Ticker

6/recent/ticker-posts

Period Dina Ya Koma Kwanaki 4 Daga Kwanaki 7 Da Na Saba Yi

TAMBAYA (04)

Assalamu Alaikum Warahmatullah dan Allah mlm inada tambaya mace ce ta saba period din ta 7days amma yanzu 3mnths kenan yadawo 4days kuma yawan zubarsa ma ya ragu to dama hakan na iya faruwa ko kuma wata matsala ce take haifar da hakan ina maka fatan alkhairi🙏

AMSA:

Waalaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhum.

Shaikh Muhammad Saleh al-Uthaymeen (Rahimahullah) yayi bayani a cikin littafinsa mai suna "Hukunce-hukuncen jinin mata" a Chapter 3 page 15 babin "Sauye sauyen jinin haila", inda ya ce:

Abubuwan da suke sauya zuwan jinin hailar mace sune kamar haka: na farko shine karuwar jinin ko kuma raguwarsa. Misali: Jinin hailar da yake zuba tsawon kwanaki 6 ya qaru da kwana 1 (yazama 7) ko kuma jinin da yake zuba tsawon kwanaki 7 sai kuma ya tsaya a kwana na 6.

Na biyu: Ci gaba da zuwa ko kuma jinkirin zuwa. Misali: Macen da take jinin haila a kowanne karshe wata sai ta ga ya zo mata a farkon wata ko kuma akasin haka.

An samu sabanin malamai akan hukuncin hakan. Amman zance mafi inganci shine idan taga jinin to zata fara irga jinin hailarta ne, duk sanda kuma ya tsaya to tana cikin halin tsarki kenan ko da kuwan an samu ci gaban zuwansa, tsaikonsa, kari ko kuma ragi a kwanakin hailar. Dalili kuwa anan shine: hukuncin jinin haila (kamar yanda akayi bayani a baya) ya ta'allaqane akan ainihin jinin hailar.

Na uku kuma: Fitar yellow din ruwa (Ko kuma Kudrah) mai launin yelo yelo da baki baki. Idan kikaga wannan kalar na fita daga gabanki a lokacin da kike jinin haila ko kuma kafin kiyi tsarkin haila to za a daukeshine a matsayin jinin haila. Amman idan sai bayan kinyi tsarkine kika ganshi to ba jinin haila baneba kamar yanda aka rawaito cewar Umm 'Atiyya (RAA) tace: "Bama daukan yellow din ruwa wanda ke fita bayan tsarki a matsayin wani abu muhimmi" (Abu Dawud ya rawaito shi da isnadi mai kyau)

Haka kuma Bukhari ya rawaito shi daga Nana Aisha (RAA) da karin: "...bama daukansa a matsayin haila" (Sahihul Bukhari Volume 1 Page 194 #324)

Sannan kuma kamar yanda al-Uthaymeen (Rahimahullah) yayi bayanin cewar mace tana iya yin jini kasa da sati 1 ko sama da haka (la'akarida kowa da irin yanda Allah ya tsara masa adadin kwanakin jinin) to kema haka zaki ci gaba da ibadarki yayinda kika kasance cikin tsarki. Ana iya samun tsaiko ko kuma karin zuwan jinin haila silar shan kwayoyin magungunan hana daukan juna biyu (family planning) wanda suke iya birkita adadin kwanakin da mace ta saba yi

Haka kuma ana iya samun sauyin kwanakin silar shan maganin tsayar da haila irinsu "macrojonon" saboda kwadayin yin azumi 30 a jere don gudun kada a biyo mace bashin ramuwa wanda wannan ba kyau a addinance la'akarida yana cutarda lafiyar mace. Yana saka: matsanancin ciwon ciki, ciwon kai da sauransu. Jinin haila cuta ne kamar yanda Allah SWT ya fada a cikin Suratul Baqara ayata 222:,

 وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ ۖ قُلْ هُوَ أَذًى

Kuma suna tambayar ka game da haila Ka ce: Shi cũta ne.

Kuma yana daya daga cikin jarabawar da Allah ya tsara ga mata (Tun daga lokacin Nana Hauwa'u). Amman a haka wasu (matan kamar masu yin family planning) suke kokarin su dinga tsayarda zuwansa. Suyi haquri su bautawa Allah SWT domin kuwa albishirinsu: A Aljannah fa babu jinin haila kuma babu ma duk wata kazanta. Birkita zuwansa yana kawo matsaloli dayawa, domin karin bayani a likitance sai a garzaya zuwa wajen kwararren doctor.

Wallahu ta'ala a'alam

Subhanakallahumma, wabi hamdika, ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka, wa'atubi ilayk

Amsawa:

Usman Danliti Mato, Usmannoor_Assalafy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

WHATSAPP👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

https:///

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments