Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Saƙon Taya Murnar Happy Birthday

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Menene hukuncin aika wa mutum da saƙon birthday a musulunci?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Bikin tunawa da ranar haihuwa (birthday) ba shi da tushe ko asali a karantarwar sahihin addinin da Annabin Muhammad Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya kawo mana. Domin ba a taɓa jin shi kansa, ko sahabbansa, ko manyan malamai da suka biyo bayansu a cikin zamunnan farko na wannan al’ummar masu cike da alkhairi da albarka ba, ba a ji wani daga cikinsu ya taɓa yin irin wannan bikin don tunawa da ranar haihuwar shi kansa ba, ko kuma na wani wanda ba shi ba, daga cikin iyayensa da malamansa da suka gabace shi.

Babu wani mahaluki da ya fi soyuwa a wurin dukkan musulmin kirki fiye da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Amma kuma sai ga shi malamai sun saɓa wa juna a kan kwanan watan da aka haife shi. Wannan kuwa dalili ne a fili cewa: Ashe shi kansa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) bai faɗi magana guda ɗaya kai-tsaye a kan hakan ba ne. Wannan kuwa dalili ne a kan cewa sanin hakan ko rashin sanin sa ba shi da muhimmanci a cikin addinin da Allaah Ta’aala ya cika masa shi, inda yake cewa:

 ِۚ ٱلۡیَوۡمَ أَكۡمَلۡتُr لَكُمۡ دِینَكُمۡ وَأَتۡمَمۡتُ عَلَیۡكُمۡ نِعۡمَتِی وَرَضِیتُ لَكُمُ ٱلۡإِسۡلَـٰمَ دِینࣰاۚ

A yau na kammala muku addininku, kuma na cika ni’imata a kanku, kuma na yarje muku musulunci shi ne addini. (Surah Al-Maa’idah: 3).

A taƙaice dai, wannan irin bikin na tunawa, ko taya murna saboda kewayowar ranar haihuwa, daga wurin waɗanda ba musulmi ba ne aka samo shi. Wasu ’yan bokon cikinmu ne suka fara kawo shi, da yin amfani da shi a cikinmu, saboda koyi da turawan yamma, waɗanda kuma tun tuni Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya tsoratar da mu daga bin hanyarsu, inda ya ce:

مَنْ تَشَبَّهَ بِقَوْمٍ فَهُوَ مِنْهُمْ

Duk wanda ya kamantu da waɗansu mutane, to shi yana tare da su. (Sahih Al-Jaami’: 6149).

Abin nufi shi ne: Duk wanda ya kamantu da su a cikin addininsu a aqeedarsu da ibadarsu da sauran abubuwan da suka keɓance sun a al’adunsu, kamar na bukukuwansu da tufafinsu da tsarin zamantakewarsu da sauransu. Allaah ya kiyaye.

Daga cikin mummunar ɓarnar da ke ƙunshe a cikin irin wannan bikin akwai mantar da musulmi ko shagaltar da shi irin abin da ya fi muhimmanci gare su, kamar yadda wani malami ke cewa:

(i) Wane bikin farin ciki da murna mutum zai yi alhali ba a gaya masa cewa Allaah Ta’aala ya karɓi ko da ƙwara ɗaya daga cikin ayyukan da ya ɗora masa a tsawon shakarar da ta wuce ba?!

(ii) Kuma ina bikin murna da farin ciki ga mutumin da bai samu wata takardar shaidar cewa Allaah Maɗaukakin Sarki ya gafarta masa ko ƙwara ɗaya daga cikin zunuban da ya tafka a tsawon shekarar da ta wuce ba?!

(iii) Sannan kuma ina bikin murna ga mutumin da bai karɓi takardarsa ta hanun dama ba, bai ga abin da mizaninsa ya ƙunsa ba, bai sha ruwa daga Tafki ba, bai haye gadar siraɗi ba, kuma bai ga kansa a ƙofar Aljannah ba?!!

Don haka dai, aika wa wani da saƙon taya shi murna don wai ya cika shekarar haihuwarsa, wannan bai yi daidai da koyarwar musulunci ba. Hanyar turawa ne da magoya bayansu, waɗanda ba ruwansu da addininmu ko kyawawan al’adunmu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RQbbrzgW

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments