuce duk taninin wani mai tunani, ni dai a dan qaramin fahimtata da sauraren kuken ma'aurata nasan ko shakka babu wannan matsalar ta jefa mata da yawa halaka wanda kuma ko shakka babu tabbasss akwai laifin mazajensu domin suna da hannu wajen jefasu halin da suka tsinci kansu ciki, sai dai fatan Allah ya tsaremana imaninmu baki ɗaya....

Allah ta'ala yasa mudace.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments