Ticker

6/recent/ticker-posts

Adalci A Tsakanin Mataye Wajibi Ne!

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahamatullah. An tashi lafiya ya aiki? Dan Allah ina da tambaya, mutum ne ya ajiye mata uku, sai ya je gina dakuna ciki uku, sai ya gyara ma sauran amma ya ki gyara ma uwargidan, mene hukuncinsa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu wa rahmatullah. Lallai wannan ko shakka babu zalunci ne, ya kamata kamar yadda aka gyara wa kowa ɗakinta ita ma uwar gida a gyara mata nata dai-dai da dai-dai, rashin yin hakan zai iya sa a kira wannan miji da azzalumi a harkar jagorancin gidansa, daga cikin sharaɗin yin mata fiye da ɗaya, mutum ya tabbatar zai yi adalci a tsakanin matayensa, idan mutum yana tsoron ba zai iya yin adalci a tsakanin matansa ba, an ce ya tsaya a auren mata ɗaya kacal, kamar yadda aya ta uku (3) cikin suratun Nisá'i tabayyana:

... فَانْكِحُوا مَا طَابَ لَكُمْ مِنَ النِّسَاءِ مَثْنَىٰ وَثُلَاثَ وَرُبَاعَ ۖ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُوا فَوَاحِدَةً أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ ۚ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَلَّا تَعُولُوا

Ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa´an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba. (Suratun-Nisa'i 3)

Sannan kuma a wani wurin Allah maɗaukakin sarki ya ce:

وَلَا تَحْسَبَنَّ اللَّهَ غَافِلًا عَمَّا يَعْمَلُ الظَّالِمُونَ ۚ إِنَّمَا يُؤَخِّرُهُمْ لِيَوْمٍ تَشْخَصُ فِيهِ الْأَبْصَارُ

"Kuma kada ka yi zaton Allah Mai shagalã ne daga abin da azzalumai suke aikatãwã. Abin sani kawai, Yanã jinkirta musu ne zuwa ga wani wuni, wanda idãnuwa suke fita turu-turu a cikinsa." (Suratu Ibrahim 42).

Manzon Allah a wani hadisi cewa ya yi: "DUK WANDA YAKE DA MATA BIYU, SAI YA KARKATA WAJEN GUDA ƊAYA, ZAI ZO A RANAR ALQIYAMA SASHEN JIKINSA A SHANYE".

Abu Dáwud ya ruwaito a hadisi mai lamba 2133.

Don haka mazaje masu yin irin wannan zalunci ga matayensu ana ji masu tsoron faɗawa cikin irin wannan mummunan hali, saboda Allah ba ya zalunci, kuma ya haramta a yi zalunci, don haka mu ji tsoron Allah mu yi adalci a tsakanin iyalanmu. Allah ya shiryar da mu hanya madaidaiciya.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments