Ticker

6/recent/ticker-posts

Ya Ƙaurace Mata…Kuma Sai Ta Ji Zai Yi Aure!

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam, wai menene matsayin mijin da ya ƙaurace wa matarsa tsawon watanni biyar saboda sun samu saɓani? Bayan sun shirya kuma bai dawo gare ta ba, sai daga baya kawai ta ji wai zai yi aure! Wai matar za ta iya neman mijin ya sake ta? Ba ta yi laifi ba ga haka?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ba ki faɗi menene saɓanin ba balle a san ko ƙauracewar tana kan ƙaida ko kuwa aa.

Amma dai a ƙaida miji ba ya ƙaurace wa shimfiɗar matarsa sama da watanni huɗu. Duk wanda ya yi rantsuwa a kan hakan, watau ya yi: Ilaa’i , to alƙalin musulunci zai dakatar da shi bayan watanni huɗu: Ko dai ya dawo ya ci gaba da saduwa da matarsa ko kuma ya sake ta, kamar yadda Ayar Suratul Baqarah ta nuna.

Maganar neman saki kuwa, kamata ya yi ta yi taka-tsantsan. Kar ya zama zafin kishi ya ɗauke ta ga yin hakan, ta tsaya ta yi nazari mai kyau, kuma ta yi shawara da iyayenta: Su kira taro a zauna a tsakaninsu da manyansa domin a samu mafita. Allaah ya ce:

إِن يُّرِيدَا إِصْلَاحاً يُوَفِّقِ اللهُ بَيْنَهُمَا

Idan dai sulhu suke nema to kuwa Allaah zai sanya dacewa a tsakaninsu.

Sannan kuma a tuna cewa: Me yiwuwa akwai ’ya’ya a tsakaninsu. Wa zai yi mata tarbiyyarsu yadda ya dace in ta fita ta bar su a gidan? Yana da kyau a yi tunani mai zurfi a kan wannan.

Shi dai Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa ya yi:

 أَيُّمَا امْرَأَةٍ سَأَلَتْ زَوْجَهَا طَلاَقًا فِى غَيْرِ مَا بَأْسٍ فَحَرَامٌ عَلَيْهَا رَائِحَةُ الْجَنَّة

Duk matar da ta nemi mijinta ya sake ta ba tare da wani dalili ba, to kuwa ko ƙanshin Aljannah ba za ta ji ba.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments