Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Da Ta Yiwa Mijinta Sihirin Mallaka

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam Khamis ga tambayata, meye hukuncin matar data yiwa mijinta sihirin mallaka a addinin musulunci.?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Hakika Sihiri Yana Daga Cikin Laifuka Masu Girma, Kuma Yana Ɗaya Daga Cikin Nau'ikan Kafirci, Sannan Yana Daga Cikin Abin da Ake Jarabtan Mutane da shi Tun Shekaru Dubban Daruruwa da Suka Wuce Har Zuwa Wannan Lokacin. Anayinsa Lokacin Jahiliyya Kuma Wannan Al'ummar ma Ba'a Barta a Baya Ba Wajen Aikata Wannan Mugun Aiki. Jahilci Yana Daga Cikin Abin da Ke Sabbaba Yin Sihiri da Kuma Karancin Imani.

Duk matar da tayiwa mijinta sihiri Ta aikata Haramun. Kuma duk abin da ya aikata ba a saninsa ba wanda idan da Ace yana sane ya aikata wannan abin za'ayi masa azaba akai, to ita Allah zai kama da kwatankwacin wannan azabar.

Hakika Sihiri Kafirci ne Mai Yinsa da Wanda Yasa Akayi Dukkansu Sun Kafirta Saboda Nassi Karara da Ubangiji Ya Kafirta Wadanda Sukeyin Wannan Aikin, Inda Yake Cewa:

ﻭَﺍﺗَّﺒَﻌُﻮﺍ ﻣَﺎ ﺗَﺘْﻠُﻮ ﺍﻟﺸَّﻴَﺎﻃِﻴﻦُ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﻠْﻚِ ﺳُﻠَﻴْﻤَﺎﻥَ ﻭَﻣَﺎ ﻛَﻔَﺮَ ﺳُﻠَﻴْﻤَﺎﻥُ ﻭَﻟَﻜِﻦَّ ﺍﻟﺸَّﻴَﺎﻃِﻴﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ﻳُﻌَﻠِّﻤُﻮﻥَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱَ ﺍﻟﺴِّﺤْﺮَ

Sai Sukabi Abin da Shaiɗanu Suka Karanta Game da Mulkin Sulaiman, Sulaiman Be Kafirta ba Sai dai Shaiɗanu ne Suka Kafirta Suna Koyawa Mutane Sihiri”.

Sai Allah Madaukakin sarki Ya Bada Labari Game Kafircinsu Na Koyawa Mutane Sihiri. Duba da Wannan Ayar Zamu Fahimci Kafircin Yin Sihiri Kai tsaye.

Duk Yanda Mai Sihiri Yakai ga Iya Yin Sihiri, Shirinsa Bazai Taɓa Yin Tasiri ba Sai da Izinin Ubangiji. Idan Allah Yaso Ya Jarabci Bawa  Sai Ya Kaddara Sihirin Yayi Tasiri Akansa. Allah Yana Cewa:

ﻭَﻣَﺎ ﻫُﻢْ ﺑِﻀَﺎﺭِّﻳﻦَ ﺑِﻪِ ﻣِﻦْ ﺃَﺣَﺪٍ ﺇِﻻ ﺑِﺈِﺫْﻥِ ﺍﻟﻠَّﻪِ

Kuma Su Bazasu Iya Cutar da Wani da shi (Sihirin) ba Sai da Izinin Allah”.

Hadisi Ya tabbata daga Sayyiduna Imrana bn Husayn (rta) ya ce Manzon Allah ya ce : "BA YA TARE DAMU DUK WANDA YAYI CHAMFI KO AKAYI MASA CHAMFI DOMINSA. KO KUMA YAYI BOKANCI KO AKAYI MASA BOKANCI DOMINSA, KO YAYI SIHIRI KO AKAYI MASA SIHIRIN DOMINSA. WANDA YAJE WAJEN BOKA KUMA YA GASKATASHI CIKIN ABIN DA YAKE FAƊA, TO HAKIKA YA KAFIRCE MA ABIN DA ANNABI MUHAMMADU YAZO DASHI". (Imamul Bazzar ne ya ruwaitoshi).

Mata kuji tsoron Allah, ku fahimci cewa samun mallakar zuciyar miji ta hanyar amfani da layoyi ko kulle-kullen tsafi ba samun yardar Allah bane. Hasali ma hanya ce ta kafirci da gushewar imani. Kuji tsoron Allah ku tsaya bisa abin da yake na halal. Wato addu'a da kuma neman mafita awajen Allah. Tare da Qaurace ma bin miyagun shawarwari irin na bokanci.

Babu wata hanya mallake miji kamar ladabi da biyayya da girmama miji, da kyautata masa, tare da gyaran jiki, da  kiyaye hakkokinsa da suke kanki, da sauransu... In shã Allãhu Zaki mallaki zuciyarsa ba tare da bin waccan hanyar bokayen ba.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RQbbrzgW

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments