Ticker

6/recent/ticker-posts

Bai Yarda Ta Sayi Ko Maggi Ba A Gidansa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam, tambayata ita ce: Ina aikin gwamnati ne sai mijina ya ce bai yarda ko ‘maggi’ in saya a gidansa ba. In na saya kuma to, Allaah ya isa! Alhali kuwa ba ya bayar da kuɗin da zai isa. To, idan na saya na yi laifi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Akwai sarƙaƙiya a cikin wannan tambayar:

Abu ne sananne cewa, mace ba ta da ikon fita daga gidan mijinta zuwa aikin Gwamnati ko na wata Hukuma sai da izini kuma da yardar mijinta. To, ta yaya kuma zai ce bai yarda ya yi amfani da wani abu komai ƙanƙantansa da ta kawo a cikin gidansa ba?!

 

Sannan kuma ya ce wai: Bai yarda ta sayi wani abu ta ƙara a cikin abincin gidansa ba, alhali kuma shi bai bayar da abin da zai isa ba, wannan kuma wace irin doka ce haka?! Lallai kam akwai kwantanciyar matsala a ɓoye a nan.

Amma ko menene dai, abin da ya fi a irin wannan halin sai kawai a nemi zama da waɗanda suka ɗaura auren da farko, domin a tattauna matsalar a cikin ruwan-sanyi da fahimta tare da manufar yin sulhu a tsakaninsu. Wannan shi ne ya fi, in Shã Allãh.

Allaah ya ce:

وَإِنْ خِفْتُمْ شِقَاقَ بَيْنِهِمَا فَابْعَثُوا حَكَمًا مِنْ أَهْلِهِ وَحَكَمًا مِنْ أَهْلِهَا إِنْ يُرِيدَا إِصْلَاحًا يُوَفِّقِ اللَّهُ بَيْنَهُمَا إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيمًا خَبِيرًا

Kuma idan kuka ji tsoron aukuwar saɓani a tsakaninsu (ma’aurata) sai ku aika da mai hukunci daga cikin danginta, da mai hukunci daga cikin danginta, idan dai sulhu suke nufi, to Allaah kuwa zai datar a tsakaninsu, haƙiƙa Allaah ya kasance masani ne, mai cikakken ilimi.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments