@Usmannoor_As-salafy
Salamu alaikum. Warahmatullahi. Wabarakatuhum.
Nasha amsar saqonnin tambayoyi akan hukuncin
sana'ar waqe-waqe da kide-kide a addini. Zanso kowanne mai sauraron kade-kade
ya nutsu ya karanta wannan saqon a matsayin amsar tambayoyinsu
Akwai wasiqar da na taba rubutawa wani mawaqi (wanda bazan kama sunansaba) saidai zan iya bayyana saqon da ta kunsa maybe hakan yazamo silar shiriyar dubban mawaqa masu saka kida a cikin waqarsu, fatana duk mai jin kade-kade ya tuba ya daina silar karanta wannan saqon. Ga wasiqar kamar haka;
Innal hamda lillah, nahmadahu wanastainuhu,
wanastaghfirhu, wanauzu billahi min shururi anfusuna, wamin sayyi ati aamalina,
man yahdiyallahu fala mudillana, waman yahdil fala hadiyala, wa ash hadu anla
ilaha illallah, wahdahu la sharikala, wa ash hadu anna muhammadan abduhu
warasulahu, amma baad
Fainna asdakal hadis kitabullah, wa khairi hadi,
hadi Muhammad SAW, washarril umuri muhdisatiha, wakullu muhdasatin bidia,
wakullu muhdasatin dalala, wakullu dalalatan finnar, aazanallahu minannar. Amma
ba'adu
️Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhum
Na rubuto wannan wasiqa ne domin tabbatarda cewar
alaqar dake tsakanina dakai babu karya a ciki domin kuwa duk mai son ka shine
zai fada maka abin da zai fissheka fiddunya wal akhira
Ka kasance mutum mai magoya baya sama da
(...) a instagram page, shawarar da zan
bada anan shine, shin mezai hana ka daina saka kida a waqoqinka domin kuwa
hakanne yake sa yan mata da zawarawa da matan aure suke tiqar rawa a tik-tok
kai kuma kana daukar video dinnasu kana posting, wanda maybe nangaba yayansu ne
zasu ga videos din kuma tabbas sai sun tsinewa mawaqin da ya zama silar rawar
tasu, anan shaidan yayi nasara kam
Burina shine (...) ya ji sautin waqar matan Hurul
Ayn a Aljannah (Alfirdous in particular) to ammanfa hakan bazata yiwuba sai an
koma hadisin ma'aiki SAW wanda ya gargadi al'ummarsa akan sharrin sauraren
kade-kade
Idan har ka goge videos din wanda Shi Allah SWT
mai gafarane, zai iya gafartawa bawansa idan yaso matuqar bai mutu yana shirka
ba. Zaiyi wuya ka daina saka kida a waqenka ni shaidane kaima kasani domin kuwa
ka saba amman idan baka mantaba akwai manyan mawaqan da duniya ta sansu kuma
sun maye gurbin sana'arsu ta industry da neman ilimin addini ka'in da na'in dakuma
yada ilimin ga masu sauraro da ganinsu, kamar irinsu Shaykh Bilal Philips wanda
kafin ya musulunta dacan ya kasance makadin guitar ne a kasar amurka, ga abin
koyi Shaykh Yusuf Estes wanda ya musuluntarda dubunnan Christians wanda dacan
mawaqine a Catholic Church a kasar amurka, celebrities kamar irinsu: Peggy Melati
Sukma, Teuku , Kartika Putri
Hakama mawaqiyar Irish Sinead O'Connor wadda ta
musulunta a shekarar 2018 ta maida sunanta Shuhada Sadaqat, wadda ta rasu a
shekararnan da muke ciki, 2023 (Allah ya jikanta tareda sauran musulmai baki
daya)
Kamar irinsu mawaqi Noor Al-Kautsar, Ucay wanda
suka bar sana'ar a 2013 suka koma yada da'awar musulunci. Irinsu Derry Sulaiman
tsohon makadin jita, a yanzun dukkansu suna amfanida sana'arsu wajen janyo
hankalin mutane su san addinin musulunci
Idan kuma ka koya musu ko da Hadisi daya ne to
tabbas zaka samu ladansu idan suka aikata aikin da yake a cikin Hadisin,
daukakarka anan duniya ga kuma lada mai tarin yawa a lahira. Bazaka iya dainawa
a lokaci daya ba saboda nisa a cikin harkar amman a hankali a hankali zaka ga
komai ya sauya idan ka kyautata niyyarka hade da neman addu'ar iyaye, to
ammanfa akwai qalubale mai tarin yawa idan ka guji masu ra'ayi sabanin naka
wato yan Kannywood. To amman ai Allah zaiji dadin haka hakama malamai masu jan
hankali akan illolin kide kiden dakuma rawar tik-tok din
Zanso ace wannan shawarar kayi amfani da ita
la'akarida gaskiyace nake fada ko da kuwan hakan bazai maka dadiba saboda duk
mai son ka don Allah to kamata yayi ya fada maka abin da zai amfaneka fiddunya
wal akhira. Kuma na tabbatar da idan kayi hakan to daukakar da Allah yabaka
saidai tayi sama ba kasa ba, domin kuwa duk wanda ma baya son ka to silar haka
saikaga Allah ya saka masa son ka. Da zaka dau wannan shawarar kuwa da kaine
zaka fara karya record din haka a tarihin mawaqan hausa baki daya, daukaka bisa
daukaka fiddunya wal akhira. Domin kuwa nidai ban taba jin labarin wani mawaqi
da yabar waqa domin Allah ba saidai zamani ya shudar da shahararsa. Burin
shatan waqa (Allah yajikan rai) shine kada yayansa su fada harkan waqa, haka
sukaita takun saqa da dansa wanda yayi qoqarin shiga harkan, a karshedai Allah
ya qaddara ba wanda zai gajeshi a cikin yayansa
A iya dan bicikena na bincika, a gaba dayan
malaman Ahlus Sunnah babu wanda yake goyon bayan sana'ar kide kide, saidai ma
suna hani ne akan hakan la'akarida illolin da hakan ya haifar ga al'umma kuma
zai haifar ga yayan musulmai masu tasowa
Yanzu dai kaduba kaga wancan quote din wanda na
gani a kofar studio din daya daga cikin yaranka, an rubuta "Only in the
listening of the music does heart find peace" ma'ana "Da sauraron
kidane zuciya take samun nutsuwa" wanda hakan yaci karo da ayata 28 cikin
Suratu Ra'ad wadda Allah ya ce: "Waɗanda suka yi ĩmãni kuma zukãtansu sukan natsu da
ambaton Allah. To, da ambaton Allah zukãta suke natsuwa," to kaga wannan
idan ya rubutane a rashin sani to yakamata ka nusar da shi illar hakan
(...), kai kanka kasandai da yawan ambaton Allah
zuciya take samun nutsuwa to amman meyasa a cikin studio din yasaka "Da
yawan sauraron kida da waqa zuciya take samun nutsuwa" ?
To wannan dalilin ne yasa naje dakaina domin bashi
shawarar ya cire wannan "quote" din, lokacin da naje wajen 10 na
dare, ban tarardashi ba amman hancina shine yayimin maraba da warin wiwi da
wani yaron yaronnaka yake nannadawa (Kuma a goman karshen watan ramadana), nace
masa ina wane-wane ya ce ya tashi saidai wane shima yaje wani waje uzuri yana
tafe, na jira a waje inata tuno wani hadisin da Ma'aiki SAW
Sahihin Hadisin yana cikin Ibn Majah ya ce:
"A karshen zamani (kafin alqiyama ta tsaya) al'ummata zasu dinga shan giya
su kirata da wani sunan, zasu dinga saka kayan kide-kide a kunnuwansu, Allah
zai sanya kasa ta hadiyesu sannan ya maidasu birrai da aladu"
A lokacin sai na tuno da cewar qwaqwalwar mutum ta
rabu kaso hudu (Temporal lobe, parietal lobe, occipital lobe dakuma fore lobe)
shikuma fore lobe dincan shine inda ake tattara ayyukan zunubban mutum sabanin
occipital lobe wajenda ake adana danasani wanda hausawa ma kance danasani
qeyace, shiyasa ma Allah ya gargadi Abu Jahal a cikin Suratul Alaq ayata 15 da
ta 16, sakamakon karyar da yake yiwa addinin musulunci:
"A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba (yin
qarya), lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa (qwaqwalwa)"
"Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi"
Nan take kuma na tuno da binciken da masana
qwaqwalwa sukai na cewar bangaren lymphatic system a fore lobe dake qwaqwalwa
shine yake adana son shaye-shaye kamarsu giya, cocaine, wiwi, ananne kuma ake
adana zunubban zinace-zinace dakuma sautin kide-kide dalilin dayasa ake rawa,
silar zubewar mutuncin kamilallen dan Adam
Sai nace a raina "Sadaqa rasulullah
SAW", tabbas ma'aiki SAW yayi gaskiya. Harkar mata tayi yawa a industry,
shaye-shaye abin burgewa ne a harkar sannan kuma jin kade-kade shine
ummul-aba'isin dake janyo faruwar ragowar laifuffuka
Idan kayi sanarwar cewar ka daina saka kida a
waqenka to tabbas wasu daga cikin yaranka zasu daina kaga kenan tun anan ka
fara samun lada da kuma qima a idon duniyar musulmi. Shin ka tuna abin da (...)
daya daga cikin fans dinka ya fada maka wani lokaci da yazo sabon studio dinka
yana sanye da (...) irinnaka da shiga irin taka ya ce "Gaskiya (...) da
ace yanda muke sauraren waqoqinka haka muke sauraron karatu da tuni munyi
sauka". To kaga wannan fan din naka yanzun a shirye yake ya fara koyon
Hadisan Manzon Allah SAW daga wajenka, kuma ko kasan cewar zata iya yiwuwa nine
na canza masa ra'ayi akan son kide-kide harma ya fada maka hakan ?
Allah SWT ya ce a cikin Suratu Luqman ayata 6:
"Kuma akwai daga cikin mutãne wanda ke sayen tãtsuniyõyi dõmin ya ɓatar da mutãne daga hanyar Allah, bã da
wani ilmi ba, kuma ya riƙe ta abin izgili! Waɗancan sunã da wata azãba mai
wulãkantãwa."
Waqar da kake danasanin fitarta itace
"(...)", kamar yanda ka fada lokinda akai interview dakai wadda har
yanzu nasan kana danasanin fitarta duniya kuma kullum za'ayita saurarenta har
komawarka ga Allah, ko kasan maybe idan ka daina saka kida din a waqoqinka Allah
zai kankare maka zunubbanka ?
Ko kasan shahararriyar jarumar Bollywood, Sana
Khan (wadda sukai film din Jai Ho da Salman Khan, haka kuma sunyi film da
Shahru Khan) ta fito duniya tace daga yau na daina film, an tambayeta dalili
tace mafarki nayi ana ganamin azaba kala-kala a kabarina sakamakon harkar film
da kide-kide da raye-raye da nakeyi. Naga interview dinta a Indian News, tana
kuka tana bayani. Harma Shaikh Dr. Zakir Naik ya ce yayi matuqar farin ciki da
Sana Khan ta tuba ta gano kuskurenta. Wanda Mufti Menk ma yayi reacting akan
lamarin tareda nuna farin cikinsa. To kaga anan Allah ne yakesonta da alkhaeri
da harma aka nuna mata makomarta idan bata tuba ba, a yanzu haka ta auri
shahararren mai kudinnan Mufti Anas, wanda sukaje aikin Hajji tare, alhalin da
Umrah take zuwa tana dawowa ta cire hijabinta ta ci gaba da film amman yanzu da
ta tuba sai gashi har aikin Hajji tayi. Ka duba tarihinta idan ka samu lokaci
Abul-sahba ya ce: na tambayi Ibn Mas'ud ma'anar
waccan ayar ta 6 dake Suratul Luqman saiyace: Lahwal hadis na nufin waka wato
al-ghina (Ibn Jarir 21/62 dakuma Hakim 2/411 da isnadi sahihi)
Ibn Abbas RTA ma ya fassara al-ghina a matsayin
waka da makamantansu
Sa'ad Ibn Yasar ya tambayi Ikhramah ma'anar
lahwal-hadis ya ce waka ake nufi, Al-hussain, Sa'id Ibn Jubayr, Qatadah da
Ibrahim al-Nakh'i duk sun tabbatarda lahwal-hadis na nufin waka
Abdullahi Ibn Umar RTA yaji sautin sarewar
makiyaya, sai ya saka yan yatsunsa a cikin dukkan kunnuwansa, ya karkatar da abin
da yake hawa ya kauce daga kan hanyar. ya ce: Ya Nafi', anajin sautin har yanzu
? ya ce: Na'am. Yacigabada tafiya yana tambaya har saida Nafi' ya ce yanzu
ba'ajin sautin, sannan sai Ibn Umar ya sauke hannayensa ya dawo kan hanya.
Sannan ya ce: Naga Annabi SAW yayi hakan a lokacinda yaji ana busa sarewa (Abu
Dawud 4925 dakuma Bayhaqi 10/222 da isnadin mai kyau)
An rawaito daga Abdurrahman Ibn Auf RTA cewar:
Manzon Allah SAW ya ce: "An haneni da sauraron saututtuka biyu, sautin
sarewa a lokacin farin ciki da kuma sautin kuka yayin afkuwar wani
iftila'i" (Tirmidhi 1005 da kuma Tayalisi 1783 da isnadi ingantacce)
Malamai sukace indai har haka magabata suke taka
tsantsan da idan sukaji sautin kida to ya zasuyi kenan idan suka tsinci kansu a
wannan zamanin namu ?
A qarshe ina son ka qara duba wannan wasiqa sannan
ka tambayi shawarar mutane nagari a cikin makusantanka, sai kayi amfani da abin
da suka ce. Kafinnan kuma zanso ka karanta tafsiran ayoyin da sukai magana akan
"Lahwal hadis" da "Al-lagwu", sannan ka duba littafin Ibn
Al-Qayyim mai suna "The Evils of Music: Devil's Voice and Instrument"
da kuma wani littafi mai suna "Music Made Me Do It" wallafar Dr.
Gohar Mustaq da kuma littafin "Talbis iblis" wallafar Ibn al-Qayyim
Wannan wasiqar na rubuta ta ne da kyakkyawar
niyyar kawo gyara a rayuwarka kuma ba ina nufin na fika tsoron Allah bane,
maybe ma ka fini kusanci da Allah ta wani bangaren, wallahu aalam, kawaidai
nayi amfanida abin da yake na zahiri ne don kawarda bidi'a a matsayin dan
uwanka musulmi. Musamman la'akari da yanda yayanka suke tasowa da ilimin
addini, kuma gashi (...) tana miming waqarka ana dorawa a media platforms, kuma
sauraren waqa baya haduwa da karatun Qur'ani kamar yanda Ibn Al-Qayyim da
magabata suka fada, gwara ayiwa tufkar hanci tunda ice tun yana danye akan iya
tankwarashi. Allah ya yafe maka, nima ka tayani da addu'a Allah ya yafemin
zunubbaina. Zanso ka sauka daga layinnan mara bullewa, ka maida hankali wajen
business dinka. Roqona Allah yasa da ni dakai da sauran musulmai mu saurari
waqe da kidan Hurul Ayn a Aljannatil Firdous
Wabi hazal qadri kifaya. Subhanakallahumma, wabi
hamdika, ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka, wa'atubi ilayk
SHARHI: Kamar yanda na fada da farko ba saina kama
sunan shahararren mawaqin ba to amman musabbabin da yasa na fitarda bayanan
yanada alaqa da zamanin da muke ciki wato zamanin social media wanda Allah ne
kadai yasan adadin mutanen da zasu karanta wannan wasiqa inmadai mawaqan ko
kuma masu sauraren kade-kaden, burina hakan yazama silar kawo sauyi ga rayuwar
wadanda shaidan ya qawata musu sauraren kida. Mutum ya karya rodi da haqoransa shine
yafi sauqi akan son zuciyarsa. Ya Allah ka rabamu da son zuciya. Amsar
tambayarki shine: Tabbas kida yana kawo munafunci a mu'amalance, kuma yana kawo
cututtukan qwaqwalwa a kimiyyance sannan yana kawo raguwar imani a addinance,
maganin hakan shine sauraron karatun al-Qur'ani mai girma. Allah ya bamu ikon
gyarawa
Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.